Free chapter · Read without an account

Chapter 7

by Maryam Usman · KOWA DA RABONSA

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 7
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━


Yana gama faɗar haka ya shiga bedroom yana faman kira wayar Dr Omar, Shatu kuwa yana shiga bedroom ta fashe da kuka, tana kwanciya a ƙasan carpet sosai take kuka domin ganin zallar ɓacin rai a fuskar Abban nata, wanda bata taɓa ganin ba.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan mintinan ashirin, zuwa lokacin M Madawaki ya fara fita daga cikin nutsuwarsa, kiran number Dr Omar ya sake yi, cikin mawuyacin hali.

Dr Omar na ɗaga wa ya ce.. 
"Sorry Mr Madawaki na bawa Yusuf yanzu za kawo ka shanye duk ko za'a dace.."

Cilli ya yi da wayar yana komawa toilet ruwa mai sanyin ya sakarwa kansa, tare da lumshe idanuwansa shi ɗaya ya san halin da yake ciki.

Shatu kuwa tana kwance a tsakiyar falon sai kuka take har lokacin, Yusuf ne ya shigo da sauri, amma ganin Shatu kwance ya saka shi dakatawa yana kallon gefenta.

"Ina Sir?"

Sake fashewa ta yi da kuka tana da cewa.
 "Abbana ya shiga bedroom ɗin can, ya kori ne wai na tafi gida...."

Shiru ta yi gani Yusuf ya nufi bedroom ɗin sai da ya buɗe ƙofa sannan ya juyo yana kallonta, dawowa ya yi da baya yana ajiyar mata maganin hannunsa ya ce.
"Ga wannan ki bashi ya sha yanzu shi zai taimaka masa.."

Ɗaukar maganin ta yi tana kallon fuskar Yusuf ɗin cikin sanyin murya ta ce.
 "Uncle Yusuf, wai mai yake damun Abbana ne?Mummy ta ba ni magani na saka masa a coffee, kai ma ka ce na ba shi....."

"Wait a minute Miss Shatu yanzu kin sakawa Sir wani magani? Kuma ya sha?"

Ɗaga masa kai Shatu ta yi tana nuna masa sauran coffeen ɗin da M Madawaki ya rage, ɗago kansa Yusuf ya yi tare da buga hannunsa a kujera, cikin zafin zuciya ya ce.
"Kina hauka ne? Kin san halin da yake ciki? "Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!.."

Fashewa ta yi da kuka za ta yi magana Yusuf ya yi mata tsawa tare da nuna mata hanya.
"Maza shiga ki kai masa.."

Da sauri Shatu ta shiga bedroom ɗin Yusuf da yake tsaye a bakin ƙofa ya tura ƙofar, zama ya yi a gefen kujera yana cewa..
"Sir ka yafe Ni ba zan iya ganinka a halin da kake ciki ba, ba Ni da zaɓi..."

Shatu kuwa cikin kuka ta shiga ciki, tsayawa ta yi tana kallon room ɗin babu kowa sai ƙamshin turarensa, duba shi ta fara yi tare da kiran sunansa, bakinta ne ya fara rawa sakamakon M Madawaki da ta ga ya fito daga toilet ɗaure da towel ƙarami yana tafiya a hankali.

Hannayenta ta saka tana rufe fuskarta, tare da juya masa baya, lumshe idanuwansa ya yi tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ƙaraso inda take tsaye, rungumota ya yi ta baya tare da kwantar da kansa a kafaɗarta yana lumshe idanuwansa dalilin shaƙar ƙamshin turaren jikinta.

Juyowa Shatu take son yi amma M Madawaki ya yi mata kyakkyawar runguma kuka ta fara tana san cire jikinta daga nasa, domin ko numfashi mai kyau bata iya yi, sautin kukan ta ne, yasa yanayinsa sake sauyawa, juyo da ita ya yi tare da rungumeta yana ƙoƙarin fara samun nutsuwar gudanaar da abin yake so.

Cike da tsoron Shatu ta rungumoshi da hannayenta biyu biyu, ajiyar zuciya ya sauke dalilin saukar tafin hannuwanta a jikinsa, ɗagata ya yi cak ya dora saman Bedside drawer tare da zubar takandunsa da suke kai, matseta ya yi a jikinsa tare da haɗe fuskarsu ya fara kissing ɗinta a haukace.

Zaro ido Shatu ta yi ganin yadda yake kissingta babu wasa, ga riƙon da ya yi mata, babu damar ƙwace kanta, ƙanƙameshi ta yi babu shiri tana fitar da numfashi daƙyar.

Tana ji ya fara yaga duka kayan jikinta, ta yi saurin riƙe hannunsa tana son hanashi,amma babu dama, haka tana ji tana gani ya yaga duk wata sutura da take jikinta yana wurgi da su, fashewa ta yi da kuka tana rintsa idanunwata.

Da sauri ta buɗe idanunwata sakamakon saman bed ɗin da ya kwantar da ita, tashi ta so yi,amma M Madawaki bai bata damar hakan ba, ta so ta ƙwace kanta domin ta hana Abbanta aikata barnar da yake son yi amma hakan ya gagara, sai ma loosing control da M Madawaki ya samu.

Wata irin sha'awa ce mai ƙarfi ke fizgarsa wanda ya saka shi kasa controlling kansa zuwa gareta sama sama yake jin sautin kukanta wanda yake shiga kunnesa da zuciyarsa direct.
 
Wani kuka mai ƙarfi gaske ne ya kama Shatu, tana ƙoƙarin ture shi da hannayenta dan ceton kanta dalilin wata azaba ta ji ta a ciki, bata san lokacin da zuciyata ta tsaya da aiki ba, numfashinta na ɗaukewa gabaɗaya domin abubuwan sun yi mata yawa duk a lokacin ɗaya.

Tana cikin wannan halin ne M Madawaki ya karɓi budurcinta wanda ta gama tanadar wa Rahim Matawalle, duk abin da M Madawaki yake bata sani ba, domin tun kafin lamarin ya yi nisa ta tafi suman wucin gadi, bata san ta yadda aka yi abubuwan suka faru ba.

Shi ma a ɓangarensa bai san da wacce yake tara ba, sai da buƙatarsa ta biya masifar da yake ji, ta fara raguwa hankalisa ya dawo jikinsa.

A hankali ya zame ya kwanta gefenta bayan dukkanin buƙatuwarsa sun biya, amma duk da haka wani irin zafi zuciyarsa da gangar jikinsa ke masa, zuciyarsa sai bugawa take kamar za ta fito.

Kansa ya ɗago yana kallon room ɗin, idanuwansa ne suka sauka akan Shatu da take kwance a gefensa, sake buɗe ido ya yi domin tabbatar da wacce take a kwance, zubura ya yi yana tashi zaune.

Fuskar Shatu ya shafa tare da lumshe idanuwansa da wasu zazzafan hawaye suka zubo, hannayensa ya saka yana dukan kansa domin gani yake mafarki ne, hannayenta ya kamo domin tabbatar da gaskiyar abin da idanuwansa suke gani.

Wani zazzafan kuka ne ya ƙwace masa tare da rungumota jikinsa, sosai yake zubar da hawaye, ganin alamu bata numfashi ne ya saka shi kwantar da ita.

A hankali ya zura ƙafafunsa ƙasa ya miƙe tsaye, yana nufar hanyar toilet ba tare da ya waiwayoba domin waiwayowar tasa ya sake ganin mummunan aikin da aikata zuciyarsa ce za ta fasahe, domin barazanar bugawar da take masa, ga tsananin dana sanin da yake ciki,a haka ya nufi toilet ya shige.

Ruwan sanyi ya sakarwa kansa yana dafa bango idanuwansa da suka yi jajir ya rintse sai yanzu yake tino sauti kukanta da ya ji a lokacin, fashewa ya yi da matsanancin kuka,ya jima sosai kafin ya fito,dalilin wani zazzaɓi mai ƙarfin gaske da ya kawo masa farmaki, domin har hucin zafi jikinsa yake ji, ga zuciyarsa kamar ta faɗo.

A hankali ya kalli gadon da jajayen idanuwansa da suke cike da nadama ganinta kwancen cikin yanayi na tsananin galabaita da azaba, ba sai an faɗa masa ba, ya san azaba ce ta sauya mata kamanni lokaci guda.

A hankali ya ƙaraso gadon tare da kallon fuskarta da take ya mutse ta yi jajir, ga lips ɗinta sun bushe domin zafin kisses ɗinsa da ya ringa sakar mata masu zafin gaske.

Ɗauke idanuwansa ya yi tare da ɗagata cak zuwa toilet wanka ya yi mata, yana kunyar rayuwarsa gabaɗaya, tun da yake bai taɓa shiga halin nadama da kunyar rayuwarsa gabaɗaya ba irin yau, da wane idon zai kalli Yarinyar cikinsa da duniya take mata kallo 'Ya ɗaya tilo gare shi, har ya gama mata wanka suka fito bata motsa ba.

Cike da takaicin kansa ya ɗauko kayanta da ya yi cilli da su, ganinsu a yage ne ya saka shi jiginar da kansa a bangon room ɗin, tsaki ya yi yana ɗauko jallabiyarsa ya saka mata domin ganinta babu kayan ma, wata masifar yake jefa shi.

Zaman rashin mafita ya yi a gefenta,har aka kira sallar asuba, kasa fita sallar ya yi dole sai a gida ya yi, sannan ya fito falo a nan ya ga wayoyinsa, ɗaya ya ɗauka tare da kiran Yusuf.

Cikin sauri Yusuf ya ɗaga wanda gabaɗaya a daren bai yi bacci ba, jin M Madawaki ya kasa magana ne, jikin Yusuf ya yi sanyin tare da kashe wayar, ya buɗe ƙofar dama tun fitowarsa daga masallaci yake tsaye a bakin ƙofar.

A tsaye ya samu M Madawaki cikin damuwa da nadama, ƙasa Yusuf ya yi da kansa domin ko M Madawaki bai faɗa masa komai ya san abin da ya faru.

Cikin ƙaramin sauti ya furta.
"I need a female doctor ban da Dr. Nadraa, I want wata who doesn't know me."

"Okay Sir, akwai wata close to my house, sunanta Dr. Maryama, she works a AA Shazalee Hospital, I don't think ta san fuskarka."

Shiru ya yi, domin ya tafi wani tuanin da ban har Yusuf ya buɗe ƙofa zan fita ya ce.
"Bana so MAMUB ya san cewa Eshaa slept here and duk wani information."

"In sha Allahu Sir."
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Tun fitar Yusuf yake zaune a falon ya kasa komawa bedroom ɗin, yana cikin wannan halin ne A Maina ya kira shi, ɗaurewa ya yi suka yi magana domin ya san zai iya fahimtar yana cikin damuwa.

Bayan A Maina ya gama yi masa bayanin ne cikin sanyin murya ya ce.
"MAMUB ina so zan tafi Abuja zuwa karfe takwas.."

"Abuja kuma? Me zaka yi?"

Rasa abin da zai faɗa masa ya yi har sai da A Maina ya sake magana sannan ya ce.
"Eshaa I will take her to rest and ka sanar da su Daada we will spend one week, kai ma ka yi zamanka, I don't want rakiya."

Dariya A Maina ya yi tare da cewa.
 "Hajarah ce ta koraka ai na san ita ce ta saka mata magani....."

Katse A Maina ya yi dalilin hucin da zuciyarsa ta fara ko sallama bai yi masa ba ya kashe wayoyinsa gabaɗaya, yana zaune Dr Maryama da Yusuf suka shigo.

Gaida shi ta yi ya amsa ciki ciki yana nufar hanyar bedroom ɗin, Yusuf ne ya ce ta bishi, shi kuma ya fita daga falon, a hankali ta shiga ciki, zaune ta same shi a gefen bed ɗin sai Shatu da take kwance.
"I want you to examine her, she was raped."

Kallonsa Dr Maryama ta yi, na ɗan lokaci sannan ta ce.
 "Can you please step out a bit."

Tashi ya yi, ba tare da ya ce komai, kayan hannuta ta ajiye, tare da fara duba Shatu cikin nutsuwa, ta jima sosai kafin Shatu ta sauke ajiyar zuciya, a lokacin M Madawaki ya shiga sama da sau goma.

Shigowarta ta ƙarshe ne Shatu ta sauke ajiyar zuciya, tare da fashewa da sabon kuka, lumshe idanuwansa ya yi yana godiya ga Allah da Shatu ta farfaɗo, a hankali ya juya ya fita.

Rarrashinta Dr Maryama ta yi tare da duba manyan raunikan jikinta sannan ta yi treating ɗinsu, ta yi mata allura,tun da Dr Maryama ta fara aikin Shatu take ihu har aka gama komai. 

Allurar da Dr Maryama ta yi mata ce, ta ji sauƙi ciwon da take ji yana fara raguwa jikinta yana sakewa ta lumshe idanuwa baccin wahala na dauketa, remote ɗin AC Dr Maryama ta ɗauka tare da rage karfinta.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A zaune ta same ya haɗa kai da gwiwa, maganar da ta yi ce ta saka shi ɗago jajayen idanuwansa yana kallonta.
"Sir na kammala yanzu haka na yi mata allurar bacci domin ƙwaƙwalwarta ta huta, amma ta samu raunika da yawa..."

Cikin ƙaramin sauti ya ce.
 "Ki zauna har ta farka, ko da wata matsalar."

"Okay zan dawo akwai patient da zan duba."

Shi ne ya buɗe mata ƙofa ta fita, Yusuf ne ya rakata ta duba patient ɗin sannan ya dawo da ita har lokacin M Madawaki yana zaune a falo, bedroom ɗin ta koma tana zaman jiran farkawar Shatu.

Sai karfe sha biyu na rana ta farka, da kuka Dr Maryama ce ta taimakata zuwa toilet, zama ta yi a toilet ɗin tana fashewa da sabon kuka, Dr Maryama ce ta sake komawa toilet ɗin cike da tausayawa take kallonta cikin sanyin murya ta ce.
"Sir Mijinki ne ko Babanki?"

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol