Free chapter · Read without an account
Chapter 9
INUWAR JIYA
UMMULKHAIR S PANISAU
(KHAIRATUP)
PG05
*
Bata yi bacci yadda ya kamata ba, bata san ma baccin ya ɗauke ta ba. Kiɗan wayarta ne ya hana ta bacci a ƙasan filo haka ta saka hannu cikin fillo ɗin ta ɗauko wayar bata ma gama buɗe idanunta yadda ya kamata ba. Ba tare da ta kalli sunan mai kiran ba ta amsa wayar.
"Rania. Me yake faruwa a nan? Ina Hamza yake?"
Tuni ta wartsake cikin sakan biyu ta farga ta dawo cikin hayyacinta.zaune ta tashi ta maida wayar kunnen ta tace
"Yallaɓai Barka da safiya."
"Ina lafiya ƙalau. Ina son magana da Hamza tun jiya,sai dai ban samu layin shi ba a kashe take, ƙanwarsa ta kira ni tana son magana da shi tun jiya da ya fita bai dawo ba."
Ta ɗan lashi leɓɓenta na ƙasa ta gyara zaman ta tace "Yallaɓai tun jiya nake neman Hamza ban same shi ba zan yi maka fowrding ɗin wayar da muka yi jiya da saƙon da ya tura min ta watsaap da kuma kiran da aka yi min kamar na barazana a kan shi."
"Kina son ki ce min ba ki ga Hamza ba?"
"Haka ne Yallaɓai ban gan shi ba."
"Amma me ya faru ki bani komai in brief."
Nan ta gaya masa tun bayan da suka dawo daga airport ake bin su a baya suka samu suka ƙubuta daga mai bin na su jiya kuma ya samo inda mutumin da suke nema ya ke ya gaya mata zai zo su tafi sai kuma ta neme shi ta rasa daga baya aka kira ta a waya ana mata barazana.
Ya sauke ajiyar zuciya yace "Kenan muna kan hanya. In har an ɗauke Hamza kuma ana bibiyar ku tabbas akwai wani abu a kan wanann case ɗin. Ni ma bani tip aka yi a kan case ɗin shi yasa na zabe ki don ki nemo mana wasu clues ɗin na gamsu daga wanann bayanin naki cewa akwai ƙamshin gaskiya a tips ɗin da na samu.Kar ki damu ki zama dai cikin shiri a yanzu dai ki ɗan dakata da binciken idon su yana kan ki zan aiko miki Daniel Ezraboh."
"Yallaɓai don Allah ban da Daniel."
" A yanzu dai shi ne mafi dacewa. Sai ya fi tallafa miki. Na san ba shi da tsoro shi ma and ki kiyaye a yanzu dai kar ki sake yin wani abu ki zama safe."
"To Yallabai." Ya kashe waya. Suka ajiye wayar.
Ta sauke numfashi,Saukowa tayi daga kan gadon ta shige banɗaki. Ta daɗe a ciki kafin ta fito. Ta shafa mai ta saka wata riga doguwa ta faka gashin ta, ta saka band a kai.
Zaunawa ta yi haɗe da ɗauko laptop ɗin ta. Ta kunna. Sai dai ta kasa yin aikin saboda tunanin ina Hamza yake. Ta sa hannu ta dafa kai.
"Me ya sa za a dauke Hamza?"
"Me ya sani?"
"Ina aka kai shi?"
"Wai ma mene ne wanann Flight 217 ɗin sannan waye ya ba wa Boss tip a kai?
Saƙo ne ya shigo mata waya ta sa hannu ta ɗauka wayar ta duba.
"Ina fata ba kuka kike yi ba?"
Bata ba da amsa ba saboda bata gane layin ba. Ba mai saƙon ne yanzu a gaban ta ba. So take ta warware wasu ƙullin. Kafin ta gama nazari ta sake jin wani saƙon.
"Ya kamata ki ɗan sauko ƙasa ina da abin baki."
A fili tace "Ha'a! Waye haka wanne irin saƙo kuma za a bani?"
"Zan bushe saboda jira kuma in na gaji tafiya zan yi."
Miƙewa tayi da sauri, ta buɗe drower ta ɗauki hijabi har ƙasa ta saka ta ɗau ki mukullin ɗakin sannan ta kashe laptop ɗin ta, bayan ta kashe ta rufe tagogin ɗakin ruf ta ja labule. Sannan ta saka laptop ɗin a ƙarƙashin gado.
Lifter ta shiga nan da nan ta sauka ƙasa.
Bata ɗauki dogon lokaci ba ta isa waje. Ta tsaya cak saboda bata ga kowa ba ta yi kusan minti biyar a tsaye tana juye -juye kafin ta juya tayi tsaki zata koma ciki. Daga baya ta ji ance.
"Miss.Airport?"
Da mamaki ta juya ta ce "Kai ne da ma?"
Ya ɗaga mata kafaɗa yana dariya har point ɗin shi na shigewa ciki.
"Me ya dawo da kai nan?"
"Zuwa nayi na gan ki. Yadda na bar ki ɗazu ne bai min ba na kasa yin komai yanzu ma zan wuce Lagos ne na ga ya dace na zo na gan ki."
"Me ya sa za ka zo ka gan ni?"
"Saboda na damu da ke."
"Me yasa za ka damu da ni?"
"Ban sani ba, amma na damu da ke hakan nan."
"Rayyan! Ina da buri a rayuwa,ina da hangen abubuwa da dama a rayuwata, ka yi rayuwar ka na yi ta wa."
"Kai! Ke ɗan dakata mana ban ce fa ina son ki ba cewa na yi na damu da ke. So kar ma ki fara ɗauka wata kyakkyawa ce ke ehe."
Sai da ta yi murmushin da bata yi niyya ba.
Shi ma murmushin ya yi. Sannan yace "A cire batun wasa ki kula da kan ki don Allah kar ki damu zan taya ki neman abokin aikin ki. Amma yanzu nan da minti arba'in zan yi tafiya zan dawo gobe ko cikin dare ina son na ji me ya sa kike binciken filin jirgin nan ni ma ina son sanin me ya faru."
Ta zura masa idanu kawai ta kasa cewa komai.
"Hey!. Tunanin me kike yi?"
"Ba zan iya gaya maka ba, ya saɓawa aikina."
Zai yi magana wayarsa ta soma ƙara.
"Hello."
Ya ɗan yi shiru yana sauraro na sakwani.
"Yanzu?"
Rania ta kalle shi.
"Okay,na fahimta."
Ya katse wayar. Ta kalle shi tace"Me ya faru?"
Ya maida wayar cikin aljihunsa yace "Flight ɗina da zai je Lagos ne aka yi postponed."
"Postponed?"
"Eh."
"Yaushe kenan zaka tafi?"
"Karfe biyu da rabi na dare."
Rania ta ɗan zaro idanu waje tace "Biyu kuma?"
Ya gyaɗa mata kai.
"Hmm."
"Me yasa kika ce Hmm?"
"Ba komai."
"Ki bani dama muje mu dawo."
"Ina da aikin yi abokin aikina yana hanya."
"Sai ya kira ki a waya ai.Ba nisa zamu yi ba."
"Captain...."
"Don Allah ina son na fita da ke ko ba za ki gaya min komai dangane da case ɗin da kike nema ba ki bari na kai ki wani wurin mu ci abinci You look stressed."
Ta sauke ajiyar zuciya sanann tace masa "Ina zuwa, bari na shirya na sake kaya."
Ya ɗan yi wulli da hannun shi sama alamar ya ji daɗi ta kalle shi ta gyaɗa kai. Ciki ta koma ta saka laptop ɗin ta a cikin jakar ta. Sai da ta ɓoye komai.
Wani wurin cin abinci suka je.Suka yi ordering abin da suke so. Bayan an kawo suka soma ci.
A hankali ta soma yi masa magana.
"Rayyan! Ina da buri a rayuwata,ina da hangen abubuwa da dama a rayuwata,ka yi rayuwar ka na yi ta wa."
"Kai!,ke ɗan dakata mana ban ga ce ina son ki ba cewa na yi kawai na damu da ke. Saboda haka ki ma daina ɗaukar kan ki a matsayin kyakkyawa."
Wallahi sai da wani murmushi ya ƙwace mata yadda ya yi maganar da serious a fuskar sa. Shi ma ya sakar mata murmushin sannan yace "A bar batun wasa. Ku kula da kan ki don Allah kar ki damu zan taimaka maki wurin neman abokin aikin ki."
"Allah Ya sa a gan shi don ba zan yafewa kaina ba idan wani abu ya samu Hamza. Hamza ba kawai abokin aikina ne ba, ɗan'uwana ne da muka ta so tare, muka yi rayuwa tare,abokina ne..." Ta kasa ƙarasawa saboda wani abu da ya tokare mata ƙirji.
"Is okay. Za a gan shi."
"In sha Allahu."
Rayyan ya jingina da kujera haɗe da rungume hannu a ƙirji yana kallonta.
"Tunda babu inda zan je daga nan har zuwa biyun dare...."
"Rayyan."
"Hmm?"
"Kar ma ka fara."
"Ai ba abin da zan fara."
"Wanann kallon na san irin shi."
Ya yi dariya sannan yace "Wani irin kallo kenan?"
"Wanda yake nuna cewa akwai wani abu da ake shirya wa."
"Ba wani abu ba ne mai zafi ba. Abun da nake shirin yi shi ne..." Sai kuma ya yi shiru ya ɗan dakata. Sai kuma ya ja numfashi yace "So nake yi na saka ki dariya kafin na tafi.
Ta ware idanu waje sannan tace "Ai na yi murmushin."
"Bai isa ba."
"Me yasa kace haka?"
"Saboda ina son na tabbatar da cewa ko na tafi za ki cigaba da murmushi."
Ta kalle shi. Sannan tace "Rayyan,kana ɗaukar kanka da muhimmanci sosai."
"Wataƙila." Ya faɗa yana ɗaga kafaɗar sa.
Ya murmusa ya kuma matsowa. "Amma ina son ki gaya min gaskiya."
"Ta me?"
"Don Allah kin yi farin ciki da kika ji na ce anyi postponed ɗin jirgina?"
Raina a ranta tace "Wannan wanne irin mutum ne haka?"
Ya daki tsakiyar tebur ɗin ta dawo hayyacinta.
"Wataƙila."
Ya murmusa har point ɗin shi na shigewa ciki sosai.
"Haka nake son ji daman."
"Ka daina wani yage baki da yawa."
Ya sake washe baki har haƙoransa suka fito waje gaba ɗaya. Ta ƙura masa ido. Wani irin dokawa ƙirjin ta ya yi. Hakan nan in ta gan shi sai ta yi wannan faɗuwar gaban yanzu da ya yi dariya sai ya yi mata wani irin kyau, ya sake burge ta. Ba ta taɓa jin irin wannan kalar abin da zuciyar ta ke ƙoƙarin gaya mata ba. Ta sauke wani irin numfashi ta ɗauki coffe ta kurɓa.
Bai sake ce mata komai ba ya duƙufa da cin abincinsa. Wayar ta ce tayi ƙara sai ta ga Daddy ne.
"Hello, Daddy."
"Rania. Fatan kina lafiya." Daga ɗaya ɓarin ya faɗa.
"Lafiya ƙalau Daddy."
Nan suka cigaba da hira a tsakaninsu. Tana wayar ya sa aka kawo musu ice cream da strawberry da vanilla sai wani cake chocolate ya yi kyau kyau a ido.
Tana gama wayar ta ajiye ta masa wani kallo.
"Amma so kake yi na zama yar lukuta ko?"
"A'a don kin ci wannan ɗan abin ba zai saka ki zama yar lukuta ba."
"Haba ya yi yawa ni dai na koshi. Ka gama mu tafi."
"A'a gaskiya ke na siyowa dole ne ki sha ki ci idan kuma wani abin kike so to ki gaya min sai na sa a kawo miki."
"A'a na koshi ba abinda nake so gaskiya."
"Ba zan ji daɗi ba in ba ki ci ba...ki ka sani ko yau ce ranata ta ƙarshen ganin ki?"
"Wannan blacmailing ne."
"Ko ma me za ki kira shi ni dai sai kin sha."
'"Rayyan! Ka san baka ji ko?"
Ya gyada kai kawai ya saki murmushi ya saka spoon ɗin ice cream a bakinsa.
Babu yadda ta iya dole haka ta haƙura ta saka a baki ta tsotsa kuma ya mata daɗi sosai."Akwai daɗi ko? Ai na gaya miki."
Ta zare masa idanu. Ya sake sakin mata wani murmushin. Sun yi zugum suna shan ice cream sai wayarta ta soma ƙara ta ɗauki wayar ta duba agogon da ke hannunta.
"Wataƙila waya ce mai muhimmanci ki ɗaga mana ki ji ki ka sani ko waya ce mai amfani."
"Na sani,ban ce ka gaya min ba." Ta faɗa tana zumburar baki gaba.
Ya ja da baya yace "My bad."
Ta ɗaga wayar.
"Hello."
"Amfanin waya ka amsa kira ba ka tsaya tunanin ka ɗaga ko kar ka ɗaga ba. Ba saurayin ki ba ne da za ki ja min aji."
Ta yamutsa fuska kamar yana ganinta sai da ta ɗauki a ƙalla sakkani biyar kafin ta ja numfashi tace da shi "Waye yake magana?'
Daga ɗaya barin wayar ya ce "Ke, har yanzu ba ki sauya hali ba kenan?"
"Waye yake magana? A amsa ko na kashe wayar sabo da ina da abin yi am busy."
Daniel daga can ya yi tsaki ya san za ta aikata hakan ya san fiye da haka ma zata aikata masa. "To Daniel ne. Za ki iya zuwa ɗauka na na iso ina bakin airport."
"Bani da mota ka samu abin hawa ya kai ka inda aka sauke ka."
"What?" Bata ba shi damar bata amsa ba ta yanke kiran ta ajiye a gefe.
Daniel ya saki tsaki ya daki ƙafarsa da iska, ya dafa goshinsa tun da aka ce masa da wanann yarinyar zai yi wannan aikin yake jera tsaki ba sa jituwa,ba sa shiri,ba sa ga maciji da ita wata iriyar yarinya ce mai girman kai da ɗagawa gani take yi ita ta fi kowa a office tun da ta samu wani ci gaba shi kenan ta ɗauki kanta a matsayin wata aba. Babu yadda ya iya dole ya hakura ya sake kiran Ogan su ya gaya masa ya isa a ina zai sauka ba tare da ɓata lokaci ba ya samu abin hawa ya faɗi inda za a kai shi.
"Ka mayar da ni hotel, abokin aikina ya zo."
"Uff! Amma bai min adalci ba."
"Saboda me ka ce haka?"
"Saboda ban gama tattaunawa da kawata ba."
Ta miƙe tsaye, ta gyara mayafinta haɗe da ɗaukar jakarta ta ce da shi "Ka mayar da ni ko ka na tafi da kaina."
Zumɓur ya miƙe yace "An gama. Muje Miss.Airport." ta yanka masa harara ta juya tayi waje. Ya bi bayanta yana dariya.
Bai ɗauki wani dogon lokaci ba ya kai ta hotel ɗin. Tana sauka ana sauke Daniel. Suka kalli juna kamar basu san juna ba sai kuma ta ɗauke kai ta kalli Captain.
"Na gode Captain."
"Ni ne ya kamata na gode miki. Kyakyawa da ke kin fita da ni."
Ta harare shi. Ya ja motar sa ya yi gaba.
Daniel ya daga hannu yace "Baki da hali Rania Sulaiman baki da mutunci."
"Na sani gaya min abinda ban sani ba."
Ta faɗa tana yin gaba. A maimakon su hau sama sai da ya gama komai sanann suka zauna a wani kebatattun kujeru suna kallon junansu.
"Ba tare da ɓata lokaci ba yaushe kuka haɗu da Hamza last?"
"Na zaci ba lauya ba ne kai ba? Na zata ɗan jarida ne kuma abin da ya saka aka turo ka daban sanin lokacin da muka haɗu da shi a karshe ba zai maka komai ba saboda ni ma ban sani ba. So muyi abin da ya kawo mu."
"Ke ba za ki taɓa sauya halin ki ko na sakanni ba ne? Kina da girman kai."
"Ko ma dai mene ne halina ne kuma haka zaka yi haƙuri da ni. Yadda ni ma yanzu hakuri zan yi da kai."
"Whatever. Me kuka samo?"
Nan ta gaya masa komai ta kuma nuna masa a laptop ɗin ta. Ya na kalla yana gyaɗa kai.
"Kenan Musa Danladi ake nema?"
"Shi ne."
"Amma me zai hana mu samo bayanai akan Captain Zayd Sulaiman?"
"Ka na da point."
"Ke ce ba kya yarda da basira ta ai."
Tayi rolling idanunta. Ta sakar masa wata iriyar harara.
Ya koma da baya ya jingina da kujerar ya ɗauki ruwa ya sha.
Tashi tayi tace "Za mu fita gobe kana da lokaci ka nemo mana adireshinsa sanann ka samo mana hayar mota muna da buƙatar mota."
"Ban gane ba? Ni ne zan nemo ma daga zuwana yau?"
"Amfanin ka kenan shi yasa aka aiko ka ai don ka yi aiki dama ance maka bacci za ka yi ne? Ranar da na sauka Jos sai da na yi aiki duk rakin Hamza sai da ya fita bare kuma kai."
"Ra...." Ta juya tayi gaba abin ta. Hannu ya sa ya daki tsakiyar teburin yana gunguni kamar wani ƙaramin yaro.
*
Yana shiga cikin falon ya tarar da ma'aikatan gidan na kai-komo daga cikin kitchen zuwa falo.
"Lafiya Atika me ke faruwa?"
Jiki na rawa tana murza yatsunta tace "Aflaha ce..." Tun kan ta ƙarasa ya yi wuf ya afka cikin falon. Kwance ya gan ta samɓal jikin ta na rawa Amma dake zaune a ƙasa tana sharar hawaye saboda yanayin da ta ga yar ta a ciki.
"Amma me ya faru me aka yi mata?"
"Rayyan! Me ya dawo da kai gida? Na za ta jirgin ya tashi?"
"Amma an ɗaga ne sai cikin dare amma me ya samu Aflaha me aka yi mata?"
"Ban sani ba, ni ma ihun su Atika ne ya fito da ni."
Functional Neurological Disorder (FND) Tun bayan rasuwar mahaifinsu da yayyunta biyu ta kamu da wata matsalar jijiyoyi da ta samu bayan mummunan shock ɗin da ta shiga.Tun daga lokacin take fama da jijjiga,rikicewar gani wasu lokutan kuma jikinta ya kan kafe ko ta fita daga hayyacinta.
Ɗaki suka kai ta. Maganin ta ya bata.Cikin hukuncin Allah sai ga shi jikinta ya soma lafawa har ta koma bacci.
Amma ta koma falo ta zauna. Ta kalli Rayyan shi ma ita yake kallo. Ganin yadda yanayin ta ya canja ya saka ya koma kusa da ita ya zauna.
"Amma..."
Ta ƙaƙalo murmushi don ta kwantar masa da hankali tace "Ba komai in da sabo ya kamata na saba."
"Amma za ta warke in sha Allahu."
"In Allah Ya yarda. Amma me ya dawo da kai?"
Sai da ya saki ajiyar zuciya sannan ya shafa kan shi yace "Amma sai an jima za a tafi."
"To. Ya yi. Ka je ka huta kafin anjiman."
"To."
"Ko za ka ci abinci?"
"A'a na ƙoshi Amma."
"Anya kuwa kai da ba ka da lokaci?"
"Allah Amma na ƙoshi."
"To na ji. Tashi ka je ka huta. Allah Ya tsare hanya na san ma ƙila ina bacci za ka tafi."
"Kamar kin sani 2 zamu tafi wurin one dai zan tafi."
"To shi kenan."
Daga nan suka rabu.
Ko da ya shiga wanka ya sake yi. Ya buɗe wata drower ya zaro wata jaka daga ciki, ya ajiye ta a kan gado.Sai da ya shafa jakar ya fitar da wani irin numfashi sannan ya buɗe ta. Hotuna ne ya fito da su kala daban-daban ya jera su a gaban sa. Ya shafa ya saki murmushi. Ya ɗauki wani hoto ya kalla tuni ƙwalla ta tarar masa a idanun sa. Wayar shi ta soma ƙara. Ya tashi ya ɗauko wayar ya kalla.
"Hello,sir."
"Hello.Captain."
"Akwai meeting yanzu haka ina son ka dawo avaition."
Ya kalli agogo ya kuma kalli waje kamar ba zai fita ba amma ya san bai isa ba aiki ne kuma duty comes first.
"Okay,Sir."
Ya ajiye waya. Ya shiga banɗaki ya sake wanka ya dawo ya tattara dukkanin hotunan nan da jarida ya mayar cikin jaka ya mai da cikin drower ya kulle.
Uniform ɗin sa ya ɗauko rigar fara da stars a jiki, sai kuma ya saka dogon wando baƙi ya ɗauko hula ya kafa a kai ya saka wani baƙin gilashi a kan fuskar sa. Tuni ya fito fes da shi Captain Rayyan Zayd kenan matashin saurayi Pilot mai ƙwazo da sanin ya kamata.
Ya ɗaura wani baƙin agogo. Ya saka takalmansa sau ciki ya fesa turare ya kalli madubi. Ya saki murmushi kawai fuskar Rania ya hanga a cikin mudubin daga baya tana masa murmushi tana masa weaving ɗin hannu a hankali kamar me raɗa tace "Captain." Sai ya juya sai kuma ta ɓace ma sa. Ya juya da sauri yace "Ya Allah!" Mukullin motarsa ya ɗauka a jikin ƙusa ya fita daga dakin.
Sai da ya haura sama, ya shiga ɗakin Amma ya ƙare mata kallo yadda take bacci cikin kwanciyar hankali ya saki murmushi ya kalli hoton da ke kan bed side drower hoton mahaifin shi ne da ita kalar hoton ma Black and white ne in their 90s era. Ya saki murmushi ya mayar ya ajiye ganin ta motsa kamar za ta tashi. Ya sake shiga ɗakin ƙanwar shi Aflaha. Ya tarar ita ma bacci take yi yana juyawa ya ji ta ce "Hamma."
Ya juya da sauri sai kuma ya saki murmushi yace "Aflaha."
"Me ya sa ka koma?"
"Na ga kina bacci ne."
"Na tashi tun ɗazu. Kuyi haƙuri ina ta gajiyar da ku ko?"
Ya harare ta sannan yace "Wane ya gaya miki haka?"
"Ni ce."
"To ba mu gaji ba.By the way ki koma baccin ki, sai na dawo."
"Sai ka dawo ina son ka."
"Ni ma haka." Ya faɗa yana shafa kanta.
*
Filin jirgin saman ya yi shiru ba kamar lokacin hada-hadar fasinjoji ba. Hasken fitilu runway na ta walƙiya daga nesa. Yayin da wasu jiragen ke shirin tashi,wasu kuma na saukowa.
Daidai dakin taron ya faka motar sa. An ware ɗakin taron ne don manyan jami'an kamfanin.A wajen ƙofar an rubuta AVIATION OPERATIONS & INVESTMENT MEETING
Rayyan Zayd ya tsaya a gaban ƙofar na ɗan lokaci. Sanye yake cikin cikakken shigar shi a matsayinsa na Captain, hular sa a hannu,fuskar sa cike da nutsuwa. Bai za ci meeting ɗin mai muhimmanci ba ne ba haka. Ya buɗe ya shiga ciki. Mutane biyar ne a ciki a cikinsu har da Alhaji.Nasir tsohon ɗan harkalla. A tsakiya kuma ya ga Mika'il ɗaya daga cikin manyan masu zuba jari a harkar sufuri da jiragen sama. Ba kasafai yake halartar irin waɗannan taruka ba sai idan akwai babban aiki da ke gabansa.
Mika'il ya ɗaga kai ya kalli Rayyan bayan ya shiga ciki.
"Captain Rayyan."
Rayyan ya yaushe su kafin ya samu wuri ya zauna.
"Good evening."
"Good evening,Captain."
Mika'il ya buɗe wani file mai ɗan girma.
Ba tare da ɓata lokaci ba ya fara magana.
"Wannan ba iya zaman management meeting ba ne ba."
Rayyan ya kalle shi yana jiran ƙarain bayani.
Haka ya saka ya ce "Me ke faruwa?"
Mika'il ya danna wani remote. Babban screen ɗin da ke bayan su ya yi haske. Hoton wani sabon jirgi ya bayyana.
Rayyan ya ɗan matsa kusa da tebur kaɗan yace "Sabon Fleet?"
"Eh."
Mika'il ya juya ya kalli Rayyan.
"Muna shirin ƙara jirage a Kamfani. Amma kafin mu sanya hannu kan yarjejeniyar saye,muna son ra'ayin Captain ɗin da zai fahimci jirgin daga ɓangaren da ba management ne ke gani ba."
Rayyan ya ɗaga girarsa. Sanann yace "Wanne irin jirgi?"
Ya nuna masa bayanan jirgin. Ya karanta su a hankali.
"Capacity?" Ya faɗa.
"Bakwai da tamanin." Mika'il ya amsa.
"Range?"
Mika'il ya faɗa masa adadin.Rayyan ya ɗan yi shiru.
"Route ɗin da za su yi amfani da shi fa?"
A nan kuma Mika'il ya yi murmushi.
"Wannan shi ne abin da muke son tattaunawa a kai."
Ya danna wani madani.
Taswirar Afrika ta bayyana a screen.
An haskaka birane daban-daban.
"Kamfanin yana son buɗe sababbin routes.Amma muna buƙatar investors kafin mu fara."
"Ban zan fara magana a kan investors ba kafin mu san route ɗin."
Mika'il ya jingina da kujerarsa. Yace "Ci gaba."
Rayyan ya nuna taswirar.
"Jirgi da kake gani ba kamar gini ba ne,da za ka sata ka bar shi ya tsaya ba. Kowacce rana da yake a ƙasa,yana cin kuɗi."
Duk mutanen da ke ke kan teburin suka yi shiru suna sauraron sa.
"Fuel, maintenance,crew, insurance, airport charges....duk suna gudana ko jirgin yana tashi ko baya tashi."
Ya sake nuna wani route ɗin.
"Saboda haka dole ne mu fara da routes da ke da passengers."
Mika'il yace "Passengers kawai?"
Rayyan ya girgiza kai.
"Ba passengers ba kawai."
Ya kalli screen ɗin yace "Corporate travellers."
Alhaji Nasir ya ɗaga kai ya kalle shi kawai. Nazarinsa yake yi yana na tuna masa da wani tsohon Captain.
Rayyan ya ci gaba da magana.
"Bankuna.kamfaninin mai da gas.Manyan business.Government contractors.International companies." Ya mayar da kallonsa ga Mika'il.
"Idan muka samu yarjejeniya da manyan kanfanoni,ba sai mun jira passenger daya bayan ɗaya ba.Za mu iya samun corporate travel contracts."
Mika'il ya yi dariya sanann yace "Wanann nake son ji dama."
Rayyan ya ci gaba da yi masa bayani.
"Misali,idan wani kamfani yana tura ma'aikatansa birane daban-daban akai-akai,za mu iya ba su corporate agreement.Su samu sauƙi,mu kuma mu samu passengers masu dawowa."
Mika'il ya ɗora hannunsa a kan tebur.
"Saboda haka kana ganin investors za su iya shiga?"
"Idan muka nuna musu business model ɗin da take da ma'ana."
"Ba jirgin ba kawai?"
"Eh."
Rayyan ya gyara zamansa.
"Jirgin kayan aiki ne. Abin da investor yake saka kudinsa a ciki shi ne kasuwar da jirgin zai yi aiki a cikinta."
Shiru ya ratsa ɗakin.
Mika'il ya juya ya kalli ragowar yace"Kun ji ko."
Sai kuma ya ce "Captain ina son ka shiga cikin wannan project ɗin."
Rayyan ya kalle shi yace "A matsayin me?"
"Ba investor ba,ba kuma iya Captain ba."
Ya tura masa wani file gaban shi.
"Za mu kafa avaition advisory team. Kai ne za ka kasance cikin mutanen da za su tantance jiragen,routes,crew requirements da operational side kafin investors su saka kuɗinsu."
Rayyan ya kalli file ɗin.
"Wanann babban project ne."
"Na sani."
"Me yasa sai ni?"
Mika'il ya yi murmuhsi yace "Saboda mutane da yawa sun san yadda ake gudanar da business."
Ya nuna uniform ɗin Rayyan.
"Amma ba kowa ne ya san abin da yake faruwa a sama da ƙasan cikin jirgi ba."
Rayyan bai ce komai ba.
Daga waje ƙarar jirgi ya cika ɗaki.wani jirgi ne zai tashi hatta dakin taron sai da ya girgiza kaɗan.Rayyan ya kalli jirgin yana lulawa cikin sararin samaniya.
Mika'il yace "Wanann shi ne farkon aikinmu,Captain Rayyan."