Free chapter · Read without an account
Chapter 8
INUWAR JIYA
Ummulkhair S Panisau
A hotel kuwa, Rania zaune kusa da taga tana kallon agogo. Karfe goma sha ɗaya da mintuna goma sha biyar. Ta shirya tun takwas dama. Ta gama saka komai cikin jakarta har da notebook ɗinta, laptop ɗinta a ciki. Wayarta na hannunta ta duba chat ɗin Hamza da ya shigo mata. Ta karanta saƙon a hankali tace "Finally." Haɗe da sakin murmushi.
"Musa Danladi na samo ka a ƙarshe. Yanzu komai zai buɗe min."
Sai ta kira Hamza amma ba a ɗaga ba ta sake kira aka katse kiran wannan ba halin Hamza ba ne ko yana tuƙi zai amsa ya saka a handsfree amma wai ya katse mata kira. Ta sake kira sai ta ji muryar computer na sanar mata da cewa wayar a kashe take.
Ta tsayar da hannunta wuri ɗaya tace "Switched off kuma?"
Ta sake duba saƙon sai ta ga bai wani ɗauki lokaci ba kuma ta kira ta shiga me yasa za ta ji Switched off? Ta sake kiran shi video call, amma bata shiga ta zauna ta ce a fili "Ko dai ba caji?"
Ta yi ƙoƙarin gaya wa kanta ba wani abu ba ne. Ta sake jira minti goma, minti ashirin, har sha biyu da rabi na rana amma Hamza bai zo ba kuma bai kira ba.
Ta ajiye wayar a kan cinyarta. Ta kalli ƙofar ɗakin ta kalli agogo kamar Hamza zai fito daga cikin agogon ɗakin.
Tana sake duba lokaci ta ga 1:00pm daidai. Ta tashi ta ɗauki jakarta ta fita daga ɗakin ta kulle.
Koda ta sauka reception ta tambaya ko Hamza ya zo aka ce mata a'a. Dole ta fita daga cikin Hotel ɗin.
A harabar hotel ta tsaya tana kallon ƙasa ta gama gajiya ƙwaƙwalwarta ma ta daina aiki. Wayarta ta sake janyowa ta kira layin still wayar a kashe take. Ba dabi'ar Hamza ba ce kashe waya ko da ma ace ba shi da caji ai da tuni ya iso tunda ya gaya mata mintuna talatin sun isa su kawo shi.
Ba ta da wani option dole ta kira Editor.
"Hello."
"Yallaɓai."
"Rania, ina ta jiran kiran ki ya ake ciki? Akwai wani update ɗin kuwa?"
"Yallaɓai an fara samun lead amma yau wani abu ne ya faru unusual."
"Mene ne? Kafin nan ina Hamza ina ta kiran shi amma wayar shi a kashe take."
"Abin da nake son gaya maka kenan Yallabai wayar Hamza a kashe take, kuma ya yi min saƙo awa ɗaya da ta wuce yace min zai zo ya samu wani lead zai zo inda nake cikin minti talatin amma har yanzu bai zo ba kuma wayarsa ma a kashe take wanda bai saba kashewa ba."
"What! Me kike son ki ce?"
"Hamza is lost."
"Rania kina da buƙatar taimako?"
"Tukunna dai Yallaɓai yanzu ina son na je gidan su Hamza ne na ga ko yana gida hankalina ba zai kwanta ba har sai na gan shi."
"Haka ya dace ki yi. Amma ki kula sosai watakila ana bibiyar ku ne."
Sai a lokacin ta tuna an bi su kuma zai iya yiwuwa an ɗauke shi.
"Kina ji na?" Maganar Editor ta katse ta.
"In sha Allahu yana lafiya Yallaɓai bari na je."
"Ki samu ko da bolt ne zan saka miki kuɗi a asusu ina son a samu strong evidence a case ɗin."
"Ba matsala Yallaɓai."
Suka kashe waya.
A hankali ta dinga takawa har ta isa bakin titi daman babu nisa tsakanin titin da Hotel ɗin.
Tunda ta fita bata samu abin hawa ba.
A hankali ta dinga tafiya har tayi nisa da layin. Cikin ranta kuma tunani ne fal na inda Hamza ya shiga gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta yadda ya dace.
"Hamza kana ina?" Ta faɗa haɗe da fesar da numfashi. Mayafinta ya ɗaga ta sa hannu ta gyara mayafinta. Wani guri ta samu ta zauna kan kujera tana kallon titi rashin Hamza ba ƙaramin sanyaya mata jiki ya yi.
Saƙon Hamza ta sake dubawa kamar zai fito ta cikin wayar. Ta sake gwada kiran shi a waya switched off. Ta mayar da wayar ta ajiye.
Wata farar SUV ce ta gota ta gabanta ta wuce. Bayan sakanni biyar motar ta dawo da baya ta tsaya a gabanta. Rania bata ma lura da wucewar motar ko tsayuwarta ba.
A hankali ya zuge glass ɗin motar yace "Hey Miss. Airport."
Ta ɗaga kai a hankali tace "Captain."
Ya yi murmushi. Ya sauko daga cikin motar ganin yanayin ta bai masa ba a kusa da ita ya zauna yace "Lafiyar ki ƙalau kuwa?"
Ta ɗaga gira tace "I'm fine."
"Wannan I'm fine ɗin taki bata yi kama da fine ba."
Ta sauke idanunta ƙasa tayi murmushi tace "Da gaske lafiya ta ƙalau."
Ya ɗan matsa kaɗan gabanta yace "Ko dai ba ki da lafiya?"
"A'a lafiya ta ƙalau."
"Wani kike jira a nan ne?"
Ta ɗago kai tace "Ya aka yi ka gane?"
"Saboda kina ta duba hanya."
Rania ta ɗan yi murmushi don ta kau da damuwar kan fuskarta.
"Kana da sa ido gaskiya."
"Eh ai ya dace da ni aikina ne sa ido."
"Pilot ai ba detective ba ne."
"Ai daman ban ce miki ni detective ba ne ba."
Ta yi murmushi kawai.
"Amma ina ganewa idan passenger ɗina yana cikin damuwa."
"Ni ba passenger ɗinka ba ce."
"Gaskiya ne."
Ta sake kallon wayarta ta yamutsa fuska.
"Abokin ki kike jira ne?"
"Eh."
"Ina ya tsaya?"
Ta girgiza kai sannan tace "Ban sani ba."
"Kin kira shi?"
"Sau ba adadi."
"Bai ɗauka ba ne?"
"A'a wayar a kashe."
Fuskarsa ta ɗan sauya yace "Ko ba shi da caji?"
"Da na yi tunanin haka amma ya tura min saƙo mintuna kaɗan wayar na ƙara amma bai ɗauka ba daga baya kuma an kashe wayar." Ta faɗa tana nuna masa saƙon.
Ya karanta ya kalle ta yace "Amma waye shi wanda kuke nema ɗin?"
"Wani tsohon ma'aikacin aviation ne."
Ya ɗan kalle ta kamar zai yi magana sai kuma ya tashi ya nuna mata motarsa yace "Tashi ki shiga."
Ta kalle shi "Me zan kalla?"
"Mota, shiga in mayar da ke hotel."
"Ba sai ka wahalar da kanka ba."
"Ba wahala ba ce."
"Ka kyale ni don Allah."
"Ba zan bar ki a gefen titi ba kina jiran mutumin da wayarsa take a kashe ba."
Ta yi shiru. Sai kuma ta miƙe tsaye ta zagaya ta shiga ciki ta zauna bata ce da shi komai ba.
Ya shiga shi ma.
"Iya hotel zaka mayar da ni amma."
"Deal."
Ya kunna motar ya kalli dashboard. Yace "Seat belt."
Ta ɗan ɗaure fuska. Sai kuma ta ɗaura.
"Happy?"
"Sosai."
Ya soma tafiya ta gaya masa inda za su bi.
Ta jingina kanta da jikin kujerar har a lokacin wayarta na hannunta.
Suna yi nisa wayar Rania ta soma ƙara. Da sauri ta duba. Ya yi saurin cewa "Ko shi ne?"
Ta kalli screen ɗin wayar.
"A'a baƙuwar lamba ce."
"Ki ɗaga kila shi ne."
"Hello..."
Ba a amsa mata kai tsaye. Ta zare wayar daga kunnen ta, ta kalli screen ɗin, har a lokacin wayar bata katse ba. Ta sake mayar da wayar kunnen ta.
"Hello."
"Na san kina son sanin wane ne mai magana kar ki tsorata kar hankalin ki ya tashi tun yanzu ina son ki nutsu ki ji abin da zan faɗa miki. Na san kina neman abokin aikin ki Hamza...."
Ta ɗan zabura tace "Wane ne kai? Ya aka yi ka san Hamza?"
Ya yi mata dariya. Kawai sai ya kashe wayar.
Ya bar ta da cewa "Hello, Hello, Hello waye kai ina Hamza yake me kake so?"
Amma babu amsa. Rayyan ya amshe wayar daga hannunta ganin yadda ta kiɗime lokaci ɗaya jikinta har rawa yake yi yace "Miss Airport ki nutsu don Allah an kashe wayar waye ya kira ki?"
"Ban san shi ba ban san wane ba ya ce min ya san ina neman Hamza."
"Amma me ya sa za a ɗauke Hamza?"
"Saboda binciken da muke yi."
"Wanne irin bincike ne?"
"It's confidential ba zan iya gaya maka ba."
Ya ɗaga kafaɗarsa yace "Shikenan. Na zata za ki iya yarda da ni ki gaya min, wataƙila na iya taimakon ki."
Ta yi shiru tana murza 'yan yatsunta tana son ta gaya masa amma ba za ta iya gaya masa ba saboda yanayin aikinsu ba sosai ta san shi ba, ba zai yiwu ta gaya masa abin da suke ciki ba. Haka ta daure ta ari dakiya tace "Babu komai ka sauke ni a nan ka tafi."
Ya kare mata kallo kamar zai yi magana sai kuma ya yi tsit ya sauke ta a bakin gate ɗin hotel. Ta fita har ta manta da jakarta a cikin motar. Ta kusan shiga ya yi saurin ce mata "Miss. Airport!"
Ta juya ta kalle shi.
"Kin manta da jakarki a nan."
Ta koma ta amsa.
A ƙasan labbanta tace "Na gode."
"Ki kwantar da hankalinki kin ji ko? Ba abin da zai faru idan kina buƙatar wani abu ki kira ni zan zo nan take."
Tayi masa murmushi ta juya ta shiga ciki.
Bayan ta ya bi da kallo. Tunani ya shiga kan mene ne binciken da suke yi wanda har ya shafi ɓatan Hamza. Su waye suka ɗauke Hamza kuma me yasa? Waɗannan su ne tambayoyi biyu da suka zauna masa a rai. Tun ran da ya gan ta a airport ya shiga shakku da kuma son sanin me take nema. Wane labari ne a airport da zai saka su bincikar shi? Idan har yana son sanin komai to dole ne sai ya san me take nema ba zai san me take nema ba dole ne sai ya fara sanin me take nema kuma sai ya shiga jikinta tukunna.
Haka ya ja motar ya tafi.
*
Tana shiga ciki tayi wulli da jakarta a kan gado. Ta buɗe tagar ɗakin ta tsaya a jikin tagar tana kallon waje. Jikinta sai ɓari yake yi. Ba zai yiwu ta iya barin Hamza wani abu ya same shi ba. Kuma ba za ta iya barin wannan labarin ya tafi a iska ba.
Tunani ta faɗa nan da nan hawaye suka fara bin kan fuskarta. Tashi tayi ta kama kai tace "No ba zai yiwu ba, ba za a yi haka ba. Dole ne na tona abin da aka binne da jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba."
Ya zama dole gaskiyar Flight 217 ta fito. Ya kamata 'yan'uwan waɗanda suka mutu su san gaskiyar rasuwarsu. Ya kamata a hukunta masu hannu a faɗuwar jirgin.