Free chapter · Read without an account

Chapter 13

by Asmeetah Writer · WASAN ƘADDARA 1

╔══════════════════════╗
        🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝

_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_

> ✍️ BY ASMEETAH WRITER

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

🌟 Under:

THE SHIDORIA WRITERS TEAM

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 CHAPTER ___25 and 26

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━



Malamin ya ɗaga hannu sama zai ba da umarnin buɗe takardun jarrabawa, kwatsam sai ga Principal ya turo ƙofa ya shigo, tare da wasu manyan malamai guda biyu.
Ajin ya ɗauki tsit, kowa ya maida hankalinsa gaba. Principal ya taka har gaban teburin malamin mai sanya ido, ya fuskanci ɗaliban sannan ya ce,

"Ku saurara duka. Kafin mu fara wannan final examination, muna da wata muhimmiyar sanarwa. Kamar yadda kuka sani, a kowace shekara, A.Y.Z Foundation tana zaɓar ɗalibai goma mafi hazaƙa daga makarantun gwamnati domin biya musu kuɗin JAMB kuma sune suka biya NECO wa waɗanda basu da ikon biya, Bayan fitowar sakamakon JAMB, waɗanda suka cimma ƙa'idar da gidauniyar ta tsara za su samu cikakkiyar tallafin karatu zuwa AYZ College of Health Sciences."

Ya gyara tsayuwarsa, ya kalli fuskokin ɗaliban ɗaya bayan ɗaya kafin ya ɗora da cewa
 "Saboda haka, da zaran kun kammala wannan jarrabawar ta yau, kada kowa ya tafi gida. Ku tsaya duka a nan, za mu fito mu ƙira sunayen ɗalibai goma da suka yi nasarar samun wannan gurbi."

Bayan ficewar shugaban makarantar, malamin jarrabawa ya bayar da umarnin buɗe takardu. Amira ta ɗauki fensir dinta da biro, hannunta na ɗan ɓari saboda jirin dake juyawa a kanta. Amma hakan bai hana ta maida hankali ba, ta dinga bin tambayoyin tana amsa su ɗaya bayan ɗaya cikin sanyin jiki.

Bayan tsawon awanni uku, waɗanda suka gama sun fiffita ciki har da Meerah, sai waɗanda ke zaune, lokaci na cika aka fara karɓan takardun kowa, ɗalibai gaba ɗaya suka fito zuwa harabar makarantar inda aka ce su taru. Amira ta nemo wani gefen bishiyar ta tsaya, jikinta duk ya yi sanyi, zuciyarta na dukan uku-uku yayin da take ta faman rera addu'ar neman kariya da nasara a ranta...

Shugaban makaranta ya fito riƙe da wata takarda ta musamman, ya tsaya a kan dakalin taron.

"Zan fara ƙiran sunayen ɗalibai maza guda biyar da suka cancanta," ya faɗa ta cikin lasifikar hannu.
Aka ƙira sunan Mubarak, da sauran maza huɗu, ɗalibai suka ɗauki tafi. Daga nan Principal ya gyara takardar ya ce, "Yanzu kuma za mu koma kan sunayen mata biyar."

Ya ɗaga murya da ƙarfi, "...Amira A. Mansur! Wacce ita ce ɗaliba mafi ƙwazo a ajin Science."

Gaban Amira ya faɗi, ta rintse idanuwanta don cikar farin ciki. Shi ne suna na farko da aka ƙira a cikin mata, domin ita ce take ɗaukar Highest Scoring Student  a fannin karatu, kuma tana cikin waɗanda ba su sami damar biyan kuɗin JAMB ba. Bayan ita, aka ƙira sunayen sauran mata huɗun da suka rage.
Shugaban makarantar ya kalli waɗanda aka ƙira gaba ɗaya ya ce, 

 "Ku goma da aka zaɓa, ku kasance a nan makaranta daidai ƙarfe 6:00 na safe gobe. Motar gidauniyar A.Y.Z Foundation zata zo ta ɗauke ku zuwa Registration Center domin a yi muku rajistar JAMB a ɗauki hotunanku da yatsunku, sannan a karɓo muku takardar bayanan rajistar waɗanda ke ɗauke da ainihin ranaku da wuraren da zaku rubuta jarabawar."

Murna a gurin Amira ta gauraye da wani irin fargaba. Ta sami gurbin, amma ta yaya zata fuskanci Uma a gida ta gaya mata cewa gobe ma da misalin ƙarfe shida na safe za ta sake fita?

Bayan tafiyar shugaban makarantar, harabar gurin ta gauraye da surutai da hayaniyar ɗalibai, kowanne yana bayyana ra'ayinsa.

"Kai! Da a ce sunana ya fito a ciki wallahi kwana zanyi ina sujjada," in ji wani ɗalibi.

Wani kuma ya amsa masa, "Wallahi wannan mutumin A.Y.Z mutum ne mai alheri mai yawan gaske."

"Na ji wai duk shekara haka yake yi wa makarantun gwamnati," wata ɗaliba ta juyo tana faɗi.

Ɗaya daga cikin rukunin ɗaliban ya sake katse su, "An ce ma ba ya son a ɗauki hoto da shi ko mutanensa idan suna tallafawa. Mutum ne mai kuɗi sosai amma yana ɓoye kansa."

"Ni kaina ban taɓa ganin fuskarsa ba ko a hoto," cewar wani.

Amira dake tsaye riƙe da jakarta ta jingina da bishiya, ta zuba musu idanu tana sauraron kalaman nasu ɗaya bayan ɗaya. Kalaman sun ratsa zuciyarta, ta runtse idanuwanta cike da tsananin godiya ga Allah.

A ranta ta ce, *"Ya Allah... Ka saka wa wannan mutumin da alheri. Ban taɓa ganin sa ba, ban san ko shi wanene ba, amma duk shekara yana canza rayuwar talakawa. Ka ba shi ladan abin da yake yi."*

Ta buɗe idonta tana kallon sauran ɗaliban goma da aka zaɓa, tana mai sake tunanin yadda zata fuskanci gida a halin yanzu.

Amira tana tsaye, ba zato ba tsammani ƙawarta Maryama ta taho da gudu ta rungume ta tana mata murnar samun wannan nasara. Sauran ƙawayensu ma suka zagaye su, har da wasu a cikin ɗalibai huɗun nan na mata da aka zaɓa.
Nan take suka shiga yi mata ya jiki bayan sun lura da ƙaton bandejin dake like a goshinta, duk da cewa ba su san takamaiman abin da ya faru ba. Maryama ta ɗago kai tana kallon fuskar Amira, "Ke kuma Amira, hatsari kika yi ne ko kuwa faɗa kika yi da wata ta fasa miki goshi?"

Amira ta ɗan yi murmushin yaƙe, "Ai kinfi kowa sani na ba ni da faɗa, ban ma iya ba. Kawai tsautsayi ne ya afku da ni. Don Allah Maryama, so nake ki raka ni gida yanzu, zan faɗa miki duk abin da ke faruwa a hanya. Kuma so nake ki taya ni ba Uma haƙuri, ki sanar mata da wannan batun na JAMB, ko zuciyarta za ta sassauta ta bar ni na fita gobe."

Maryama ta zaro idanu cikin mamaki, "Ke kuwa me kika yi mata haka da ya kai har sai an ba da haƙuri?"

Amira ba ta ba da amsa ba a gurin, ta ja hannunta suka shiga sahun ɗaliban dake ta tafiya gida bayan an tashi.

A kan hanyarsu ta komawa ne Amira ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar wa Maryama, tun daga maganar Zaitun, hatsarin da suka yi, kwanan asibiti, mutumin da ya ɗauko ta a kan babban mashin da asuba, har zuwa dukan da Uma ta mata. Maryama ta cika da mamaki tana jinjina kai, nan take ta amince zasu je gidan tare, domin kuwa dama Amira ba ta da ƙawar da ta wuce ta, ita ma haka.

Suna cikin tafiyar ne suka koma hirar batun JAMB da kuma jami'ar AYZ College of Health Sciences. Maryama ta ce,
 "Ai wallahi Amira, ko nawa ne kuɗin registration ɗin makarantar nan sai na sa Abbana ya biya min.."

Amira ta yi murmushi ta ce,
"Ni kuwa idan ban samu scholarship ba, ai mafarki ne kawai... Ba zan taɓa iya haɗa kuɗin form ɗin ba."

Maryama ta ce
"Kada ki yi saurin yanke ƙauna. Allah na iya buɗe ƙofa daga inda ba kya zato."

Dama ita Maryama dake ƴan Principal ce, don haka tuni aka biya mata kuɗin jarrabawar JAMB, ba a wasa da duk wani abu dake da alaƙa da karatunta da kuɗin makaranta. Saboda haka ita ba ta cikin masu neman gurbin kyauta na JAMB, sai dai kawai idan lokaci ya yi ta sayi gurbin shiga babban kwalejin wanda kowa ya sani akwai tsada sosai...

Maryama ta juyo ta kalli Amira ta ɗora da cewa, "Na ji daga Abbana cewa, waɗanda gidauniyar A.Y.Z ta zaɓa ba wai an ba su gurbin makarantar kai tsaye ba ne. Sai idan sun ci JAMB da maki mai kyau, sannan su ci sauran matakan tantancewa. A lokacin ne za a ba su cikakkiyar scholarship. Wanda kuwa bai ci nasarar tsallakewa ba, to fa sai dai ya nemi wata makarantar daban."

Amira ta ce, "ai kin sanar mun tun a gidanku..."

Maryam tayi murmushi tare da faɗin "ai jaddada miki nayi akan mu dake sosai, idan muna son shiga makarantar, domin wurin yayi a rayuwa, yadda kasan aljannar duniya kuma na ƴaƴan masu kuɗi ne..."

Amira ta yi shiru bata ce komai ba, ta cigaba da faɗin 
"Abu na farko yanzu da zai dame ki shine sutura masu kyau, saboda ki fita raini..."

Amira ta kalle ta sannan ta ce, "Abu ɗaya ne zai dame ni idan na shiga...shine yadda zan kammala lafiya na fito da result ɗin da ake buƙata sannan na samu aiki, idan na fara aiki ina samun kuɗi duk wannan suturan mai sauƙi ne, sannan na taimaki mahaifiyata..."

Haka suka ci gaba da tattauna yadda tsarin jarrabawar zai kasance cikin fargaba da fatan alheri, har suka fara tunkarar layin gidan su Amira...

★★★

A gefe guda kuma, a cikin wani katafaren gida na alfarma dake tsakiyar birnin Kaduna...

Hajiya Mairos tana zaune a kan kujera ta alfarma tana duba wasu takardu. Jim kaɗan sai ga Ahan ya shigo falon ya zauna riƙe da kofin ruwan sanyi. Daga shi sai gajeren wando da singlet, gabaɗaya harkar karatu na neman gundurar sa. Wannan ita shekara ta biyar da zai zana jarrabawar JAMB, ya zana ta farko, ta biyu, ta uku, da ta huɗu duka bai taba samu maki mai kyau da zai ba shi gurbin shiga jami'a ba. A wannan karawar, babban Yaya ya gama jan kunne tare da gargaɗi mai tsanani, inda ya ba shi tabbacin cewa idan har bai kawo makin da ake buƙata ba a wannan karon, to fa zai ɗauki tsauraran matakai a kansa..

Hajiya Mairo ta ɗago kai ta kalle shi, ta gyara zamanta ta ce, "Wato kai kana nan zaune ko? Kana sane da cewa gobe za a tafi rukunin registration na JAMB ko?"

Ahan ya kurɓi ruwa, ya ce, "Eh, na sani."

"To kamata ya yi ka maida hankali sosai a wannan karon," Hajiya Mairo ta faɗa cikin sigar gargaɗi. "Ka dai ji kalaman da Yayanka ya gaya maka a kan wannan jarrabawar. Ya ce indai baka ci ba a wannan karon, to kasan sauran."

Ahan ya haɗe fuska guda, ya ajiye kofin hannunsa cikin ƙosawa da fushin maganar ya ce, 
"Hajiya, wallahi wannan JAMB ɗin ce take ƙina."

Hajiya ta ce
"Ba JAMB ce take ƙinka ba, kai ne kake ƙin littafi."

Yana turo baki ya ce,
"Ai ni da littafi mun yi sulhu tun shekaru biyu da suka wuce."

Hajiya ta harare shi tare da faɗin 
"Ka sani ko? Gobe waɗanda gidauniyar Yayanka ta zaɓa daga makarantun gwamnati ma za su zo registration."

Ya ce, "Eh, na ji."

Ta kuma cewa,
"Allah Ya sa akwai masu ƙoƙari cikinsu waɗanda zasu taimaka maka."

Cikin rashin jin daɗi maganar ya ce,
"Wai me ake so na yi ne? Mutum fa iyakar ƙoƙarinsa yake yi. Shi JAMB ai ba wai don mutum yana da ilimi ne yake sa shi ci ba, kawai tsautsayi ne da tsarin kwamfuta ke gurbata sakamako."

Hajiya ta girgiza kai, suka ci gaba da tattaunawa a kan yadda Yayansa ya tsara masa tafiyar gobe da kuma tsauraran dokokin dake jiran sa idan har abin ya sake lalacewa...

★★★

Amira da Maryama suna shiga tsakar gidan, suka tarar da Uma tana zaune a kan tirmi dake kusan murhu, fuskarta babu ko ɗigon walwala. Gaba ɗaya gidan ya yi tsit, domin su Malam da Kaka duk sun fita.

Ganin Uma ya sa jikin Amira ya sake yin sanyi, ta ja da baya kaɗan ta bar Maryama ta matsa gaba.
Maryama ta ƙarasa cikin girmamawa ta tsuguna har ƙasa, "Ina wuni Uma."

Uma ta juyo ta kalli Maryama, ta tilasta kanta yin ɗan murmushi, "Lafiya lau Maryama, ya gidan naku?"

"Lafiya lau wallahi Uma," Maryama ta gyara zamanta, ta kalli Amira sannan ta dawo da kallonta kan Uma cikin sigar rarrashi. 

"Uma, don Allah na zo ne a matsayin ɗiyarki na roƙe miki Amira a kan abin da ya faru na jiya. Wallahi tsautsayi ne na hatsari ya tsare ta a asibiti, ba wai don tana son yin hakan ba."

Uma ta ja numfashi, ta ajiye iccen hannunta ta ce, "Maryama, bar wannan zancen kawai. Amira ta riga da ta tamka babban kuskure."

Maryama ta matso kusa da ita, "Muna neman afuwa Uma, an wuce gurin... Amma babban al'amarin ma, yau an fito da sakamakon waɗanda za a biya wa JAMB cikin ikon Allah, Amira ce ta zo ta farko a fannin mata duka"

Jin sunan Jamb kyauta ya sa Uma ta ɗago kai da sauri ta kalli Amira, sannan ta dawo kan Maryama, "JAMB kyauta kuma?"

"Kwarai kuwa Uma," Maryama ta yi hanzarin amsawa. "Gidauniyar masu kuɗi ne zasu ɗauki nauyin hakan, kuma an ce gobe da safe daidai ƙarfe shida motar gidauniyar zata zo ta ɗauke su zuwa gurin registration na JAMB gaba ɗaya. Idan aka hana ta fita gobe, to fa an soke sunanta an tashi a banza."

Uma ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallon Amira dake tsaye cikin sanyin jiki. Takaicin kwanan waje da ta yi yana nan a ranta, amma kuma tana matsanancin son ganin ɗiyarta ta yi karatu ta zama wani abu a rayuwa don su fita daga wannan kangin wahala da wulaƙanci da suke ciki...

Bayan wasu daƙiƙu ta ce, 
"Maryama, ba fitan ne ya fi min ciwo ba. Abin da ya fi ciwo shi ne ɗiyata ta kwana a waje ban san inda take ba. Da kin kasance uwa, da kin fahimci abin da nake ji."

Maryama ta sunkuyar da kai.
"Na fahimta Uma... Amma wallahi ba da son ranta ba ne. Kuma wannan damar ba ta zuwa sau biyu."

Uma ta dubi Amira, ta ga yadda kanta yake ɗaure da bandeji, zuciyarta ta motsa amma haka ta danne ta ce murya ƙasa-ƙasa 

"Shiga ciki... Zan yi tunani."

Murna ta cika ran Amira da Maryama, suka nufi ɗaki da sauri domin su bar Uma ta yi nazari cikin natsuwa...

★★★

Misalin ƙarfe biyar na asuba, Amira ta farka cikin fargaba. Bayan ta gabatar da sallar asuba, ta zauna a kan sallaya tana addu'o'i, idanunta cike da hawaye. Tana matsanancin fargabar ko Uma zata sauƙo ta barta ta fita, ko kuma haramcin jiya yana nan daram..
Tana nan zaune, kofar ɗakin ta ɗan buɗe a hankali. Uma ce ta shigo, fuskarta babu walwala amma babu alamun fushi kamar na jiya. Ta kalli Amira, sannan ta bata kuɗin tare da faɗin 

"Ga kuɗi nan, idan kuna buƙatar abin sha ko wani abu a hanya, da kuma 'yar dambun da na dafa miki yanzu kici kafin ku tafi..." daga nan ta juya ta koma kicin...

Wani farin ciki ne ya ratsa Amira. Cikin sauri ta shirya cikin kayan makarantarta, ta ɗauki takardunta ta fito...

Daƙiƙa talatin kafin ƙarfe shida na safe, Amira ta isa ƙofar makarantarsu tana maida numfashi. Ba da daɗewa ba, wata bus mai ɗauke da tambarin A.Y.Z Foundation ta faka a kofar get ɗin. Haka su goma da aka zaɓa suka shiga, bayan su akwai wasu waɗanda aka ɗauko a wasu makarantun gomnati, ...motar ta nufi AYZ Digital CBT & Registration Centre, cibiyar da gidauniyar ke gudanar da rajistar JAMB da sauran ayyukan fasaha...

Suna isa gurin, gaba ɗaya jama'a sun taru. Amira da sauran ɗaliban makarantarsu suka shiga sahu gwanin ban tausayi, kowannensu riƙe da takardunsa.
A daidai wannan lokacin, aka ji ƙaran taya da gurnanin wata tsaleliyar mota ta alfarma ta faka a daidai gurin. ya turo ƙofar motar yana faman miƙa da yamutsa fuska, gaba ɗaya yanayinsa na nuna tsananin gajiya da ɓacin rai. Ya gyara zaman riga da wandon jeans ɗinsa na alfarma, ya kalli direban motar tasu yana turo baki..

"Wallahi Hajiya ta hana ni barci yau saboda wannan bala'in JAMB. Da asuba ta tashe ni kamar wanda zai tafi yaƙi."

Direban ya yi murmushi kawai ya ja motar ya bar gurin, yayin da Ahan ya nufi cikin rukunin ofishin rajistar yana bubbuga ƙafa cikin layin VIP, ransa yayi wasar saboda yadda ya hango kyawawan 'yan mata manya da ƙanana a gurin..

A can cikin babban ofishin gidauniyar dake kallon babban zauren rajistar ta kyamarorin CCTV, babban mataimakin shugaban gidauniyar ya turo ƙofa ya shigo cikin natsuwa.
A.Y.Z yana zaune a kan kujerarsa ta alfarma, kansa yana duƙe yana duba wasu muhimman takardun kuɗi na kasuwancinsa, bai ma ɗago kai ya kalli mataimakin nasa ba.

"Sir, ɗaliban makarantun gwamnati da gidauniyarka ta ɗauki nauyi duk sun iso gurin rajista yanzu haka,"

 Assistant ɗin ya faɗa cikin girmamawa.
A.Y.Z bai ɗago kai ba, ya juya shafin takardar hannunsa kawai ya ce, "Ku tabbatar babu wanda zai biya ko naira ɗaya a cikinsu. Komai yana kan asusun gidauniya."

"Yes Sir," Assistant ya gyaɗa kai..

"Idan akwai wata matsala, a ƙira ni," ya ƙara da faɗi a takaice cikin dakakkiyar muryarsa ba tare da ya kalli kyamarorin dake nuna fuskokin ɗaliban ba...

A can zauren jiran layi, ɗalibai sun yi jugum-jugum a kan kujeru suna jiran a ƙira lambobinsu. Kujerar da Ahan ya zauna tana daidai kusa da ta Amira.
Ahan ya ciro takardunsa ya duba, sai ya fito da wata 'yar ƙaramar takarda dake buƙatar cike wasu bayanai na gaggawa. Ya bincika aljihunsa na gaba da na baya, ya duba cikin takardunsa amma bai ga biro ba. Ya waiga hagu da dama, idanunsa suka sauƙa akan Amira dake riƙe da biro guda biyu a hannunta.
Ya ɗan gyara zama, ya dube ta ya ce, "Excuse me... zan iya aron biro?"

Amira ta ɗago da kyawawan idanuwanta ta kalle shi, ta miƙa masa biron guda ɗaya ba tare da ta ce uffan ba, sannan ta maida kanta ƙasa tana jujjuya takardunta.
Ahan ya karɓi biro
 ya cike abin da zai cike cikin hanzari. Bayan ya gama, ya miƙa mata biron...

Amira ta kalli biron, ta kalli Ahan dake shirin maida kansa ga wayarsa, ta ce,  "Kai..."

Ahan ya juyo da sauri yana kallonta cike da mamaki, ya ce, "Meya faru ne?"

Ta ɗege goshi ta kalle shi cikin tsiwa, "Saboda ba ka yi min godiya ba."

Ahan ya taɓe baki ya harare ta kaɗan,
 "Yoo... abin da na fi ƙarfi sai na miki godiya akai?"

Amira ta gyara zamanta, ta fuskance shi gaba ɗaya, "Eh, amma ai ara ka yi yanzu...Abin da kake da'awar ka fi ƙarfi ɗin, shi kake nema aro yanzu don ka biya buƙatarka... Da sai ka yi rubutun da hannunka tunda ka fi ƙarfin biron"

Ya kawar da kansa tare da faɗin 
"To nagode."

"Sai da aka tilasta maka." Ta furta tana harararsa

Ya ɗago yana kallonta ya ce, 
"To me kike so? In yi miki sujjada ne?"

Ta ce,
"Ai godiya ba ta rage girman mutum."

"Ni dai ban saba yin godiya akan ƙaramin abu ba... Amma idan kina so sai in biya ki"
   Ya ƙarasa yana danna wayarsa.

 Tana masa kallon up and down ta ce, 
"Ai ba cewa nayi ka biya ni ba, domin Ni ba matsiyaciya ba ce"

Ahan ya dube ta sama da ƙasa shima ya ce, 
"Ohh na gani fa, tin daga kan takalminki ke ba matsiyaciya ba ce..." 

 ta duba takalminta ta ga yadda fatar ta fara ɗaɗɗage wa, duk ya tsufa tasan gatse yake mata.

Ta buɗe baki zatayi magana sai ga Assistant ya zo wuce wa ta wurin ya ce, 

"Don Allah ku rage magana. Wannan registration center ne."

Bayan ya wuce ta harari Ahan ta ce, "ɗan rainin wayo..."

Yana kallon wayarsa ya ba ta amsa 
"Da wayon ta zo ai naga ta girmamaki saboda matsayinki..." 

Tayi shiru tana jujjuya biro ta, 
Ganin bata bashi amsa ba ya kuma cewa 
"Ke mai bakin tsiwa....meye sunanki ne?..."

ta yamutsa fuska ta ce, "ba na ba da suna ga marasa kunya..."

Ahan ya ja tsaki ya ce, 
"Mtsw! wai akan biro kike cin mutuncina haka? Inda kin san matsayina da baki zauna kusa dani ba,  kawai ƙaddara ne yasa zan rubuta Jamb da ku..."

Amira ta ɗago ta kalle shi cikin mamaki ta ce, 

"To me yasa kake zaune nan kana neman aro biro? Ɗan gidan mai kuɗi fa ya kamata ya zo da jakar biro gaba ɗaya."

Ahan ya rasa abin da zai ce. Sai ya shiga duba Instagram...

Kwatsam aka ji an ƙira,

"Na gaba... Number 27 da Number 28... 
Amira A. Mansur da Ahan Y. Zarkhan. Ku zo counter number 3"

Dukan su biyu suka ɗago lokaci guda.

Amira ta girgiza kai ta ce,  "Ashe Ahan ne sunanka? Na zata dai Mai Girman Kai ake ƙiranka."

Shima ya harare ta tare da faɗin 
"Ke kuma na zata Mai Bakin rashin kunya ake ƙiranki..."

 Assistant ya ce,
"Don Allah ku ƙarasa counter."

Suka tafi gefe-da-gefe zuwa counter...  

Suka tsaya matar dake rajista ta kalle su ta yi murmushi...

"Amira A. Mansur?" 
 
"Ni ce." Amira ta miƙa takardunta.  

Ta duba bayananta a computer sannan ta ce, "Ke kina cikin ɗaliban da A.Y.Z Foundation ta ɗauki nauyin registration ɗin JAMB ko?"

Amira ta gyara zamanta ta ce,  "Eh."

Matar ta danna wasu maɓallan computer sannan ta yi murmushi. "To Alhamdulillah. An riga an biya miki komai. Ba za ki biya ko naira ɗaya ba."

Ahan da ke gefe ya ji. Ya juya ya kalleta. 
A ransa ya ce, _"Wannan talaka ce fa amma sai shegen tsiwa..."_

Registration Officer ya ce da Amira,
"Kina da lambar waya?"

Amira ta girgiza kai da sauri  "A'a..."

"To email fa?"

Ta sake girgiza kai.
"Ban taɓa buɗewa ba."

Officer ɗin ya ɗan yi shiru.
"To ba za mu iya kammala registration ba sai an samar da number da email."

Nan Amira ta rikice, hawaye suka cika idanunta...
Ahan da yake gefe yana kallonta sai ya taɓe baki ya ce,

"Kai... har Gmail ma ba ki da shi?"

Amira ta harare shi tare da faɗin 
"Ai ba kowa ne yake rayuwa da waya ba."

Officer ya ce,
"Don Allah idan akwai wanda za ta iya amfani da lambarsa, a kawo yanzu."

Ahan ya ja numfashi ya ce,
"Kaiii! Hajiya za ta kashe ni idan na ba wa gardiya sim ɗina..."

Officer ya ce,
"To sai dai gaskiya ki haƙura da jamb ɗin nan indai babu layi ko Gmail..."

Ahan ya ciro wayarsa tare da buɗe wa ya zaro sim yana faɗin..

"Ga SIM na biyu nan. Ba na amfani da shi sosai. Ku yi registration da shi."

Officer ya ce,
"Kyauta ko aro?"

Ahan ya ɗaga kafaɗa.
"Ai bayan JAMB zan iya karɓa idan ina so."

Amira ta zaro ido.
"A'a... To ya zan yi idan jamb ya fito? ta ya zan duba..."

Officer ya ce, "ai za'a buɗe miki Gmail ne, zaki iya amfani da shi a kowani layi...kiyi masa godiya domin yayi miki abu mai wuyan..."

Ahan ya ce da ɗan tsaki,
"Ta yi shiru kawai...Ni ban yi don ita ba. Ina so kawai a gama surutun nan."

 Officer ya saka SIM ɗin a wayar office, ya buɗe mata sabon Gmail da sunanta, ya yi linking da lambar...daga nan aka buƙaci ta miƙo yatsa don ɗaukar fingerprint, suka ɗauki hotonta... 

Bayan ya tabbatar komai ya kammala, ya buga takardar rajistar ya miƙa mata.
"Ga takardarki. An rubuta lambar wayar da kuma adireshin Gmail ɗinki a ƙasa. Ki kiyaye su sosai."

Amira ta karɓa cikin rawar hannu. Ta ɗan yi shiru kafin ta juya ta kalli Ahan.
Cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce,
"...Nagode."

Ahan ya ɗan yi murmushin gefen baki.
"Ashe kina iya godiya ma? Na fara tunanin baki san kalmar ba."

Amira ta taɓe baki itama ta mayar masa,
"Kai ne ya kamata ka koya tun farko."

 Ya ɗaga gira,
"To ni ma na koya. Ke kuma ki rage wannan bakin tsiyar taki kaɗan."

Amira ta juya tana murmushi a ɓoye.
"Sai ka fara zama mai mutunci."

Bayan sun gama da Amira, sai jerin Ahan..
  
Matar mai registration ta ce, "Ahan Y. Zarkhan... kai ma an biya maka ne?"  

Ahan yayi saurin girgiza kai, "To fa! Family ne ya kula da komai."

Matar ta yi murmushi ta yi masa rajista.

Lokacin da za su fita, Ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon Amira, kamar zai ce wani abu. Amma sai ya taɓe baki ya juya ya fice...a ransa ya ce,

"Yarinya mai bakin tsiwa..."

Amira kamar ya ji me yace a ransa itama ta furta a ranta,
"Mutum sai rashi kunya, ko kaɗan bai burge ni ba."

Bayan kusan sa'o'i biyu, aka kammala rajistar kowa. Ma'aikatan cibiyar suka rarraba wa ɗaliban JAMB Registration Slip wacce ke ɗauke da ainihin ranar jarrabawa, tare da ba su littafin karantawa na JAMB na wannan shekarar da wasu shafukan bayanai.
Haka direban motar gidauniyar ya tattara ɗaliban makarantun domin mayar da su gida...

A gefe guda kuma, kafin su bar rukunin ma'aikatar, Ahan ya wuce kai tsaye zuwa cikin katafaren ofishin yayansa na sirri bayan ya kammala tashi.
A.Y.Z yana zaune a kan kujerarsa yana rubutu da wani zafafan biro na alfarma. Jin motsin shigowar mutum ya sa ya ɗago, idanunsa suka sauƙa a kan Ahan...

"An gama registration ɗin?" ya tambaya a takaice, muryarsa na fita cikin natsuwa.

Ahan ya turo baki kaɗan, ya ajiye takardunsa a kan tebur, "Eh, an gama."

A.Y.Z ya gyara zamansa, ya tsare shi da idanu, "Ka tabbata ka maida hankali a wannan karon, ba zan sake amsar wani uzuri na daban ba."

Ahan ya sunkuyar da kansa ƙasa, amma a cikin ransa ya furta, 

“Kai dai kullum maganarka JAMB... mutum sai kace an haife shi a cikin hukumar JAMB ɗin.” A fili kuma sai ya ce, "In sha Allah Yaya."

Misalin ƙarfe sha ɗaya na rana, motar gidauniyar ta sauƙe Ɗaliban a makarantarsu, daga nan kowa ya koma gidansu...

★★★

 Cikin sa'a ta tarar tsakar gidan shiru,
Uma tana zaune a bakin kicin tana wanke kwanuka. Amira ta ƙarasa cikin sanyin jiki ta tsuguna, ta ciro takardar rajistar da littafin ta miƙa mata.
Uma ta share hannunta da zaninta, ta karɓi takardar tana duba bayanan dake kai, ta sauƙe ajiyar zuciya tare da kallon Amira, ta taɓa kafaɗarta a hankali ta ce,

 "Allah Ya sa ki ci wannan jarabawar, Amira... Ubangiji Ya buɗe miki ƙofofin alheri... Allah Yayi miki albarka."

Amira ta ji idanunta sun cika da hawayen farin ciki, ta gyada kai cikin jin daɗin addu'ar mahaifiyarta...

"Amin Uma."

Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara da murya ƙasa-ƙasa..
"Ki nuna musu cewa talauci ba ya hana mutum ilimi..."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol