Free chapter · Read without an account

Chapter 20

by Hauwa Salihu · MATAR SALMAN

*💫MATAR SALMAN 💫*



*➡PART ONE*
*PAGE 20*



Amina ta isa Kaduna lafiya, sai dai zuciyarta cikeda fargaba ta nufi gidansu haka ta daure ta shiga sai dai abin mamaki ba su tasamu ba wasu mutane ne daban, anan ta shiga yi musu bayani amma basu gane ba.
Abin mamaki makwaftansu ma data ke shiga sun kaura dake gidan hayane.

Amina a karshe dai gidansu Zuwaira taje gaskia taga kallon banza babu wanda ya kulata sai maigadine yake fada mata su Zuwaira sun koma Kano da zama shekaru kusan shidda yanzu.

Don haka Amina bata tsaya ba ta sake samun motar Kano ta tafi har cikin dare ta isa, daya ke tasan gidansu na gado don nan ne Yayyenta suka dawo.
Duk da haka sai da tasha wahala sannan ta gane, ta shiga gidan da sallama yayinda take bin gidan da kallo sun gyareshi yayi kyau ginin zamani a lokacin, lallai arziki yaci uban nada.
Wata matace ta fito rikeda yarinya. Don tayita sallama basu jita ba duk sun shiga ga karar generator.
Anan fa Amina ta fara tunanin ko ba gidan ne ba.
Suka gaisa dai da matar cike da fara'a. 
Amina ta kalleta tace "Don Allah nan ne gidansu Moh'd da Kasim?"

Matar tace "Eh nan ne."
Amina tayi ajiyar zuciya tace "Zuwaira na nan?"

Matar tace "Eh yanzu kuwa ta tafi sashinta bari na fada mata tayi bakuwa."
Anan matar ta tafi Amina ta bita da kallo a ranta tana fadin wannan din kuma wacece oho.

Tana cikn wannan tunanin suka fito Amina tuni ta gane Zuwaira amma ita sai da ta matso ta karewa Amina kallo ta dafe kirji tace "Amina!"
Hawaye ne ya ciko idon Amina suka rumgume juna da Zuwaira suna kuka wanda yaja hankalin yaran gidan kanana.

Sai kuma Shatu data fito wanka ganin Amina yasa ta saki salati tace "Wa nake gani haka? Amina! Kece? Dama kina raye? Tabdijam.......bari dai nayiwa Yayyenki albishir."

Da sauri ta wuce Palo inda su Kasim da Moh'd suke hira sai su Salman da Salim wanda a lokacin suna da shekara 10 a duniya."
Anan shatu ta sanar dasu dawowar Amina.
Gabadaya suka fito tsakar gidan ganin da gaske Aminar ce, yasa Moh'd yin murmushin takaici yace "Amina dama nasan dole ne ki dawo duk daren daɗewa, don bakida wa'yanda suka fimu."

Ya kalli shatu yace "Shatu kuje da ita ku kwanta dare yayi, koma meye a bari sai gobe, duk kuje Ku kwanta....."

Kasim da yaketa cika da maganar Yayansa yace "Haba Yaya ina zata je kuma? wlh ta bar mana gidanmu, mu muka san daga ina ta fito?"

Shatu ta karba "Kuma gata da goyo ko ina ta sami yarinya kuma oho Amina kinyi aurene?"
Sai lokacin duk suka lura da goyon 

Kasim ya kalli Mohd6 yace "Kagani ko Yaya? Amina sai da tagama yawonta taje ta debo mana abin kunya sannan ta dawo wlh sam zaman Amina a gidan nan bazai yiwu ba."

Shatu tace "Wannan nn gaskiane Kasim nikaina ina bayan ka."

Ta kalli Amina dake kuka tace "Sai yanzu da kika gama yawon karuwancin ki zaki dawo mana da goyo? Amma Amina kinji kunya wlh ......"

Ta karasa fada hade da fashewa da kukan munafurci tana fadin "Yanzu fisabilillah abinda zaki mana kenan, duk kokarinda yayyenki sukayi akan ki sai da kika watsa musu kasa a ido, dama tunda kika tafi danginku na Yakasai sai kananan maganganu suke wai mun kasa rikeki mun barki kin tafi karuwanci alhalin sauran sati daya da bikinki, yanzu shine kika dawo da yarinya don ki tabbatar musu karuwancin kika je Amina?"

Maganar Shatu tayi tasiri sosai a zuciyan Moh'd da Kasim.
A fusace Kasim ya kalli Amina yace "Ki fita daga gidan nan tun kafin na canza miki kamanni, in yaso kije kici gaba da karuwancin naki."

Matar can ne da ta fara ganin Amina ta kwantar da murya tace "Haba Baban Salim ai kamata yayi ku saurareta tukunna ai..,....."

Moh'd ya tari numfashinta da fadin "Kar ki shiga maganar nan Rabi domin baki san komi akai ba."

Zuwaira ta goge hawayenta tana kallon Moh'd tace "Amma Yaya ai ya kamata ace ku saurari Amina watakila abinda kuke tunani ba haka bane, don Allah ku barta haka sai da safe........"

Kasim ya katseta da fadin "Ke Zuwaira bari kiji Amina bazata kwana a gidan nan ba don haka ta fice daga gidan nan kawai ta koma gun wa'yanda ta zabesu fiye damu......"

Zuwaira tana kallon shi da mamaki tace "Yanzu a cikin daren nan saboda Allah ? A naka tunanin ina zata je yanzu?"

Kai tsaye yace "Ta koma inda ta fito Zuwaira."

Zuwaira tace "Tabdijam wlh bazai yiwu ba babu inda Amina zataje don itama nan din gidan mahaifinta ne kuma tana da gadonta ko karyane? Don haka ba inda zata je don naga ka dage da yawa, baka san kuskure bane ko bakasan kaddara ba?"

Kasim ya harzuko yana shirin yiwa Zuwaira magana Moh'd ya katseshi da faɗin "ka rabu da ita kawai Kasim, barsu Aminan ta kwana in yaso gobe sai tasan inda dare ya mata.

Kasim ya kalli Zuwaira cike da jin haushi yace "wlh da ba don Yaya ba kema da sai kin bar gidan nan cikin daren nan kibi Amina."

Zuwaira tayi mishi wani irin kallo sannan ta watsar ta kalli su Salman tace "Kai Salim kuzo ku dauki kayan Goggonku ku kai mata dakina."

Lokaci guda sukace To Ummee." 
Zuwaira ta kama hannun Amina tace "Zo muje ciki Amina yi hakuri."

Shatu tabe baki tace "Ba shakka Zuwaira har wani hakuri kike bata? nan nan kiri kiri babu tsoron Allah tace bata son ɗan'uwanki."

Zuwaira tace "To sai me don tace bata son dan'uwan nawa, ana so dole ne?Kuma ke meye naki a ciki? Ai ɗan'uwana ne koh?"

Mohd da Kasim shiru kawai sukayi.
Yayinda Rabi ta wuce dakinta, Shatu kam har lokacin magana takeyi tana kara ingiza su Moh'd.

Zuwaira kuwa ranar taki zuwa turaka anan suka zauna da Amina sukaci kukansu har suka gaji don kansu...

Zuwaira tace "Amina ina kika tafi kk barmu cikin tashin hankali ni da yayyenki? Amina baki kyauta ba magana ta Allah."

Amina tace "Aunty Zuwaira nasani nima kuma wallahi nayi nadama...... labarin mai tsawone sai gobe in Allah ya kaimu zan fada miki."

Zuwaira tace "To Allah ya kaimu.....kin dawo kinga gida ya cika da yara ko?"
"Bayan tafiyarki Shatu ta maida yayyenki kamar remote control sai yanda tayi a gidan, ni nan bata barni ba duk da ba kulata nake ba amma saida tasa yayanki ya tsaneni, Amina ba abinda bangani ba na makircin Shatu sai da na tashi tsaye da rokon Allah ba dare ba rana snn Allah ya kawo min sauyi ba kiga tun kan Salim ban kuma haihuwa ba, sai yanzu dana samu Fa'iza. To wlh munfi shekara huɗu da yayanki a gidan can ko hannuna baya rikewa. Har mata Shatu ta samo mishi a garinsu ana shirin aurensu sai asirinsu ya tonu ashe wai tanada aure a can ƙasar tasu mijinta bai saketa ba, hmm wai ashe haka wasunsu keyi, ni ban taɓa jin irin wannan jahilcin bama sai a lokacin, kedai abubuwa kam sun faffaru......

Amina cike da mamaki take Zuwaira tace "Lallai Aunty Zuwaira duk wannan kuma kika jure?"

Zuwaira tace "To ya zanyi da aikin asiri, harfa gidanmu na koma wlh amma abin mamaki bai taba nemana ba sai da nayi good 3 years ance ya sakeni yaki karshe dai haka Abbana ne yace in dawo inci gaba da addu'a don sunsan abin ba haka kawai bane, don haka sai na dawo Shatu kam sai abinda taso takeyi a gidan babu abinda ya fasa, mun zama kamar bayinta. Bayan 
 tafiyarki ma har ta haihu har sau biyu amma yaran Allah baiyi zasu rayu ba. Haka mukaci gaba da tutturawa sai kuwa lokaci guda Allah ya amshi addu'ata komai ya dawo normal.
Inda reshe kuma ya juye da mujiya, Shatu ta soma girbar abinda ta shuka ita da Yayanki a gidan nan watarana har dukanta yayi da cikin Sadiya kinsan kuwa ta kure hakurinshi, sannan yaje ya kawo mata kishiya wato Rabi matar kirki wlh bata da tashin hankali da kowa kinga lokaci guda da zuwanta gida ya canza, Shatu bayan ta haifi Sadiya ta sake samun Raihana, ta haifi Raihana da wata daya na haifi Fa'iza sati daya akai itama Rabi ta haifi Sakina sune kika gansu gabadaya suka taso Kansu daya yanzu shekarunsu bibbiyu da dorin watanni."

Amina ta jinjina kai tace "Aunty kinyi matukar kokari wlh gaskia na jinjina miki don Shatu babu alkhairi a tare da ita zama da ita sai an jajirce, Allah yasa mu dace 'ya'ya kuma Allah ya musu albarka, amma harga Allah ina tausayin Salman ɗina, don bai yi dacen uwa ba..,...

Zuwaira ta sauke ajiyar zuciya tace "To ya za'ayi, sai dai yanzu Alhamdulillah mun gama gininmu a Abuja ma zamu koma har da Salman ɗin kuma, don dama nike kula da kominsu shida Salim yadda suka taso kamar twins haka muke so har su girma tare, yanzu mu da Kano sai dai muzo hutu.

Amina taji daɗi sosai a ranta tace "Gaskiya Aunty Zuwaira na tayaki murna kuma nauyin tarbiyyan Salman da kk dauka Allah ya biyaki, domin tashinsa a gaban Shatu ina fargaba. Allah ya saka muku da alkhairi kuma."

Zuwaira tace "Amin yanzu ki kwanta nasan kin gaji da yawa sai da safe."
Da haka suka kwanta Amina dai bata yi bacci ba sai juyi take ta rasa me yake mata dadi a rayuwar nan guda ɗaya, tunanin abinda Ib ya mata kawai takeyi.
Gari na wayewa Zuwaira ta tashi ta shirya wa Amina breakfast mai rai da lfy yayinda ta dumama ruwa tayiwa Rumaisa wanka ta shirya ta tsaf cikin pink din Riga da wando masu nauyi don ana sanyi daganan ta bata maganinta ma."

Ta kalli Amina tana murmushi tace "Meenah wannan yarinya tana kama da Ibrahim ko dai 'yarsa ce bani labarinki don Allah."

Su Salman suka shigo cikin shirin makaranta, Salman na ɗora ido kan Rumaisa ya kai hannu ya ɗauketa yana ta kallonta ta mishi kyau sosai gashi bata kin mutane, sai ma dariya take mishi.

Aunty Zuwaira tace ”Ya dai tayi maka kyau koh?”

Kafin yace komi Salim yace "Ummie tun jiya yake ce min yarinyar nan ta mishi kyau, ko nima kuma tayi min kyau tafi su Fa'iza fari.

Aunty Zuwaira tace "Kaji shirmenka kai wato farin kawai kagani koh?"

Shidai Salman baice komi ba, Amina ta kalleshi da murmushi tace ”Aunty kinga yadda Rumaisa ke ta masa dariya.... To inaga fa Salman kam ya sami mata in sun girma kawai ayi tuwona maina, kaga Babana, na baka ita kaji?"

Aunty Zuwaira tana dariya tace "Nikuwa shaida indai muna raye Rumaisa ce MATAR SALMAN."

Dariya Salim ke masa, shidai baice musu komi ba. Sai Aunty Zuwaira ta karbi Rumaisa tace "To maza kuje breakfast na palo kuyi maza kafin school bus yazo.... Allah bada sa'a ayi karatu sosai."

Suka amsa da biyayya suka fita.
Anan Zuwaira ta kalli Amina tace "Ina sauraranki Meenah."


Amina ta gyara zama da niyyar fara baiwa Zuwaira labarinta kawai sai ga Shatu ta fado dakin ko sallama babu ta kalli Amina fuska daure tace "Kin wani mimmike kafa kin dauka zamu barki kici gaba da zama ne a gidan nan malama? To ki tashi Yayyen naki na kiranki."

Amina ta zubawa Shatu ido sai kuma ta danyi murmushi tace "Shatu kinci sa'a kura tayi lafiya, amma babu komi kici gaba.....

Ta be baki shatu tayi tace "To ya kika iya dani dama, ai Amina yanzu ni Shatu nafi karfinki sai dai ki kalleni ki cire ido, don da ba yanzu bane."

Zuwaira tace "Kinga Shatu kawai kije tana zuwa."

Shatu tace "Kema Zuwaira ki yi taka tsan tsan da Amina in ba haka ba igiyar aurenki na daf da tsinkewa."

Zuwaira tace "Tunda ke kika kulla ko kuma igiyar a hannun ki yake ba, ai sai ki tsinke."

Shatu ta fita tana fadin "Na dai gaya miki."

Amina ta tashi ta fita zuwa palon Moh'd, sai da ta tsaya a tsakar gida ta gaisa da Rabi cike da fara'a sannan ta shiga palon ta samesu zaune dukansu biyu fuskarsu kamar an aiko musu da sakon mutuwa, ta zauna tana shirin gaishesu Moh'd ya daga mata hannu hade da fadin "Ba mu bukatar gaisuwarki Amina kawai ki fada mana me kika dawo yi mana nan gidan?"

Amina ta sunkuyar da kai hade da fadin "Na dawo ne kawai Yaya...."

Kasim ya karba "Oho saida kika gama yawon iskancinki da Ibrahim din zaki dawo? To bari kiji idan har kina so zama da mu to sai dai ki dauki shegiyar yarinyarki ki maidata gun ubanta!"

Amina ta dago a tsorace tace "a'a Yaya don Allah ku rufan asiri wlh bazan iya rabuwa da 'yata ba."

Mohd yace "To kuwa zaki bar gidan nan don bazamu rike shegiya ba, dangi suzo suna nunamu, zabi ya rage naki."

Amina ta saka kuka tace "Wlh Yaya Rumaisa ba shegiya bace, karkuyi saurin yanke min hukunci..... "

Kasim yace "Kinga kar ki manna mana hauka kawai mun baki nan da 24 hrs ki zaba ko ki maida wannan shegiyar yarinyar inda kika sameta ko kuma ki tattara ta ku bar mana gida fakat!"

Nan Amina ta fusata sosai don haka ta mike ta share hawayenta ta kallesu tace "Wlh babu wanda ya isa ya rabani da 'yata kwaya daya da nakeji da ita kamar raina, don kawai na dawo shine zaku wulakantani saboda kunga iyayenmu basa raye wnn shine wasiyyar da mahaifinmu ya bar muku a kaina? A tunanina ko me zan yi a rayuwa baza ku gujeni ba kukam, amma na gode kuma in dai na amsa sunana Amina ni kuma daga yau na yanke duk wata alaka dake tsakanimu bazan sake nemanku a rayuwa ba HAR ABADA! Zanje inyi rayuwata ni ɗaya da ƴata."

Tana fadin haka ta fita cikin fushi taje ta dauko kayanta tana kuka Zuwaira ma kuka takeyi tana "Don Allah Amina ki tsaya Ku fahimci juna da Yayyenki saurin fushi yana haifar da nadama, duk kuna bukatar.......

Amina ta katseta da fadin "Aunty Zuwaira kinsan irin zuciyata sarai, wlh bazan tsaya ba kawai ki barni zanje inyi rayuwata ni kadai da 'yata har abada, na rasa iyaye ma bare su?"

Ta fita da sauri ta bar gidan tana kuka ba tare da ta san inda zata nufa ba, ko ganin gabanta bata yi ga kaya kuwa katon jaka ga goyo!

 ********************

Mama ta kalleni yayinda ta share hawayenda ya zubo mata tace "kinji dalilin zamana a kauyen can knn don bazan iya zama cikin gari dangina suna nunani ba. Bayan tafiyata Ummienku Hajiya Zuwaira bata hkr ba, ta dinga nemana, har bayan sun bar Kano sun koma Abuja anan ta dinga bama Salman da Salim labarina da yadda na ke sonsu tun suna kanana, da taimakonta dana Salman da Salim su Yaya suka sauko daga fushin da suke har sukaje kauye suka nemeni muka yafewa juna sannan suka ce suna son na dawo gidan nan da zama, ni kuma a lokacin bana son dawowa nan gidan saboda Shatu, shiyasa na amince wa Marigayi Alhaji Aminu kawai don ya dade yana son muyi aure ina kauce masa saboda ke, don bana son abinda zai taba mutuncinki RUMAISA, shiyasa ban yarda nayi aure ba, balle a kiraki agola a lokacin.
Sannan ina son ki sani na baki labarin ki ne domin hankalinki ya kwanta ki daina zargina amma ko kadan bana son tunawa da rayuwa da nayi a YOLA har yanzu, don babu wanda na tsana a duniya irin MAHAIFINKI.
RUMAISA yanzu me kika ga yafi dacewa dake zaki hkr da neman mahaifinki ne ko kuma zaki je neman nashi?"

Nima kuka nake sosai na daure na goge fuskata nace "Mama gaskia kin fuskanci abubuwa da yawa a rayuwa, amma inshaa Allah komai zai zo karshe. Ni na yanke hukuncin neman mahaifina koda kuwa bazai karbeni ba, na tabbata dangina suna sona, Mama zan tafi Yola goben nan kuma ki kwantar da hankalinki zan dawo cike da farin ciki in Allah ya yarda Kuma INNA zataji KUNYA!"

Mama ba don ranta naso ba tace "Shikenan Rumaisa, ni kuma ina miki addu'an fatan alkhairi Allah baki sa'a, amma kamin ki tafi ina son ki daure kije ki faɗawa Salman da kanki kuma ina son ki daina jin haushinshi ki masa uzuri dik abinnan da yake faruwa ba laifinshi bane. Rumaisa Salman na sonki sosai matsalar daga mahaifiyarshi ce, sai dai muci gaba da addu'a kawai."

Na goge hawaye daya sauko min na ci gaba da kallon photon mahaifina IBRAHIM AHMAD GALADIMA ( LAMIDO)
haka kawai na tsinci kaina da sakin murmushi na kalli Mama nace "Mama amma kinsan ba'ason sa ba ya miki haka ba, daga jin labarin asiri aka muku don a rabaku kuma nasan zuwa yanzu asirin nan ya karye komi karfinsa."

Mama tace "To in har hakane a tunani ya kamata ace ya neme mu zuwa yanzu kam ai ba wai nitsan wuri ba."

Jikina a mace nace "Hakane kuma amma ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita insha Allah!"

Tace "To Allah yasa."

Da haka muka kwanta gaskia ranar nayi baccin dadi don har mafarki nayi wai ina hanyar tafiya YOLA



 *
Gari na wayewa kuwa tun shidda na gama shirina tsaf cikin doguwar riga Abaya na nade gyalen tsaf sai na fito tamkar jinsin larabawa. Tea kawai nasha saboda ɗokin tafiya, nacewa Mama bari inje in sallami Ya Salman din."

Ina zuwa na gidan na hangoshi a harabar gidansu na yana goge motarsa.

Jin takuna yasaka shi juyowa sai kuwa mukayi ido hudu, nikam saida naji gabana ya fadi. Kaii Ya Salman akwai kwarjini gaskiya.
Da sauri na cire idona shikam ya shagala da kallona har ya manta mota yake gogewa.

Ina shirin karasawa wurin nashi kawai naji an bugeni da karfi babu shiri na juya, dubawan da zan yi sai naga ashe Nabila ce da wannan aikin, a hakan wai ta kawo ma Ya Salman breakfast shine fa kamar an korota tsabar rawar kai da rashin nitsuwa hmm.
Bata ma san ta bugeni ba tuni ta isa wurinsa tana kauɗi, shikam fada ya shiga yi mata yana haɗawa da filatanci kamar zai daketa duk da bajin su nake ba amma na fahimci yana fada ne akan tureni da tayi kuma bata ce min ko sannu ba.
Sai naga ta juyo jikinta a mace ta kalleni hade da fadin "Isa wadu munyal mi anda on( sannu kiyi hkr ban kula bane)"

Na gane hkr take bani tunda bajin fulatancin nake ba, don haka murmushi nayi na girgiza mata kai nace "Babu komai ya wuce."
A raina kuwa cewa nayi yanzu wnn abun ne Ya Salman ze aura? Lallai kuwa akwai aiki."

Tuni ta wuce palonsa don ta ajiye mishi abincinsa. Gabadaya binta mukayi da kallo tfy take yanzu ma babu nitsuwa har tana tuntuɓe.
Na ɗan sauke numfasa snn na karaso gabansa nace "Yaya ina kwana?"

"Lafiya lau kin gama shiryawa ne?" (Da yake dama Abuja zan je hutu kafin zuwan Yayar Ahmad Dr Surayya, dama da Yayan zamu tafi.)

Kawai sai nace mishi "Eh na shirya."

Yace "To ki ɗan je ki jirani barin inyi breakfast nayi wanka, zan tura a kiraki."

Na danyi shiru kaina a sunkuye sai kuma nace mishi "Ni ba Abuja zanje ba Adamawa zan tafi, yanzu ma tasha zani shine nazo na sallameka dama."

Zuba min ido yayi na dauka ma bazaiyi magana ba sai naji ya danyi kasa da murya yace "Wato bazaki hkr da zancan tfyr yolan nan bako?"

Shiru na masa yaci gaba da fadin "Shikenan a sauka lfy Allah ya kiyaye hanya ya kuma bada sa'a."

Nace "Amin, kuma dama so nake in rokeka duk abinda nayi maka ka yafe min......."
Na fadi hakan yayinda hawaye ya zubo kaina a sunkuye.
Shima jikinsa a mace sosai yace "Babu komai Allah ya kiyaye hanya ya tsare."
Nace "Ameen na gode."

Na juya jikina a mace kwata kwata na lura kamar fa Ya Salman har yanzu fushi yake don ya kasa sakin jiki dani mukoma kamar da.
Har na fara tfy a hankali naji kira sunan "RUMAISA!"

Ajiyar zuciya nayi na juyo da sauri muna kallon juna nace "Na'am." 
Ina sauraren jin me zaice amma shiru yayi. Sai naga ya juya yaci gaba da goge motarsa yace min "In kin fita ki rufe min get pls."

Haushi ne ya kamani har sosai amma haka na amsa mishi, sannan na fita.

 Tare da Mama muka shiga cikin gida don yiwa Abba sallama gaskia Abba baiso na tafi ba, sai dai ba yanda ya iya tunda yaga dagani har Mama muna so.
Na sallami Maman Sakina ma. Inna kam bance masu komi ba na fita kayana, tuni Mama ta saka min kayana a mota ina zuwa kawai na shiga ta ja motar sai park.
Mun sami mortar Adamawa yola mai kyau Sienna, saura mutum biyu Mama ta biya sannan ta bada number dinta.
Sai da ta tabbatar zamu tafi komi ya kammala sannan ta kalleni sai naga hawaye tuni ya cika a idonta tayi sauri ta goge tace min "Rumaisa ki kula da kanki ki kuma tsare mutuncinki kinji? Allah ya baki sa'ar haduwa da danginki lafiya, idan sun karbeki Alhamdulillah in kuma kinga da matsala, don Allah kar ki damu kanki, ki dawo gareni Rumaisa zanci gaba da baki dukkan kulawa, Bawa baya taɓa wuce ƙaddararsa kinji?"

Nima hawayen ke zubowa ina jin babu daɗi rabuwa da mahaifiyata, amma dole ce ta kama, na share hawayen nace "Inshaa Allah Mama karki damu komi zai daidaita kici gaba da min addu'a kawai."

Ta daga min kai sannan tace" Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo min dake lafiya ya tsareki da dukkan sharri."
Na kasa jurewa na fashe da kuka da kyar na iya faɗin "Amin Mama nagode."

Da kyar muka rabu don har motarmu ya tashi tana tsaye tana ta daga min hannu har motarmu ta bace.

Munyi tafiyar kusan awa daya kafin na rarrashi kaina na daina kuka.......

Wasa gaske tafiya muke tayi driver na ta sharara gudu, muna wuce garuruwa kauyuka da jeji ni dai sai kallo nake domin iyakacin nitsan tafiya ta shine cikin Kano, sai kuma Abuja.
Don haka tuni na fara gajiya da zaman motar ga yunwa kuma amma na kasa cin komai, ina ganin abokan tafiyata nata ciye ciyensu, wasu har da amai sukeyi bayan sunci abincin kamar dole.
Koda naga munyi azahar a hanya a tunani mun kusa ashe tfy kam da saura. Tabdijam sai da naga karfe hudu ta cika na kalli abokiyar tafiya ta wacce muke dan taba hira sama sama kasancewar ta mai son bacci a mota.
Nace "Yar'uwa har yanzu bamu kusa ba ne wai?"

Ta kalli agogo tace "Hmm zamu kai karfe bakwai na dare fa domin hanyar Adamawa bata da kyau tana cin lokaci sosai."
Na zaro ido nace "Subhanallah to nan din ina ne yanzu?"

Tace "Yanzu dai nan Kumo LGA na Gombe ne bamu fita Gombe bama tukunna, kuma tsakanin Gombe da Yola awa hudune." 

Kwantar da kai kawa nayi jikin seat ina lumshe ido nace "Ya Salam!"

*
Sosai driver yake sharara gudu sai gashi mun shiga hanya mai cike da gargada, sai fadawa ramuka motar keyi muna ta bigewa, tun ina daurewa amma ina har na fara korafi domin cikina sai ciwo yake tsabar jijjigar da muke sha gashi ban sababa jikina ya soma ciwo, da nasan hakane wallahi da nabi flight don inada kudi sosai a account tun wanda Ahmad ke saka min, kuma nasan tsaf zasu isheni kudin jirgi.

Matar ta kalleni tana murmushi tace "Daga gani baki saba dogon tfy ba ko?"

Nace "Koda wasa kuwa."

Tayi dariya tace "Karki damu mun kusa nan din dajin Savannah ne."

A haka dai munaji muna gani har magriba tayi mana a wata LGA na Adamawa Numan mukayi sallar magrib muka sake daukar hanya.

Mama ta kirani har sau biyu da layin Mmn Sakina don tace min wayarta ta nema bata gani ba harda kudin Jakarta saidai tana ganin kamar a tasha aka sace mata bata dai san yadda akayi ba.
Fa'iza da Sakina ma munyi waya dasu, haka Abba ma da Ya Salim sun kira ni.

Ina gyara zama sai kawai na hango 

*WELCOME TO YOLA👍🏻*




*Anan na kawo karshen Book 1 na labarin *MATAR SALMAN* *ku biyoni a book 2 akan 500 kacal domin jin yadda labarin Rumaisa zai kasance. Masoyana nagode sosai da hakurin bibiyata da kukayi, da kuma comments dinku zafafa Allah ya barmu tare ya bar soyayya, zaku samu labarin akan mahajar Arewapen. Nagode sosai*

*A karshe ina mika ta'aziyyata ga iyalan JAMILA UMAR TANKO JUT wato marubuciyar (Adon dawa, makwabtaka, Gangar jikinsa na aura, Duk kyan takalmi....) da sauran su, Allah ka gafarta mata kurakuranta kasa aljanna ta zama makoma a gareta damu baki daya 🙏🏽 Hakika munyi babbar rashi a duniyar mu ta marubuta, amma Allah yafi mu sonta😭*



➡️MATAR SALMAN BOOK 2 500 🥳

➡️*** Opay Hauwa Salihu

➡️Send evidence via ***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol