Free chapter · Read without an account

48. ...Between hope and fear...🖊️

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)





Bayan Roman ya idar da salla, ya ci gaba da zama a wurin yana karatun Alƙur'ani har zuwa lokacin da rana ta fito. Sai da ya kammala ne ya ajiye Alƙur'anin, ya miƙe yana miƙa jikinsa a hankali.

Da ya isa gaban window, hasken safiyar ya daki idanunsa, waɗanda suka yi wani irin haske mai duhun gaske. Hannunsa ya miƙa ya taɓo reshen bishiyar da ya yi kusa da window ɗin. Ya ɗan tsaya yana kallonsa kafin ya sauke ajiyar zuciya.

A hankali ya juya ya fice daga ɗakin.

Yana sauka daga stairs yana yamutsa sumar kansa, kamar wanda bai gama farkawa daga barcin da ya yi ba.

Bayan counter ya tsaya, ya buɗe cupboard ya ɗauko irin ganyen shayin da yake sha a gida. Ya haɗa shi da mint, sannan ya ɗora a wuta na tsawon mintuna biyar.

Bayan ya tsiyaye shayin, ya ƙara masa zuma, ya ɗauki kofin ya nufi balcony.

A hankali ya zauna a kan kujerar dake wurin, yana shan shayin yayin da yake sauraron kukan tsuntsayen dake shawagi a cikin bishiyoyin da suka kewaye gidan.

A wannan lokacin, komai ya yi masa shiru. Babu hayaniya, babu tambayoyi, babu wanda yake buƙatar wani abu daga gare shi.

Just him and the morning breeze.

Ya ɗan karkatar da kansa yana kallon sararin samaniya kafin ya furta a hankali.

"Alhmadulillahi,Anch'io, adesso sono libera."

(Alhmadulillahi,Ni ma, yanzu ina da 'yanci.)

Bayan ya gama shayin, ya koma kitchen. Ba tare da wani dalili na musamman ba, sai kawai ya ji yana son cin wani abu mai zaƙi.

"Tiramisu..."

Ya furta yana ɗan gyada kansa bayan wannan tunanin ya faɗo masa.

Ya buɗe fridge yana duba abubuwan da yake da su. Abin farin ciki, duk abubuwan da yake buƙata suna nan, kuma expiring date bai ƙare ba.

Ya ɗaura baƙar apron, sannan ya sanya hular masu girki.

Ya ɗora ƙaramin bowl a kan counter, ya zuba mascarpone cheese a ciki. A gefe guda kuma ya fara bugun whipping cream har sai da ya yi kauri da laushi.

Ya haɗa cream ɗin da mascarpone a hankali, yana tabbatar da cewa sun gauraya sosai kafin ya koma ga ladyfingers ɗin.

Kofin espresso mai sanyi ya jawo kusa da shi, ya riƙa tsoma biscuits ɗin a ciki cikin sauri kafin su yi laushi fiye da kima.

Yana cikin wannan aikin ne tunaninsa ya koma ga Abeedah.

A yadda take yawan tsayawa a gabansa da tambayoyinta marasa ƙarewa, sai kuma ya koma tunanin abinda ya faɗa ranar __ did he really kiss her? was she making things up? She looks like a whole package of trouble!

Ya jera tiramisu ɗin a cikin plate, sannan ya ɗauki cocoa powder ya yayyafa a saman.

Bayan ya gama, ya ɗan ja baya yana kallon abin da ya ƙera.

The arrangement was perfect.

Wani irin gamsuwa ya mamaye zuciyarsa. Bai san dalilin da ya sa ƙaramin abu irin wannan yake sa shi jin daɗi ba, amma a wannan safiyar, ya ji daɗin kasancewa shi kaɗai, yana yin abin da yake so.

ABEEDAH

Kwanaki goma na Dhul-Hijjah suka shigo, amma har zuwa lokacin ba mu sake ganin Roman ba.

Gaskiya na damu sosai da rashin ganinsa, amma mutanen gidan kamar ba su ma lura da hakan ba. Wataƙila sun saba da irin halinsa ne, ko kuma kawai ba sa ganin rashin zuwansa a matsayin wani sabon abu.

Ni kuwa, a kwanakin nan na ƙara dagewa da ibada iri-iri.

Sallar dare ba ta wuce ni, haka azumi da karatun Alƙur'ani. Sadaka ma ba ta tsaya ba. A duk lokacin da zan yi buɗa baki, sai na ɗauki lokaci mai tsawo ina addu'a, kuma a kusan kowace addu'ar, sunan Roman yana cikin abin da nake roƙon Allah a kai.

Ina son shi.

Kuma ina son ya zama nawa.

Rashin ganinsa ya ƙara sanya ni cikin damuwa, duk da cewa ina ƙoƙarin ɓoye hakan. Khalil ma a nasa ɓangaren kamar yana cikin wani irin yanayi na damuwa. Amma duk lokacin da na tambaye shi, amsarsa ɗaya ce: lafiya lau, babu abin da yake damunsa.

Zaune muke ni da Diyaam bayan sallar La'asar muna addu'a, kasancewar ranar Juma'a ce.

Na buɗe tafin hannuwana, na fara zuba duk abin da ke zuciyata cikin addu'a. Har da waɗanda na daɗe ban yi ba, waɗanda na manta da su, da kuma waɗanda na daina ambatonsu saboda ganin kamar ba za su taɓa yiwuwa ba.

A gefena, Diyaam ma tana addu'a a fili da Fulfulde. Ban fahimci abin da take faɗa ba, amma na ji daɗin yadda ta nutsu cikin addu'arta.

"Ina fatan ba cewa kike Allah kada ya amsa min addu'a ba?"

Na yi maganar da wasa, amma duk da haka idanuna suka ciko da hawaye.

Duk lokacin da nake tuno addu'o'ina na baya, waɗanda har yanzu ba su zama gaskiya ba, zuciyata tana karyewa. Sai waswasi da ƙunci su mamaye ta.

Idan ba ta kasance ba a lokacin, me zai sa ta kasance yanzu?

Wani sashe na zuciyata yake yawan maimaita min wannan tambayar.

Amma akwai wani ƙaramin sashe da har yanzu yake ƙoƙarin ba ni fata.

Ƙila yau ne. Ƙila yanzu ne lokacin da kika daɗe kina jira. Kada ki rasa wannan damar.

Na runtse idanuna.

Duk da ƙarancin ƙarfinta, na zaɓi in saurari wannan ƙaramar muryar dake ƙoƙarin riƙe min fata.

Diyaam ta buɗe idanunta, ta kalle ni ta sakar min murmushi.

"Idan nace kada addu'arki ta karɓu, ai kaina nake yi wa!"

Na gyada kai, na share hawayen da suka silalo a kumatuna.

"Meyasa kike kuka?" Ta tambaya.

Ban cika son bayyana damuwata ga mutane ba. Musamman abubuwan da suka shafi addu'ata. Amma a wannan lokacin, na kasa riƙe abin da ke zuciyata.

"Idan fa addu'a ta..." Na fara, amma muryata ta kasa ɗauka.

Na ɗaga idona zuwa sama ina ƙoƙarin mayar da numfashina daidai.

"Kamar kullum... idan ba ta faru ba..."

Muryata ta yi ƙasa sosai a kalmar ƙarshe.

Sai na share hawayena da sauri, ganin yadda take kallona.

"Na cika kuka sosai ko?"

Maganar Anaam ta faɗo min a rai.

Wataƙila tana da gaskiya.

Diyaam ta girgiza kai.

"You're not wrong for crying. Mutane da yawa suna tunanin rashin kuka shi ne jarumta. But according to psychology, crying is actually a healthy way of expressing emotions. Ba wai rashin kuka ne yake nuna ƙarfi ba."

Na sunkuyar da kai.

A ganina kuwa, mutanen da ba sa kuka su ne jarumai. Ina ma ace ni ma zan iya kasancewa kamar su.

"You're an emotional person, Abeedah. Kina jin komai har cikin zuciyarki. Shi ya sa. Akwai mutanen da za su biya kuɗi saboda su samu damar yin kuka su sauke abin da ke damunsu. Ina faɗa miki!"

Ta yi tagumi tana kallona.

Maganarta ta ba ni mamaki.

"Da gaske?"

"Eh mana."

Na ɗan yi shiru kafin na tambaye ta.

"Ke ma akwai wani abu da kike ta addu'a a kai na tsawon lokaci?"

Ta gyada kai.

"Eh."

"Ya faru?"

Ta girgiza kanta.

"Sai kallo daga nesa..."

Ta faɗa cikin wata murya mai ɗauke da wani irin yanayi, kafin ta girgiza kanta. Hakan ya ƙara tayar min da tambayar me take nufi.

"Duk da haka ban daina addu'a ba, Abeedah. A duk lokacin da wani sashe na zuciyata yake gaya min cewa ba zan taɓa samu ba, sai in ƙara ƙarfin addu'ata. Kuma na san Allah ya ji ni. Lokaci ne kawai bai yi ba."

Ta sakar min murmushi mai kyau.

Such optimism.

Ina ma ace ni ma haka nake ji a raina.

Ta ɗora hannunta a saman nawa.

"Ban san tsawon lokacin da kika ɗauka kina addu'a ko kina fatan samun abin da kike so ba. Amma ki kwantar da hankalinki. Insha Allah, Allah ba zai ba ki kunya ba. Jiran amsa ba yana nufin ba a karɓi addu'a ba, UHM?"

Na gyada kai.

Na yaba da hankalinta da kuma imaninta. Amma a lokaci guda, sai na ji kamar nawa bai kai nata ba.

Da ace nawa ya kai nata, da watakila ba zan riƙa jin irin wannan nauyin a zuciyata ba.

Da na iya yin imani ba tare da wannan tsoron da yake biye da shi ba.

Da na iya yin tawakkali ba tare da jin kamar na bar abin da nake so a baya ba.

Na haɗe fuskata da guiwa, na fashe da kuka.

Diyaam ta fara lallashina, amma a wannan lokacin na ji kamar na ƙara nutsewa cikin wani irin baƙin ciki da ban san yadda zan fito daga cikinsa ba.

Bayan mun yi sallar Isha'i da Taraweeh, na ɗauko wayata muka fara chatting da Jay D.

A gefe guda kuma, Diyaam ta ɗauko littafin sirrinta tana rubutu.

Na ajiye wayata na matsa kusa da ita a hankali, ba tare da ta lura ba. Na leƙa littafin ina ƙoƙarin karanta abin da take rubutawa.

'Sama ta yi wa yaro nisa. Wuta ba abin wasa ba ce. Na gan shi tsaye nesa da ni. Idan na ƙara taku ɗaya, zai ƙara taku dubu. Zuciyata ta ƙi sadaukar da shi. Duk wani ƙaramin mutunci da yake nuna min yana ƙara shafa gishiri ne a ciwon dake cikin raina...'

Ganin motsin mutum a bayanta ya sa Diyaam saurin rufe littafin.

Ta juya da sauri, fuskarta ta yi ja.

"W...wa... ke? Abeedah, meye haka?"

Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

"Meyasa za ki leƙa min littafi?"

Sai ga hawaye sun fara zubo mata.

Nan take gabana ya faɗi.

Juyawa ta yi min baya, kamar ba ta son ta kalle ni.

Na yi ƙoƙarin murmushi, na miƙa hannuna domin in riƙe nata.

Ta fisge hannunta da ƙarfi.

Hakan ya yi min ciwo.

Kuma na san ba ni da wani dalilin jin haushinta. Ita ce aka yi wa laifi. Amma duk da haka, sai na ji wani abu ya tokare min zuciya.

Idanuna ma suka ciko da hawaye.

Na kasa magana.

Sai sheshsheƙar kuka nake kamar wadda aka yi wa wani babban laifi.

Me zan ji zafi a kai? Ai ni na yi mata laifi.

Diyaam ta juyo da sauri, ta share hawayenta.

"Innalillahi! Wasa fa nake. Yi haƙuri..."

Amma maganarta kamar ta ƙara min abin da ya cika zuciyata. Hawayena suka ƙara kwarara, idanuna suka yi jawur.

Ta fara ƙoƙarin lallashina.

"Don Allah, ki yi haƙuri..."

Ta riƙo hannuna ta zaunar da ni a bakin gado. Ita kanta ta shiga damuwa.

Da ƙyar na samu na rage kukan, amma zuciyata ta riga ta karye.

Ba don abin da ta yi min kaɗai ba, har da tunanin yadda nake a matsayin mutum.

Ban iya ɓoye abin da nake ji.

Wasu lokutan, ko da kuwa na san da wasa aka faɗi abu, zuciyata tana ɗauka kamar an yi niyya ne.

'Ku dai bi a hankali da Abeedah, kada ta fashe muku da kuka!'

A da haka yaran ajinmu suke faɗa idan aka zauna ana hira ko wasa, ni kuma ina cikin waɗanda suke yi wa maganar.

Kowa ya san ni abu kaɗan sai in yi kuka.

Ina ma ace sun fahimci cewa ni ma ba da son raina nake yin hakan ba.

Ina ma ace zan iya hana kaina.

Diyaam ta kawo min ruwa na sha, sannan ta zauna kusa da ni.

"Ki yi haƙuri. Amma dai ban ji daɗin abin da kika yi min ba!"

Ta faɗa bayan wani ɗan lokaci.

Na sunkuyar da kai.

Wasu hawayen suka sake taruwa a idanuna. Da sauri na kai kofin bakina ina shan ruwan, ba don ina jin ƙishirwa ba, sai don bana son ta ga ina sake kuka.

Love how emotional you are? Well, I hate how emotional I am.

Wannan ce maganar da zuciyata ta ci gaba da maimaitawa, har na ji kamar zan yi mata dogon tsaki.

Autumn: Dama zuciya na jan tsaki?

Abeedah: Sosai ma kuwa. Ko da zuciyar kowa ba ta jan tsaki, ni tawa tana ja.

Autumn: Saboda taki zuciyar Ultra Pro Max ce ko?

Abeedah: A'a, Hyper Sonic ce! Mtsche***

Autumn: 🤐

"Ki yi haƙuri. Na duba miki littafi."

Na ja dogon numfashi kafin na iya furta kalaman.

Gaskiya ina jin kunyar kaina.

Meye ya kawo ni kusa da littafinta? Me ya sa na kasa barin abin da ba nawa ba?

Duniya na tsani in yi wa mutum abin da zai ɓata masa rai, ko kuma in jefa shi cikin wani yanayi na kunya. Shi ne ma dalilin da ya sa nake ƙoƙarin riƙe mutuncina a duk lokacin da na samu dama.

Amma a wannan karon, na kasa yin hakan.

"Ba komai. Ni ma ki yi haƙuri."

Ta amsa.

Na jinjina kai, sannan na wuce banɗaki.

Da zarar na shiga, na runtse idanuna, na fashe da kuka.

Ina jin kamar in sauya kaina gaba ɗaya, ko zan samu hutu daga irin wannan halin.

Na daɗe kafin na wanke fuskata na fito.

Na tarar Diyaam ta kwanta. Wataƙila ta yi barci.

Na kashe fitilar, na kwanta a gefena.

Ba da daɗewa ba barci ya ɗauke ni.

ROMAN

Yau ce ranar Arfa.

Roman ya fito daga ƙaramin gidan, ya rufe ƙofar da makulli. Ya ɗan tsaya yana kallon gidan na tsawon lokaci, kafin ya hau mashin ɗinsa ya bar wurin.

Yana sharara gudu a kan titi. Ciwon da yake fama da shi ya riga ya warke, duk da cewa bai yi wani ƙoƙari na musamman wajen neman magani ba.

A yau yana cikin wani irin yanayi na nishaɗi.

Bayan ɗan lokaci, ya isa wani wuri mai ɗauke da mutane. A hankali ya rage gudun mashin ɗin bayan ya hangi wani saurayi durƙushe a ƙasa, mahaifansa biyu kuma sun juya masa baya.

Yaron yana kuka, yana roƙonsu gafara.

Da ƙyar yake jan jikinsa, ya kai hannunsa ya riƙe ƙafar mahaifinsa.

A fusace mutumin ya juya kamar zai mare shi, amma kafin ya kai masa duka, mahaifiyar yaron ta yi saurin rungume shi.

Hakan ya hana mahaifin kai masa bugun.

Roman ya rage gudun mashin ɗinsa.

Ya ji muryar yaron yana roƙon su.

"Na tuba. Don Allah ku yafe min..."

Mahaifiyar ta shafa bayansa cikin tausayi.

"Na yafe maka, ɗana. Ban taɓa yin fushi da kai ba..."

Ganin yadda ta rungume shi ya sa mahaifin ma ya sassauta fuskarsa.

Bayan ɗan lokaci, ya matso kusa da su.

"Nima na yafe maka."

Sai shi ma ya shiga cikinsu.

Uwa, uba da ɗansu suka haɗe cikin runguma.

Roman bai san tsawon lokacin da ya ɗauka yana kallonsu ba.

Abin da ya gani kamar ƙaramin abu ne a idon wani, amma a gare shi, kamar an buɗe wani tsohon ƙofa ne da ya daɗe yana ƙoƙarin mantawa da wanzuwarta.

Ya ci gaba da tuƙin mashin ɗinsa, amma hankalinsa ya riga ya bar wurin da yake.

Sai da ya kusan karo da wata bishiya sannan ya dawo hayyacinsa.

Zuciyarsa ta yi wani irin nauyi.

Kamar an ciro ta daga ƙirjinsa an aje ta a ƙarƙashin zafin rana.

Hannayensa suka ƙara matse handle ɗin mashin ɗin, har yatsunsa suka fara yin fari.

Ya haɗiye yawu.

Bai so ya ƙara tunanin abin da ya gani ba.

Bai so ya tuna komai.

Da ƙarfi ya taka pedal ɗin mashin ɗin, ya ƙara gudu yana barin wurin.

Kamar yana ƙoƙarin tserewa daga wani abu da yake binsa.

Amma bai ankara ba sai da tayar mashin ɗin ta taka wani dutse.

A take sai ya rasa daidaitonsa.

Mashin ɗin ya faɗi a gefe, shi ma ya faɗi a ƙasa.

Ya kasance kwance yana kallon sararin samaniya.

His chest was heaving.

Bakinsa a buɗe kaɗan, yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa.

Babu wani babban rauni da ya same shi, sai ɗan ƙurji a goshinsa.

A hankali ya ɗaga hannunsa ya ɗora a saitin zuciyarsa.

"Ya Allah..."

Ya furta.

Idanunsa sun yi wani irin sanyi, suna kallon sama ba tare da wani takamaiman abu da suke nema ba.

ABEEDAH

Yau dai tun daga lokacin da na tashi nake cikin aiki, bakina kuma bai daina maimaita:

La ilaha illallahu wahdahu la sharika lah, lahul mulku wa lahul hamdu...

Ina haɗawa da sauran tasbihi da istighfari, sannan in shigar da addu'o'ina a tsakaninsu.

Kamar rayuwata ta dogara ne da hakan.

A wannan karon ina jin wani irin fata a zuciyata cewa Insha Allah, zan yi sa'a.

Na ji kamar na kusa cinye jarabawar da nake ciki. Insha Allah, sauran damuwowin da nake da su, waɗanda na faɗa da waɗanda ban taɓa faɗa wa kowa ba, duk sun kusa zuwa ƙarshe.

Da misalin ƙarfe biyar na yamma, bayan na tashi daga bacci, Diyaam ta nuna min wasu fararen ledoji guda biyu da Khalil ya kawo mana.

Da sauri na sauko daga gado muka shiga duba abin da ke ciki.

Ɗinkakkun kaya ne, laces, atamfofi da kuma wasu materials.

Gaskiya kayan sun yi kyau sosai. Daga gani ba ƙaramin kuɗi aka kashe wajen sayensu da ɗinkarsu ba.

Muka shiga dubawa.

Bayan na gama kallon kaina a madubi, na sauke ajiyar zuciya.

Amma a hankali, sai na fara jin wani irin rashin daɗi.

Na yi ƙoƙarin ɓoye abin da nake ji, musamman saboda Diyaam dake ta murna.

Wata doguwar riga mai launin light purple ta gwada.

Da ta fito gabana, bakina ya ɗan buɗe saboda mamaki.

Sosai rigar ta kamata. Ta fito da surarta yadda ya kamata.

Duk da cewa ba ta da ƙiba sosai kuma ba ta da tsawo, Allah ya yi mata wata irin halitta mai kyau.

Gata fara, kyakkyawa, da fararen idanunta masu kama da launin zuma.

Hancinta dogo, bakinta kuma ɗan ƙarami ne. Gashinta ya kai kusan mazaunanta.

Na sake kallon kaina.

I felt small and incompatible.

Ban ga wani abu da zan iya cewa na yi kama da ita ba.

Na yi ƙasa da idona da sauri, domin ba na son sake komawa ga al'adar da na daɗe ina ƙoƙarin fita daga cikinta.

Haɗa kaina da wasu ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suke raunana min zuciya.

Amma duk da haka, na kasa dainawa.

Ni ma ina son in so kaina
Ina son in yi kyau effortlessly, ba tare da na tsaya ina tunanin abin da ya rage mini ba.

Duk da cewa pimples ɗina sun ragu sosai, har yanzu akwai wasu da suke damuna. Haka nan, ina yawan kallon wasu sassan jikina ina ganin kamar ba su kai yadda nake so ba.

Sai na tuna da Diyaam, Asma'u, Jay D da Anaam.

A raina, ni ce ta ƙasa da su a komai.

Diyaam ta juyo gare ni da wani murmushi mai kyau.

"Nayi kyau?"

Na buɗe baki, amma kalma ta kasa fitowa.

Na tsaya ina kallonta, ina ƙoƙarin haɗiye wani abu da ya tokare min maƙogwaro.

Ita bata ma lura ba sai dariya take tana cigaba da wasar ta...ƙara kallon ta nayi.. naji wani irin abu kamar kishi...zaro ido nayi da sauri na miƙe na matsa inda take na rungume ta...ina ta ƙoƙarin haɗiye kukan dake taso min...taya zanyi kishi da abinda ba ita taba kanta ba?

'' kinyi kyau kamar ba yar Nigeria ba...'' Dariya ta saki itama ta rungume ni '' waih na ɗauka banyi kyau ba..'' sai taja baya.


"Amma dai ba zan iya saka waɗannan kayan ba. Sun matse ni sosai."

Ta faɗa tana buɗe zip ɗin.

Daga nan ta ɗauko tawa rigar ta jefa min.

"Kema ki gwada taki mu gani."

Na ji kamar ƙasa ta juya min.

Me zai sa in gwada rigar, alhali kuwa tun kafin in saka ta, na riga na san abin da zan gani?

"A'a..."

"Uhm-mm. Sai kin gwada, Abeedah."

Ta ɗora rigar a kafadata, ta tura ni cikin banɗaki, sannan ta rufe ƙofar.

Da zarar na samu kaina ni kaɗai, sai na zauna na haɗa kaina da guiwa.

Na fara kuka a hankali.

Ɗazu fa na tabbatar addu'o'ina sun karɓu. Amma yanzu fa?

Waswasi ya sake mamaye zuciyata.

Yaya zan yi?

A duk lokacin da na fara yarda cewa komai ya zo ƙarshe, sai in ga kamar ashe ba haka ba ne.

Na miƙe a hankali na ɗauki sabulu, na fara shafawa a fuskata.

Sai kawai na saki wani irin ihu.

Diyaam ta shigo da sauri.

"Meye ya faru?"

Na ɗaga fuskata, ina ƙoƙarin haɗiye kukan.

"Diyaam... sab...ulu ya shiga... min cikin ido."

Baiwar Allah ta ruɗe.

Ta ɗauko towel tana share min fuska, tana hura min ido domin na daina jin zafi.

"Subhanallah! Ki buɗe idon mana. Yana ciwo ne?"

Ta tambaya cike da damuwa.

Na gyada kai, ina ƙoƙarin ɓoye ainihin dalilin hawayena.

Da wannan na fake.

Ba zan iya gaya mata cewa ba sabulun ne ya sa nake kuka ba.

Ko bayan ta gama hura min idon, muka fito daga banɗakin, kukan bai tsaya ba.

Ta ci gaba da lallashina tana ƙoƙarin ganin abin da zai sa na samu nutsuwa.

Sai da na yi kuka mai yawa, na gaji sosai, sannan na kwanta.

Ba da daɗewa ba, bacci ya sake ɗauke ni.



Drop your comments like and share ..


((★Wa'yanda ke tambayar complete yanzu nake rubuta littafin

★Wa'yanda ke tambayar account number gashi nan a ƙasa don't come to my DM asking for it pls🙏

★idan banyi replying message ɗin mutum a Whatsapp ba pls banda kira send SMS...

★If you're not buying the book don't come
 to my DM pls...

★Wayanda ke tambaya daga farko akwai shi a cikin links ɗin nan don't come to my DM


★Wa'yanda ke son yin comment zasu iya tafiya a shafina na Arewa pen suyi a can or you can get into the group..or Mi DM))



🌹 ❤️📖✨



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin ***..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️
























Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol