Free chapter · Read without an account

Chapter 19

by Maryam Usman · KOWA DA RABONSA

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 19
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━


A daren, ya sanarwa da Shatu cikin farinciki ta dago hannayenta tana addu'a.

"Ya Allah, ka sanya wannan tafiya ta Saudiyya ta zama mafita, halin da muke ciki Ni da Abbana, ka biya mana dukkanin buƙatunmu."

Da Amin M Madawaki ya amsa yana rungumota.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Washegari, Jeddah - Saudi Arabia - Dar Al Bait.

Bayan $45M deal ɗin Spain, private jet ya sauka a King Abdulaziz Airport da yamma.

Amma wannan karon M Madawaki ya ki Four Seasons, ya ce wannan tafiyar tasu ce shi da Shatu  ba ta kasuwanci ba ce, shi ya zaɓa musu wuri mafi tsada da kebantacce a Jeddah.Niyama Private Villas - Obhur Bay - Jeddah.

Villa ce mai zaman kanta gabaɗaya a bakin teku, babu makwabta, Gate mai tsayi. Pool mai zaman kanta da ke kallon Red Sea.

Villa ɗin an yi mata ado ne don su - _Ultimate Honeymoon Setup, a saman Bed ɗin ana shimfiɗe shi da fararen rose petals da ja, sannan ana rubutun "Eshaa & Her Abbana - Forever" da hasken mai ƙayatarwa.

A gefe, jacuzzi madara ce da furanni, a saman table ɗin don yin dinner dare, suna shiga Shatu ta dafe kanta tana furta.

"Abbana... this is... fiye da Madrid. This is..."

Ta kasa ƙarasa maganar idonta yana cika da hawaye.

Rufe ƙofar M Madawaki ya yi a hankali, ya karaso, yana cire mata hijabin jikinta a hankali, ya kalli fuskarta.

"Eshaa, ina so mu manta da komai, mu zama mu kadai. No business, no A Maina, no Yusuf. Just you and me."
Rungumoshi ta yi tare da sanya bakinta cikin nasa, daƙer suke yi wanka suka kwanta bacci domin su huta.

Dare - Private Dinner, a bakin teku suke a zaune Chef ne ya dafa abinci ya tafi. 
Suka zauna a kasa a kan carpet mai laushi a bakin pool, ƙafafunsu na cikin ruwa mai dumi, suna cin grilled lobster da lamb chops_ da ruwan zabibi.Iska mai dumi ta Red Sea na kada musu.

Kwantar da kanta Shatu ta yi a cinyarsa, tana kallon taurari.

"Abbana."


 Sunkuyo wa ya yi yana sumbaci goshinta a hankali, ya rungumeta da ƙarfi.

A wannan dare, ba su yi wani abu da ya wuce runguma mai daɗin gaske, ko magana ba su fiya yi ba, sannan suka kwanta a kan lounger a bakin pool har bacci ya dauke su, jikinsu a rufe da blanket guda ɗaya, suna sauraron karan ruwan teku.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Makkah - Karfe 4:00 na safe.

Daga Jeddah zuwa Makkah,tafiya ce ta awa ɗaya, karfe biyar suka isa.
Suna sauka a Raffles Makkah Palace hotel ɗin da ya fi kusa da harami, wanda tagarsa ke kallon Ka'aba kai tsaye.

A Maina da Yusuf kuwa tun safe suka iso suna tare da Shekyh Mohaj.

Sheikh Mohaj mutum ne mai kimanin shekaru 70,mai natsuwa mutumin M Madawaki ne sosai, Shekyh da A Maina ne suka shigo masauƙin nasu. 

Da murmushi a fuskar Shekyh ya ce.
"M Madawaki, My son. A Maina told me everything about London. Alhamdulillah for the hope. Allah is the best planner."

Murmushi M Madawaki ya yi tare da ɗan rungumoshi, Shatu Shekyh ya kalla da ke rufe da nikab mai fari, idonta kadai ke bayyana, haka suke wayo tun da wannan Bature ya ce tana da kyau M Madawaki ya fara rufe mata fuska.

"My daughter, Shatu. Allah will not test you beyond what you can bear. Kije ki yi Umrah, ki roke shi a gaban gidansa."

Ɗaga masa kai Shatu ta yi, tana kallon fuskar A Maina. Washegari ranar da asuba suke shiga Harami da Hasken Ka'aba na haskakawa ko'ina.

Shatu ce ta rike hannun M Madawaki da karfi lokacin da taron ya fara yawa, shi kuma ya rungumeta ta baya, yana kare ta daga taron jama'ar, A zagaye na farko, Shatu ta fara addu'a cikin kuka.

M Madawaki yana ji kukan, ya matso kusa da ita, ya rufe ta da jikinsa.

"Eshaa, what are you praying?"

Kallon fuskarsa ta yi cikin hawaye, tana shafa Ka'aba ta ce.

"Ina cewa, Ya Allah, Dr ta ce akwai hope, ta ce Cervical Cerclage zai taimaka, amma kai ne mai bada hope ɗin gaskiya. Ya Allah ka bani lafiya, ka bani ciki wanda zai tsaya. Ka bawa Abbana abin da yake nema a duniya da lahira.

M Madawaki da kansa idanunsa sai da ya cika da hawaye, bai taɓa ganinta cikin rauni haka ba. hannayensa shima ya ɗaga.

"Ya Allah, ka ji addu'ar matata. Ka ba mu zuriya ta gari. Ka sa wannan gwajin ya zama tarihi."

Lokacin da suka gama Tawafi 7, da Sa'ayi. Sun gajiya sosai, shi yasa suna dawowa kwance suke yi.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Kwanakinsu 10 Kenna da yin Umrah.

Yau kwana biyu kenan Shatu ba ta fita ba saboda da kasala da take fama da ita ga yamma na yi za ta fara jin tashin zuciya.

Da farko su dauka saboda gajiyar tafiya ce daga London zuwa Spain, Spain zuwa Jeddah, Jeddah zuwa Makkah, Amma M Madawaki ya lura ba haka ba ne.

 Dawowarsa kenan daga wani meeting ya same ta zaune a gaban mirror, da pale, hannunta, wanda ya fita ya barta da shi tun safe, a hankali ya ƙaraso yana cewa.

"Eshaa? What happened? Ba ki ci abinci ba tun safe."

Kanta ta ɗago idonta cike da ruwa hawaye ta ce.
"Abbana, ina jin jiri, ina jin... ina so in yi amai, kuma ƙirjina ciwo suke min. Kamar... kamar.........."

Ƙasa ƙarasawa ta yi tana rike hannunsa,tsugunawa M Madawaki ya yi a gabanta, zuciyarsa na bugawa da karfi.

"You mean...?"

Ta girgiza kai, hawaye ya gangaro.

"Ban sani ba, Abbana..."

Shiru ne ya ratsa room ɗin, sai sautin kiran Azahar daga Harami kadai.M Madawaki ne ya kira A Maina a waya cikin hanzari.

"MAMUB ka zo, yanzu da Dr."

Bayan kamar minti 15, A Maina ya shigo da likita mace ta private hospital a Makkah, saboda Raffles yana da doctor on call.

Likitar ta yi mata quick check, ta yi murmushi.

"Mrs. Madawaki, we need a blood test, but your symptoms... nausea in the morning, fatigue, breast tenderness... this is very early, but it looks like early pregnancy signs. When was your last period?"

Shiru Shatu ta yi tana kalli M Madawaki, domin kunyar A Maina da ta ji, dole sai M Madawaki ne ya bada amsar.

"About 2 weeks ago, before London."

Miƙewa Likitar ta yi tare da cewa.
"Let's do Beta-hCG test now. You will get result in 2 hours. But please, because of your history of Cervical Insufficiency that I saw in your file from Portland Hospital London, you must not stress, no long travel, no..."

Ta kalli M Madawaki, tana yi murmushi.

"...you understand, complete rest for now."


Likitar tana fita, Shatu ta fashe da kuka ta fada jikin M Madawaki.

"Abbana, idan da gaske ne fa? Idan Allah ya amsa addu'ar da na yi a gaban Ka'aba?"

Ya rungumeta ya yi da karfi, shi ma idonsa ya cika da hawaye, karon farko da A Maina ya gan shi da hawaye, tun fara faruwar abubuwan da suke faruwa.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan kamar awa biyu A Maina ya shigo da sakamakon hannunsa na rawa, muryar shi cike da farinciki.
"MAMUB... Alhamdulillah she is pregnant, I am so very happy.

Alhamdulillah, !Alhamdulillah,!Alhamdulillah.
Shi ne abin da yake fitowa a bakin M Madawaki.

"We need to tell Baba Malam! And Daada!"


Dafa kafadar A Maina, M Madawaki ya yi tare da cewa.

"MAMUB, remember what the doctor in London said. 'Once she becomes pregnant again, she should contact us immediately. We will plan the cerclage between 12 and 14 weeks.' Yanzu tana da kimanin week 5 We need to go back to London soon, or arrange with Portland Hospital."

Tuna maganar ne ya hana A Maina sanarwa su Baba Malam, suka maida hankalinsu wajen kula da Shatu, domin wannan cikin wahalar da ita yake yi sosai.

Komai sai da M Madawaki ya yi mata, dukknsu tausayinta suke ji sosai, har rasa wanda ya fi tausayinta a cikinsu take yi, domin A Maina ajiye komai ya yi, yana maida hankalinsa ga kula da ita, har maka M Madawaki.

Duk bayan kwana biyu, suna ziyarar Hospital domin a duba lafiyar abin da yake cikin har Allah ya taimakesu cikin ya shiga satin na sha biyu, a ranar suka so dawowa UK amma Shatu sai ta tashi da zazzafan zazzaɓin, wanda sai da suka kwana biyu a Hospital, sannan ta ji sauƙi.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
 London, Portland Hospital.

Saukarsu kenan a private jet, zuciyoyinsu cike da fargaba,

A cikin jirgin, kuwa Shatu ce kwance a kan bed, M Madawaki na riƙe da hannunta, A Maina kuwa yana zaune a gefensu yana duba saƙon da ya turawa  Dr Emily, na sakamakon Beta-hCG da ultrasound na Makkah zuwa ga Dr. Emily.

A ranar ba su samu damar zuwa Hospital ɗin ba, sai da suka yi kwana biyu Shatu ta sake hutawa sannan suka tafi, Yusuf ne a gaba sai M Madawaki da A Maina da suka saka Shatu a tsakiyarsu.

Da murmushi Dr. Emily ta tare su tana rugume Shatu.

"Shatu M Madawaki I congratulate you, I've been happy since I got the message from A Maina's email."

Zama suke yi tana kunna ultrasound, a screen, wani dan abu ne ƙarami ya fara bugawa, thump!thump!thump.!

Fashewa da kuka Shatu ta yi tare da riƙe hannun M Madawaki.

"Abbana, kaji? Kaji bugun zuciyarsa?"

Ƙasa magana M Madawaki  ya yi yana kallon screen, a hankali ya kalli Dr. Emily.
"Doctor, will it stay? Tell me it will stay this time."

Gyaɗa masa kai Dr. Emily ta yi tare da cewa.
This is why we do the _Cervical Cerclage_. Because her cervix opens too early, and now that she is at 12 to 14 weeks is the perfect time that we should stitch it closed, like a purse string, so it can hold the pregnancy until 37 weeks. It is just a 20-minute procedure under spinal anaesthesia. Very safe.

Ɗaga mata kai ya yi alamar ya fahimta, a Hospital ɗin suke yini ƙarfe 7:00 na dare, za'a yi mata aikin.

Shatu ce kwance a kan gadon tiyata, an saka mata spinal anaesthesia, M Madawaki aka bawa damar shiga, sanye da scrubs koren likitoci, yana rike da  hannunta.

"Eshaa, I'm here. Look at me, not at the doctors. I'm here."

Riƙe hannunsa ta yi da ƙarfi, cikin sanyin murya ta ce.
"Abbana, ina jin tsoro."

"You are the bravest woman I know. After this stitch, our baby will be safe insha Allah."

Murmushi ta yi, lokacin da za'a fara aikin ne ya fita, zama ya yi a inda su Yusuf suke tsaye jiki a sanyaye.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
Dr. Emily ta fara aiki, ba'a ɗauki lokaci ba suke gama.
Shafa kan Shatu Dr Emily ta yi bayan ta maida ita ɗakin hutu ta ce.

"It's done, Shatu. The stitch is in. The cervix is closed and long. Perfect."

Fita duk suka yi a room ɗin domin ba ta damar hutawa, ranar da M Madawaki suka kwana domin kasa tafiya ya yi, sai da safe, Dr. Emily ta zo ta yi checking.

Everything is fine. The baby's heartbeat is strong. No bleeding. Now, what I want is for her to have complete rest for one week, no long travel, no stress. And I know you will be going back to Nigeria, but please, have the pregnancy monitored (ultrasound) every month, there is a doctor I will connect you with in Abuja. She will take care of everything in sha Allah.

Shafa cikin Shatu ta yi tare da cewa.
"Doctor, I'm vomiting in the morning, I'm feeling tired. Is it normal?"

Dariya Dr. Emily ta yi, tana kamo hannayen Shatu.
It's very normal. This means your hormones are strong. The baby is growing. Eat food, drink slowly, everything will reduce.

Cikin farinciki suka dawo hotel ɗin da suka sauka, A Maina rasa inda zai ɗorata ya yi, saboda farinciki haka Yusuf, fita suka yi suna yi mata siyayya sosai, amma babu abin da ta iya ci.

Sati ɗaya suka sake yi domin ta huta, sannan suka fara shirye-shiryen dawowa gida Najeriya.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Najeriya.
Tun bayan tafiyarsu Shatu, Daada take addu'a, haka ma Baba Malam, lokacin da A Maina ya sanar da su matsalar da take damun Shatu ne suka shiga damuwa duk family domin kuka Daada ta zauna take yi.

Matan gidan na bata baki, a ɓangaren Rahmah ma ta shiga damuwa sosai, ta so su yi magana da Shatu amma A Maina ya ce babu waya a hannunta M Madawaki ya karɓeta, dole sai haƙura ta yi.

Nadiya, Rima, Meerah, Nimrah, Banisha, kuwa kuka suka zauna suna yi, ga suna son magana da Shatu babu dama, sai da Shamsudeen ya yi musu magana sannan suka yi shiru.

A ɓangaren Inayaa da Zulaihah kuwa farinciki suka yi sosai, Inayaa har addu'a take Allah yasa a wajen yi wa Shatu aiki ta mutu, domin ta samu A Maina ya aura mata M Madawaki.

Lissafi Daada ta fara na kwanakinsu tun tana yi ita ɗaya har ta samu masu taya ta, ganin sun yi wata huɗu har da wasu kwanakin ne ta cire rai, tana kwantar da hankalinta kamar yadda Abubakar Madawaki yake so.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Zaune suke a falon Daada, har Baba Malam shi da Baba Haruna da suka dawo gida gabaɗaya, Hajiya Safiya ce suka tsara yadda bikinsu Nimrah da Shamsudeen, Meerah da Muhammad A Maina, Rima da Omar Aminu Madawaki, Banisha da Walid Makama, Nadiya da Yusuf wanda A Maina ya haɗa auren.

Nadiya ta so ta nuna bata so amma Rahmah bata, bata goyon baya ba, Daada ce ta yi mata nasiha tana bata misali da Shatu, sannan ta kwantar da hankalinta take ɗaga wayarshi.

A ɓangaren Inayaa kuwa lokacin da Baba Malam ya ce kowa ya fito da Miji cewa ta yi bata da saurayi, domin so take Shatu ta mutu a wajen aikin da ta ji suna cewa za'a yi mata, ita kuma ta aurin M Madawaki.

A Maina ne ya ce Baba Malam ya rabu da ita sai ya dawo, haka suka zuba mata ido ita da Uwarta.

Ƙarar wayar Daada ce ta sa duk suka yi shiru, Rahmah ce ta ɗaga mata wayar sannan ta saka a kunne.
"Assalamu alaikum waye yake kirana da sanyin safiya...."

Dariya duk suke yi domin lamarin Daada sai ita, tsayawa suka yi da dariyar suna kallonta ganin tana washe baki, tare da cewa.
"Alhamdulilah! Abubakar na gode sosai dama, so nake na ce, ku dawo min da Shatu ku sai ku koma dama kun saba yawanku..."

Tana gama faɗar haka ta kashe wayar tana kallon Anne tana cewa.
 "Alhamdulilah wai Abubakar ne ya kira Ni, gobe za su dawo......"

Ihun su Nimrah ne ya hana Daada ƙarasa maganar tana jefusu da pillow, tafi suka yi duk suna murnar dawowar Shatu.

A ranar babu wanda Daada ta bari ya zauna lafiya, kowa aiki take bashi, Baba Jamila kuwa abubuwa ne suka yi mata yawa ga gyaran ɓangaren M Madawaki ga aikin Daada, komai na gidan nan sai da aka gyara abincin kuwa har rasa kalar wanne za'a yi, sukai.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Washegari Abuja ,Nnamdi Azikiwe Airport misalin ƙarfe 3 na rana,jirgin ya sauka. 

Cikin farinciki suka fito Shatu, M Madawaki ya ɗaura  a kan wheelchair ba don ba za ta iya tafiya da kanta ba, sai don ra'ayinsa domin ciki umarnin Dr Emily da ta ce ba'a so ta yi tafiya mai tsawo.

Ɓata fuska Shatu ta yi domin bata son zama saman wheelchair ɗin kawai babu yadda za ta yi ne. Gane ma'anar ɓata fuskarta ta ne,M Madawaki ya yi murmushi tare da cewa.

"Doctor said complete rest for one week, Ni kuma one month nake buƙata.."

Har suka isa kusa da wasu motoci guda uku baƙaƙi kirar Prado tana turo baki,Yusuf ne ya fara shiga M Madawaki ya ɗaga Shatu, A Maina ya ɗauke wheelchair ɗin, cikin nutsuwa motocin suke tafiya domin cika umarnin Yusuf, har suka isa Madawaki Dynasty babu motar da ta yi gudu.

Tun fitowar A Maina ma'aikatan gidan suke miƙa gaisuwa, cike da sakin fuska yake amsa musu, Yusuf ne ya fara shiga da kayayyakin M Madawaki da Shatu, a hankali M Madawaki ya fito da Shatu a jikinsa, bai tsaya amsa gaisuwar da suke masa ba, ya nufin falon Daada.

Da sallama a bakinsa ya shigo falon yana ɗauke da Shatu a jikinsa. Daada ce ta fara miƙewa tsaye, tana kallonsu da murmushi mai cike da farinciki.

"Alhamdulillah! Shatu M Madawaki ta dawo Allah na gode maka.Sannu da zuwa, Allah ya dawo da ke lafiya."

Murmushi Shatu ta yi, tare da kallon fuskar M Madawaki tana turo baki, sauƙeta ya yi a hankali sannan ya zauna suka gaisa da Daada, wacce hankalinta duk yake kan Shatu.

Rungume Daada Shatu ta yi tare da fara hawayen farinciki,
Su Meerah kuwa tun shigowarta suke tsaye, so suke su rungumeta amma suna tsoron M Madawaki, Daada kuwa sai hawayen farinciki take yi, Hajiya Safiya da Hajiya Maryam ne suka rungumesu ita da Daada.

A Maina ne ya miƙe tsaye yana kallon agogon hannunsa, ya ce.
"MAMUB Shatu ta ci abinci sannan ga maganinta ta sha.."

Karɓa M Madawaki ya yi shi ma ya miƙe tsaye yana kamo hannayen Shatu, kafin wani ya yi magana ya ɗauketa, ya nufi ɓangarensa da ita.

Duk zaro ido suke yi, suna bin bayansu da kallo, Anne ce ta da ta fito yanzu ta fara faɗa akan ɗauke Shatu da M Madawaki ya yi, shiru Daada ta yi tana kasa magana domin lamarin ya bata mamaki sosai.

Da saurin Baba Jamila ta matsa tana basu hanya, master bedroom ɗinsa ya shiga, tare da kwantar da Shatu, toilet ya shiga babu jimawa ya fito, ya taimakawa Shatu ta cire kayanta suka shiga toilet ɗin, shi ne ya yi mata wanka ta yi alwala shi ma ya yi suka fito.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol