Free chapter · Read without an account

7

by Zainab Amzah · Nour Ayn

*PAGE 7*

Cikin tsari da natsuwa suka miƙe gabaɗaya, kamar ‘yan leƙen asiri suka bi ta bayan su har suka isa in da suka yi parking. Zuciyarsu cike da farinciki saboda ɗokin gano abin da suka daɗe suna nema. Cikin ikon Allah, har suka kai wurin da motar su take Fahad bai lura da su ba. Suka zauna a cikin mota, suna lura da kowane motsi nasa. Har sai da ya gama tattaunawa da Adam’s, sannan ya shiga motarsa mai kyau ya yi reverse, cikin ƙwarewa ya kama hanyar gida. A hankali yake driving, sanyin AC na shigar sa da kyau, ga wani cool music mai dadi da yake tashi a motar, Waƙar ta ƙara masa natsuwa da kwanciyar hankali, ba tare da sanin cewa akwai wasu idanu da ke bibiyar duk motsinsa ba.

Cike da ƙwarewa su ke bin sa a baya, ba su bar wata alama da zai nuna suna binsa. A daidai bakin wani restaurant mai kyau ya tsaya, wuri ne da yake yawan zuwa siyan abinci, ko da yana gida order kawai yake su kawo masa. Ya ɗan jima kadan cikin mota yana magana a waya, kafin ya fito ya nufi entrance na restaurant din. Bai dade ba sai gashi ya fito riƙe da wata ƙaramar bag mai ɗauke da abinci. Suna a wurin har ya fito sannan suka ci gaba da binsa har suka isa unguwar da gidansa yake. Suka yi parking ɗan nesa da gidan, akan idan su ya fito ya nufi apartment ɗinsa. Kuma har lokacin bai lura da su ba. Shiru suka yi, babu wanda ya ce komai a cikinsu. Gabaɗayansu sun mayar da hankalinsu kan apartment ɗin da yake shiga. Manisha kuwa, zuciyarta cike take da wani irin ɗokin shiga wurin. Jasmine ta yi breaking silence din, "You guys, ina tunanin nan ne apartment ɗinsa, zamu iya tafiya yanzu." Waafa ta girgiza kai ta ce, "No Jaz, let's wait a little bit. Coz we're not sure apartment ɗinsa ne wannan ko na wani ne ya zo." Manisha ta karyar da kai cikin amincewa ta ce, "Yeah... you're right, Waafa." Gabaɗayansu sun gamsu da shawarar da Waafa ta bayar. Don haka suka gyara parking ɗinsu da kyau, suka koma gefe domin su ci gaba da sa ido. Sun daɗe sosai a wurin, har rana ta fara faɗuwa. A ƙarshe suka yanke shawarar komawa gida. Duk da haka, wata zuciyar tana gargadin manisha cewa kada ta tafi, Tana jin kamar idan ta bar wurin a yanzu, Fahad zai iya fitowa, ta rasa ganinsa, kuma wannan damar ta iya zama ta ƙarshe. Ba ta da ra’ayin tafiya amma ba ta san me zata ce masu ba. Tana gudun a samu matsala kamar yadda hakan ya sha faruwa da ita. Duk da haka, ba ta da yadda za ta yi, dole ta bi su ko da kuwa ba ta so. Amma a cikin zuciyarta ta ɗauki alƙawarin cewa za ta dawo washegari, za ta sake zuwa domin ta tabbatar da cewa wannan ne apartment ɗin sa.
A hanya kuwa, Jasmine ta ci gaba da ba ta shawarwari a kan yadda za ta jawo hankalin Fahad ya karkata gare ta.
Ta ce, "Manisha, dole ki yi amfani da kyawunki, iliminki da wayewarki. Namiji irin Fahad ba a barin shi haka kawai." 
Ta ɗan yi murmushi sannan ta ƙara da cewa, "Kin ga yana da kyau sosai, ga ilimi da wayewa, ga kuma arziki. Kusan komai ya haɗa, ko da ba a faɗa ba duk wanda ya kalli Fahad zai fahimci cewa ba ƙaramin mutum ba ne, sannan akwai kaya a wurinsa." Jasmine ta ɗan yi shiru tana kallon Manisha, kafin ta sake cewa, "Kuma fa, ba kyau kaɗai za ki dogara da shi ba. Ki nuna masa ke ɗin mace ce mai hankali, wadda ta san abin da take so. Ki riƙa nuna masa kulawa, ki sa ya saba da kasancewarki a rayuwarsa har ya kasa jin daɗin rashin ganinki." Manisha ta yi murmushi, ta gyara zamanta sannan ta ce, "Ai ni ma wannan nake tunani. Wallahi Jasmine, ban taɓa ganin namiji da ya ɗauke mini hankali irin Fahad ba. Tun ranar farko da na fara ganinsa na kasa cire shi daga raina." 

“Na sani Manisha, Amma duk da haka ki yi komai cikin hikima. Kada ki yi saurin nuna masa komai gabadaya. Ki bar shi shi ma ya ji yana son sanin ko ke wacece." Manisha ta gyada kai, amma a cikin zuciyarta ta riga ta yanke shawarar cewa babu abin da zai hana ta mallakar zuciyar Fahad. A ganinta, Fahad ba irin mazan da za a bari su wuce ba ne. Kuma idan akwai abin da take so a rayuwarta a wannan lokacin, to shi ne ta zama macen da yake alfahari da kasancewa tare da ita.

Ita kanta Jasmine Fahad ya burge ta sosai, duk da cewa babu namiji a tsarin yaruwar ta gabadaya, kuma ba ta taɓa nuna wata sha'awar yin mu’amala da maza ba, amma Fahad ya yi mata kyau matuƙa. 

Suna isa gida, dare ya riga ya yi. Abinci kawai suka ci, sannan suka haura kan gadajensu, suka ci gaba da hirarsu cikin nishaɗi. Dukkansu wayoyinsu ne a hannunsu, suna ta dannawa. Babu wanda ya tuna da sallah balle ya yi tunanin tashi ya yi ta. A gaskiya, ba wai sun damu da sallah ba ne. Sai Waafa ce kaɗai wadda a wasu lokutan take ɗan ƙoƙarin yin sallah, saboda Mom ɗinta tana tsaye a kanta. Kawai dai ta ɗan fandare ne sakamakon haɗuwa da ƙawayen banza, ’yan bariki irin su Manisha. Ita kanta Waafa ba kullum take yin sallah ba, amma duk da haka ta fi Manisha tarbiyya kaɗan. To daman iyayen su sunfi kuɗi. kuma sun fi shagwaɓa su. Duk da iyayen Waafa su ma manya ne kuma suna da arzikin su, kasancewar mahaifinta shi ne Commissioner of Land, Kuma duk da hakan ba su fi Waafa komai ba. Saboda itama parents dinta tsaye suke a kanta wurin komai, sun tsaye a kanta sosai wajen tarbiyya da kula da duk wani al'amari nata kawai dai kowa da tarbiyyar da aka ba shi.

Washe gari, tun ƙarfe bakwai na safe, Manisha ta riga kowa tashi a gidan. Ko barcin kirki ba ta yi ba, domin da tunanin Fahad ta kwana a ranta. Ko wanka ba ta yi ba, ta canza kayan jikinta daga na barci zuwa baƙar abaya, ta ɗauki key ɗin motarta sannan ta fice daga gidan. Kai tsaye unguwar da Fahad yake ta nufa. Tana isa, sai ta hangi motarsa a parking lot, a daidai inda suka bar ta jiya. Wannan ya ƙara tabbatar mata da cewa nan ne apartment ɗinsa. Da alama tun jiya bai fita ba, domin yadda suka bar motar haka ta tarar da ita. Ta daɗe tana bibiyar sawunsa, amma kullum sai ya ɓace mata a hanya. Wani lokacin kuma gidan friends ɗinsa yake wucewa, sai ta koma daga baya take gane ba gidan sa ba ne, wasu lokutan kuma a tsakiyar hanya yake ɓace mata, kamar ya san cewa tana binsa. Sai jiya Allah ya ba ta sa'a, har ta gano gidan da yake zama. Ta so ta shiga gidan, amma sai ta ji ba za ta iya ba, saboda ba ta yi wanka ba, sannan kuma safiya ce sosai.  Cikin farinciki ta juya motarta ta koma gida. Tun tana kan hanya ta tura wa Mommy saƙo, tana sanar da ita cewa ta gano gidan Fahad. Ba ta tsaya ta kiran ta ba, saboda ta san tana barci a wannan lokacin.

A wani ɓangaren kuwa, Mimi, yau tun da suka tashi suke aiki cikinfarin ciki. Dalili kuwa shi ne yau Daddy zai dawo daga doguwar tafiyar da ya yi. Kowa ka kalla a gidan, cikin farinciki yake, yana kuma ɗokin ganin dawowarsa.

Tun da sassafe Mimi tare da ’yan aiki suka fara gyara ko'ina a gidan, da wuri taje school yau ta na gama abin da za tayi ta dawo. Tunda ta shigo gidan wanka kadai ta yi ta shiga kitchen. Ita ce ta ɗauki nauyin duk abin da za a girka, saboda tana matuƙar son girki da ayyukan gida. Kusan ita tayi komai. Gabaɗaya ba ta da ƙyuya ko ganda wajen aiki. Tana son ayyukan gida sosai, musamman girki, wanda yake ɗaya daga cikin hobbies ɗinta tun tana ƙarama. Babu irin girkin da ba ta iya ba, domin har catering school ta yi. Har da welcoming cake da small chops ta shirya wa Daddy domin tarbar dawowarsa. Ko da Ammi ta zo ta ce zata Kama masu aiki, marairecewa ta yi ta ce taje ta huta za ta yi komi da kanta don ta ma kusa gamawa. Ammi ta saka mata albarka sannan ta koma ɗakinta. Wajen ƙarfe hudu na yamma suka kammala komai. Mimi ta kira Amina ta ce, "Amina, ni na gama nawa. Sauran naki. Ki gyara kitchen, sannan ki tabbatar kin saka turaren wuta na Scents by Teema a ko'ina, especially marshush."
Amina ta amsa, "To, Aunty, in sha Allah."

 Mimi ta juya ta nufi staircase, ta haura zuwa ɗakinta. Ta shiga banɗaki, ta yi wanka da alwala. Bayan ta fito, sai ta saka doguwar riga mai laushi, sannan ta gabatar da sallarta tare da azkar kamar yadda ta saba kullum. Bayan ta gama, ta zauna a gaban mirror tana shafa cream ɗinta. Da ta kammala, sai ta shafa oils ɗinta masu daɗin ƙamshi na Scents by Teema, sannan ta fesa body spray mai daɗin ƙamshi. Ta buɗe wardrobe ɗinta, ta ciro wata tsadaddiyar doguwar riga, abaya mai matuƙar kyau da ta yi mata matuƙar kyau. Ta haɗa ta da scarf ɗin da ya dace da ita. Ba ta yi makeup ba, sai ɗa powder da lip gloss kadan da ta shafa. Haƙiƙa kyawunta ya fito sosai, har ta zama abin kallo. A daidai lokacin newayarta ta fara ringing. Fahad ne yake kiranta ta video call a Instagram. Sai da ta yi murmushi kafin ta ɗaga kiran.
Suka kalli juna na ɗan lokaci ba tare da wani ya ce komai ba. Fahad ya ɗan kawar da idonsa daga kallonta, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Wani irin kyau ya ga Mimi ta ƙara yi masa a wannan lokacin. A ransa yana jin kamar ya ɗauko ta ya kawo ta London, su ci gaba da rayuwa tare cikin farinciki. A hankali ya ce, "Someone has forgotten about me."
Ya karasa faɗa tare da ɗan ɓata fuska. Mimi ta yi dariya ta ce, "Haba, Bae! Ni na isa na manta da kai?"
Ya ɗaga gira kaɗan.
"Kin isa mana. Ba gashi kin manta da ni ɗin ba?"

Ta girgiza kai ta ce, "Ba haka ba ne fa. Ka san yau Daddy zai dawo, kuma tun da zun nake kitchen ina masa girki. Sannan ka san ni ba na son masu aiki su yi mini komai, musamman abincin Daddy."
Ya ɗan yi murmushi sannan ya ce, "Haka ne, yar gidan Daddy. Allah ya yi miki albarka."
"Amin," ta amsa a taƙaice.
"Ina Nadiya?" Ya tambaye ta.
"Tana school, ba ta dawo ba tukuna. Amma Malam Tukur ya je ɗaukota."
"Okay. Yaushe zaku fara CA test?"
"Next week, in sha Allah." "Okay, Allah ya kai mu lafiya."
"Amin. Thank you."
Shiru ya ratsa tsakaninsu gabaɗaya. Kowannensu ya yi shiru na wasu daƙiƙu, har sai da Fahad ya sake magana.
"Idan kun gama exams, result ya fito, mene ne next?"
Mimi ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta ce, "Sai shiga next class mana, Bae."
Ya gyara zamansa, ya miƙe ya zauna da kyau, sannan ya kalleta cikin kulawa. "Ba ki ganin in yi wa Daddy magana ya dawo da maganar aurenmu kusa? If possible ma, nan kusa. Ko kuma in ce bayan kin gama exams ɗinki?" Hannunta ta sa ta rufe fuskarta da murmushi. Kunya ta kama ta ba tare da ta shirya ba. Haƙiƙa ta ji kunyar maganar da ya yi.
Fahad kuwa dariya ya yi, domin yadda ta sauya fuska ya ba shi dariya da sha'awa. "Haba, love! Ba ki ce komai ba."
"Um... um," ta yi ƙoƙarin amsawa.
"Um um me? Faɗi abin da kike so a yi."
"Um um... Ni dai not now, Yaya." Ya ɗan karkatar da kansa.
"Calmly, ya ce “why?"
Ta gyara zama sannan ta ce, "I'm too young to get married. Kuma fa ka ce sai na gama university." Ya ɗan yi murmushi sannan ya ce, "To, yanzu na canza mind ɗina. Yanzu nake so a yi." Ta girgiza kai cikin sauri. "A'a, please, Yaya. Daddy ma ba zai yarda ba." "In ji wa ya faɗa miki?" Ya tambaye ta. Ya ɗan dakata sannan ya ƙara da cewa, "Allah zai yarda, in dai kin amince. Kin san duk abin da kike so, shi Daddy yake yi miki." Ta yi murmushi kaɗan ta ce, "Haka ne, amma... Mu bar maganar please."
Ya girgiza kai.
"Ba za mu bari ba. Sai mun ƙarasa ta." Ta marairaice ta ce, "Me ya sa?" Ya kalleta cikin wani irin yanayi na soyayya, sannan ya ce, "Saboda muna buƙatar junanmu gabaɗaya."
A hankali ta ce, "Yaya, karatun fa?"
"Sai mu taho nan, ki ci gaba da yi. Dama ba ki yi nisa ba." Ta kalle shi cikin mamaki. "Amma Yaya, me ya canza mind ɗinka da wuri haka? Bayan ka ce sai na gama school, ko na kai 300 level." Idanunsa masu kaifi ya zuba mata. Take jikinta ya yi sanyi.
Ya ɗan karkata kansa, sannan ya tambaye ta, "Kina so ki san dalili?"
"Sure, Bae."
Ya sak is e zuba mata idanunsa masu kaifi, kafin ya furta a hankali:
"Saboda kina buƙata ta."
Ta zaro ido.
"Kamar ya? Ina buƙatarka, Yaya?" "Yes. Kina buƙata ta. Ni zan magance miki matsalarki da kike fama da ita shekara da shekaru. Matsalar da take yawan ba ki wahala."
Mimi ta kafe shi da ido.
"I don't understand. Wace matsala ce wannan da za ka magance mini ita?"
Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, kamar yana neman kalmomin da suka dace. Daga bisani ya ce: "Wannan bakin ciwon da kike fama da shi duk wata, wanda yake ba ki wahala. Shi ne ni ma nake son in ba shi wahala har ya gudu ya bar mini matata ta huta." Wani irin yanayi ne ya mamaye Mimi. Lokaci guda ta ji kamar komai ya tsaya mata. Tsabar kunya ta kasa cewa komai. Ba shiri ta kashe wayar gaba ɗaya!

✨𝐍𝐨𝐮𝐫 𝐀𝐲𝐧✨

𝐁𝐲 𝐙𝐚𝐢𝐧𝐚𝐛 𝐀𝐦𝐳𝐚𝐡

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol