Free chapter · Read without an account
Chapter 21
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 21
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Shagwabe masa ta yi, shi kuma ya fara aikin rarrashi, ranar babu inda ya fito suna tare, dare na yi M Madawaki ya sake komawa ruwa, yanzu kuma da gaske Shatu take kuka domin ta ji, jiki sosai a hannunsa.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Mummy.
Abubuwan duniya sun yi mata yawa,komai ya tsaya, duk abin da take samu a koyarwa baya kaita wata, har lokacin Abdul Rahman bai fito ba, ga Halimatu ƙawarta Amina ta jata bariki.
Ga babbar masifar da take damunta shi ne, bincike halin da M Madawaki da Shatu suke ciki, da farko Dr Nadraa na bata labari, amma tun da Yusuf ya kamata ta janye jikinta daga lamarin Mummy, ta kama aikinta domin shi ne ma madogararta.
Bibiyar ma'aikatan gidan Mummy ta fara, amma bata samu abin da take so ba, dole sai wajen Dr Nadraa ta koma, a lokacin ne ta ji mummunan labarin da ya ɗaga mata hankali fiye da sakin da M Madawaki ya yi mata.
Dr Nadraa ce ta bata labarin cewa Shatu ta sake samun ciki wanda har London suka je aka yi mata ɗaurin mahaifa, ihu Mummy ta fara yi tare da tara mutane a kanta.
Zamewa Dr Nadraa ta yi, domin bata so wani ya san Mummy wajenta take zuwa, a rabata da aikinta domin ta ga alamun hakan,yanzu M Madawaki baya yadda ta duba Shatu, kullum in za su zo da Dr Maryama suke zuwa ta dubata su koma gida.
Dr Nadraa na ganin haka ta yanke shawarar haƙura da M Madawaki, ta bawa wani mutum dama ya tura gidansu aka yi maganar aure, cikin lokacin ƙanƙanin aka yi bikin ta tare a ɗakinta.
Mummy ta yi haukan har ta gaji, bata samu damar haɗuwa da Shatu ba.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
BAYAN WATA HUƊU.
Tun da cikin ya shiga wata 8 Shatu take kuka ita ta gaji kullum sai ta yi kuka kafin ta yi bacci, ga ƙafafuwanta kullum kumbura suke.
Cikin kuwa ya yi girma sosai, kamar ba cikin fari ba, kullum sai an taimaka mata take zama, hankali Rahmah duk yana kanta har ma Daada kullum bata cikakken bacci, saboda tunanin kada haihuwa ta zo da daddare M Madawaki bai san komai da ya shafi haihuwa ba.
Yau ma kwance suke ita da shi domin baya bacci sai ya samu bacci ya ɗan ɗauketa, cikin sanyin murya ta ce.
"Abbana, na gaji, wai har yanzu garin bai waye ba, Ni fa so mu tafi.."
Cike da tausayawa ya rungumeta a hankali, ya rike ta kamar kwai, yana matsa mata ƙafafuwanta da suka kunbura sosai, har ya samu bacci ya ɗauketa sannan shi ma ya kwanta.
Washegari ranar suka shirya domin komawa London wannan lokaci har da Rahamah da Daada sai Anne da Hajiya Maryam.
A ɓangaren mazan gidan kuwa, Baba Malam ne sai Sayyid Madawaki, sai Aminu Madawaki, tare da su duk suka tafi, dama A Maina tun satin da ya wuce yake London ɗin shi a can suka same shi.
London - Portland Hospital.
A ranar da suka sauka, suka je Hospital ɗin domin Shatu ta damu a cire ɗinkin ta haihu, Dr Emily na ganinta ta fara murmushi, tana gaisawa da su Rahamah, duba ultrasound ɗin ta yi tare da cewa.
"Perfect, Shatu. The baby is head down, already 3kg. The cervix is still closed because of the stitch. Today we will remove it. Within 24 to 48 hours, labor will start naturally, or we will induce you."
Turo baki Shatu ta yi, domin ita burinta a cire ɗinkin ta haihu, Dr Emily ce da Rahmah suka kamata,zuwa room ɗin da za'a yi mata aikin, bayan kamar minti ashirin Dr Emily ta fito da Shatu.
Masauƙinsu suka koma, ta ci abinci sannan ta ɗan kwanta. Tun bayan cire ɗinkin suke jiran haihuwa amma shiru har suka yi satin biyu, a lokacin Hajiya Safiya ta biyo su, da farko Baba Malam ya so komawa Najeriya, amma ganin jikin Shatu kullum ƙara gama yake ya zauna suna zubawa sarautar Allah ido.
Sai da cikin ya yi wata tara da kwana goma, sannan cikin dare naƙuda ta zo, sautin kukanta ne ya farkar da Daada ita da Rahmah, dama tare suke kwana da Shatu.
Rahmah na ganin halin da take ciki ta kira wayar A Maina tana sanar da shi haihuwa ta zo, cikin sauri suka fito da mota, M Madawaki ya sakata a ciki suka nufi Hospital ɗin.
Suna isa Hospital ɗin, Dr Emily da nurses suka ruga da Shatu ciki. M Madawaki yana riƙe da hannunta, Shatu kuwa sai kuka take yi, tana kamo hannunsa tare da cewa.
"Abbana kada ka tafi, don Allah ka zauna tare da ni..."
Kallon Dr Emily ya yi, ta gyaɗa masa kai tana murmushi.
"Mr Madawaki, you can stay. She needs you."
Tare suka shiga ya zauna a gefen gadonta, yana goge mata gumi, tare da rike hannunta.
A ɓangarensu Rahmah da Daada suna waje a zaune sai addu'a, suke yi, Baba Malam ma yana zaune yana tasbihi, A Maina kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye zuciyarsa na bugawa kamar zai fita.
Cikin dakin, kuwa Dr Emily ce ta duba Shatu ta ce.
"Shatu, you're 7cm dilated. You're doing very well. Just a little more. Breathe with me."
Cikin mawuyacin halin Shatu ta dago kai tana kallon M Madawaki, idanuwanta cike da hawaye ta ce.
"Abbana, na gaji... ba zan iya ba..."
Sumbatar goshinta ya yi, cikin sanyin murya ya ce.
"Eshaa, za ki iya."
Matse hannunsa ta yi sosai, dalilin wani ciwo mai karfi da zo, ihu ta yi ta kwantar da kanta a kirjinsa.
Cikin wannan yanayin suka yi awa uku, har asuba haihuwa shiru bata zo ba, a lokacin Shatu ta gama kaiwa ƙarshe a gaji,Daada ma da Rahamah har sun gaji da kallon hanyar, tashi tsaye Daada ta yi tana cewa.
"Ya Allah, ka sauƙaƙa mata, ka bata lafiya."
Su M Madawaki ne suka dawo daga sallar asuba, sun shigowa sai ga Dr Emily ta fito da sauri, ta kalli M Madawaki.
"It's time! The babies are coming!"
M Madawaki ya shiga ciki da sauri, ya kama hannun Shatu.
Dr Emily ta ce.
"Shatu, push! Shatu, the push has come!"
Rintsa idonta Shatu, ta yi, da dukkan karfinta, tana fashewa da kuka, tare da cewa.
"Abbana!"
Ƙasa jurewa M Madawaki ya yi, ya fita daga room ɗin idanuwansa jajir, yana fita ta yi wani nishi mai ƙarfi sai ga jariri
Dr Emily ce ta ɗauki jaririn tana murmushi.
"First baby, a boy! 3.2kg!...."
Maganar ta katse ne sakamakon sabon kuka da Shatu fara,nakuda ta dawo farko, Dr Emily ta bada jaririn tare da taimaka mata, babu jimawa ta sake haifar wani yaron.
Mintinan gamo sha biyar tsakanin ta sake haifar wani, na ƙarshen na fito ta sume.
Dr Emily ce ta dauke ta da murmushi mai kyau ta ce.
"And the third baby, a beautiful girl! 2.8kg! Congratulations, Mr and Mrs Madawaki. Triplets! Two boys and one girl, all healthy!"
Yaran nurses ɗin suka gyara, Dr Emily ta duba Shatu, tare da yi mata allurar ana kaita room ɗin da za ta huta.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Zaune suke jugum jugum, kowa da abin da yake zuciyarsa, Dr Emily da nurses ɗin suka fito da yaran, duk tashi tsaye suka yi kawo na miƙo hannun.
Murmushi Dr Emily ta yi tare da bawa M Madawaki na hannunta, A Maina ne ya karɓa ɗaya yana hawayen farinciki, macen Baba Malam ya karɓa, yana rungumarta duk rasa bakin magana suke Sayyid Madawaki kuwa saman tsaye ya yi ganin yara har uku.
Rahmah ce ta fashe da kuka tana rungumar Daada.
"Daada! Ta haihu! Har Uku duk ita ce ta haife su?"
Rungume Rahmah, Daada ta yi, tare da cewa.
"Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allah ya raya su, Allah kai ne abun godiya."
Aminu Madawaki,Baba Malam ya bawa yarinyar, tare da yi sujjada a corridor ɗin Hospital ɗin, yana godiya ga Allah.
M Madawaki ma Dr Emily ya bawa yaron yana yi sujjada, cikin kuka yake godiya ga Allah.
A hankali ya ɗago tare da kallon fuskar Dr Emily ya ce
"Doctor, where is Eshaa? I hope she is fine, there is no problem."
Murmushi ta yi tare da cewa.
"Mother and all three babies are stable. The babies
will remain under observation by our neonatal team."
Murmushi M Madawaki ya yi.
"Thank you so much, Doctor. I really appreciate everything."
"You're welcome. We'll continue monitoring them closely."
Da yaran suka koma, Dr Emily ta aka kai su Neonatal Unit domin a tantance numfashinsu, yanayin jikinsu, nauyinsu da sauran alamomin lafiyarsu.
Bayan an kai yaran Neonatal Unit, duk suka zaune, sai M Madawaki wanda ya kasa samun nutsuwa. Duk da tabbacin da Dr Emily ta ba shi cewa Shatu da yaran suna cikin ƙoshin lafiya, zuciyarsa tana wajen matarsa.
A hankali ya juya ga A Maina wanda yake zaune cikin farinciki yana sanarwa da Yusuf da yake ta faman kiransa, a hankali M Madawaki ya kamo hannunsa ya ce.
"MAMUB kana ganin waɗannan yaran da gaske namu ne?"
Murmushi A Maina ya yi
"MAMUB Ni ma har yanzu kamar mafarki nake ji. Yara uku fa! Allah ya ba mu arzirƙinsu lokaci guda."
Sunkuyar da kansa M Madawaki ya yi, yana murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillah. Allah ya raya su, ya sa su zama bayin Allah na gari."
Baba Malam ne ya katse su da cewa.
"Ku dai ku gode wa Allah, wanda ya ɗauki nauyin komai, shi ne ya ba da sakamakon da ya fi tunaninku."
Dukkaninsu suka amsa da Amin.
A gefe su, Daada da Rahmah kuwa sai hawaye suke yi, musamman Rahmah wadda ta kasa daina murmushi da hawaye duk a lokacin ɗaya, ta ce.
"Daada, ban taɓa tsammanin Shatu za ta haifi yara uku a lokaci ɗaya ba."
Murmushi Daada ta yi, tana gyara zama ta ce.
"Ni ma ban yi tunanin hakan ba, amma Allah ya nuna mana ikonsa, bayan duk wahalar da yarinyar nan ta sha. Kai! Gaskiya Allah abun godiya ne.Allah ya ba ta lafiya, wannan shi ne abin da nake nema."
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sai yamma sannan aka basu damar shiga inda Shatu take, M Madawaki ne ya fara shiga a zaune ya sameta kamar ba ita ce ta haihu ba, ta yi wanka an sauya mata kayan jikinta zuwa na marasa lafiya.
Rungumeta ya fara domin bakinsa ya yi kaɗan wajen yi mata magana, a kunneta yake raɗa mata irin farinciki da yake ciki, tare da sanar da ita irin kyautar da Allah ya yi musu, cike da farinciki ta rungumoshi sosai, tana cewa.
"Abbana Yara uku! Ma sha Allahu, Allah na gode maka da yau ka nuna min ranar da Abbana yake nuna irin farincikin da yake ciki...."
"Alhamdulilah! Eshaa tabbas ina farinciki sosai Allah ya raya mana su bisa sunnar ma'aiki...."
Dr Emily ce ta shigo da yaran sai su Daada a bayanta, bakin Shatu kasa rufuwa ya yi ta ɗauƙi wannan ta ajiye ta sake ɗaukar wani, Daada da Rahmah ne suka taimaka mata ta shayar da yaran.
A ranar Mahaifinsu ya yi musu huɗuba, na farkon Abubakar wato A Maina. Na biyun Aliyu wato Baba Malam, sai macen Ruƙayyah, kowa ya yi farinciki sosai da sunan da M Madawaki ya saka musu.
A ranar da Rahamah suka kwana a Hospital ɗin duk da Dr Emily ta ce basa buƙatar mai zaman jinya, washegari ranar Dr Emily ta sallamesu domin duk suna cikin ƙoshin lafiya.
Tun bayan dawowarsu daga Hospital ɗin Hajiya Safiya da Rahamah suke kula da Shatu da yaran har suka ciki sati ɗaya, bayan raɗawa yara suna Baba Malam ya ce gobe za su koma gida, M Madawaki bai so hakan ba amma babu yadda zai domin cika umarnin Baba Malam ɗin.
Washegari ranar kuwa suka sauka a gidan, wanda ya ciki da yan Uwa na kusa da na nesa, Hajiya Maryam ce ta shigo da NI'IMATUL RAHMAN, wato Ruƙayyah, sai Rahmah da take ɗauke da RIZQ KARIM wato Aliyu.
Da sauri. Matan gida suka karɓe su, Shatu ce ta shigo ita da Daada, sai Sayyid Madawaki da MOHAAJIR AMEEN, wato Abubakar, da gudu Rima ta rungume Shatu har tana ƙoƙarin faɗowa dukan Rima Daada ta yi cike da masifa ta ce.
"Ke baki da hankali ne? Kada ita kike son yi?"
Dariya Shatu ta yi tana rungumesu, Ihun murna suka fara tare da cewa.
"An dawo! An dawo da triplets!"
Ihun su ne ya saka yaran fara kuka domin tun zuwansu duniya ba su ji ƙara mai ƙarfi ba, sai yanzu Hajiya Safiya ce ta yi musu tsawa tare da cewa.
"Wai baku da hankali ne?"
Shiru suka Shatu na zame jikinta a hankali ta tashi Daada ta yi saurin cewa.
"Ke! Kuma ina za ki tafi kina ji sun fara kuka?"
Hijabin jikinta ta cire tana turo baki ta ce.
"Toilet zan shiga yanzu zan fito........"
Ƙasa ƙarasa maganar ta yi tana komawa ta zauna ganin kallon da Rahamah take mata,
Rima ce ta ɗauki NI'IMATUL RAHMAN tana cewa.
"Wallahi Shatu, kin gama aiki. Uku a lokaci daya? Ke jaruma ce!"
Murmushi ta yi tana bawa RIZQ KARIM nono, M Madawaki da A Maina ne suka shigo ta yi saurin cire RIZQ KARIM tana saka hijabi, girgiza kai M Madawaki ya yi, yana ɗaukar Yaron wanda yake kuka.
MOHAAJIR AMEEN Hajiya Maryam ta bata tare da cewa.
"A taimakawa Yaya Maina wannan kukan na yauwa yake yi, tun da muka taso sau ɗaya ya sha.."
Tashi M Madawaki ya yi domin ya san in yana wajen ba za ta bawa Yaron ya sha ba, ɓangarensa suka shiga da A Maina wanda ya karɓi NI'IMATUL RAHMAN a hannun Rima.
Suna tashi Shatu ta cire hijabin tana shayar da MOHAAJIR AMEEN, yana gama sha ta shiga bedroom ɗin Daada Hajiya Maryam ce ta shiga tana yi mata wanka sannan aka bata abincin tana ci sai bacci.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sai takwas na dare ta fito ita da yaran cikin kayan sanyin, gaisawa suka yi da matan gidan suna mata barka, Anne ce ta kalleta tare da cewa.
"Sannu Shatu yara uku lokacin ɗaya gaskiya kin yi ƙoƙari sosai."
Murmushi ta yi tana kallon fuskar Inayaa da bata yi mata magana ba, ta ce.
"Anne ai ban san haka ake ji ba, sai da na kusa mutuwa fa.."
Girgiza kai Baba Malam ya yi, yana yi wa yaran addu'a, su Nadiya ya kalle tare da cewa.
"Nadiya, ke da Banisha ba za ku koma gidajanku ba?"
Ƙasa Nadiya ta yi da kanta tana ƙoƙarin magana sai ga Yusuf ya shigo, gaisawa suka yi da Shatu yana karɓar yaran addu'a ya yi musu, sannan ya kalli fuskar Nadiya, tashi ta yi tare da rungume Shatu ta ce.
"Sai da safe zan dawo ki kula mana da baby's."
Murmushi Shatu ta yi, tana kallon fuskar Inayaa da take cewa.
"Sannu Shatu ashe haihuwa kike yi?"
Mamaki ne ya kama duk wanda yake falon, suna kallon Shatu, murmushi ta yi ba tare da ta amsa ba, har M Madawaki ya fito, babu kunyar ya zauna kusa da ita tare da miƙewa Hajiya Safiya hannun ta bashi NI'IMATUL RAHMAN.
A hankali Shatu ta ɗora kanta a kafaɗarsa tare yin ƙasa da murya ta ce.
"Abba, bana son sake ganin Inayaa a gidan nan, har yanzu tana da wannan cutar sonka a zuciyarta, bana so na ɗauƙi mataki da kaina..."
Bai yi magana ba, sai miƙewa da ya yi tare da kamo hannayenta suka nufi ɓangarensa, baki sake Anne take kallinsu, sannan ta juyo kan Daada ta ce.
"Daada wai Muhammad bai san mace sai ta yi arba'in take komawa wajen Miji ba?"