Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 39

by Rabi'atu kabiru Fulani · LOKACI

***


⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳ 

RABI'ATU FULANI 

YOTA

Under Team Yota's Amazing Pen's.

   FULANI ❣️ 
***

     PAGE3️⃣9️⃣

A kusa da gadon ya tsaya, sai kuma ya zauna ba tare da ya ce mata komai ba, ya fahimci sai ya yi aiki tuƙuru kafin ya sa ka ta mantawa da abin da ya faru, cikin kwantar da murya ya ce.

"Ki kwantar da hankalinki Besty, babu abin da zan miki nayi miki alƙawari, ba ni da tsarin raba ɗaki da matata, bayan muna cikin gida ɗaya da ita, zo ki kwanta"

Ya ƙarasa yana nuna mata gefen sa.

Sauke idanunta tayi ƙasa, tana son bin abin da ya ce, kuma ta na son yin aiki da nasihar Ammie, amman kamar an ɗaure mata ƙafafu ta kasa matsawa kusa da shi.

"Muhan ni.."

"Shhhh, ba sai kince min komai ba, zo ki kwanta"

Shiru tayi sai faman wasa da zoben hannunta da take, a hankali ta fara matsowa gaban gadon kamar mara laka, ta jima a tsaye kafin ta kwanta ta cure jikinta waje ɗaya, tana kallonsa ya kashe hasken ɗakin, sannan ya kwanta a gefenta, cikin dubara ta ke kallonsa, dan ba ta son ta nuna masa tana ganin abin da yake yi.

Ya na kallon duk abin da take, amman bai nuna mata ba, space ɗin ke tsakaninsu ya isa mutum uku ko huɗu su kwanta, shiru ne ya mamaye ɗakin, ajiyar zuciya ta sauke wadda sai da ya jita, ya na kallon yanda take ta juyi kafin daga bisani, ya fahimci bacci ya ɗauketa, sai da ya tabbatar baccin nata ya yi nisa sannan ya gyara mata bargo ya janyota jikinsa, a haka shima bacci ya ɗaukesa....

★★

*Bayan sati uku*

Har ta shiga sati na uku a dawowarta daga gidan Ammie, sun koma asibiti an tabbatar da ta warke bata da wata matsala, tun wajen sati biyu da ya wuce, a halin yanzu komai ya sauya a gidan, idan har ta ce bata farin ciki tabbas ta yi ƙarya.

Muhan ba ta san a yanda zata bayyana yanda yake ba, sai dai duk yanda zaka yi tunanin haka yake ya wuce hakan, tun da ta dawo gidan shi yake kula da komai, kafin ta tashi daga bacci ya haɗa musu breakfast, haka da rana ko ya fita zai aiko mata da abinci, babu abin da take a gidan sai hutu, baya barin gidan sai ya gama mata duk wani aiki da ke cikinsa, koda ta yi ƙoƙarin hanasa baya barinta, ta samu hutu fiye da wanda aka ce tana buƙata.

Ba ya gajiya da kula da ita, haka kuma ba ya gajiya da nuna mata soyayya, tun bayan dawowarta, bai sake neman komai a wajenta ba, soyayya kawai yake nuna mata, wadda take saka ta taji ashe itama ta kai a so ta har haka, tana mamakin irin son da Muhan ya ke mata, a da ba ta fahimta ba, amman a yanzu ta fahimci irin girman da ta ke da shi a wajensa.

A hankali ya gina wani irin sabo a tsakaninsu.

Baya taɓa barinta ta zauna ita kaɗai, duk yanda zata saka tazara a tsakaninsu sai ya cike ta, a duk lokacin da ya matso kusa da ita sai ta matsa, zai yi kamar bai gani ba, ya matsa kusa da ita sosai, haka kuma baya taɓa barin su zauna hannunsa ba'a cikin na juna ba, duk yanda zata yi ƙoƙarin ƙwacewa ba zai taɓa bata damar hakan ba, duk inda ta zauna anan zai zauna, haka idan kwanciya tayi shima zai kwanta, idan za su ci abinci da kansa yake ba ta a baki, da haka ya gina wani irin kusanci a tare da su ba tare da ta shiryawa hakan ba.

Haka kawai zai ce tazo suyi kallo, duk da ta fahimci shi ɗin ba ma'abocinsa bane, amman haka zai kwanta akan sofa ya ɗora kansa a cinyarta ya ce kallo ya ke, wani lokacin kuma sai ya yi ta yi mata hira, wani lokacin kuma zaman shiru suke, haka kawai kuma zai ɗauketa ya ɗora a cinyarsa ya ce suyi hira, ya yi mata wani irin sabo da jikinsa, ta yanda bata taɓa jin daɗin kwanciya idan ba'a jikinsa ba, haka zama tafi son duk abin da za ta yi ya kasance yana kusa da ita, ba ta son ya yi nesa da ita ko kaɗan.

Ba ta san ya akai ba, ita dai kawai ta wayi gari ta nemi tsoron da take masa rasa.

Zay'd da kansa ya kula da sauyin da aka samu a tare da ita, mussamman yanda ta dena nisanta kanta da shi, za ta zauna suyi hira koda sama_sama ce, sannan da akwai abin da ya kula ta na so a tare da shi, sumar kansa da gemunsa, ya fahimci tana matuƙar sansu, saboda indai zai kwanta a jikinta, hannunta baya rabo da wasa da su, shi da kansa yasan yanzu babu wannan tsoron da take masa dan haka ya cika wani irin farin ciki...

WANNAN KENAN..

★★★

Zaune ya ke a kan gado ya jingina bayansa a jikin gadon, hankalinsa gaba ɗaya yana kan wayar hannunsa, yana duba saƙon da aka tura masa daga office ɗinsa na Abuja. Itama ta na kwance a gefensa, kanta akan cinyarsa tana game a wayarta, hannunsa ɗaya da babu waya a ciki, yana cikin nata yana wasa da ƴan yatsunta.

"Besty"

Ya kira ta cikin sanyin murya, ba tare da ya bar abin da yake ba.

"Muhan"

Ta amsa tana ci gaba da game ɗinta.

"Mun yi magana da Sameer ɗazu akwai ayyukan da suka taru a can Abuja, suna jirana, kuma ina ganin daman ya kamata na koma"

Ba ta san sanda ta juya ta kallesa ba.

"Abuja?"

Ɗago kansa yayi daga kan wayar hannunsa, jin a yanda tayi maganar, idonta yake kalla da har sun sauya kala.

"Hutun da na ɗauka ya ƙare"

Ya bata amsa yana ci gaba da kallon cikin idonta.

Shiru ta yi sai wani irin kallo da take binsa da shi, wanda ya kasa gane kona menene, janye idonta tayi a kansa ta mayar kan wayarta, duk da cewa a zahiri hankalinta baya kan wayar yanzu.

"Ok"

Daga haka ba ta kuma ce masa komai ba. Ajiye wayar hannunsa ya yi ya juyo da ita ta fuskance sa.

"Me ya faru?"

Ya tambayeta yana kallonta.

"Babu komai"

"Besty"

Hannunta da ke cikin nasa ta fara ƙoƙarin zare wa, amman ya hanata.

"Za ka daɗe?"

Ta tambayesa kamar za ta yi kuka.

"Bansaniba, ya danganta da irin aikin da naje na tarar"

Shiru ta yi kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ƙara tambayarsa.

"Yaushe za ka tafi?"

"Nan da kwana biyu"

Shiru ta yi ta cire hannunta a nasa, sakar mata ya yi, ganin kamar tana buƙatar hakan, kallonta yake saboda yanda yaga tana ta faman juya zoben da ke hannunta, abin da ya daɗe da kula, idan tana cikin damuwa ne take hakan, ko kuma idan ba ta son magana.

"Kalleni Besty"

Ba ta kallesa ba, saboda har idonta ya ciko da hawaye, sai da ya ƙara maimaita mata, sannan ta ɗago a hankali ta kallesa.

"Za ki kewata idan na tafi?"

Ya tambayeta yana kallon cikin idonta.

Da sauri ta kawar da kanta, hawayen da take ƙoƙarin shanyewa suka zubo mata. Murmushi ya yi kaɗan ya juyo da fuskarta wajen tasa, hannunsa ya sa yana share mata hawayen.

"Tambayarki na yi fa za ki kewata menene abin kuka?"

"Ba komai"

"Me yasa ki kukan?"

Kanta ta girgiza masa, ɗagota ya yi daga kwance ya rungumeta, da ƙarfi ta saka hannayenta ta rungumesa, tana sauke ajiyar zuciya.

"Za ki bini muje tare?"

Kanta ta ɗago da sauri tana kallonsa.

"Ni?"

"Ehh"

Ya bata amsa yana murmushi.

"Zamu je tare shikenam dena kukan"

Ya yi maganar yana jan dogon hancinta.

"Ko ba za ki ba?"

Ba ta san sanda ta ware idanunta ba, ta kasa ce masa komai har lokacin akwai shakku akan fuskarta.

"Za mu je gobe ayi miki passport, ki dena kuka mijinki ba zai tafi ya barki ba"

Da sauri ta cusa kanta a ƙirjinsa tana murmushi cike da jin kunya, dagaske ba za ta so ya yi nisa da ita ba, ba ta san ta ina zata fara zama babu shi ba a yanzu, idan har iya kewarsa za tayi ma ai da sauƙi.

Saman kanta ya sumbata a hankali ya na murmushi, a cikin zuciyarsa kuma wani irin farin ciki ya ke, wannan wata kyakkyawar dama ce da ya ƙara samu a kanta.

Washe gari yana tafiya masallaci bayan tayi sallah, ta shige kitchen da kanta take son haɗa musu breakfast dan tun da tazo gidan ba tayi girki ba, simple ta haɗa ta jera musu shi a dining, tayi tunanin idan ta koma za ta same sa a saman sai taga bai dawo ba, toilet ta shige ta yi wanka, ɗaure da towel ta fito ruwa na bin jikinta, a gaban mudubi ta tsaya ta fara shiryawa, tana cikin shafa mai ya turo ƙofar ɗakin ya shigo.

Wata iriyar kunya ce ta rufeta da ta hanata ci gaba da abin da take yi.

Kamar wanda bashi da laka haka ya ƙaraso bayanta ya tsaya, a hankali kuma ya saka hannunsa ya rungumeta ta baya, jikinta ne ya fara rawa a hankali, ba tayi ƙoƙarin raba sa da jikinta ba, duk da yanda ya ke ta sauke mata numfashi a fatar wuyanta, jin abin da ya fara mata ne ya sa ta juyowa babu shiri ta rungumesa, tana riƙe hannunsa, bata san ya aka yi ta tsinci kanta a gado ba, ba tayi yunƙurin dakatar da shi ba, duk da har zuciyarta tana fargaba, bata san me ya tuna ba sai gani tayi ya juya gefenta yana sauke numfashi.

Ya jima a kwance kafin ya tashi ya shige toilet, ruwa ya sakarwa kansa, ajiyar zuciya ya sauke saboda yanda sanyin ruwan ya ratsa sa, ya jima a cikin toilet ɗin kafin ya fito, bai kalleta ba ya shirya ya fita daga ɗakin.

Bayansa tabi da kallo tana jin wani iri a cikin ranta, bata san me ya dakatar da shi ba, amman tasan ita bata hanasa ba, ya yi haƙuri kuma ko iya haka ya cika alƙawarin da yayi, dan haka itama a shirye take da ta basa haƙƙinsa, tashi tayi ta koma toilet ɗin ta sake wanka, bata iya tsayawa kwalliya ba, turare kawai ta fesa ta saka doguwar riga ta fita.

"Best friend"

Ta kira sunansa tana dafa kafaɗarsa.

Idonsa da ya yi ja ya ɗago ya zuba mata. Kasa jurewa tayi tayi ƙasa da nata idon. Hannunta ta miƙa masa suka yi musabaha kamar yanda suka ba.

"Na haɗa maka abinci Muhan"

Ɗan ƙaramin murmushi yayi.

"Tea kawai zan sha Besty"

Tsugunnawa ta yi a gabansa tana leƙa fuskarsa, ganin yaƙi kallonta, duk da ta na jin kunyarsa, haka ta dake ta ci gaba da kallon fuskarsa.

"Muhan"

"Uhm Falmata"

Rasa abin da zata ce masa ta yi, kawai sai ta ja hannunsa suka nufi dining ɗin, abinci ta zuba masa sannan ta haɗa masa tea ɗin da ya buƙata, kaɗan ya sha ya ce mata zai je ya kwanta. Itama ba ta iya cin abincin ba ta tashi tabi bayansa. A kwance ta same sa ya yi rufda ciki, hannunsa a cikin sumar kansa. Kwanciya ta yi a bayansa itama ta saka hannunta a cikin sumar ta shi.

A hankali ya birkitota ta koma ƙasansa, ya jima yana kallonta kafin ya yi murmushi.

"Besty bacci zan yi kije ɗakinki, kafin na tashi ki shirya zamu fita wajen da za'a miki passport, idan mun gama zamu je shopping"

Ƙoƙarin ɗagata yake ta saka hannunta ta riƙesa, bata san abin da zata ce masa ba, kuma bata san me ya kamata tayi ba, ba ta da wani zaɓi face ta kai masa kanta da kanta, amman kuma anya zata iya aikata hakan, sun jima a haka kafin ya kwanta ya janyota jikinsa, a hankali taji saukar numfashinta a wuyanta, alamun ya yi bacci, itama baccin ne ya ɗauketa.

Sai wajen sha biyu suka farka, ya riga ta tashi wanka ya yi shirya cikin ƙananun kaya, sannan ya tsaya a kanta.

"Zan jure Besty har sai kin furta duk abin da yake ranki da bakinki"

Fuskarta ya fara shafawa a hankali ta buɗe idonta. Wani irin murmushi ya sakar mata, bata iya mayar masa ba, sai kallon da ta bisa da shi, ɗagota ya yi ya kaita har bakin toilet, tana shiga ya ja mata ƙofar, kafin ta fito ya gyara kan gadon da suka kwanta, sannan ya fita ya bar mata ɗakin.

"Besty kin shirya?"

Ya tambayeta yana tsaye a bakin bedroom, yana gyara agogon hannunsa.

Ta na tsaye a gaban mudubi tana gyara rolling ɗin fuskarta, bayan ta gama jakarta ta ɗauka, sannan ta juyo ta na kallonsa.

"Na gama"

Murmushi ya yi mata sannan ya miƙa mata hannunsa, hannunta ta miƙa masa ya riƙe suka fito tare, ƙasa suka sauka suka nufi inda motarsa take , buɗe mata ƙofar gaba ya yi ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga driver seat.

"Ina zamu fara zuwa Muhan?"

"Wajen yi miki passport"

Ya faɗa yana kunna motar, horn ya yi me gadi ya buɗe musu get suka fice, already ya yi magana da wanda zai mata, dan haka da suka je basu daɗe ba, a ka yi mata duk abin da ya dace, bayan sun gama kuma ya ɗauki hanyar nasarawa.

*Barakat store* ya kaita da kenan a titin gidan Gwamna, bayan sun fito daga motar bai damu da idon mutanen dake wajen ba, ya riƙe hannunta suka shiga, kai tsaye ɓangaren kayan mata ya kaita.

"Besty ki ɗauki duk abin da kike buƙata"

Ya yi maganar yana sakin hannunta.

Babu abin da take buƙata, dan har yanzu bata ma fara amfani da kayan lefenta ba. Ganin ta tsaya ne ya sa shi fara zaɓar mata duk abin da yaga yayi masa kyau, bayan ya gama anan ɓangaren ƙananun kaya yaje nan ma duk abin da ya burgesa sai da ya ɗauka.

"Muhan kayan nan fa sunyi yawa"

Ta dakatar da shi ganin duk abin da yazo hannunsa ɗauka kawai yake.

Ɓanagaren jaka da takalmi suka je, bayan ya gama danan, suka koma ɓangaren turare, sai da ya gama siyayyar tsaff, sannan ya yi mata shopping nasu chocolate da biscuit, wajen biyan kuɗi suka je ya bada atm ɗinsa aka cire, sannan aka saka masa kayan a manyan shopping bag, yaron shagon ne suka kai masa kayan mota. Yana shirin tayar da motar ta dakatar da shi.

"Besty ina buƙatar kayan snacks please"

Fasa kunna motar ya yi suka koma ciki, ba su jima ba suka fito.

Gidan Ammie take son zuwa, amman bata son zuwar mata haka, shiyasa tace ya yi mata siyayyar.

Sanda suka koma gida ana shirin sallar magriba, dan haka tana shiga gida, shi kuma masallaci ya nufa..

Bayan tayi sallah wanka ta yi ta sakko ƙasa jiransa, tasan ba zai dawo ba, sai yayi sallar Isha'i ba ta buƙatar yin girki kuma, saboda sun tsaya sunci abinci kafin su dawo gidan, wayarta ta ɗakko tana shige shige anan ta samu Khairiyya a online suka fara hira, duk da ba tayi nisa ba, saboda amarcin da take ci.

Tabbas ta yadda Allah Allah ne, cikin *LOKACI* ƙalilan ya canza musu rayuwarsu, idan ta tsaya ta kalli rayuwarta da ta Khairiyya sai ta rasa tunanin da ya kamata tayi, yanzu duk abin da Khairiyya ta fuskanta, gata ta sake aure auren ma na saurayi, kuma daga yanda ta bata labarinsa, ta fahimci mutumin kirki ne.

Idan kuma ta duba kanta, sai ta ƙara tabbatar da ikon Allah, kamar ƙiftawar ido Muhan ya dawo cikin rayuwarta, da bayyanar sa da aurensu har yanzu ba'ayi cikakken wata uku ba, idan har ba Allah ba waye zai yi haka, ta ƙara tabbatar da komai *LOKACI* ne da shi dan haka a yanzu dai babu abin da za ta ce Ubangijinta sai godiya.

Jin ana sallar Isha'i ne ya sa ta koma sama, bayan ta idar ɗakinta ta koma, wardrobe ɗinta ta buɗe ta tsaya a ɓangaren ƙananun kaya, tunda ta zo gidan bata taɓa saka su ba, a yanzu ma tunanin ta saka ko kar ta saka take yi, sai dai bata san me yake jan ta ba, tana jin har a cikin ranta itama tana son ta faranta masa kwatankwacin yanda yake faranta mata, rasa wacce zata ɗauka tayi, kawai ta rufe idonta ta taɓa wata, buɗe idon tayi taga wacce ta ɗauka, doguwar riga ce blue Black, gaban mudubi ta matsa, har ta fara cire kayanta ta koma ta sakawa ƙofarta key sannan ta dawo ta ci gaba.

Rigar ta saka da kaɗan ta wuce gwiwarta, sosai rigar ta lafe a jikinta, ƙaramin hannu ne da ita, powder ta shafa kaɗan, sannan ta saka kwalli a cikin idonta, sai kuma ta saka lipstick light pink, mascara ta saka ta gyara gashin idonta, sannan ta gyara girarta, gashin kanta taje tayi parking ɗinsa a tsakiya da ribbom pink, sai ta saka gel ta kwantar da shi, turare ta fesa a jikinta.

Daidai lokacin da aka fara mata knocking, sai da ta kalli kanta a mudubi sannan ta juya ta kalli ƙofar, har ta kusa ƙarasawa ta juyo ta ƙara kallon kanta, anya zata iya fita gabansa a haka.

"Besty kina ina ne?"

Muryarsa ta katse mata tunanin da ta tafi. Buɗe ƙofar tayi ta koma bayan ƙofar ta tsaya, cikin ɗakin ya shigo.

"Best...."

Maganar ta maƙale masa a maƙogaro, ido kawai ya zuba mata baya ko ƙiftawa, ga bakinsa a buɗe ya kasa rufewa, tunda ga sama har ƙasa yake ƙare mata kallo.

Ƙasa tayi da kanta saboda wata iriyar kunya da ta rufeta ganin yanda yake ta yawo da idonsa a kanta, kasa jurewa tayi ta juya masa baya.

Idonsa ya tsayar a kan ƙugunta, yasan daman tana da dirin jiki, amman bai taɓa tunanin halittarta ta kai haka ba, bata taɓa zama a gabansa da kayan da suka matseta ba, duk irin kusancin da suka samu kuwa, kayanta basa wuce doguwar riga kuma masu faɗi, tabbas ta shammace sa, faɗin yanda tayi masa kyau ma ɓata baki ne, cikin sassarfa ya ƙaraso bayanta ya tsaya, saukar numfashinsa kawai taji akan wuyanta.

Idonta ta lumshe ta ɗora hannunta akan hannunsa dake kan cikinta, sun jima a haka kafin ya juyo da ita ya riƙe fuskarta a cikin hannunsa, goshinta ya sumbata sannan ya ce.

"Kinyi kyau sosai Besty dole na baki tukwuici"

Murmushi kawai tayi masa ba tare da tace masa komai ba.

"Me kike so?"

"Idan har kayi farin ciki shine abin da nake so Muhan"

Ta basa amsa tana sauke idanunta ƙasa.

Cak ya ɗagata suka fita daga cikin ɗakin, suka nufi ɗakinsu.

"Wai baka jin nauyi nane da kake iya ɗaukata Muhan"

Ta tambayesa da ɗan mamaki a fuskarta, dan dagaske tana mamakin yanda yake iya ɗaukarta, kamar bai ɗauki komai ba.

"Ba wani nauyi da kike da shi, dukanki nawa kike?"

Ya faɗa yana kallon fuskarta.

"Aikam ina da nauyi, kuma kai zance wa duka nawa kake da kake iya ɗaukata"

Wani irin miskilin murmushi ya saki, yana kallonta.

"Gaskiya kam duka nawa nake"

Da sauri ta dafe bakinta, tana fito da idonta waje, sai a lokacin ta tuna da abin da tace masa ai, tana shirin magana ya ajiyeta a kan gadon yana kallonta, har lokacin da murmushi da fuskarsa.

"Muhan nifa ba haka nake nufi ba"

Tayi maganar kamar za tayi masa kuka.

"Hmm" 

"Allah dagaske nake"

Ta ƙara faɗa tana marairaice fuska.

"Wani abu nace?"

Ya ce yana haɗe fuska, duk da a cikin zuciyarsa dariya yake, duk ta bi tsorata kanta.

"Kin san mantawa nake ni yaro ne, shiyasa ma nake ɗaukarki, amman naji daɗi da kika tuna min"

Zumbur ta miƙe tsaye.

"Bacci na ke ji, yau a ɗakina zan kwanta sai da safe"

Ba ta jira cewarsa ba ta ɗauki hanyar barin wajen, ƙafarsa ya saka mata ta faɗo kansa. Mutsu nutsu ta fara ya hanata damar tashi.

Duk ta riga ta canza masa yanayi, hasken ɗakin ya kashe, bayan wani lokaci ya sauke ajiyar zuciya, bargon da suke cike yaye ya shiga toilet. Ajiyar zuciya ta sauke tana bin bayansa da kallo a cikin duhun, taji daɗin kasancewarsu, duk da bai je can ba, ba ta san kuma meya hanasa ba, amman dai koma menene taji daɗin abin da ya faru.

Bai jima ba ya fito, bargon ta rufa a jikinta, ta nufi ƙofar toilet ɗin, sai da ta shiga ta sake sa, sannan tayi wanka itama ta fito, lokacin shi har ya kwanta yana jiranta, tana da kayan bacci a ɗakin dan haka ta saka ta kwanta a jikinsa.

"Thank you Besty Allah ya yi miki albarka"

Ya raɗa mata a cikin kunne. Cikin jin kunya ta sunne kanta a ƙirjinsa, ba su jima bacci ya ɗaukesu....

ASUBA TA GARI Z&Z

FULANI
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol