Free chapter · Read without an account

CHAPTER 46.

by HAERMEEBRAERH✍️✨ · ZAWARA.

ZAWARA.











NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ 












PAGE 46.







Washegari da safe yanda Nasibah ta ji labarin daren farko a wajen Nawwarah tun suna makaranta sai ta ga ashe abun ba haka bane,da kanta ta tashi ta shiga banɗaki ta gyara jikinta sannan ta yi wankan tsarki ta fito. Duk wannan motsin da ta dinga yi Samir bai motsa ba,baccinsa yake ta sha kamar wanda ya sha wata ƙwayar. Sai da Nasibah ta gama shiryawa sannan ta tashe shi dan yayi wanka yayi sallar asuba da basu samu damar yi akan lokaci ba. 

Juyi Samir yayi yana bin Nasibah da wani irin kallon da ya sanya ta jin kunyarsa ta ruga da gudu ta bar masa ɗakin,murmushi ya saki yana tuna yanda daren nasu ya kasance,dare ne da ya shiga cikin tarihin rayuwarsa wanda ba zai taɓa mantawa da shi ba. A wannan daren ya tabbatar da cewa lallai mata suna suka tara. A da ya zaci ba zai taɓa samun mace budurwa dal a leda ba kamar yanda ya samu Munirah,sai gashi ya sake samun Nasibah a matsayin budurwa mai cikakkiyar ni'imar da ta zarta Munirah. Kalmar Lucky bastard da Nuh ke yawan kiransa da ita ta tabbata a kansa. Murmushi ya sake saki a karo na babu adadi ya miƙe a hankali ya isa gaban drawer ɗinsa ya fito da abokiyar nishaɗinsa ya ɓalle bakin gwangwanin ya kafa kai ya sha sannan ya mayar ya kulle,ajiyewa yayi a can ƙasan ƙananan boxers ɗinsa sannan ya faɗa bathroom,brush ya fara yi kafin yayi wanka ya ƙarashe da na tsarki ya fito ɗaure da towel; yana jin kansa yana yi masa wani irin nauyi. Da ƙyar ya shirya ya gabatar da sallah,sannan ya fita zuwa ƙasa dan ya samu abinda ya saka a cikinsa. Nasibah na kallonsa ta ji gabanta ya faɗi domin idanuwansa sun bayyana alamun maye a tattare da shi. Ɗaure fuska ta yi ta bar wajen dinning table ɗin ta haye sama da sauri ta shige ɗakinta ta kulle. Wayarta ta ɗakko ta kira Yasmin, ringing ta dinga yi amma bata amsa ba,sai ta tuna ashe fa safiya ne maybe tana makaranta. Wurgi ta yi da wayar ta dafe kanta tana neman wanda za ta tattauna damuwarta da shi. Kwantawa ta yi a bakin gadon hawaye na zuba ta gefen idanuwanta. A haka baccin gajiyar da Samir ya tara mata a daren jiya ya ɗauke ta.

A ɓangaren Samir kuwa sam bai yi tunanin Nasibah ta fuskanci halin da yake ciki ba,dan haka yana gama karyawa ya fita wajen Hajjah domin ya gaishe ta,yana zuwa ɗakinta ya tarar bata nan,ko da ya fito sai ya tarar da Sameerah da Sakeenah suna karyawa,kallo ɗaya Sameerah ta yi masa ta kawar da kanta tana cin magani,shima bai bi ta kanta ba sai ya amsa gaisuwar Sakeenah ya ce mata.

"Ina Hajjah?"

"Ta fita office,ta ce a sanar da kai idan ka tashi ka je office ɗinta akwai wasu takardu da ake buƙatar saka hannunka."

"Ok."

Samir ya ce ya ɗauki apple ɗaya ya bar parlourn. Kai tsaye motarsa ya nufa ya shige tare da tayar da ita ya kunna kiɗa zai je kiran Hajjah. Yana fita daga gidan Nuh ya kira shi a waya,Samir na ɗauka sai ya fashe da dariya ya ce.

"Maaaannn you need to get married oooo,kai ka san irin ni'imar dake cikin aure kuwa?"

Tsaki Nuh ya ja a hankali ta yana jin ransa na ƙuna,a zahiri sai ya fashe da dariya ya ce.

'Aure ai naku ne Dr. Mu kam muna nan da ƙadangarun bariki muna shan iska,sai mun gama ɗanɗana kowacce kankana sannan zamu zaɓi ta shukawa.'

Dariya suka fashe da ita Samir ya ce.

"Ka san Allah tun jiya da safe nake kiran kaina da sunan da ka laƙaba min."

'Wanne suna kenan?'

"Lucky bastard mana,da idan ka faɗa ji nake yi kamar na shaƙe ka,amma a daren jiya na tabbatar da cewa ni mai sana'a ne a duniya. Nasibah ta yi a rayuwa nake faɗa maka,yarinyar nan Kaiii ba za ka gane ba,amma dole ne na baka shawara a matsayinka na abokina,kai ma ka je ka lallaɓa ka samo ƴar shila irin Nasibah ka aure."

Zama Nuh ya gyara kafin ya ce.

'Kuma ka san a wajen dinner na ga wata ƙawarta me shegen rawar kai,na so na ɗan latsa na ji ko da jini sai ban sake ganin yarinyar ba.'

"Yaya take? Kwatanta min ita ko zan gane ta."

'Tana nan wata siririya amma tana da faɗin ƙugu sosai,tana da haske amma ba sosai ba,ta saka attachment."

"Tabɗijam! Wai Nawwarah kake nufi? Ni fa duk a ƙawayen Nasibah na tsani yarinyar nan,ita kanta Nasibah na kula ba wani sosai take mutunci da ita ba coz yarinyar akwai hassadar masifa."

Murmushi Nuh yayi ya ce.

'Ni kuma ita ce zaɓi na,don Allah ka yi min hanya mana a wajen Madame na gana da ita.'

"Ok,dama bahaushe ya ce daidan wani karkataccen wani,zan yi mata magana,na iso wajen Hajjah za mu yi waya later."

'Ok Man,ka gaishe ta.'

"Alright."

Da haka Samir ya ƙarasa shiga kamfanin nasu ya samu waje ya ajiye motarsa,yana shiga ma'aikatan wajen da suka san shi sai suka hau gaishe shi,har cikin office wani dattijo ya raka shi suna ta hira da Samir ɗin. Ko da ya shiga office ɗin Hajjah sai ta kawo masa takardun da take buƙatar saka hannunsa saboda fitar da wasu manyan kuɗaɗe dan cigaban kamfanin nasu,ko amsa gaisuwarsa bata yi ba saboda fushin da take yi da shi. Haka ya gama saka hannun ya fita ba tare da ya bata haƙuri ko ya lallashe ta ba. Wannan abun da yayi ya sake rura wutar ƙiyayyar Nasibah a cikin ranta. 

Samir kuwa yana barin kamfaninsu sai ya wuce asibitinsa ya duba marasa lafiyan da ya kamata ya duba,sai dai yanayin da yake ciki bai bashi damar yi wa kowa aiki ba,sai ya tura takardun da ke gabansa zuwa ɗaya office ɗin likitan dake yin komai idan baya nan. Ya jima a cikin asibitin nasa kafin ya warware ya fito ya nufi super market,siyayya yayi mai yawa dangin kayan abinci da kuma na maƙulashe ya nufi gidan Makaɗi. Jakar kayan maƙulashen ya ɗauka ya shiga har cikin gidan. A bakin ƙofar parlour ya tsaya yayi sallama,Najlah dake wasa a ƙofar parlour ita ce ta fara ganinsa,da gudu ta je wajensa tana murna tare da tambayar sa Nasibah. Murmushi ya sakar mata ya ce.

"Tana can gida lafiya,ita ce ma ta ce na zo na ɗauke ku ke da Faihah da Yah Rabi da Yah Usman na kai mata ku. Na so na zo tun ɗazu to aiki ne ya riƙe ni."

Ihun murna Najlah ta kurma tana sanar da dika mutanen gidan abinda Samir ya faɗa,ledar hannunsa ya ajiye a parlourn ya ɗauke ta yana dariya,babu jimawa su Mama suka fito parlour suka zauna suka gaisa da Samir cikin mutunci da mutunta juna,kansa a ƙasa yake gaishe su saboda mutuncinsu da ya ƙaru a idanuwansa. Suna tsaka da hira Usman ya dawo daga shago inda yake taya Makaɗi zama. Lokacin da ya ji za su je wajen Nasibah sai shima ya hau murna kamar ƙaramin yaro. Da gudu ya shiga ɗakinsa ya watsa ruwa tare da sauya kaya ya fesa turare. Ba tare da sun nemi izinin Makaɗi ba suka shiga motar Samir suka nufi gidan Hajjah Barirah.

A hanya Rabi ta so ta sanar da Yasmin da ta damu da rashin ganin Nasibah,idan ya so sai ta roƙi Samir ya biya su ɗakkota su je tare,sai ta fasa saboda tana ganin kamar idan ta yi hakan Samir zai ga ta yi masa gayya. Lokacin da suka isa gidan sai Samir yayi horn Lawi ya buɗe masa gate. Kai tsaye ya shige da motarsa ciki ya ajiye ta a wajen da yake parking ya buɗe wa su Rabi suka firfito,kayan da ya siyo suka taya shi ɗauka suka shiga cikin gidan su Faihah na ta santin gidan tare da murna. Sameerah na zaune a parlour tana mommotsa hannunta da har a wannan lokacin yake yi mata ciwo ta ji hayaniyar yara. Da sauri ta ɗaga kanta ta ga yara masu kama sak da Nasibah,murmushin takaici ta yi sannan a ce.

"Ahaf! Ai na sani,yanzu za ka yi ta ganin dangin matsiyata suna zuwa cin arziƙi da sunan sun zo ganin ƴar'uwarsu."

Rabi da Usman da suka fahimci abinda ta ce sai suka yi banza da ita suka shige inda Samir ya shiga. A parlour ya tarar da Nasibah kwance tana latsa wayarta. Sallamarsa da ihun su Faihah yayi daidai da tashinta zaune,a guje yaran suka isa wajenta suka rungume ta,Yah Rabi da Usman na shiga ta yi watsi da su Faihah ta nufi Yah Rabi ta faɗa jikinta ta fashe da kukan murna. Itama Yah Rabi ƙwalla ce ta taru a idanuwanta,da ƙyar ta daure ta ce.

"Meye haka yanzu za ki saka ni kuka daga zuwa na?"

"Ai kukan farinciki ne Yah Rabina. Na yi kewarki sosai,Yah Usman na yi kewarka."

Nasibah ta bashi hannu suka tafa sannan suka ɗunguma suka zauna a kujera. Murmushi Samir ya dinga dokawa saboda ya ji daɗin ganin fara'a a saman fuskar Nasibah. Itama murmushin ta yi masa daga ƙarshe ta aika masa da hararar wasa tare da gargaɗi da ido. Kai ya ɗaga ya motsa laɓɓansa ya ce.

"I am sorry babe."

Kanta ta juyar ta ce da Yah Rabi.

"Yah Rabi Yasmin na zuwa gida kuwa tinda na tafi?"

"Ohh Nasibah dika-dika gobe ne fa zaki cika sati ɗaya cif a gidan nan,amma shine kike tunanin Yasmin ta je gida ko bata je ba."

"Ina kewarta ne sosai Yah Rabi. Su Nawwarah uwar kaɗaɗi fa? Ina Nadiya? Wayyooo ina su Ummah da Mama da Baba?"

"Sai yanzu kika tuna da su? Ai na zaci ƙawayen naki dai kika fi so."

Usman ya faɗa yana mai gyara zamansa. Suna nan zaune Samir ya kawo wa su Rabi juice da cups da kansa,ba su Yah Rabi ba hatta Nasibah sai da ta ji kunya. Da sauri ta miƙe ta karɓa ta ajiye a gabansu tana faɗin.

"Kaii Yah Samir,so kake yi Yah Rabi ta je ta sanar da Baba ya biyo dare ya yanke min kai ko?"

Dariya suka fashe da ita gaba ɗayansu. Zama Samir yayi a cikinsu suka taɓa hira kafin daga ƙarshe ya shige ɗaki ya kwanta. Sosai Yah Rabi ta dinga mamakin sauƙin kai irin na Samir,wanda a baya kaf unguwar ta ɗauka ɗan gidan marigayi Alhaji Yusha'u Gwamnati ɗan girman kai ne,sai gashi haɗuwarsu da Samir ɗin sun ga saɓanin abinda mutane ke faɗa akansa. Yamma na yi Yah Rabi ta taya Nasibah suka yi girkin dare,sai da suka yi sallar Isha'i sannan Samir ya ce su shirya ya mayar da su gida. Ɗaki Nasibah ta shiga ta buɗe lefenta ta ɗaukar musu abubuwan da ta san zai yi musu amfani,Usman kuma ta bashi turare sannan ta ba wa Yah Rabi dubu goma ta ce ta kai wa su Mama. Mita ta dinga yi wa Yah Rabi da ta ƙi biye wa su Usman ta hau sama ta ga ɗakin Nasibah,a cewarta kada Samir ya ganta ya ga rashin dacewar hakan,Usman da su Faihah kuwa babu inda basu leƙa ba sai ɗakin da Samir yake ciki. Mayafi Nasibah ta saka suka fito tare za ta raka su. Suna shiga parlourn Hajjah sai suka tarar da su gaba ɗaya suna hira, ganin Nasibah da ƴan'uwanta sai ya sanya su Hajjah yin shiru suka bi su da kallo. Yah Rabi da su Najlah har ƙasa suka durƙusa suka gaishe da Hajjah. Ko kallo basu ishe ta ba ballantana ta amsa gaisuwarsu,Sakeenah ce ta amsa musu sannan ta ƙara da tambayar sunayensu,bayan sun bata amsa sai ta miƙe tsaye ta raka su har bakin mota,bayan sun shiga Samir ya ja motar sai Nasibah da Sakeenah suka juya za su koma cikin gida. A hanya Sakeenah ta tsayar da Nasibah ta ce.

"Jiya na samu labarin abinda ya faru a tsakaninki da su Hajjah,ina so na baki shawara dan ni gobe da safe zan tafi Qatar karatu,kin ga ba lallai ne na san abubuwan da za su dinga faruwa a gidan nan ba,ina so ki jajirce wajen yi wa Hajjah biyayya,bar ganin Yah Samir yana son ki a zuciyarsa soyayyar Hajjah ta daban ce,dan haka ki kula sosai,kada ki saki jiki da duk abinda yake faruwa a yanzu,Hajjah da Sameerah ba mutane bane da suke da daɗin sha'ani;musamman idan suka nuna mutum a matsayin maƙiyinsu."

Murmushi Nasibah ta yi kafin ta ce.

"Kada ki ji komai ƴar'uwa,ni ɗin nan da kike ji da gani warki ce daidai ƙugun kowa."

Hannu Sakeenah ta ɗaga ta rausayar da kai ta ce.

"Okk ooo,kar ki ce ban gargaɗe ki ba ki yi zaton bana son ki. I love you Nasibah a matsayinki na matar Yah Samir,ni ban ma taɓa ganin mutumin da ya shiga raina a lokaci ɗaya ba sama da ke,duk sun san halayyata bana shiga sabgar kowa,ba kuma na bari a shiga tawa,but ban san me yasa ni da ke muka samu wani connection na musamman ba."

Kafaɗar Sakeenah Nasibah ta dafa suka shige cikin gidan kafin ta ce.

"Daga Allah ne."

"Indeed daga Allah ne."

Dogon tsakin da Sameerah ta saki ne ya ja hankalinsu zuwa wajenta. Ita ɗaya ce a wajen da alama Hajjah ta shige ciki,rai a ɓace Sameerah ta ce.

"Ke dai Sakeenah kin ji haushin halinki a rayuwa,wai yarinya ta zagi mahaifiyarki amma ki dinga sakar mata fuska."

Nasibah bata kula ta ba ta shige cikin sashenta tana tunanin da an kwana biyu za ta buɗe ƙofar da ta gani a kusa da kitchen,idan ta yi baƙi ko za fa fita ba sai ta haɗu da su Hajjah ba.

Da misalin goma na dare Samir ya koma gida. Sosai Nasibah ta saki ranta da jikinta ta faranta wa Samir a wannan daren,hakan sai ya ba wa Samir satar amsar yanda zai dinga faranta ran Nasibah,cikin ransa yake ayyana zai ɗakko mata Yasmin ma,wataƙila za ta sake sakar masa jikinta yayi yanda ya so da ita.

**************************

A can gidan Makaɗi kuwa bayan Samir ya tafi ya saka su Mama da yaran a gaba ya dinga zazzaga musu faɗa yana cin alwashin idan har ziyarar su ta girgiɗe masa auren ƴa duk sai dai su nemi wajen zama amma ba dai gidansa ba. Duk yanda Kilishi ta so ta fahimtar da shi abunda ya faru Makaɗi sam ya toshe kunnuwansa ya ƙi fahimtar su.

*******************************

Bayan sati ɗaya da Nuh ya ɗauka yana roƙon Samir No Nawwarah bai samu ba,sai kawai ya shirya da kansa ya zo har Kano ya kawo kansa gaban Nasibah,duk yanda Samir ya dinga ƙyafta masa ido kada yayi zancen No Nawwarah sai Nuh yayi kamar bai gani ba,cikin hira Nuh ya soko zancen Nawwarah,a cikin amsar da Nasibah ta bashi ya fuskanci wacece Nawwarah,sosai ya ji hankalinsa ya kwanta da ita domin kuwa halayyarsu ta zamo iri ɗaya,kuma da alama burinsu na ganin bayan farincikin Samir da Nasibah ɗaya ne. Babu ɓata lokaci Nasibah ta bashi lambar wayar Nawwarah ta ce.

"Kada ka ji na ce bata da hali ka fara soyayya da ita ka barta,ni da ka ganni nan ba a cin amanar ƙawayena na ƙyale mutum ah toh."

Dariya Nuh yayi ya ce.

"Baki da matsala Madame,ni dai ƙawarki ta yi min."

"Za kuwa ka haɗu da Samee,dan na rantse maka idan ta ji kana neman auren wata ba ita ba sai ta ci maka ƙaniya a gidan nan,kai shiga gidan nan ma sai ya gagare ka."

"Na san yanda zan yi handling kayata."

"Ai ni dama na san ba sonta kake yi ba,gashi lokaci ya nuna za ka auri wata ka bar ƙanwata."

Shiru kawai Nuh yayi yana gwada lambar da Nasibah ta bashi zai kira,yana danna No zai kira sai ya ga ashe ma ya taɓa saving No da MUNAFUKINA. Nan take Nuh ya gane ashe Nawwarah ce ta yi masa videon nan a ranar dinner party ɗin su Samir. Murmushi ya saki tare da jinjina kai ya ce.

"Lallai Nuhu ka yi babban kamu. Ai dole ne ma na ƙulla alaƙa da wannan yarinyar wataƙila ta dalilinta na cimma burina."

Samir ne ya kalle shi da sauri yace.

"Wanne buri kake son cimmawa kuma Nuh?"

Daburcewa Nuh yayi ya hau sosa kai ya ce.

"Matsalata da kai sa ido,ni na tafi sai da safen ku. Yanzu amarya ta gaje min waje bani da wajen kwana a gidan nan."

Murmushi kawai Nasibah ta yi,ta bi su Samir da kallo har suka bar parlourn.

Bayan an kwana biyu sai Nuh ya sauya layi ya fara chatting da Nawwarah,a hankali ya fara jan ra'ayinta ta hanyar tura mata katin waya na dubu biyar,wani lokacin ma har na dubu goma,ita kuwa ganin yana saka mata katin waya mai yawa sai ta fara roƙon kuɗi yana tura mata ta account. Cikin sati ɗaya da fara soyayyarsu Nawarah ta yi demanding ganin Nuh. Shi kuwa bai yi ƙasa a guiwa ba wajen amsa gayyatar ta,alƙawari yayi mata zai zo ya ganta daga Abuja bayan sati ɗaya. Cike da murna Nawwarah ta kira Nasibah dan ta sanar da ita itama dai bana Allah ya dube ta ya bata miji mai kuɗi irin wanda take buri da fata a rayuwarta. Fatan alkhairi Nasibah ta yi mata ta yi kamar bata san Nuh ne ke nemanta ba. Suna gama waya da Nasibah Nawwarah ta zari mayafinta ta nufi gidansu Nadiyah. Ko da ta je sai ta tarar da an kawo lefen Nadiyah gida ya cika da yan'uwa da abokan arziƙi ana ta sanya albarka. Sosai hakan ya ɓata ran Nawwarah sai ta ja gefe da Nadiyah ta ce.

"To da baki sanar dani an kawo lefen ki ba;ni gani na zo sanar da ke wani satin wanda zai aure ni zai zo gidanmu daga Abuja. Daɗin abun dai ni ba irin aurenki auren talauci auren cushe zan yi ba;har da kike ɓoye min abubuwanki."

Kafin Nadiyah ta ce wani abu Nawwarah ta bar gidan ranta a ɓace tana cin alwashin ko bikin Nadiyah ba za ta je ba,kuma itama ba za ta gayyaci Nadiyah bikinta ba.....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol