Free chapter · Read without an account

Chapter 16

by Maryam Usman · KOWA DA RABONSA

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 16
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

Shiru ya mamaye room ɗin, a hankali Shatu ta ɗago jajayen idanunta tana kallon Baba Malam, sai kuma ta mayar da dubanta ga Dr Maryama.
"Aunty Maryam, ni dai ina so ki taimaka min bana son na sake shiga wannan halin ina shan wahala."

Cikin tausayawa Dr Maryama ta matso kusa da ita, ta riƙe hannunta.
"Shatu, ki saurare ni da kyau, abu na farko da nake so ki sani shi ne, ba ke kika jawo wannan abin da yake faru ba, kuma zubar da ciki sau biyu ba yana nufin cewa ba za ki iya haihuwa ba."

"Abun da za mu duba shi ne muna da bukatar mu bincika dalilan da ke jawo hakan A likitanci, muna kiran wannan da (Recurrent Pregnancy Loss)."

Ɗago kai M Madawaki ya yi, hankalinsa ya furta
"Recurrent Pregnancy Loss?"

Eh, Sir. Ma'anarsa mace ta fuskanci zubar da ciki akai-akai. Akwai dalilai da dama da ke iya jawo hakan, kuma muna bukatar a yi bincike mai kyau kafin a yanke hukunci (diagnosis)."

A hankali A Maina ya gyara zamansa yana kallon fuskar Dr Maryama ya ce.
"To, wane irin bincike za a yi?"

Shiru dr Maryama ta yi na ɗan lokaci tana duba takardar da ke gefenta ta ce.
"Da farko ina son mu binciki tsarin mahaifarta ta hanyar Pelvic Ultrasound. Za mu kuma yi wasu gwaje-gwajen jini domin mu tabbatar da cewa babu wata matsala a hormones ko kuma wasu cututtuka da za su iya shafar ɗorewar ciki."

 Juya takardar hannunta ta yi tare da nunawa A Maina wasu bayanai, ta ce.
"Ɗaya daga cikin cututtukan da muke bukatar mu tabbatar da akwai shi ko a'a shi ne Antiphospholipid Syndrome, wanda aka fi sani da APS. Wannan wata cuta ce ta garkuwar jiki (autoimmune) da ke iya ƙara hadarin zubar da ciki akai-akai......"

Sayyid Madawaki ne ya yi saurin katseta tare da cewa.
"Kenan cutar ce take sa cikin ya zube?"

"Ba lallai ba ne ita ce matsalar Shatu ina bayyana muku ne, abubuwan da za mu bincika, haka kuma akwai matsalar chromosomes da wasu matsalolin tsarin mahaifa da za su iya haifar da hakan."

Shiru duk suka yi suna sauraron bayaninta, tashi Shatu ta yi cikin sanyin murya ta ce.
" Doctor, ni ba zan iya haihuwa ba kenan?"

Murmushi Dr Maryama ta yi, tare da kamo hannayenta ta ce.
"A'a, Shatu. Ba haka nake nufi ba fuskantar zubar da ciki akai-akai ba yana nufin wata barazana ce ba. Mata da yawa da suka fuskanci zubar da ciki sau biyu ko fiye, daga karshe suna samun ciki har haihuwa."

A hankali M Madawaki ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya furta.
"Yanzu wane mataki za mu ɗauka?"

"Za mu fara da cikakken bincike, zan duba sakamakon Ultrasound ɗin da aka yi mata a lokacin da take da cikin idan akwai buƙatar ƙarin bincike, za mu yi shi, ba na son mu yi gaggawar ba ta maganin da ba mu tabbatar tana buƙata ba."

Baba Malam ne ya ce.
"Allah ya sa a gano abin da yake damunta."

"Amin," duk suka amsa.

A ranar a Hospital ɗin Shatu ta kwana sai washegari Dr Nadraa ta sallamesu.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
HAJARAH.

Abubuwan duniya sun isheta komai ya tsaya dama M Madawaki ne yake taimaka mata, ganin za ta ƙashe kanta ne ta koma koyarwa.

Ku san kullum sai ta zo bakin Gate ɗin Madawaki Dynasty ko za ta ga Shatu, tun da in ta kirata bata shiga, kuma dama iya number Shatu take da ita sai ta M Madawaki, shi kuma ya jima da yin Black contact ɗinta.

Mahaifinta ne ya kwanta jiya sakamakon kama Abdul Rahman da aka yi, sun yi wa yarinya yar shekara bakwai fyade, hawan jini ne mai ƙarfin gaske ya kada Malam Sani.

Lokacin Mummy bata da kuɗi dole sai Madawaki Hospital ta yanke shawarar zuwa, ko da suka je Dr Nadraa ce ta duba shi, tare da yi masa duk abin da yake buƙata, sai da suka yi kwana biyu a Hospital ɗin.

Dr Nadraa ce ta kirata office ɗin, bayan ta zauna Dr Nadraa ta kalleta tare da cewa.
 "Miss Hajarah na ji labari marar daɗi da ya faru, Allah ya kiyaye gaba, ina me sanar da ke wani mummunan labari, wanda yafi na mutuwar aurenki.."

Cikin sanyin jiki Mummy ta ce.
 "Dr Nadraa ke ma kin san halin da nake ciki ko? Don Allah ki taimaka min da number Shatu M Madawaki wacce take shiga, na san ita ɗaya ce za ta saka M Madawaki ya maida Ni gidansa......."

Murmushi Dr Nadraa ta yi tana cewa.
 "Ai mummunan labarin da zan baki kenan, M Madawaki yana haihuwa, sannan abu mafi munin shi ne, ciki ya yi wa Shatu amma alhamdulilah cikin ya zuɓ......."

"Ciki ciki Dr Nadraa na shiga uku yaushe M Madawaki ya karɓi Shatu a matsayin matarsa Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Wai dama yana haihuwa?"

"Tabbas yana haihuwa domin da bakinsa na ji ya faɗa a gabana, Ni na shiga tashin hankali sosai domin duk zaman da nake yi shi nake jira, ina buƙatar na yi aure amma nakasa saboda da tsananin kaunar shi da nake yi..."

Fita Mummy ta yi daga office ɗin a ranar bata iya bacci ba, ita da Amina suka fara yawan neman mafita, duk hanyar da suka bi, bata bullewa dole sai wajen Dr Nadraa suka koma, suka haɗa baki.

Domin duk abin da yake faruwa a Madawaki Dynasty tana sanar da su. Tun daga ranar Dr Nadraa ta fara saka ido a kan lamarin Madawaki Dynasty tana sanar da Mummy.

 Tun fara sanar da Mummy Yusuf ya ganota, bai sanar da kowa ba, sai da ya tabbatar ya kamata tana waya tana sanar da Mummy, Shatu ta sake Miscarriage, M Madawaki ya sanarwa, amma bai ce komai ba, dama ya san ba magana zai yi ba.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan wata biyu, duk wani bincike Dr Maryama ta yi amma har lokacin bata samu wata matsalar ba.

A ɓangaren Shatu kuwa ta koma yanayin shiru shiru, bata fiya murmushi ba, sai tana tare da M Madawaki, duk halin da take ciki Daada ta fita shiga damuwa, A Maina ma sosai yake cikin damuwa.

Cikin wata biyun nan ko kwanciya Daada ta ga Shatu ta fiya yi za ta fara cewa ko ciki ne tun Shatu bata jin haushi har ta fara jin haushin Daada, to a ɓangaren A Maina ma haka ne, domin akwai wata rana da M Madawaki bai fito sai yamma da ya tambayeshi abin da ya hana shi fito ya ce Shatu ce take zazzaɓi.

Murna ya fara tare da cewa ai ciki ne da ita shiru kawai M Madawaki ya yi masa domin ya kula A Maina da Daada sun fara samun matsala.

A safiyar wata Asabar, tana zaune a gefen gado tana wayar da Nimrah da aka saka ranar bikinsu da Shamsudeen, zuciyarta ce ta fara tashi da farko ba ta damu ba, domin tun bayan zubar da cikin take fuskantar wasu sauye-sauye a jikinta.

A hankali ta ajiye wayar ta nufi toile, kafin ta isa ta tsaya tana dafe cikinta, tana furta.
"Wayyo Allah!"

Da sauri ta shiga toilet ɗin ta jima sosai sannan ta fito,M Madawaki ta samu zaune yana duba wasu takardu, a hankali ya ɗago yana kallon fuskarta.
"What happened?"

Girgiza kai ta yi tare da zama tana kwantar da kanta a jikinsa.
"Babu komai, kawai cikina ne yake min wani irin ciwo."

Ya ajiye takardun ya yi tare da furta.
"Since when?"

 Miƙe wa ya yi tare da kamo hannayenta.
"Mu je asibiti."

Zame hannunta ta yi tana kwance ta ce.
"A'a Abba, ba wani abu ba ne."

Ya kalleta na ɗan lokaci.
"Eshaa mun yi magana akan lafiyarki bana son ki riƙa raina duk wani abu da kika ji a jikinki."

Dole ba dan ta so ba suka tafi Hospital ɗin.
Bayan sun isa asibiti, Dr Nadraa ce ta fara duba ta, ta tambayi Shatu wasu tambayoyi game da lokacin jinin hailarta na ƙarshe, sannan ta ba da shawarar yin gwajin ciki.

Kafin M Madawaki ya yi magana Shatu ta ce.
"Doctor, amma ai kwanan nan na yi miscarriage."

Murmushi Dr Nadraa ta yi kaɗan.
"That is exactly why we need to check. Pregnancy can occur again after a miscarriage, even before the next menstrual period."

M Madawaki ne ya ce a yi gwajin, Shatu na turo baki suka fita, babu jimawa ta dawo tun da ta shigo bata yi masa magana ba, murmushi ya yi tare da janyota jikinsa.
"Eshaa."

Shiru ta yi bata ce komai ba, domin ita haushi take ji.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan ɗan lokaci sakamakon gwajin ya fito, takardar Dr Nadraa ta nuna masa yana dubawa ya ga, Positive. Lumshe idanuwansa ya yana yi wa Allah godiya, a fili ya furta.
"Alhamdulillah."

Iya A Maina ya sanarwa domin baya so Daada ta sani har ta saka damuwa a raina.

Kwanaki suka fara ja, Shatu tana bin duk umarnin da Dr Maryama ta bata an yi mata gwaje-gwaje, aka kuma tsara yadda za a riƙa bibiyar ci gaban cikin.

Duk da cewa ba a gama binciken dalilan zubar da cikin da ta yi a baya ba, M Madawaki ya yi ƙoƙarin ganin komai yana tafiya yadda ya kamata.

Wata rana da safe yana shirin fita aiki, ya tarar da ita zaune a gefen gado tana kallon cikinta.
"What are you thinking about?"

A hankali ta ɗago kanta ciki shagwaɓeɓiyar muryarta ta ce.
"Abbana kana ganin wannan karon zan haihu lafiya?"

 matsowa ya yi kusa da ita, ya zauna a gefenta tare da kamo hannayenta.
"I hope so, Shatu. We are going to do everything medically possible."

Kanta ta ɗora a kafadarsa.
"Ni dai ina roƙon Allah, ya sa wannan ya zauna"

Sumbatar goshinta ya yi tare da cewa.
"Allah ya ba mu abin da ya fi alheri."
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan sati biyu, duk yadda suke boyewa sai da Daada ta gane, ranar kuwa ta yi kukan farinciki sosai, tun daga lokacin kulawar Shatu ta dawo hannunta.

Satin da ciki ya ciki wata biyu, safiyar wata Laraba, Shatu ta farka da wani irin ciwon ƙasan ciki. 

Da farko ta yi tunanin ciwon da yake zuwa mata lokaci-lokaci ne, amma tana shiga toilet ta ga jini, rufe ido ta yi tare da cewa.
"Abba!"

Ta kira shi cikin wata irin murya da ta sa ya zabura daga inda yake ya shigo da sauri.
"What is it?"

Jinin da ya zubo ta nuna masa cikin firgita, jikinsa ya yi sanyi cikin sanyin murya ya furta.
"Eshaa don't panic. Let's go to the hospital."

Shi ya taimaka mata ta shirya, sannan suka tafi, ko a hanya ƙasa magana suka, sai ita ce take riƙe da hannunsa,shi kuma ya saka samun kalmar da zai yi amfani da ita wajen kwantar mata da hankali.

Suna isa Hospital ɗin Dr Nadraa ce ta karɓeta ta fara duba lafiyarta, aka yi mata gwajin ultrasound.

M Madawaki kuwa yana tsaye ya kasa sanar da wani halin da suke ciki, ko A Maina da ya kira bai sanar da shi ba, yana tsaye Dr Nadraa ta fito, a hankali ya furta.
"Doctor?"

Cike da tausayawa Dr Nadraa ta kalle shi, cikin yanayi na damuwa ta ce.
"Sir, I'm sorry. The scan has confirmed that the pregnancy is no longer viable."

 Lumshe idanunsa ya yi na ɗan lokaci sannan ya furta.
"Are you sure?"

"We have confirmed the pregnancy loss. We need to make sure Shatu is medically stable and discuss the appropriate management."

Ƙasa magana ya yi, cikin sanyin jiki Dr Nadraa ta koma ciki, Shatu ta samu tana hawaye cikin kuka ta ce.
"Dr Nadraa ya sake faruwa ko?"

"Yes, my dear. I'm sorry...."

Katse ta Shatu ta yi tana cewa.
"No! No! Why does this keep happening to me?"

Ta fara kuka mai tsananin gaske ciki tausayi Dr Nadraa ta ce.
"Listen to me, Shatu. Please don't blame yourself. We still need to understand why these losses are happening."

Shiru Shatu ta yi da maganar dr Nadraa ta dubata.

Wannan a ranar suka koma gida, babu wanda ya sani, har ta gama jiyarta ta ji sauƙi sai dai ta sake komawa cikin damuwa sosai ko falon Daada ba ta fita.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol