Free chapter · Read without an account
49. ... He came...🖊️
49. ... He came...🖊️
Sai da aka sha ruwa Diyaam ta tayar dani,idona sun kunbura sunyi luhu luhu,na shiga baye na wanke fuskata na fito nasa hijab muka tafi kitchen..mutanen gidan dukansu suna zaune a dining suna shan ruwa,kowa da farin ciki a fuskarshi.. kitchen nida Diyaam muka tsaya muka karya namu azumin sannan muka nufi É—akin Khalil danyi mashi godiya amma bai nan, muka wuce É—akin mu daidai wayata na ringing da sauri na isa na É—auka... muryar Mama ta fito daga É—ayan gefen
Zama nayi bakin gado nayi ƙasa da kaina wasu sabbin hawayen suka ciko idona,da ƙyar na samu ina magana lafiya lau,duk da haka sai tambaya take in lafiya lau...
'' zaki zo gobe?" Ta tambaya.. girgiza kaina nayi kamar tana ganina '' wai ba zamu iya ɗaukar Hutu ba tunda gobe ba ƙarshen wata bane!" na faɗa da baƙin ciki
'' ba komai kiyi zamanki kawai..''
'' toh..'' na amsa tareda share hawayen daya zubo
'' Asma'u ta faÉ—a maki ta rubuta jamb?" zama da kyau nayi ido wajen nace
'' yaushe?"
'' oh baki sani ba kenan? Tun da aka fara sayarda foam...muma ganinta kawai mukayi da result taci duka makin!" S
Fafe zuciya ta nayi..ni ko a mafarki nasan abune da bazan taɓa iya yiba...
'' ina Asma'un?" Na tambaya murya ƙasa..
'' hello gani!" Muryar Asma'u ta sauka a kunnena..'' Congratulations,shine baki faÉ—a min ba mun rubuta tare...''
'' kwantar da hankalin ki,sani nayi saikin sake maimaita waec da neco ɗinki shine yasa!" Ta ƙarashe da dariya.. gabana yayi mummunan faɗuwa...ƙirjina ya fara sama da ƙasa.idona yayi zafi haka ma iskan dake fitowa daga ciki.
'' ba'a son wulaƙanci...ƙila make zaki sake maimaita jarabawar ki!'' Anaam ta fisge wayar daga hannun Asma'u
'' ke kada ki damu da abinda ta faÉ—a insha Allah babu wanda zai maimaita komai cikin mu! Ina fatan ba kuka kike ba...'' tayi tambayar kamar wata uwata
'' a'a!'' na furta da ƙyar.. zuciya ta kamar zata fashe...
Inna sarai ta karɓi wayar tana min magana,sosai nake a matse suyi su gama in fara abinda na saba...
Sai da muka É—auki lokaci mai tsawo muna magana batare da sun fahimci kuka nake ba sannan muka yi sallama..
muka haÉ—a ido da Diyaam bata cemin komai ba..and I was grateful to her for that..
Bayan mun gama sallah na tafi lambu na zauna cikin furanni ni kaɗai ina ta sharɓar kuka,a raina ina ji inama ace zan yi doguwar suma idan na farka duk wani abu dake damuna ya ɓace wanda nake so ya faru ko kuma dai in manta da duk wani abu dana taɓa so...
Nasan mutane zasu ga kamar ai duk wannan abun da nake kuka akai bai kai ya kawo ba, amma babu wanda ke iya fahimtar yanda ake ji sai wanda ke a wannan yanayin..bazaka san yanda ake jiba sanda ka rasa natsuwa da kwanciyar hankali..a koda yaushe kake cikin fargaba da waswasi.farin cikin ka, kwanciyar hankalin ka,natsuwar ka da darajar ka ta ta'allaƙa da wannan abu...
Kuma sai ya kasance ka kasa samun wannan abun,ka kasa barin abun...kuma koda yaushe kana cikin ƙunci, baƙin ciki da damuwa saboda rashin samun wannan abun..ni Abeedah ba sau ɗaya ba nayi ƙoƙarin barin shi,nayi ƙoƙarin rayuwa batareda cikar buri ba amma na kasa...saboda na daɗe ina addu'a akai..na daɗe ina son wannan abu..na daɗe ina saka efforts da lokaci da komai nawa dan cikar burin nawa...taya zaka ji idan ka daɗe kana gina abu na tsawon shekaru da daɗi ba daɗi sai wani yazo yace ka bar abun nan?
Musamman idan wannan abun samun shi shine cikar burin ka, farin ciki, nutsuwa da jin daÉ—in ka?
Na tsoma kaina a cikin burina sosai da har nake ji idan ban samu ba to ba zan taɓa zama daidai ba,bazan taɓa warkewa daga karayar zuciyar da hakan zai haifar ba...bazan taɓa cigaba da farin ciki ba... efforts ɗina da addu'oina na tsawon shekaru shida...bazan iya barin su sutafi a banza ba...nasan da cewa ba laifi idan mutum ya nemi cika burin shi..ko yake fatan samun wani abu,amma hakan kawai na zama matsala idan ka bari ka rasa kanka wurin neman wannan abun...wanda ni Abeedah na shiga a wannan sahun...na neman inyi kyau...halittar jikina ta canja,a soni,a yaba mani,a damu dani,in zama irin matan novel koma fiye da haka.
wannan dogon burine wanda wurin neman wa'yannan abubuwan na rasa kaina,na rasa farin cikina, baƙin ciki,damuwa da rashin hutun rai sun zama wani babban jigo a rayuwata...har na dena ganin abubuwan da nake dasu... ni'imar da Allah yayi min...abun da idona da zuciya ta kawai suke iya gani shine... addu'oin da nake jira su zama domin in cigaba da farin ciki amma har yanzu sun kasa gano hanyar su zuwa inda nake....sai binsu nake suma suna guduwa a guje...
Kamar yanda na faɗa...a rayuwa ta babu fari,sai baƙi da ruwan toka...ina matuƙar tsoron kasancewa ni kaɗai ko in cigaba da rayuwa cikin rashin so da ƙauna...ko in rasa farin ciki da walwala ta har abada ...
''ya Allah... nayi Ad...du'ar da sadaƙar da komai na tsawon ....shekaru meyasa baka amsa min ba? meyasa ....nake ganin mutane... suna samun amsar addu'ar su banda ni? Ya zanyiiii" Nayi maganar a rarrabe tare da kife kaina a ƙasa ina risgar kuka...ina ji ina ma ace mutum zai iya koke duk wani baƙin cikin shi...wani sashe na zuciyata na faɗin' gobe bazata kasance ta daban da sauran ranakun ba,baƙin cikin nan dashi zaki tashi..'
Na daɗe a wurin ina kuka kafin nayi shiru sai ajiyar zuciya...can na miƙe na isa bakin bangon glass ɗin wurin ina hango harabar gidan..daren yayi tsit...inama ace kawai inga wani alama cewa Allah ya karɓi addu'a ta koda a mafarki ne...sai dai ni ɗin bani da ƙwaƙwalwar fahimta ai..taune lips ɗina nayi hawaye suka ciko idona...ƙarshen hijab ɗina nasa na goge hawayen...
Bayan minti shabiyar har lokacin ina nan tsaye a wurin flowers ɗin kafin na juyo na tsinki rose baƙa na fita daga wurin zuwa roof top...ina fata a cikin zuciya ta ace Roman zai dawo kafin gobe..amma nasan wannan kawai..is a wishful thinking...
Ban daɗe da tsayuwa a wurin ba ina juya rose ɗin a hannu na, iska mai sanyi na dukan fuskata..bugun zuciyata ya sauya... vertiver scent ya daki ƙofofin hancina..kafin na fara jiyo quiet footsteps...a wani irin slow na juyo idona suka sauka akan shi,saye yake da farar riga ya ɗaura baƙar jacket a sama, hannayen shi soke cikin aljihun baƙin wandon shi fararen ƙafafunshi saye da slippers baƙaƙe...gashin shi ya ƙara tsawo har saman kafaɗarshi yana ta bin iska...fuskarshi na kallon wani gefe...fatarshi ta ƙara fari sosai...
Ɗauke idona nayi zuciyata na cigaba da bugu da ƙarfi musamman dana ji yana tunkaro inda nake...ya ganni?
Juyawa na sake yi idon mu ya haɗu...ɗauke idonshi yayi fuskar shi a ɗaure...wani gefen can ya nufa ya tsaya... kallon shi nayi nima ina so inyi tsaye a nawa wurin amma zuciya ta takasa daurewa,ƙafafuna suka jani har inda yake tsaye...na danne kukan dake ƙirjina da murmushi nace '' ya kake?" Share ni yayi kamar bai san da akwai ni wurin ba..nayi ƙasa da idona da suka ciko
'' fine..'' naji amsar shi a bazata...oh..wannan plaster dake goshin shi fa?
'' kayi kewata?" Tambayar ta fito daga bakina ba shiri...kallona yayi ya ƙanƙantar da idonshi ya faɗi wani abu da italian..
''.toh ai ban jin Yaren ku!amma nasan abunda ka faɗa" Na zaro ido,yake kallona fuskarshi a sake kamar yana jira yaji abinda zan ce,na ɗan ƙara matsowa sai na mashi alama daya kawo kunnen shi kusa
duƙowa yayi na share gashin sa gefe baki na saitin kunnen shi
'' cewa kayi nayi kewar ki sosai Abeedah kamar inci kaina...shine yasa na tarkato na dawo!" Ja baya yayi kunnen shi yayi ja kaÉ—an.
sai nayi tsalle kamar wacce ta lashe wani gagarumin abu, har ina kusa faÉ—awa jikin shi yayi saurin matsar dani cike da farin ciki nace
'' wallahi na faÉ—a dai dai...''
'' strana(weird)"
'' nifa bana jin taliya..'' na É—an tsuke fuska
'' I'm glad!" Ya furta tare da É—auke idonshi daga kallona
Tsalle nayi na taɓo gashin shi dan yafini tsawo sosai...bana tsammanin zan cimma ƙirjinshi...harara ta yayi yace
'' yanzu da babu painting you're targeting my hair ?" expression É—in dake fuskarshi yaban dariya...sai dana dara,ya share ni ya cigaba da gyara gashin shi
'' Italy ka koma ne?"
'' miss me?" yayi ƙwafa ya juya zai bar wurin
'' nayi kewar ka sosai.'' da sauri na rufe baki na dan maganar suɓucewa tayi,sai so nake in ɗago in kalle shi sai dai na kasa yin hakan
'' wai kasan sunana?" Na canja topic É—in cike da kunyar abinda na faÉ—a, ..shi kamar ma baiji abinda na faÉ—a É—in ba
'' UHM...'' ya ban amsa
'' TOH me yasa baka taɓa kira ba? Oh ashe ka kira sau ɗaya!'' ƙifta idonshi yayi alamun bai yarda ba
'' haka kace Fuuuck Abeedah!" Zaro ido yayi tareda rufe bakin shi
'' waya koya maki wannan kalmar?" ya sauke hannun shi a hankali
'' kai mana!" Na turo baki,wani kallo yayi min daga sama har ƙasa batareda yace komai ba.
'' yanzu ka kira sunan inji!" na matso kusa dashi amma bai kulani ba. hawayena da suka sauka a hannun shi yasa ya juyo yana Kallona utterly dumbfounded
'' kuka kike?"
'' ban sani ba,dariya nake!" Na amsa da takaici...yana ta kallona yana ƙifta ido
Sai kuma ya kalli ƙofar shigowa wurin '' ki Dena kuka kada a ɗauka na maki wani abu fa...'' nikam sai na ƙara ɓare baki ina kuka kamar ya yimin wani abun
ya sosa ƙeyarshi yana rarrabar ido kamar mara gaskiya...can ya zaro chocolate daga wandon shi '' here.. have this I'm sorry..''
Lokaci guda hawayen suka tsaya...na kalle shi da mamaki...wai shine yake ban haƙuri harda chocolate...kamar zanyi murmushi amma sai na dake...na karɓi chocolate ɗin kafin ya canja ra'ayi...ban koce na gode ba...ya mayarda hannun shi cikin aljihu yana kallon chocolate ɗin '' ko in baka abunka?" yayi ƙwafa zaice wani abu sai kuma '' forget it!" Na ɗage kafaɗa na buɗe chocolate ɗin..wannan na daban ne da wanda yaba Diyaam.. murmushi nayi kamar ba nice na gama kuka yanzu ba na fara shan chocolate ɗin..yana ta kallona kamar yaga sabuwar halitta... expression ɗin fuskar shi was unreadable
''kada ki damu da abinda mutane zasu faÉ—a akan ki...zasu iya amfani da wannan su cutar dake...'' ya kauda kanshi yana kallon nesa...lips É—insa kamar an manne da super glue...sai kuma ya juya yabar wurin...tafiyar shi ta haifar da rami a zuciya ta kamar in jawo shi mu cigaba da tsayuwa...
'' Roman!" Na kira bayan ya kusa fita zuciya har kunnena...dakatawa yayi batareda ya juyo ba '' na gode!" GyaÉ—a kai yayi ya cigaba da tafiya na sake faÉ—in
'' Barka da Sallah in Advantage..'' yanzu kam sai da ya juyo ya kalleni sai ya girgiza kanshi slowly yace
'' Barka da Sallah in Advance!"
'' thank you!" Nayi murmushi
'' i was correcting you!" Ya ɓata fuska
'' hhh..koma meye ai ka faÉ—a!" girgiza kanshi yayi ya fita...na rage ni kaÉ—ai a wurin...
Washegari sallah kowa da kowa ya ɗau wanka an shirya za'a tafi masallaci...da ƙyar na shirya cikin wata abaya baƙa nasa hijabi rabin guiwa shima baƙi banko shafa mai ba...muka fito tare da Diyaam da tasa farar abaya idan ka kalleta dole ka sake kallonta...nayi ƙasa da idona zuciya ta ƙuntace muka fito anan parlor'n ƙasa ma kowa ya shirya...sai ɗaukar hotona suke suna farin ciki da yima juna Barka da Sallah...
Yan matan suma ba'a baya ba...kowa yayi kyau iya kyau banda ni...nice nayi ta daban...kowa sai kallon mu yake...suna banko mana kallon tsana...amma dai nafi zaton tsanar Diyaam da sukayi saboda tafi su kyau ne,ni kam ban san dalilin su na kallona a haka ba .tunda dai sun fini kyau da komai nesa ba kusa ba
'' ji ƙirjinta kamar an shafe allo..'' Seraphina ta raɗawa Khaleesat a kunne
'' fuskarta kamar mai chickenpox...'' dariya waya'nda ke wurin suka saka...da sauri nasa hannu na a gaban hijabi na...hawayen da nake ƙoƙari kada su zuba suka cika idona
'' ni wallahi da nice ita ko fitowa baxanyi ba...haba... looking at her could hurt my eyes...'' kasa cigaba da tafiya nayi
Diyaam tayi ƙasa da kanta...
Gaba ɗaya idonsu ke yawo akan mu... juyawa nayi da gudu na hau stairs hawaye suka rufe ganina har na iso 3rd floor ina jiyo dariyar su daga bayana..naci karo da Farzan da shima yaci uban wanka sai ƙamshi yake
'' Queen of tears..MEYA faru kuma?" Ya kalle ni sama da ƙasa...ƙwace jikina nayi na shige ɗakin mu tare da banko ƙofa...na wurgar da hijabina tare da jan gashina kamar zan ɓaɓɓake shi daga matsirar shi...na fashe da matsanancin kuka
Kamar zan haukace..naji kamar in sa abu in dinga kankare fata ta ko zanji sauƙin wutar dake ci a zuciya ta
'' WHYYYYYY!!!!!!!" na faɗi a ƙasa ina birgima ina dukan ƙasar da hannu na cigaba da kurma ihu kamar wacce akayi ma wani abu...
kamar rayuwata tazo ƙarshe..can na tsagaita na tashi na isa bakin taga na hango su suna tafiya zuwa garage..kowa yana tafiya lafiya Lau.. gashi kayan yan matan sun fito da shape ɗinsu mai kyau...they walk confidently kamar sune da ƙasar babu wanda kejin shi a takure...
Sai gunjin kuka nake..hannuna damƙe da labule.. unfortunately for me,baxan taɓa kasancewa ɗaya daga cikinsu ba...wannan confidence ɗin...mafarkine da bazai taɓa faruwa dani ba...
sakin labulen nayi jiki a mace na koma na kwanta ƙasa na naɗe wuri guda...idona sunyi mahaukacin ja...zuciya ta kamar ana hura wuta a ciki...
Ɗakin ya koma min ƙarami duk da girman shi..naji komai ya fita daga raina...
Wurin ƙarfe tara naji an turo ƙofar ɗakin,ƙamshin turaren Khalil ya cika hancina kafin ya duƙa kusa dani daga baya
'' Oh...Kitten!" Ya kira a tausashe muryar shi É—auke da damuwa...ina jinshi amma ban motsa ba..bana ra'ayi..ko magana bana son yi...