Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by Maryam Usman · KOWA DA RABONSA

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 14
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━


MAMUB shiga ka fito mu wuce jirgin ƙarfe uku za mu tafi.."

Tsaki ya yi tare da tashi bedroom ɗin Shatu ya shiga, a zaune ya sameta, zama ya yi yana kwantar da kanta a kafaɗarsa tare da shafa gashin kanta.
"Eshaa!"

A hankali ta ɗago kanta, tana kallon fuskarsa..
"Zan yi tafiya Germany sati biyu zan yi don Allah ki kula."

Har zuciyarta ta ji daɗin wannan tafiyar tasa ko babu komai za ta huta, ɗaga masa kai ta yi..

Murmushi ya yi yana kamo fuskarta.. 
 "Eshaa ba za ki min magana na ji muryarki ba?"

Hawayen da suka zubo mata, ta goge tana buɗe bakinta da take ji yana mata nauyi ta ce..
"Allah ya kiyaye don Allah ka ce Abbansu Nadiya ya yi haƙuri na shiga wajen su Daada bana jin daɗin zama ni ɗaya.."

Rungumota ya yi tare da cewa.
 "Shi kenan ki shiga har islamiyya ma ki koma amma duk dare ki dawo nan ki kwana."

Ɗaga masa kai ta yi, tana cire jikinta daga nasa, kissing ɗin lips ɗinta ya fara kamar sabun maye, shiru ta yi tana rufe ido har ya gama ya fice bata buɗe ido ba, lokacin da ya fito A Maina baya falon bedroom ɗinsa ya shiga tare da fito da kayansa.

Falon Daada ya shiga, suka yi sallama da Yan uwansa kasa haƙuri Daada ta yi ta ce.
"Muhammad."

Baba Malam ne ya kallonta domin san abin da za ta ce.
Juyawa Baba Malam baya ta yi tare da cewa.
 "Amma dai Shatu M Madawaki a gida za ta zauna saboda da islamiyya ko?"

Ɗaga mata kai ya yi tare da ficewa, ya so ya koma wajen Shatu amma kiran da A Maina yake masa ya saka shi fitowa, Yusuf ne ya karɓe kayan hannunsa suka fita daga gidan.

Shatu kuwa gajiya ta yi da zaman ta fito Baba Jamila ta samu da Hindu suna aiki, zama ta yi tana turo bakinta wanda ya gama shan tsotsa a wajen Abban nata ta ce.
"Baba Jamila Abbana ya fita?"

Murmushi Baba Jamila ta yi tare da cewa.
 "Ya fita tun ɗazu, na kawo miki wani abuncin?"

Wayarta ta ɗauka tare da cewa.
 "A'a zan ci a wajen Daada."

Hanyar falon Daada ta nufa Baba Jamila ta bi bayanta da kallo, Hindu ce ta kasa haƙuri tana kama bakinta ta ce.
 "Uhm Baba Jamila Ni kam ba ki kula da yanayin Shatu M Madawaki ba, duk ta sauya ta koma shiru shiru....."

Tashi Baba Jamila ta yi tare da cewa.
 "Ki yi aikinki shi ya fi miki sauki."
━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Zaune suke a falon duk matan gidan sai Rahmah da suka shigo, Nanny ce take shafawa Daada maganin ciwon ƙafa, sautin takalminta ne ya sa duk suka juya, san ita ce duk gidan take amfani da takalmin mai tsini.

Waya ce a kunnenta, shiru duk suka yi suna kallonta, ƙaramin murmushi ta yi tare da cewa.
 "Ai na ji sauƙi yanzu."

Gyaran zama Daada ta yi tana zuba mata ido, sai da ta zauna sannan ta ce.
"Shi ne ya ce ki zo? Amma tare za mu kwana?"

Dariya ta yi domin jin abin da Dr Maryama take cewa, kashe wayar ta yi tana kallon fuskar Daada wacce ta zuba mata ido.

Cikin sanyin murya ta ce.
 "Hey Daada."

Washe baki Daada ta yi tare da cewa.. 
 "Ba ki da lafiya ne na ji kina magana......"

Tashi Shatu ta yi tare da cewa.
 "Ni babu abin da yake damuna."

Rahmah ta rungume tana gaida sauran matan da suka kallonta, cire jikinta ta yi daga na Rahmah tana kallon mai aikin Daada.
"Baba Hauwa ina so zan ci abinci amma kaɗan.."

Jikin na ruwa Baba Hauwa ta nufi hanyar kitchen su Meerah ne suka shigo, ganin Shatu zaune suka fara ihu suna faɗawa jikinta, lumshe idanuwanta ta yi domin har lokacin tana jin raɗaɗin ciwon jikinta.

Cike da masifa Daada ta kawo musu duka, tashi suka yi duk suna dariya, a hankali Inayaa ta ƙaraso tana mai sake kallon fuskar Shatu wacce ta sauya mata, murza ido ta sake yi tana buɗe wa a kan Shatu da take murmushi.

Baba Hauwa ce ta kawo mata abincin Rima ta karɓa suka shige bedroom ɗin Rima, a can ta ci abinci sannan ta kwanta suna hira har ta yi bacci, bata farka ba, sai lokacin tafiyarsu islamiyya cikin sanyin jiki ta shirya suna kallonta.

Dafa kafaɗarta Meerah ta yi tare da cewa.
 "Shatu M Madawaki na ga alamun fa, ba ki da lafiya ki yi haƙuri gobe sai muje islamiyyar tare."

Lumshe ido ta yi tare da nufar hanyar fita, bayanta duk suka bi, mamaki ne ya kama matan gidan ganinta da Unifrom a jiki, shiru duk suka yi babu mai bakin magana, Baba Jamila ta kira.

Zama ta yi domin jiri da take ji cikin sanyin murya ta ce.
 "Baba Jamila ki ɗauko min key ɗin motata a bedroom ɗinna......."

Daada ce ta shigo ta katse mata maganar tana cewa.
 "Ita Jamila ta san bedroom ɗin naki? Ina ma za ki je naga Unifrom a jikinki?"

Rima ce ta matso kusa da Daada ta ce.
 "Allah Daada bata da lafiya, yanzu Meerah ta gama faɗa mata ta yi haƙuri gobe ta je school ɗin amma ta yi shiru."

Kafin Daada ta yi magana Shatu ta miƙe tsaye hanyar ɓangaren Abbanta ta nufa babu komawa ta fito da key ɗin, duk maganar da Daada take yi sai da ta fita, ko su Rima bata ɗauka ba ta ja motar da gudu.

Girgiza kai Baba Malam ya yi wanda ya shigo yanzu Daada ya ga tsaye a bakin ƙofar shiga falon tana kallon motar da Shatu ta ja da mugun gudu, ciki ta koma cike da damuwa.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Tun da su Rima suka shiga aji suke mata magana babu wanda ta kula sai da aka tashi, lokacin ma tambayarsu ta yi akwai wacce za ta ja motar su koma gida.

Nadiya ce ta ja motar domin ita bata zo da mota ba, har suka isa gida bata yi magana ba, ɓangaren Abbanta ta shiga ta ƙofar baya, domin ta san Daada tana jiran dawowarta, wanka ta yi sannan ta yi sallar magriba, sai lokacin ta shiga falon Daada.

Abubakar Madawaki ta samu da Baba Malam, sai Baba Haruna a zaune Abubakar Madawaki kawai ta gaida ta shige bedroom ɗin Meerah, girgiza kai Baba Malam ya yi yana murmushi.

Sai karfe takwas suka fito cin abinci, ko a wajen cin abincin ma, babu wata maganar kirki da ta yi, abincin ma kaɗan ta ci, ta miƙe tsaye domin wayarta da Abban nata yake kira.

Rungume Daada ta yi tare da cewa.
 "Sai da safe Daada."

Har ta juya ta dawo hannun Baba Malam da yake cin abinci ta kamo tare da yin murmushi ta ce.
"Sai da safe Baba Malam, na san kai ne ka zuga Abbansu Nadiya ya yi yanke min wannan hukunci ko? To Abbana ya ce ina fitowa, kuma gobe ma har shopping zan fita..."

Kiran da ya sake shigowa ne ya sa Baba Malam kallon wayar, sunan da ya ganin ne ya saka shi kallonta, juyawa ta yi tana fita daga falon, sai da ta zauna a falonsa sannan ta ɗaga kiran.
"Assalamu alaikum."

Gyara kwanciya M Madawaki ya yi tare da yin murmushi, cikin nutsuwa da yanayin da yake ciki na kewarta ya ce.
"Eshaa ya jikin ya yi sauƙi sosai?"

A taƙaice ta ba shi amsa da cewa.. 
 "Eh."

"Okay ba na kira video call sai na tabbatar.."

Ita ce ta fara kashe wayar tana shiga bedroom ɗinta, tana kwance ya kira, tun da ya kira bai yi magana ba, sai kallonta da yake, sai da ta yi bacci sannan ya kashe wayar, yana shiga bedroom ɗin A Maina, bacci ya samu yana yi...

Zama ya yi na ɗan lokaci domin ya kasa kwanciya, har karfe biyu yana zaune a gefen A Maina da yake bacci, farkawa A Maina ya yi yana kallon fuskarsa.

A hankali ya tashi zaune tare da cewa.
 "Lafiya akwai abin da yake damunka ne?"

Tsaki ya yi tare da juyawa zai fita dariya A Maina ya yi tare da cewa.
 "Wai MAMUB ko shirya maka komawa gida zan yi gobe?"

Bai yi masa magana ya fice, murmushi A Maina ya yi tare da komawa kwanciyarsa.
━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A haka M Madawaki ya fara rayuwar ciki rashin sakewa, kullum baya iya bacci sai dare ya raba, ga Shatu tun da ya yi sati ɗaya ta fara kashe wayarta da daddare domin takura mata da yake da kira.

A ɓangaren Shatu kuwa alhamdulilah jikinta ya yi sauƙi ta koma rayuwarta, kullum suna tare da su Meerah sai ƙarfe goma zuwa sha ɗaya take komawa ɓangarensa, tun bayan tafiyarsa ba ta sake shiga master room ɗinsa ba.

Kullum sai M Madawaki ya kiranta video call tun bata iya magana har ta saki jiki take masa magana, ranar da suka cika sati biyu, ya biyo jirgin ƙarfe uku na dare ya dawo, duk yadda A Maina ya so ya yi haƙuri da safe su dawo babu wanda ya kula a cikinsu shi da Yusuf.

Da asuba ya sauke sai da ya yi sallar asuba sannan ya shiga cikin gidan, lokacin da ya shiga bedroom ɗinta ko bacci bata tashi ba, wanka ya fara yi sannan ya tasheta, mamaki ta yi tana kallon fuskarsa.

Bayan ta yi sallah ne ta zauna a gefen bed ɗin ganinsa a kwance, cikin sanyin murya ta ce.
 "Sannu da dawowa Abbana yaushe ka dawo?"

Lumshe idanuwansa ya yi tare da saka hannayensa yana janyota jikinsa, a hankali ya kwantar da kansa a bayanta cikin ƙaramin sauti ya furta.
"Cikin dare na dawo.."

So take ta tashi daga saman ƙirjinsa da ya kwantar da ita amma ya hana hakan ta hanyar kwantar da kansa da ya yi a bayanta, sun jima a haka sannan ya ɗago kanta buɗe idonuwanta ta yi tana kallon fuskarsa, lumshe idanuwansa ya yi tare da ɗora lips ɗinsa saman nata.

Cikin sanyin da nutsuwa ya fara barkita mata ƙwaƙwalwa, ta ko'ina saƙonin yake aika mata.

Yadda komai ke gudana ne ya sake gigita ƙaramar ƙwaƙwalwarta da wani hot romance ne yake wakana, duk abin da yake saman bed ɗin nan sai da M Madawaki ya zubo da su har pillows domin gani yake za su rage masa jin daɗi.

Duk wahalar da ya kwaso a Germany sai da ya sauketa, domin a wahalalce ya yi satin biyu nan, samun abin da yake so ne ya saka shi sauke ajiyar zuciya.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
 Fitowarsa kenan daga wanka ɗaure da towel ɗinta a ƙugunsa,idanuwansa ya ɗago yana kallon fuskarta da idonsa wanda har lokacin bai gama komawa daidai ba, yana kallon fuskarta wacce hawaye suke kwance a samanta, gyara kwanciya ta yi tare da jan blanket tana rufe kirjinta da suka yi jajir dalilin cakudar da suka sha a hannun Abban nata.

A hankali ya zauna bakin bed ɗin tare da saka hannuwansa duk biyun yana janyota zaunar da ita ya yi, yana kallon yadda ta kasa zama daidai saboda raɗaɗin da take ji a ciki jikinta, babu shiri ta bude idanuwanta da sauri cikin azaba tare da rungumoshi, hannayensa ya sa tare da rungumar da kyau, wani sabon yanayi na fizgarsa na komawa gareta amma ganin hanli da take ciki ne ya yi controlling kansa ta hanyar danne abin yake ji.

 A hankali ya miƙe tsaye da ita a jikinsa ya nufi toilet tana ji ya sakar musu ruwa yana riƙe da ita, sun jima a haka sannan ya sakata cikin ruwan zafi, yana zaune a gefenta bayan wasu mintinan ya sake mata wani, yanzu kuwa kuka ta fara tana nunawa bata so.

Bai kulata ba, haka ya maida ita cikin ruwan zafi, na ɗan lokaci sannan suka fito, kaya ya saka mata shi kuma ya fita zuwa nasa bedroom ɗin, babu jimawa ya dawo a kwance ya sameta tana rawar sanyi.

Tea ya karɓo a wajen Baba Jamila ya bata, kaɗan ta sha ta amayar da shi, cikin sanyin jiki ya kwanta a gefenta yana sakata a jikinsa, bacci suka yi mai nauyi tsawon lokaci, basu tashi ba,sai ƙarfe ɗaya, Masallaci ya fita ita kuma ta yi sallah a gida.

Tana idar da sallah ta saka dogowar riga ta fito falon Daada ta wuce, a can ta samu Daada na mitar Shatu bata fito ba, zama ta yi tare da cewa.
 "Gani na fito me zan miki?"

Dariya Rima ta yi tare da cewa.
 "Yawa ga Shatun sai ki bata abin da za ki bata tun safe take masifar ba k.........."

Hannayenta ta saka tana rufe bakinta, tare da zaro ido, tana mamakin yaushe ya dawo, a hankali ya zauna yana kallon fuskar Shatu, cike da mamaki Daada ta ce.
 "Yaushe ka dawo? Ina Abubakar ɗin?"

A hankali kamar mai ciwon baki ya ce.
 "Da asuba, na same ku lafiya?"

Murmushi ta yi tare da kallon fuskar Shatu tana washe baki ta ce.
 "Alhamdulilah amma Abubakar ya ce yau karfe biyu na rana jirginku zai sauka."

Tashi ya yi yana nufar hanyar dinning room ɗin ya ce.
 "Ni jiya na tawo.Ina buƙatar breakfast."

Shatu ta kalla tare da cewa.
 "Tashi ki taimakawa Abbanki da breakfast..."

Kwanciya ta yi tana lumshe ido, ganin ba tashi za ta yi ba, Daada ta saka Rima gabatar masa da abin da zai buƙata, har ya gama Shatu bata motsa ba, shigowar Anne ce ta sa Shatu komawa bedroom ɗin Daada tana kwanciya ta yi bacci.

Har yamma bai samu damar ganinta ba, kuma har lokacin bata tashi daga kwanciyar da ta yi ba, Daada ta yi faɗa har ta haƙura, sai gabanin sallar magriba sannan ta shiga toilet ta yi wanka ta sallah.

A hankali ta fito falon A Maina ta samu da duk manyan gidan a falon, ƙasa ƙasa ta gaida su ta juya za ta koma Daada ta ce.
 "Wai Ke! Me yake damunki tun yaushe kike kwance yanzu ma kwanciya za ki koma, yau fa ban ga kin ci abinci ba..."

A hankali A Maina ya ɗago kansa yana kallon fuskarta, gefen M Madawaki ya kalla ya ga ya kafe Shatu da idanuwasa, gyaran murya ya yi tare da cewa.
 "Dawo ki ci abinci, in kuma baki da lafiya ne ki sanar da mu.."

Dawowa ta yi ta wuce dinning room ɗin tea kawai ta sha, shi ma babu madara ta taso, message ɗin M Madawaki ta ga, na kada ta koma bedroom ɗin Daada, tana karantawa ta wuce ɓangarensa.

Sallar isha'i ta yi ta kwanta a falo, babu ɓata lokaci bacci ya ɗauketa, karfe tara suka shigo shi da A Maina sai Yusuf da yake bayansu, kallon ɗaya A Maina da Yusuf suka yi mata suna ɗauke ido.

A hankali ya saka hannayensa ya ɗagata cak bedroom ɗinta ya kaita tare da rufe mata ƙofa a hankali ya zauna yana kallon fuskar A Maina da yake magana.
"Ya kamata ka saka ido sosai a kan Matarka kada ta sake samun wani cikin ta yi mana asarar shi...."

Murmushi Yusuf ya yi, domin shi ma abin da zai faɗa kenan dan babu dama ne, ko ɗago kai M Madawaki bai yi ba, magunguna suka yi masu muhimmanci, sannan duk suka fita,rufe ƙofa ya yi yana cin abincin da Baba Jamila ta ajiye.

Bedroom ɗin ya shiga yana tasota abincin ya fara bata, duk da tana nunawa bata so, sai ta ci da yawa sannan ya barta, zaunar da ita ya yi a gefensa shi kuma ya fara aiki, a hankali ta kwanta a jikinsa tare da saka hannayenta ta rungumoshi.

Dakatawa ya yi da aikin yana kallon fuskarta ajiyar zuciya ya ji tana saukewa, a hankali har bacci ya ɗauketa, dole duk son da yake na kasance da ita a daren, sai haƙura ya yi ganin tana bacci wanda yake nuna tana jin daɗinsa.

Tsawon sati biyu suna haka duk daren duniya kafin ya dawo ta yi bacci duk tashin da zai mata bata farkawa, dabara ya samu yana idar da sallar asuba zai dawo gida a lokacin ita ma ta tashi, a nan yake biyar buƙatarsa.

Cikin lokacin kaɗan ta sauya shi ma ya ga alamun haka, zargin ya fara ko maganar A Maina zai bi ya saka a duba masa ita ko ciki ne da ita, tun da shi bai taɓa ganin mace mai ciki ba, bai san alamumin ciki ba.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Dr Maryama ya yi wa message ta zo ta duba masa Shatu, lokacin da ta zo Shatu bata ɓangarensa shi da kansa ya rakata falon Daada, a kwance ya sameta a cinyar Rahmah sai Daada da take faman faɗa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol