Free chapter · Read without an account

Chapter 7

by Ummulkhairi Sani Panisau · INUWAR JIYA

INUWAR JIYA
Ummulkhair S Panisau
Laptop ɗinta ta ɗora a kan wani ƙaramin tebur da ke a tsakiyar ɗakin. A gabanta notebook ɗin ta ne wanda bata rabo da shi, sai wani cup ɗin coffee da aka jima da kawo mata shi har ya huce, da wasu takardu da Hamza ya tattara ya kawo mata su.
Ta buɗe wani tsohon shafin jarida.
AURELIA SKIES FLIGHT 217 CRASH: PILOT ERROR SUSPECTED
Ta karanta taken sau biyu. Sannan ta sake buɗe wani.
CAPTAIN ZAYD SULAIMAN UNDER INVESTIGATION OVER ALLEGED NEGLIGENCE.
Wani kuma aka ce.
QUESTIONS RAISED OVER PILOT'S DECISION-MAKING BEFORE CRASH.
Rania ta ɗan koma da baya tace "Hmm." Ta janyo notebook ɗinta ta soma rubutu.
Captain Zayd Sulaiman.
Official narrative: Pilot negligence.
Ta sake komawa kan tsohon rahoton ta sake bi. "An ce Captain Zayd ya kasa yanke shawarar da ta dace lokacin da matsalar ta fara bayyana. An ce ya yi jinkirin ɗaukar matakin gaggawa. An ce kuskurensa ne ya ƙara dagula lamarin har jirgin ya kasa dawowa lafiya."
Rania ta ci gaba da nazari abin da ya fara damunta ba abin da aka rubuta ba ne, abin da ba a rubuta ba shi take son sani.
Ta buɗe wani sabon shafi ta rubuta.
Captain Zayd Flight 217.
Sakamakon bincike ya cika screen. Hotonsa, sunansa, tsofaffin labarai. Wasu sun ce shi ne ya ja hatsarin, wasu kuma sun yi amfani da kalmomin pilot negligence da poor decision making. Amma duk labaran suna komawa ne ga abu ɗaya wato Official report.
Rania ta ɗan runtse idanunta.
"Ina ainihin hujjar take?"
Ta koma search. Wannan karon ta rubuta: Captain Zayd Flight 217 maintenance. Sai wani rahoto ya bayyana.
Ta buɗe da sauri.
A cikin rahoton an ambaci cewa akwai disagreement tsakanin cockpit crew da maintenance personnel kafin jirgin ya tashi. Rania ta gyara zamanta a hankali an ambaci sunan wani tsohon maintenance officer, sunansa Captain Faruk.
Rania ta buɗe wani rahoton.
Captain Faruk ya yi magana bayan hatsarin.
A cewarsa, Captain Zayd yana sane da yanayin jirgin kafin tashi, kuma ya kamata ya ɗauki matakin da ya dace.
Rania ta sake tsayawa, zuciyarta ba ta yarda da wannan bayanin na Captain Faruk ba. Ta sake karantawa sai ta buɗe wani rahoto da ya shafi maintenance.
A can ma aka sake wata maganar da ta ɗauki hankalinta. Wani daga cikin ma'aikatan maintenance ya ce an yi gwajin jirgin kafin tashinsa kuma an bayyana cewa jirgin yana cikin ƙoshin lafiya zai iya tashi.
Ta daɗe tana kallon screen ɗin wayar, ta fara kwatanta bayanan.
Captain Faruk: Ya kamata Captain Zayd ya san abin da zai yi.
Maintenance: Jirgi ya samu clearance.
Official report: Pilot negligence.
Ta ɗauki alƙalaminta, ta fara jan layi tsakanin sunayen. Sai ta tsaya. Ta kuma cewa "Amma..." A fili sai ta yi saurin komawa tsohon rahoton, akwai abin da bai yi daidai ba idan har jirgin ya samu clearance me ya sa Captain Zayd ya ƙi sa hannu? Idan shi ne ya yi negligence me yasa za a ga bayanai cewa ya nuna damuwarsa akan jirgin game da tashinsa?
Ta sake shiga wani tsohon archive ta buɗe scanned newspaper daga 2019.
Hoton jirgin ya bayyana.
A ƙasan hoton an rubuta.
"Captain Zayd Sulaiman, the pilot of the ill-fated Flight 217, has been described as one of the most experienced pilots in the airline."
Ta ci gaba da karantawa.
Akwai wani ƙaramin paragraph da ba ta taɓa jin an ambata ba.
"Source close to the airline alleged that the captain had raised concerns about the aircraft prior to departure."
Idanunta suka sauka akan kalmar Raised concerns.
Ta koma baya ta sake karantawa sau uku.
Tambayar kanta tayi "Me yasa ba a sa wannan a main report ba?"
Ta sake buɗe wani shafin. Ta fara duba tarihin Captain Zayd.
Shekarun da ya ɗauka yana aiki, flying hours, previous safety records, disciplinary history. Ba ta ga wani babban hatsari ba, babu wani disciplinary action mai girma, babu wani abu da ya taɓa nuna cewa shi mutum ne mai sakaci.
Rania ta jingina da jikin gado a hankali tace "Amma ina proof?"
"Accusations." Ta furta a hankali. Ba ta tsaya ba ta ci gaba da bincike ta ga wani interview da aka yi da wani ma'aikacin airline bayan hatsarin.
Ya ambaci cewa wasu ma'aikata sun yi mamakin yadda aka mayar da hankali kan matuƙin jirgin cikin gaggawa.
Rania ta sauke numfashi.
Ta sake yin rubutu.
Narrative was formed too quickly.
Sai ta buɗe wani rahoton na daban.
A nan an ambaci maintenance issue. A wani wuri kuma an ambaci cockpit decision. A wani wurin kuma an ambaci weather, bayanin ya kasance a warwatse, babu cikakken bayani da ya haɗa komai. Rania ta fara haɗa abubuwan.
Maintenance concern.
Captain refused to sign.
Clearance issued.
Crash.
Pilot blamed.
Records altered.
Ta tsaya kan kalmar ƙarshe records altered ba ta da hujja tukuna. Amma yanzu tana da dalilin tambaya ta duba agogon laptop ɗin ta.
2:17 a.m
"Ya Allah."
Ta shafa fuskarta.
Ta sa hannu zata rufe laptop ɗin sai kuma hannunta ya ƙi ba ta haɗin kai ya koma kan keyboard. Ta buɗe wani tsohon archive sai wani document ya fito.
FLIGHT 217-CREW & TECHNICAL NOTES.
Rania ta danna page ɗin ya ɗauki lokaci kafin ya buɗe ta tsaya jira. Rubutun ya bayyana ta fara karantawa. Sunayen ma'aikata ne da na Captain Zayd.
Komawa tayi kan kujerarta ta zauna don ta ɗan huta ko na minti biyar ne. Sai dai a hankali bacci ya ɗauke ta.
Safiya ce. Hasken rana ya fara ratsawa ta cikin labulen ɗakinsa. A cikin ainihin gidan ana ta haɗa-hadar haɗa abin kari da kimtsa wuri.
Zaune yake a cikin ɗakin karatunsa, cikin farar jallabiya mai tsada. Jarida ce a hannunsa yana karantawa. Gabansa kofin shayi ne a ajiye, da tablet ɗinsa da wasu files da zai duba kafin ya tafi taron hukumar Aurelia Skies Airways.
Zahiri karatun jaridar yake yi amma babu abin da yake fahimta a cikin jaridar. Ya samu bayani Rania Sulaiman ta shiga airport jiya har ta samu tsofaffin bayanai game da tsofaffin ma'aikatan wancan lokacin.
Ya sani tana bincike a kai dama kuma ta samu damar tattaunawa da wasu daga cikin jami'ai ciki har da Idris. Duk an sanar masa da zuwanta.
Yana son sanin abin da ta sani ne, ya ɗauki wayar da ya danna wata lamba.
"Hello, Nasir ne."
"Na ɗauki murya. Alhaji."
"Na samu labarin ta samu ganin Khadija jiya."
"Haka ne Alhaji."
"Me ta samu?"
"Ba ta samu wani abu mai muhimmanci ba sai iya abin da ta sani."
Alhaji Nasir ya lumshe idanunsa yace.
"Kenan ta samu abin da muke son ta samu ko kuma ta tsallaka wani wurin?"
Ya faɗa yana ɗaukar cup ɗin tea ya sha.
"Ina tunanin Musa Danladi ne na gaba."
Ya zaburo gaba yace "Ta san inda yake kenan?"
"Tukunna dai amma tabbas tana neman shi don jiya da dare wannan abokin aikin na ta yana ta tambaya a kan shi."
"Ya samo?"
"Tukuna dai."
"Good."
"Me ya kamata mu yi in har sun samu kusanci da Musa?"
"Kafin ya gan shi ya kamata shi ku gan shi, na san ka gane me nake nufi."
"Na gane Yallaɓai."
Ya kashe wayar.
Ya buɗe wata drawer a gefensa. A ciki ya hangi tsohon file ɗin Flight 217-2019. Ya fito da shi ya ɗora a kan tebur ya ajiye a gabansa. Ya jima yana kallon file ɗin amma bai buɗe shi ba.
Shekaru bakwai da aka yi wannan hatsarin ya gama yin imanin cewa komai ya mutu tare da mutuwar matafiyan. Yau kuma an samu wata yarinya 'yar jarida tana son ta shiga gonarsa.
Ya saki wani irin murmushi yace "Rania Sulaiman." Ya ambaci sunanta a hankali.
Wayarsa tayi ƙara sai ya ga kiran wanda yake son nema shi ma.
"Captain, za ka yi tsawon rai tunanin ka nake yi yanzu haka."
"Ba wannan ba wani labari nake ji. Ko ka san da abin?"
"Na sani. Dalilin tunanin ka kenan."
"Amma ba ka gaya min ba? Ta fara shiga tsofaffin files fa."
"Na sani."
"Har fa ma'aikatan da wancan lokacin ta fara bincikar su."
"Wannan ma na sani."
"Alhaji Nasir amma na ji ka cikin nutsuwa."
"To ya za a yi? Ka sa mata ido ba abin da za ta sani."
"Idan kuma ta duba Technical reports fa?"
"Ba wannan ne damuwata ba. Ina son sanin me ta sani."
"Ta samu official report."
Alhaji Nasir ya yi ɗan murmushi sannan yace "Ba za ta tsaya a iya can ba."
"Me ta samo?"
"Tana son sanin dalilin da ya sa Captain Zayd ya ƙi saka hannu a wancan ranar."
"Ka kwantar da hankalinka ba za ta samu komai ba."
"Idan kuma ta samu fa?"
"Sai mu ɗauki matakin da ya dace."
"Shi kenan sai an jima."
Suka kashe waya.
Alh. Nasir ya buɗe fayil ɗin gabansa. A saman takardun hoton wani jirgi ne. Ya daɗe yana kallon hoton. Sai ya juya shafin ya ga wani rahoto.
CAPTAIN ZAYD SULAIMAN-PILOT NEGLIGENCE
Ya karanta taken babu abin da ya canja ya rufe fayil ɗin.
Wani daga cikin ma'aikatansa ne ya shigo yace "Alhaji mota na jira."
"Ina zuwa." Ya faɗa ba tare da ya juya ba.
Ya tashi ya fita daga ɗakin karatun ya koma na shi ya sake wasu kaya daga jallabiyar da ya saka. Sai ga shi ya fito a Alhaji Nasir ɗinsa.
A idon al'umma Alhaji Nasir mutum ne mai ƙima da daraja da sanin ya kamata. Ɗan kasuwa ne, mai taimakon al'umma, yana daga cikin hukumomin jirgin sama, mutum dai mai mutunci irin asalin mutuncin nan da kowa ke daraja shi.
Sai dai akwai wani ɓangare na rayuwarsa da bai taɓa bari ya fito fili ba. Ga shi yanzu cikin kwana biyu Rania Sulaiman na ƙoƙarin tsallake iyakarta don tona abin da aka binne. Ba ta san shi ba, ba ta san irin mutumin da take son tono sirrinsa ba.
Shi ne kaɗai ya san amsar tambayarta yana kallonta da duk wani takunta.
*
Daga cikin wani office ya fito. Office ɗin ba mai girma ba ne a kusa da wani tsohon filin ajiye motoci yake. Yana riƙe da wayarsa a hannu, yana tafiya da sauri don ya isa cikin motarsa ya je ya samu Rania akwai abin da ya samo.
Ya samo bayanai da adireshin Musa Danladi.
Tun a daren jiya ya dinga tambayar tsofaffin abokan aikinsa a haka ya samu tsohuwar lambar da ta kai shi ga mutumin da ya san inda yake. Ya shiga cikin mota ya rufe har ya kunna motar sai kuma ya tuna da Rania ba ta san ya samo bayanai ba. Sun yi magana da ita da safe kan cewa akwai inda za su je interview.
Ya ɗauko wayar ya buɗe chat ɗinta. Ya fara rubutu.
"Na samo inda Musa Danladi yake yanzu zan taho Hotel ɗaukar ki ina son ki shirya ba zan shigo ciki ba only 30 minutes na iso."
Ya ƙara bi sannan ya aika mata saƙon.
Ya ajiye wayar a kan dashboard. Sai ya ji kamar an taɓa motar ta baya ya juya ya ga babu kowa sai ya ɗaure fuska ya fita daga cikin motar don ganin abin da yake faruwa.
Sai dai bai ga kowa ba ya ɗan ɓata rai ya juya zai buɗe murfin motar sai aka taɓa shi ta baya.
"Wa..." Kan ya kai aya ya ji an watsa masa abu a fuska. Ya yi ƙoƙarin yin baya yana ƙoƙarin kama mutumin amma ƙarfinsa ya soma raguwa cikin 'yan sakanni ya daina ganin komai yana ƙoƙarin yin magana amma ba ta fitowa sai ya daina ganin komai ko ina ya masa duhu. Ya faɗi a wurin.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol