Free chapter · Read without an account
Chapter 2
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 2
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Baki sake Shatu take kallon Mummy tana mamakin abin da take faɗa, har suka shiga Madawaki Dynasty babu wanda ya sake magana a cikinsu, Shatu ce ta fara fita da gudu tana shiga cikin gidan.
━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A zaune ta same su, A.maina ya gama yi musu bayanin auren da Shatu ta faɗa musu M Madawaki zai yi, a tsaye ta same M Madawaki yana duba wayar hannunsa.
Da gudu ta shigo tana kuka,tashi tsaye Daada ta yi za ta yi magana, sai ta ga Shatu ta faɗa jikin M Madawaki tana sake fashewa da sabon kuka, kallon hanyar da ta shigo duk suka yi domin ganin ita da waye, Mummy suka ta shigo ita ma rai a ɓace.
Amma ganin Shatu a jikin M Madawaki da yake tsaye, sai ta saki fuska, tana cewa.
"Wai Baby ba ki san wasa ba? Okay sorry na yi miki alƙawarin zan yi wa M Madawaki magana....."
Daada ce ta katse mata maganar tana cewa.
"Ke! Hajarah me yake faruwa? Kuma waye ya baki damar fita da Shatu daga gidan nan?"
Ƙasa Mummy ta yi da kanta tana tunanin kalaman da Amina ta ɗora mata, cikin sanyin murya ta ce.
"Daada ki yi haƙuri, mun fita ban sanar da ke ba, a lokacin ina cikin damuwa ne, Shatu ce ta saka ni a gaba wai dole sai na faɗa M Madawaki ita aure take so tana gama NECO & WACE shi ne fa na rarrashinta muka fita kuma gidanmu muka je yanzu ma kukan da take kenan...."
"Wait!"
Shiru duk falon ya ɗauka har Shatu da take kukan tare da ɗagowa idanuwanta tana kallon fuskar Mummy cike da mamaki bakinta na rawa ta ce.
"Mummy! Ni ni yaus...."
Hannunsa da ya saka yana rufe mata baki ne ya hanata ƙarasa maganar, fashewa ta sake yi da kuka, A Maina ya kalla yana yi masa sallma, kafin ya amsa ya ja hannayen Shatu ya nufi ɓangarensa da ita.
Kallon bayansa Daada ta yi wacce tun fara maganar ta yi saman tsaye, fita A Maina ya yi ba tare da ya ce komai ba, Aminu H Madawaki ne ya kalle fuskar Baba Malam da yake zaune bai motsa ba, bai kuma ce komai ba.
A hankali Mummy ta nufin ɓangarenata, dama addu'a take Allah yasa Shatu ta kasa kare kanta, cike da farinciki ta shiga cikin tana kiran number Amina tare da kora mata labari suna dariya.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Suna shiga falonsa Shatu ta ƙanƙameshi tana sake fashewa da sabon kuka, cireta ya yi daga jikinsa yana shiga master bedroom ɗinsa, da kallo Shatu ta bishi har ya rufe ƙofa.
Abubuwa biyu ne suka saka Shatu kwanciya a saman Turkey carpet ɗin da yake tsakiyar falon tana fashewa da sabon kuka, maganar Mummynta da fushi da ta ga a fuskar Abban nata, ita fushinsa ya fi ɗaga mata hankali, tana cikin wannan yanayin ta ji alamun buɗe ƙofa.
Da sauri ta miƙe tsaye, tana goge fuskarta Baba Jamila ta gani da wasu daga cikin masu aikin ɓangarensu suna shigo da kayayyakinta.
M.Madawaki ne ya fito sanye da jallabiya da alama wanka ya yi, kayayyakin da su Baba Jamila suka shigo da su, ya fara shiga da su bedroom ɗin kusa da nasa, cikin sanyin jiki Shatu ta tashi tana taimaka masa, da kansa ya jera mata kayanta a cikin wardrobe tana rakuɓe a gefe.
Kunya ce ta kamata sosai, gani yana shirya mata panties da bra da gudu ta faɗa jikinsa tana karɓar bra ɗin hannunsa tare da cusasu a cikin wardrobe ɗin tana rufewa.
Tashi M.Madawaki ya yi zai fita ta yi saurin riƙe hannunsa tana girgiza kai..
"Sorry Abbana, ba zan sake ba, Allah ban faɗa..."
Yatsan hannunsa ya ɗora saman lips ɗinta, tare da saka ɗaya hannunsa ya cire hannunta daga nasa ya fita, fashewa da kuka Shatu ta yi tare da bin bayansa, a bakin ƙofar falon ta ganshi yana rufe ɓangaren nasa.
System ɗinsa ya ɗauko tare da zama a kujerun falon yana aiki, ita ma Shatu kusa da shi ta dawo tana zama a ƙasan Carpet ɗin kusa da ƙafafuwansa bai ɗago ya kalleta ba, ya cigaba da aikinsa.
Tun tana hawaye har baccin damuwa ya kamata, cikin baccin ta kwantar da kanta a ƙafafuwansa a hankali ya ɗago yana kallon yadda ta kwanta a ƙasan Carpet ɗin, ajiyar system ɗin ya yi a gefe yana ɗagota.
Farkawa ta yi tare da rungumoshi, dole ba dan ya so ba, ya rungumeta tare da gyara zamansa ya ɗorata saman cinyarsa yana kai bakinsa kunneta ya furta.
"Eshaa."
"Abbana... please forgive me, forget what Mummy said. I swear, I didn't do it."
"What happened? Ina kuke je? Who touched you har na ji turaren jikinki ya sauya? Is it Hajarah that took you? Waye ya kalle miki jiki?"
Zaro idanuwanta Shatu ta yi tana kallon fuskar Abban nata da take nuna zallar zafin da yake ji a zuciyarsa, baki na rawa ta ce.
"It was Abdul Rahman who tried to kiss me...."
Tarin da M Madawaki ya fara ne ya saka Shatu shiru tana kallonshi, idanuwansa ta ga sun yi jajir da su lokaci ɗaya, lips ɗinsa na rawa ya kamo kunnuwanta da hannayensa duk biyu, da sauri Shatu ta riƙe hannunsa tare da cewa.
"Sorry Abbana, ba zan sake zuwa gidansu Mummy ba, please forgive me, wallahi guduwa na yi..."
Maganar ta tsaya ne sakamakon yatsan hannunsa da ya buga a saman lips ɗinta, ya kamo lips ɗin tare da matsewa, kuka Shatu ta fara tana riƙe hannayensa, amma M Madawaki bai saki ba, sai ma sake matsasu da yake.
Wahala ce ta saka Shatu dukan ƙirjinsa tana son guduwa, sakinta ya yi ta yi saurin tashi tsaye, shi ma miƙewa ya yi tare da nuna ta da yatsan yana jinjiga kansa.
"From today, kin dawo ɓangarena da kwana! Don't you ever enter any other section da sunan kwana, ko da wasa! The day hakan ya faru, wallahi that same day zan mayar da ke Private Quarters, kin fahimta? Sannan I will punish you severely saboda zama da kika yi har wata da wani banza suka yi ƙoƙarin taɓa miki jiki!"
Yana gama maganar ya shiga master bedroom ɗinsa tare da rufe ƙofar da karfi, zaman yan bori Shatu ta yi tana fashewa da sabon kuka, cikin kukan ta nufi bedroom ɗinta ta faɗa saman bed ɗin da gudu ko ƙofar bata rufe ba.
A ranar haka suka kwana zuciyoyinsu babu daɗi, ita da Abban nata, da asuba ne ma ta ga sassauci a fuskarsa domin har zama ya yi a bedroom ɗinta yana tambayar damuwarta.
Goge hawayen fuskarta ta yi tana sake bashi haƙuri akan abin da ya faru, tana sake tabbatar masa bata faɗi abin da Mummyta ta faɗa ba.
Jinjina mata kai kawai ya yi, sannan ya taimaka mata ta gyara sauran kayanta, ɗago da idanunwansa ya yi yana kallon fuskarta ganin ta tattara bra ɗin da suka zubo, tana cusasu cikin wardrobe.
Kallonsa ta yi tana turo baki, tashi ya yi yana komawa saman bed ɗin, ganin haka ya saka ta yi sauri ta gyara komai, sannan ta zauna a gefen bed ɗin tana kallon agogon room ɗin.
Da sauri ta miƙe tana langwaɓe da kai cikin shagwabe ta furta.
"Abbana ina so zan tafi school."
Kallon tambaya ya yi mata yana ɗaga mata gira, ƙafafuwanta ta buga a ƙasa ta nuna shi da hannu, tashi ya yi tare da yin murmushi, sai da ya je baƙin ƙofa ta ce..
"Sorry Abbana ina shiryawa zan fito, na zauna kana kallona har sai ka gaji..."
Dawowa da baya ya yi, Shatu ta yi saurin shiga toilet tana rufewa da karfi, murmushi ya yi tare da girgizar kansa, sannan ya fita zuwa nasa bedroom ɗin, wanka ya yi, yana zama shiryawa.
━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Har Shatu ta gama shiryawa bai fito ba, sai da ta fara buga ƙofarsa sannan ya saka kaya ya fito, a tsaye ya sameta da wayarsa a hannunta, karɓar wayar ya yi, tare da kama hannunta suka fito.
Zaune duk suka samesu, Hajiya Safiya ce ta yi murmushi mai kyau tare da shafa kan Shatu ta furta.
"Shatu M Madawaki za ta yi albarka a rayuwa, kun yi kyau ke da Abban naki."
Dariya Shatu ta yi tana riƙe hannun Hajiya Safiya da yake kanta, sannan ta ɗago kai tana kallon fuskar M Madawaki da yake tsaye har lokacin ta ce.
"Ammie ai Abbana yafi Ni kyau sos..."
Rufe mata baki da M Madawaki ya yi ne ya sakata yin shiru tana kallon Baba Malam da yake murmushi manya, zama M Madawaki ya yi tare da kallonta sannan abin da yake nufi ne ya sakata zama kusa da Nimrah.
Ita ce ta fara gaida kowa har Mummynta da take kallonsu tun shigowarsu, breakfast ɗin suka fara ba tare da sun yi dogowar magana ba, Yan Makarantan ne suka fara tashi suna sallama da Iyayensu.
Sai da suka fita Shatu ta dawo, tana kamo hannayen Mummynta tana mata magana a kunne sannan ta fita da gudu, tashi Baba Malam ya yi yana girgiza kai.
"Wai har yaushe ne Shatu M Madawaki za ta daina gudu a Madawaki Dynasty?"
Hajiya Maryam ce ta yi murmushi tana kallon fuskar M Madawaki da ya nuna kamar bai ji abin da Baba Malam yake faɗa, ta ce.
"Baba Malam har yanzu fa Shatu M Madawaki yarinya ce sai a hankali za ta daina, ka ga Banisha ma kullum faɗan da nake mata kenan."
Hanyar fita Baba Malam ya nufa ba tare da ya sake magana ba, Nimrah ce ta yi ƙasa da kanta tare da cewa.
"Abban Shatu, I want a car even for Banisha"
Goge bakinsa ya yi, yana ɗaukar phone ɗinsa take saman dinning ɗin sannan ya haɗa labɓansa kamar mai ciwon baki ya furta.
"Okay, talk to Yusuf, including Rima, Nadiya, Meerah."
Murmushi Daada ta yi tana kallonsa har fita yana fita Shamsudeen A Madawaki ya hararar Nimrah yana cewa.
"Ke! Wai me za ki yi da mota ne?"
Turo baki ta yi tana magana ƙasa ƙasa, Hala ce ta yi saurin cewa..
"Sannu Nimrah Ni mamaki kika bani da har kike iya tambayar Abban Shatu abu Ni fa ko gaisawa muke jikina rawa yake.."
Tashi Nimrah ta yi tana kallon fuskar Shamsudeen ta ce.
"Ni ma Aunty Hala ɗaurewa na yi amma gabana yana faɗuwa na yi maganar, Ni ko magana ya yi sai na ji kamar na yi fitsari....."
Maganar ta tsaya ne sakamakon Shamsudeen da ta ga ya nufuta da gudu ta shiga bedroom ɗin Daada, kafin ta rufe ƙofa ya shiga, ganinsa a bedroom ɗin ne ya sa ta turo baki tana cewa.
"Sorry Uncle Shamsudeen Ni fa..."
Kamota da ya yi ne yasa ta yi shiru tana zaro ido, murmushi ya yi tare da kwantar da murya ya ce.
"Rouhi kin fara raina ni ko?"
Zame jikinta ta yi daga jikinsa tana kallon gefen fuskarsa ta ce.
"Kai ne fa ka ƙi siya min, dama na faɗa maka ina zuwa Madawaki Dynasty sai na saka Abban Shatu ko Daddyn Meerah sun siya min."
Murmushi ya yi tare da kamo hannayenta yana ƙasa da murya.
"Ai da Daddy kika faɗa wa."
Rufe fuska ta yi tana murmushi tare da cewa.
"Ai kasan kunyar Daddyn Meerah nake ji...."
Bugo ƙofar da Daada ta yi ce tana shigowa ya hana Shamsudeen magana yana saurin sakin hannun Nimrah, tsaki Daada ta yi tana cewa.
"Karyar banza ai na gani har wani rungume mata hannaye ka ke yi, ana jin tsoron Allah dai?"
Hararar Daada Nimrah ta yi tana yin tsaki.
"Wai ke Daada ina ruwanki? Ni fa saboda ke ne bana son zuwa Madawaki Dynasty kin fiya masif..."
Shamsudeen ne ya rufe mata baki yana kallon Daada.
"Sorry Daada ba zamu sake ba, dama tambayarta nake."
Zama Daada ta yi a gefen bed ɗin tana nuna musu hanya, fita suka yi sannan Shamsudeen ya saki hannayenta, kafin wani ya gani a Iyayen nasu.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Zaune yake a office ɗinsa da wasu File yana dubawa, a hankali aka turo ƙofa, ɗagowa ya yi domin ganin waye, A Maina ya ga tsaye yana tsareshi da idanuwansa aikinsa ya cigaba da yi ba tare da ya ce komai ba.
Murmushi A Maina ya yi yana zama a kujerar da take kallo M Madawaki, dariya ya yi yana nuna M Madawaki da hannunsa, ajiye file ɗin ya yi tare da kallon fuskar A Maina.
"MAMUB ashe jiya gyara aka yi maka? Gaskiya Shatu M Madawaki na son Abban nata da yawa.."
Kallon da yake masa ne ya sa shi, sake fashewa da dariya, tsaki M Madawaki ya yi yana nunawa A Maina hanya, tsayawa A Maina ya yi da dariya yana cewa.
"Daga school ɗinsu Shatu M Madawaki nake, na je ne na ji inda suka je ita Hajarah da kuma tabbatar da abin da nake zirgi.."
Lumshe idanuwansa ya yi, ciki sanyin murya ya ce.
"MAMUB wannan kalaman daga bakin Hajarah suka fito Eshaa ba za ta iya faɗa ba.."
"Na sani amma ina gudun wata rana Hajara ta yi nasara akan Shatu M Madawaki."
Murmushi ya yi mai ciwo yana tashi tsaye.
"Na yanke wannan hanyar."
Murmushi A Maina ya yi tare da cewa.
"Amma Hajara ta yi aiki wai Shatu M Madawaki ce ke faɗa min, ta raka Mummynta ta gyara wa Abbanta jikinta ne..."
Lumshe idanuwansa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, domin ba shi da abin faɗa, ya san Hajarah ta yi nasarar rage masa tarbiyyar Shatu, kuma yana tsaron ta ƙarasa, shi ne dalilinsa na dawo da Shatu ɓangarensa, yana kula da duk wani motsita.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━