Free chapter · Read without an account
Chapter 2
*DAREN ALKHAIRI*
1
MARYAM LITEE
Karfe shida na safiya agogon bangon dakina ya buga tare da farkawa ta daga barci.
Na tashi zaune da kyar duk da na san na makara sallar asuba a sakamakon raba dare da muka yi da mijina Yusuf muna hira.
Murmushi ya subuce mini maimakon gaggauta tashi in ba da farali sai na ɗora hannuna a haɓata na fara tunano hirar tamu da ta zamanto mai matuƙar daɗi.
Na farko muna sa ran Yusuf zai samu aiki da kamfanin inshora da ya tafi takanas ta Kano tun daga nan Kaduna har Lagos don halartar Interview da suka gayyace shi.
Sai na biyu ya yi mini albishir "My Happiness na samu maganin matsalar mu. Wani mai magani shahararre na yi arangama da shi ya ba ni maganin kara girman gaba da rashin kawowa da wuri.
Take na cika da farin ciki a tsakanin albishir na farko da na biyu sai na rasa wanne ya fi mini daɗi.
Hasken da ke sulalowa ta labulai ya ƙara tunasar da ni ban yi sallah ba.
Na mike har ina haɗawa da gudu na faɗa toilet, sai da na shafe minti bakwai a ciki kafin na fito idona na kan agogo na hau sallayata, na kabbara sallah.
Da idarwa ta istigfari kaɗai na gabatar ban tsaya yin Azkar ba da malamar da Daddyn mu ya daukar mana ta koya mana, na kuma tsaya akan yin sa ban watsar ba.
Na mike ina yaye hijab din da na yi sallar sai na fara gyara gado, sabon bedsheet na ciro fari tas mai dan karen tsada don order din su mom dina ta yo mini daga China.
Da kyar na shimfiɗa don nauyin su.
Lokacin da na kammala ina goge dakin zufa ke ta yanko mini, duk da sanyin safiya saboda rashin sabo.
Na zauna kaɗan ina mayar da numfashi, watanni goma kenan yau da zamantowar mu ma'aurata ni da abin kaunata Yusuf.
Na lumshe ido tuna kalaman sa a jiya, daren yau da zai dawo zai zame mana daren alkairi, saboda samun maganin matsalar mu don a kullum mu'amalar aure ta hada mu sai ya faɗi "Ba na gamsar da ke my Happiness. "
Shiru nake masa saboda kara da kunya ta diya mace.
Na mike na dauko Bunner ta daidai da maido da wutar lantarki, na jona bayan na zuba turaruka masu kamshin gaske, su ɗin ma tun na aurena ne.
Dakin ya gauraye da kamshi na rufe kofar na fita zuwa Kitchen.
Kallo nake ta ƙare ma Kitchen ɗin, duk da ba datti ina sa ran idan Yusuf ya fara aiki zan samo yar aiki da za ta rage mini ayyukan gida.
Wanke-wanke na fara wanda bai wuce tukunya da plate sai cup.
Na goge Kitchen din sai na bude fridge duk da na san ban ajiye komai ba, komai na ciki ya ƙare.
Na bude ɗayan hana rantsuwa akwai ruwa guda daya sai dai drinks ko robarsa babu.
Na ja ajiyar zuciya na wuce Store ina ayyana yadda za a yi in samu kuɗaɗen da zan yi cefane na taryar Yusuf.
Komai ina da shi na kayan abinci, a shekara guda da nake niyyar haɗawa har yau kayan garar da aka kawo mini mota guda suna nan kamar ba a taɓawa.
Na fito daga Store ɗin na koma Kitchen ina ci gaba da tunanin ta inda zan samu kuɗi.
Na koma daki da sauri kamar ana tunkuɗa ni na dauki wayata da na bari bisa side drawer na zauna saman gado sai na bude ta na shiga asusun ajiya ta.
Kamar yadda na riga na sani 2000 ce kadai ita ma ta transport ce.
Na ja ajiyar zuciya sai na latso lambar momy na daga ban da wata mafita idan ba hakan na yi ba.
Bugu daya ta daga tana tambayar "Yaya Zee kira da safe haka? "
Na langabe kai cikin shagwaba na ce "Kudi nake so Mom. "
Ta ja karamin tsaki "Kuɗi dai kudi dai Zainab? "
Na ce "Sorry Mom. "
"Me za ki yi da su? "
Ta jeho mini tambayar.
Na gyara zama "Wani amfani zan yi da su Mom. "
Ta ja wani guntun tsaki "Shi kenan zan sanya miki. "
Na fara ihun yi mata godiya ta katse kiran.
Na mike ina mai addu'ar Allah ya sa ta sanyo mini da kauri, na koma Kitchen sai sannan na tuna ina jin yunwa, da daddare Tea zalla na sha na kwanta.
Dankali na debo a Store, shi ma da na je gida na debo, na zauna na fere na soya shi na hada Tea ba ni da ƙwai sai na zauna a Kitchen din ina karyawa, sako ya shigo wayata da ya sa na yi saurin dubawa.
Kamar yadda na yi zato kuɗaɗe ne Mommy na ta turo, na gintse fuska don ganin kuɗaɗen ba su yi mini yadda na so ba 50k ne, na tsame hannuna daga dankalin na fara lissafin yadda zan yi, su ishe ni.
Zan yi cefane, akalla ina son nama mai ɗan yawa, ina buƙatar Veggies sai kuma gyaran jikina da nake da bukata shi ma.
Na daɗe shiru cikin nazari kafin na kira Mommy na, ban tsaya faɗi mata na ga kudin ba na hau tambayar ta cikin masu aikin ta wa za ta turo mini na aike ta kasuwa?
Cikin kwanciyar hankali ta ce "Kudin sun zo?
Na shafa kaina ina murmushi, " Sun shigo Mommy na. "
Ta ce "Cefane za ki yi maku da su ko? "
Na yi saurin girgiza kai tamkar tana kallo na "A'a Mommy ya turo kudi ne. "
Ta bar zancen na san ba don ta yarda ba, ta ce za ta turo Asabe direban Mommyn zai kawo ta.
Na mike na koma daki na sanya wayar caji na dawo falona ina gyara shi duk da babu dattin komai saboda ni kaɗai ke rayuwa aka fara bugun Gate tamkar za a ragargaza shi.
Takaici ya tokare mini kirji don na tsani irin wannan dukan Get ɗin.
Na zura silifas ɗina ina jan tsaki na fita falon ina mitar, kai ba bugawa ka yi ba, ka ji ba a buɗe ba, da za ka ce ko barci masu gidan suke bari ka tashe su.
Na bude kofar muka yi tozali da Aliya ƙanwar Yusuf.
Budurwa ce da za ta yi shekaru ashirin cif.
"Aliya ke ce ke bugun ƙofa? "
Ta ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa sai ta miko mini wayarta "Yaya ya ce na kawo miki wayarsa za ku yi magana. "
Na miƙa hannu na karɓi wayar ina faɗin "Ikon Allah shi ne sai ya taso ki? "
Daidai wayar ta ɗauki ƙara na kara a kunne ina jin Aliya tana ƙunƙunai.
"My Happiness. "
Shi ya fara furtawa cikin wata irin murya "Me ya same ki me ya samu wayarki?"
Ya watso mini tambayoyin.
Na saki murmushi "" Na tashi lafiya. Wayata kuma a kunne take sai dai Network. "
Na ji ya ja ajiyar zuciya "Na kasa aiwatar da komai ina jin kamar wani abu ne ya same ki ba ki kira ni ba, na kira ki kuma ba ta shiga. "
Na kara sakin lallausan murmushi ina girgiza kai "My Yusuf. Shi ya sa ka taso wa ma Mama 'ya? Kai da Mama. "
Na ji sautin murmushinsa, muka ci gaba da hira anan don na yi ma Aliya tayin shigowa ta girgiza kai ta ce in gama in ba ta wayar.
Mun ɗauki ya kai minti talatin a wayar, Aliya ta cika kamar ta fashe sai tsaki take ja a hankali.
Lokacin da muka kammala na miƙa mata wayarta na ce ta gaishe da Mama.
Ba ta ko amsa ba ta karbi wayarta ta kama hanya.
****
Wani irin sauri take zubawa tamkar wadda za ta tashi sama.
Ta kosa ta gan ta gaban Mamansu ta faɗa mata wulakancin da matar yaya Yusif ta yi mata.
Akwai yar tafiya a tsakanin gidajen nasu, Yusuf ya kama haya a Sabon kawo, gidan iyayensa kuma yana a Kawon.
Tana shiga gida ta fashe da kuka, uwar da ke Kitchen tana dama koko ta fito tana tambayar lafiya wani abu ya samu matar Yusuf ɗin?
Ta share hawaye "Don Allah Mama ki yi wa yaya magana ya bar aike na wurin matarsa. Duk tafiyar nan da na sha ko gidan ba ta bari na shiga ba, daga waje ta shanya ni ina tsaye suka ɗauki awa daya suna waya. "
Maman da ta cika fam ta fara amayar da ruwan masifa ta ce kanen Yusuf din Habu ya miko mata wayarta.
Har aka ba ta fada take, ba ta ko amsa gaisuwar Yusuf ba da sallamar da ya yi mata.
"Na fara gajiya da wannan mata taka Yusuf. Tun da ka auro ta me aka ƙaru da shi? Sai karyar ɗiyar masu kuɗi, kai kanka ba abin da suka tsinana maka, Kana yawo a gari sun kasa samar maka aiki. "
Yusuf da ya rasa abin da Zainab ta yi ya yi ta ba mahaifiyar tasa haƙuri, ƙarshe da ya samu ta yi shiru ya tambayi laifin da Zainab ta yi, cikin sabon fushi ta kora masa wulakancin da matar tasa ta yi wa Aliya. Ya kara ba da haƙuri ta katse kiran tana ci gaba da faɗan, Aliya ta matso tana kara zuga ta.
Don ita dai ta tsani matar ɗan'uwan nata ne tun da ta ga ba fuskar da za ta je gidan ta yi yadda take so kamar yadda ta fara a farkon auren, ta kwashi kawayenta su je gidan ta shige Kitchen kai tsaye tana kwaso duk abin da ta gani a ciki, har da kiran kawayen su shigo su yi girki.
Zainab ta dawo daga part din makociyarta da ta tafi ta bar su a falon ta samu yara a Kitchen.
Ta daure fuskarta ta ce su fito.
Da ta sake dawowa bayan kwana biyu da wasu kawayen Zainab ta daure fuska, shi kenan sai ta sa mata karan tsana.
*****"*
Na ci gaba da gyaran gida cikin ga dajiya saboda har yanzu na kasa sabo da aikin da ba yi nake a gidanmu ba, ina yi ne kawai saboda soyayyar mijina Yusuf.
Ƙwanƙwasa gidan aka ƙara yi na fita na buɗe.
Asabe ce daya daga cikin masu aikin Mommyna, da gani na ta ɗan rusuna cikin fara'a ta fara gaishe ni.
Na juya ina amsawa na ce "Shigo mu je Asabe. "
Ta ce "To Aunty. "
Ta biyo ni zuwa ciki, ta zauna a falo na wuce Bedroom na dauko ATM dina na dawo na miƙa mata ina mata lissafin abin da za ta sawo mini.
So samu na sayi nama na duka 50k din don na daɗe ban nema ba amma matsalolin nawa da yawa, har 10k nake so na rage na transport saboda zuwa makaranta.
Naman 15k kawai na ce ta saya mini sai Veggies na 10k sai drinks da ruwan roba na 10k
Ta gama saurare na ta yi mini sallama ta fita.
Na zauna ina tunanin yadda zan kasafta 15k da ta rage mini a transport da gyaran da za ni Sallon.
Sai na yanke kawai in yi gyaran gashi a wanke mini ƙafa saboda ƙarancin kuɗin.
Har na yi wanka na zauna jiran Asabe ta kawo mini sakon, Yusuf ya kira ni, ya shaida mini suna hanya sun yo nisa. Sai ƙara faɗa mini daren yau daren alkairi ne a gare mu saboda abin da zai gudana cikin sa.
Gabaɗaya ya kashe mini jiki ya saka ni nishaɗi, muna ta wayar har Asabe ta dawo ta kawo mini sakon na bi su suka sauke ni a Sallon.
Ana mini gyaran gashin ma waya muke da Yusuf san da aka kammala mini lokaci ya ja don haka a gagguce na fita daga Sallon din na samu keke napep zuwa gida.
Sallah kaɗai na gabatar na faɗa Kitchen ko yunwar cikina ba na ji saboda buri na na yi duk yadda zan yi na faranta ran Hubbyna.
Ina yanka albasa wayata ta yi ƙara, kamar na yi banza da ita sai kuma na juya inda take na ɗauka.
Ganin sunan Daddy na ya sa na riƙe numfashina sai kuma na ɗaga kiran, rashin sakin fuskarsa gare ni tun bayan aurena da tirka-tirkar da aka tafka da ni kan auren Yusuf nake ɗari-ɗari da shi.
Na gaishe shi a sanyaye, cikin dakakkiyar muryarsa ya tambaye ni me ya hana ni zuwa Sch?
Gabana ya buga na ja numfashi sai na ce "Ba ni da Lactures.
" Karya kike Zainab!
Ya faɗa cikin daka tsawa sai na ji hawaye sun goce mini.
Daddyna da tsananin son da yake ma momnyna ya shafe ni, don ita ce first Love din sa, mahaifinta ya hana shi aurenta, har sai da ya yi aure da yar'uwarsa ɗiya ga yayar mahaifinsa, har sai da suka haihu uku, lokacin ita kuma ta kammala karatun digiri dinta ya dawo neman ta a wannan karon mahaifinta ya ba shi.
Kowa ya san irin son da yake mata, sai ya zamanto kuma ni kaɗai ta haifa masa, kuma yana faɗin ni ɗin kama ta ɗaya da matarsa momnyna kenan.
Ban san yawan rigimar da Daddy na suka yi da momnyn su Aysha ba, Uwargidan sa saboda ni.
Sai dai zaben Yusuf da na yi na ƙi ɗan yayansa ya raba wannan soyayyar.
Na share hawayena da bayan hannuna ina jin yana fada mini darasin da muke da shi yau da lokacin da muka shiga.
Shiru na yi ina kara gasgata zargina kan yaron maigadin mu da Daddy ya biya ma makaranta muke karatu tare yana masa CID dina ne.
Tunani na ya dawo yana faɗin "Ki mayar da hankali kan karatun ki Zainab, ba zan lamunci wasa da karatu ba, kin sani kuma yana daga cikin dokokin da na sanya kafin na amince ki aure shi."
Jikina gabaɗaya rawa yake na ce "Ka yi haƙuri Daddy. "
Ya kashe wayarsa na ajiye ta a inda na ɗauko na ci gaba da zubar da hawaye na tuna ƙaunar da ke tsakani na da Daddy na amma yau sanadin zaben Yusuf komai ya tafi ya zama tarihi tamkar ba a taɓa yi ba.
Na gama kukana na ci gaba da aikina muna waya da Yusuf da ya dage bayanin daren yau da ya yi wa laƙabi da daren alkhairi.
Na kammala girkina wanda shi ma saboda ƙauna ta da Yusuf na tsaya na koya don yar'uwa ta da muke Baba daya Aysha take yi mini dariya za a auri talaka dole a koyi girki daga ba kudin dauko Hause help.
Da na gama faɗa da ita sai momnyna ta dube ni cikin daure fuska tana harara ta "Da me kike tunani har kike fada da Sister ɗin ki don ta fada miki gaskiya?
Ta ja mummunan tsaki ta bar mini falon ina huci ni kaɗai.
Sai kuma da na nutsu a makwanci na na gane gaskiyar kenan dole na shiga Kitchen a gidan Yusuf.
Mafari na nemo wata CHEF ta koyar da ni girke-girke.
Sai da na yi sallah wanka shi ne abu na karshe da na yi wanda na ɓata lokaci ina ƙalƙale jikina na fito na hau Mirror don yin kwalliya gyaran gashin da aka yi mini ya yi matuƙar kyau ya fito da fuskata, ina mulke tattausar fatata da mayuka na ina jan tsaki, don duk suna hanyar ƙarewa, aikin Yusuf da yake samun dubu Saba'in a wata ta ina zai fara sayen mayuka da turarena, na dubi jikina ina tuna kalaman family na akan aurena da Yusuf.
"Ki dube ki ki dubi surar da aka yi miki ina ke ina auren talaka ta ina zai fara da daukar responsibility naki?
Na girgiza kai ina kallon jikina yar duma-duma ce ni fara tas, kirjina ko da yake a cike albarkatun krjin ba su zube ba. Ga diri da nake da shi mai daukar hankali.
Face dina yar kewayayya duk da ba ni da dogon hanci da manyan ido ina da kyau da mutane ke yawan kallona da fadin ina da kyau ina burge su.
Gashin kaina ba wani mai mugun tsawo ba ne iyakar sa kafaɗa sai na ci sa'a yana da cika ga shi aka yi sa'a ban wasa wurin kula da shi.
Na gama kwalliya ta dakin ya karaɗe da kamshi na turarukan da na yi amfani da su.
Na buɗe ma'ajiyar kayana na dauko wata shadda dinkin doguwar riga momnyna da ta yi ma Daddy rakiya ƙasar China ta kawo mini ita.
Yau ce rana ta farko da zan fara sanya ta.
Ta zauna das a jikina tamkar an gwada ni, komai nawa ya fito ma sha Allah, na yi ta juyi gaban Mirror ina tunanin yadda Yusuf zai shiga cikin kiɗima idan ya yi tozali da ni, da kullum ba ya gajiya da faɗin kyawun surata.
Na fita na koma falo abinci na zubo na zauna shiru cikin duhu sai rechageble da na kunna.
Ina cin abincin muna waya da Yusuf da ya shaida mini saura kaɗan ya shigo gida.
Sai dai har na kammala bai shigo ba, ina son fita in jira shi a waje hakanan sai nake jin tsoro.
Wayata ta yi kara na duba shi ne ya ce ya biya gidan Mama, har na fara tura baki ina kallon agogo sai na ji muryarsa yana kiran suna na.
Na saki wayar na kwasa a guje na bude ƙofar.
Sai na yi arba da shi yana tsaye rataye da jakarsa bakin bafulatani siriri dogo mai dogon hanci da Kanannaɗaɗɗiyar sumar kai.
Na kai masa runguma, ya yar da jakar ya sa duka hannayensa ya rungume ni.
Mun daɗe a tsaye yana kissing dina kafin na yi ƙoƙarin jan shi ciki sai sannan ya janye, ya ɗauki kallo na daga sama har ƙasa ya fara fadin irin kyan da na yi cikin sansanyar muryarsa da ke ƙara hura mini wutar son sa.
Sai da na ga abin nasa ba na ƙare ba ne na kamo hannunsa zuwa Toilet sai da na tura shi na rufe, na koma bakin gado ina jiran shi.
Ya fito daure da towel na taya shi ya shafa mai ya fesa turare sai ya sanya riga da wando na barci muka fita ya ci abinci.
Muna hira ta tafiyar tasa da hasashen nasara da muke, ina ta hamdala don nasan yana fara aiki shi kenan ƙarshen matsala ta ya zo.
Yana gamawa na fara hamma don na matsu mu isa gado don sati biyun nan a daddafe na yi su ina cike da bukata, ga kwaɗaita mini da ya yi ya samu kanshi na matsalar saurin kawowa da ƙanƙancewar gaba.
Muka nufi daki ya hau gado ni kuma na tube kayan jikina na sauya da wata riga ta barci mai ruwan hoda iyakar ta gwiwa.
Na shiga Bathroom na wanke bakina na fito na kashe hasken dakin na hau gado.
Sai dai me ina jira Yusuf ya taɓa ni shiru sai numfashinsa na fara ji shedar ya samu barci.
"Kan banten baƙin biri. Na tashi zaune na rasa me ma zan yi kai ba zai yiwu ba.
Na miƙa hannu na fara shafa shi kafin na kwanta bayan sa na kankame shi ina sakin wani numfashi da zai ja hankalinsa.
Sai dai me, cikin muryarsa mai sanyi ya ce "Bari mana Zee. Kin san na kwaso gajiya. "
Kawai na zare jikina na fashe da kuka.
Ai kam ya tashi da sauri ya kunna fitilar wayarsa.
Ya ruɗe da tambayar abin da ya same ni, cikin kuka don na ma manta da zancen kunya na ce "Ka gama kashe mini jiki da kwaɗaita mini wannan dare, sai kuma ka dawo ka kwanta mini har kana kiran daren da daren alkairi. Wannan ne alkairin? Ya jawo ni jikinsa " Sorry my happiness my princess. Ki yafe mini amma wlh ina rungumar ki farkon dawowa ta sha'awa ta ta yi karfin da na kasa rike kaina kawai na ji na kawo. "
Kan babbar butar mai shayi.
Na tattakura na ture shi na fashe da kuka.
Dai dai da jin takun mutane ni da shi gaban mu ya ce ras!
"Leka ki ga mene ne? "
Muryar sa ta ratsa shirun da ya gifta.
Ban motsa ba aka haske mu da wata fitila mai haske tare da bayyanar wasu karti majiya karfi har hudu a kan mu.
Na bude baki zan kwalla kara wata murya ta katse ni da fadin "Kina mini ihu ina fasa kyakkyawar kafar nan taki. "
Muryar ta juya a cikin kaina Sauban Salis mai Sara ya bayyana.
Shi din yaron yayan Babana ne, kuma shi ne aka yi juyin duniya na aura bayan ya dawo karatu an turo shi gidanmu ya zabi daya a cikin mu ni da yan'uwana da muke uba daya su uku.
Ya kuma zabe ni ni kuma na ƙi.
"Me kake nema a gidana cikin daren nan Sauban?
Na faɗi ina jin salama gane Sauban ne.
Ya tako zuwa filin dakin kafin ya karaso ya zauna a bed side Drawer.
Na matsa don na fi kusa da ita.
Ya yi wani fito sai ya nuna ni " Wutar son ki ta yagalgala ni My Zee, na kasa hakura da ke, a kullum na kwanta sai kin zo mini a mafarki, kin hana ni sakat, ina yi ma mata kallon ki kina yi mini gizo. "
Ya duba agogon hannunsa "Gobe zan koma Canada daga ban same ki ba ba amfanin ci gaba da zama Nigeria. Sai dai na zo ki ba ni kanki, na yau kaɗai gobe zan tafi. "
Ban san yadda aka yi ba sai dai na ji na zabga masa mari.
Ya dafe kuncin kartin nan suka zaburo ya tsayar da su.
Ya sumbaci hannun da ya shafa kumatun sai ya huro mini iska, kafin ya kara wani fiton, wani cikin su ya zaro bindiga ya cafe ta sai ya nuna Yusuf.
Wanda na tabbatar idan aka tsaga jikinsa a lokacin ba za a samu jini ba.
"Kina da zaɓi Zee. Ki ba ni kanki na yau kadai a cikin wannan daren ko na harbe mijinki!
Gaba na ya harba da tsananin gaske na fashe da kuka " Wallahi babu wanda zan zaɓa ka tashi ka fita. "
Na faɗi cikin hargowa.
Cool down Zee. Amma wallahi wallahi sai kin zaɓa ki ba ni kanki ki fanshi wannan shashashan da kike iƙrarin kina so.
Ya mike tsaye "Yes na yarda kina son sa domin dubi gidan da kika kawo kanki saboda soyayya. "
Ya zare rigarsa ya yar kyakkyawan jikinsa ya bayyana cikakken namiji ne majiyin ƙarfi fari mai murdadden jiki wanda zai alamta maka ya ci karfe, kyakkyawan gaske don mahaifiyarsa mutuniyar Morocco ce, duk da a Najeriya aka haife ta iyayenta daga can suka zo suka yi kaka gida a Nigeria.
"Me na rasa me wannan lusarin mai kama da macen ya fi ni?
Cikin karaji na ce " Wallahi sai dai ka kashe ni amma ba za ka same ni ba ba za ka taba wulakanta ni ba. "
Tas! Karar harbi ta ratsa dakin "Tabbas ba zan maki ta ƙarfi ba amma zan harbe wannan. "
Ya saita Yusuf.
"Don girman Allah ki taimaka mini Zainab ki yi masa yadda yake so kar ya kashe ni.
A karo na farko Yusuf ya yi magana.
Na juya gare shi bakina na rawa " In ba shi kaina fa kake nufi ya yi zina da ni?
"E Zainab kar su kashe ni ki yi masa yadda yake so.
Na fashe da kuka ina kallon sa ina girgiza kai tamkar wadda ta samu taɓi.