Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Ummulkhairi Sani Panisau · INUWAR JIYA

INUWAR JIYA
NA
Ummulkhair S Panisau 

06.

*

"Then let's find the right investor."
Mika'il ya buɗe baki zai yi magana sai dai kafin ya ce komai aka buɗe kofa aka shigo ciki.

Wani dogon mutum ne ya shigo shekarunsa zasu kai arba'in da biyar,babu hayaniya a shigar sa yana da kwarjini.Yadda kowa ya yi shiru ya maida hankali kan mutumin kaɗai ya isa ya nuna matsayin mutumin ba ƙarami ba ne.
Mika'il ya miƙe tsaye.
"Alhaji Hamdan."
Rayyan ya kalle shi.
Alhaji Hamdan ya gaishe da kowa ya ja kujera ya zauna.
Mika'il yace "Captain Rayyan,wannan shi ne Alhaji Hamdan Kareem. Ɗaya daga cikin mutanen da suke nazarin yiwuwar saka hannun jari a aikinmu."
Alhaji Hamdan ya kalli Rayyan irin kallon sama da ƙasan nan.
"Captain."
"Eh Captain Rayyan." Ya amsa cike da nutsuwa.
"Flying for how long?"
"Years."
Alhaji Hamdan ya ɗan yi murmushi.
"Ya yi kyau!"
Ya buɗe file ɗin da aka ajiye a gabansa.
"Na karanta proposal ɗin."
"Ka amince?" Mika'il ya tambaye shi.
Alhaji Hamdan bai ba shi amsa a take ba. Ya kalli taswirar routes ɗin da ke kan screen ɗin.
"Jiragen uku."
Ya nuna bayanan.
"Wanann shi ne abin da kuke son ku fara da shi?"
"Eh su ne." Mika'il ya faɗa.
"Investment ɗin ya yi yawa."
"Mun sani."
"Return ba zai so cikin gaggawa ba."
"Mun sani."
Alhaji ya jingina bayansa da kujerarsa.
"To me zai saka na saka kuɗi na?"
Suka yi shiru.
Mika'il ya kalli Rayyan.
Rayyan ya fahimci abinda yake faruwa.
Ya ɗan matsa gaba yace "Saboda ba za ku saka kuɗinku a jirage ba."
Hamdan ya kalle shi.
"Ƙarain  bayani."
"Za ku saka kuɗinku ne a cikin tsarin da zai sa jiragen su samar da kuɗi."
Hamdan ya ɗaga girarsa.
Rayyan ya miƙe ya tsaya a gaban screen ɗin.
"Idan muka sayi jirage uku kawai saboda muna son mu faɗaɗa fleet,wannan ba investment strategy na ne." Ya canja slide.
"Amma idan muka samu routes masu amfani,muka ƙulla corporate travel agreements,muka tsara flight schedule bisa buƙatar kasuwa,muka rage unnecessary operational costs,sannan muka gina tsarin da zai iya faɗaɗa...." Ya juya "Wannan investment ne." Hamdan ya kalli shi na wasu sakanni.
"Na gamsu,ka yi magana kamar ɗan kasuwa."
Rayyan ya saki murmushi."Na yi magana kamar Captain ɗin da ya san cewa kowanne minti jirgi yana ƙasa yana da farashi."
Mika'il ya yi murmushi.
Hamdan kuwa ya ɗauki alƙalami ya yi tunani.
Yace "Okay." Ya buɗe wata takarda.
"Ina da sharaɗi."
Mika'il yace "Wanne irin sharaɗi?"
"Ba zan saka kuɗina a cikin project ɗin da management ɗinsa ba shi da cikakken iko ba."
Mika'il ya gyara zamansa.
"Me kake nufi Alhaji?"
"Ina son a kafa wani independent avaition board."
Rayyan ya kasa kunne kawai.
"Board ɗi zai kula da fleet acquisition,route expansion da operational performance."
Mika'il ya yi shiru.
Hamdan ya ci gaba da magana.
"Ba wai so nake na mallaki kamfanin ba ne,ina son na tabbatar da cewa kuɗina ba za su shiga inda bai kamata ba."
Sai kuma ya juya ya kalli Rayyan.
"Captain Rayyan."
"Na'am Yallaɓai."
"Ina son ka kasance a cikin wanann board ɗin."
Rayyan ya yi shiru. Mika'il ya kalle shi yace "Me?"
Hamdan ya cigaba da bayani.
"Ba saboda ka fi kowanne Captain ba.Sai don kau ne mutumin da zai iya gaya mana gaskiyar abin da ke faruwa a cikin operation,ko da gaskiyar ba ta yi wa management daɗi ba."
Rayyan ya kalli file ɗin.
"Wanann ba ƙaramin nauyi ba ne. Amma zan yi tunani a kai."
Hamdan ya yi murmushi yace"Take your time."
Ya miƙe yace "Akwai abu ɗaya da nake so ku fahimta."
Duka suka kalle shi.
"Idan za ayi wannan project ɗin,ba zan saka kuɗina saboda sunan kamfani ba." Ya faɗa yana kallon Rayyan. "Zan saka ne saboda mutanen da suke bayan kamfanin." Ya buɗe kofar ya fita.
Ɗakin ya yi shiru. Mika'il ya kalli Rayyan yace "Captain."
Ba tare da ya kalle shi ba yace "Uhm."
"Ka fahimci abin da yake nufi?"
Rayyan ya ɗaga idanunsa yace "Eh."
Mika'il ya ce "Ba aikin pilot ba ne abin da yake so."
"Na sani."
Daga waje wani jirgin ya sake ratsa runway.Rayyan ya kalli hasken jirgin yana ɓacewa cikin duhun dare.
A karo na farko bayan zuwan shi ɗakin taron ya fara tunanin cewa wataƙila rayuwarsa ba za ta tsaya a iya cikin cockpit ba.
*

Bayan an kammala meeting ɗin ya duba agogo 1:17 am.
Flight ɗin da zai jagoranta zai tashi da karfe biyu. Ya ɗauki wayarsa yana fita daga ɗakin taron ya dinga scrolling har ya samo lambar wayar da yake nema ya saki murmushin da bai san dalilin yin sa ba. Ba tare da wata shawara ba ya danna kira.

A ɗaya ɓarin kuwa Rania na tsaka da bacci ta soma jin vibration ɗin wayarta dake gafenta cike da kasala ta ɗaga kiran ba tare da ta kalli waye yake kiran ba.
"Hello."
Muryarta ta fito hankali.
Rayyan ya yi murmushi.
"Good evening,Miss airport."
Rania ta buɗe ido da ƙyar.
"Captain."
"Hmm."
"Me ya faru?"
"Nothing."
"Then me yasa ka kira ni a wanann daren?"
Rayyan ya kalli agogon hannunsa.
"Na ga zan tashi zuwa Lagos nan da yan mintuna,sai na tuna akwai wata Miss Airport da ban yi wa sallama ba."
Rania ta ja numfashi.
"Captain,ka kira ni ƙarfe ɗaya na dare saboda sallama?"
"Eh."
"Ka kira wani lokacin mana."
"Wanne?"
"Lokacin da mutane ba sa bacci."
Rayyan ya yi dariya a hankali ya buɗe motar sa ya shiga ciki.
"Amma ke ai Miss.Airport ce. Na zata kina aiki da dare.'
Rania tayi shiru na yan sakanni.
"Captain."
"Hmm."
"Ka san me?"
"Me ne?"
"Ka kashe min bacci na da wayar ka."
"Good."
"Good?"
"Eh.Yanzu kin tashi."
Rania ta yi murmushi duk da yana iya jin kasa kar da ke cikin muryarta.
"Ni zan koma bacci."
"Ba ki tambaye ni inda zan je ba."
"Na sani ai."
"Lah ta yaya?"
Ta harari wayar tace "Captain ba dementia nake fama da shi ba. Jiya ka gaya min da muka je cin abinci."
Ya yi dariya,yana sane daman tsokana ce. Ya fashe mata da dariya."
"Okay,okay.Miss Airport ta yi fushi."
"Ba wani fushi."
"Kin yi."
"Ban yi ba."
"Then smile."
Rania tayi shiru.
"Me?"
"Na ce ki yi murmushi."
"Ba ka gani na ai."
"Amma zan iya ji."
"Ta yaya?"
"Saboda lokacin da mutum ya yi murmushi ana ji a muryarki saboda tana sauyawa."
Ta rasa me zata ce masa yace "Kin yi?"
"Me?"
"Murmushi."
"Maybe."
"Good."
"Captain ."
"Yes,Miss Airport."
"Flight ɗin ka fa?"
"Akwai sauran lokaci."
"Ka tafi ka shirya."
"A shirye nake.kawai so nake na ji muryar ki kafin na tashi ne."
Rania ta sauke numfashi.
"Safe flight Captain."
"Na gode."
Sai ya yi shiru kuma sai ya ce"Rania?"
"Na'am."
"Ki kwanta."
"Zan kwanta ai."
"Good girl."
"Captain!"
"Okay,Okay na daina."
"Ka daina zolaya don Allah."
"Ba zan daina ba ke kaɗai nake yiwa fa."
"Why?"
"Saboda ke Miss Airport ce."
Tayi dariya a hankali tace"Allah Ya tsare."
"Amin.Goodnight Miss Airport."
"Good night."
*

Wani irin ciwo kan ta yake yi. Kafin ta san me yake damunta wani irin zazzaɓi ya lulluɓe ta. Hannunta dafe da goshinta tana yamutsa fuska.

A lokacin da take girgiza kan gadonta,lokacin kiran waya ya shigo mata da ƙyar ta janyo wayar daga gefen gado kan beside drower ta ɗauki wayar ta sa a kunnenta.

"Salamu alaikum, Rania da gaske ne ba a ga Hamza ba tsawon kwanaki biyu?"

Ta ɗan dafa kai ta murza goshinta sannan ta sake mirginawa ta kwanta ta shigar da ƙafafunta cikin bargo.

"Daddy waye ya gaya maka haka?"

"Na san abin da baki sani ba so ki ba ni amsa."

"Daddy tunda haka ne ya kamata ka san inda Hamza yake."

Daddy ya yi shiru sai kuma yace "Komai aka gaya miki kina da amsar bayarwa kamar ba mahaifinki ba ne ni me yasa kike son gaya min magana anyhow?"

"Daddy,ba magana nake faɗa ba kai ne ka faɗa ka ce ka san abinda ban sani ba...."

"Ki yi min shiru. Na gama yanke hukunci,zan aiko Sajjid ya taho da ke kin gama wanann aikin."

"Daddy ka sani ba zan bi shi ba so kar ma ya zo ba zan bi shi ba."

"For once Rania ki yi abinda na saka ki."

"Daddy Wallahi zazzaɓi nake yi ba ni da lafiya ka bari na dawo hayyacina tukunna. Already Oga ya aiko Danial Erabor don ya zama madadin Hamza still ana neman Hamza ba zan iya tahowa ba a same shi ba."

"Rania zan aiko Sajjid." Bai bata damar cewa komai ba ya kashe wayar. Ta zamar da wayar daga hannunta ta sake cusa kanta cikin bargo ta dunƙule saboda sanyin da ke ratsa ta. Kan ta ya yi zafi ɗau.
Wayar ta ce ta sake soma ɗaukar sauti. Kiɗan ringtone ɗin iPhone ya ishe ta. Ta janyo wayar ta duba "Captain" ta gani. Ta amsa ta saka a handsfree ta bar ta a gefen ta.

"Hello."
"Ms.Airport."
"Captain."
Sai ya ji muryar ba yadda ya saba ji ba.Nan da nan ya ɓata rai ya ɗaure fuska kamar tana ganin shi. Ya ce "Lafiya?"
"Lafiya ƙalau."
"Kin tabbata?"
"Me ya sa kake tambaya?"
"Saboda muryar ki tana gaya mini wani abu dadan."
Rania ta saki murmushi irin na ƙarfin halin nan. "Ba wani abu ba ne zazzaɓi na tashi da shi kawai."
Rayyan ya miƙe daga kan kujerar da yake a zaune, da sauri ya ce "Rashin lafiya?"
"Ba fa wani babba ba ne ƙarami...."
"Ke! Yi min shiru Please. Rashin lafiyar ne ƙaramin abu?"
Ta kalli screen ɗin wayar kamar shi take kalla sai kuma tace "Ba sosai ba ne."
"Kin je asibiti?"
"A'a,amma zan je."
"Rania." A karon farko da ya ambaci sunan ta kuma sunan ya mata daɗi a kunne duk da ba shi ne ya fara kiran sunan ba kuma ba yau ta taɓa ji ba sunan ta ne dai ba na wani ba sai da ta ji tsigar jikinta ta tashi.
"Na'am Captain."
"Kar ki raina rashin lafiyar nan. Da ace ina Jos yanzu,da na zo da kaina na kai ki asibitin."
"Ga shi kai Captain ne, ba za ka iya zama a wuri ɗaya ba."
"Na sani. Shi ya sa abin yake min zafi a halin da nake ciki yanzu ina jin kamar na zama tsuntsu ne na zo na gan ki." Ya faɗa muryar shi a sanyayye.
"To me yasa ka wani damu haka am okay."
"Duk da haka ina mai baki haƙuri."
"Haƙurin me?"
"Saboda bana kusa da ke."
A wannan gaɓar Rania ta yi shiru na yan sakanni. Sai kuma ta ce da shi "Captain ba dole ba ne ka kasance a kusa da ni ba ko da yaushe."
"Na sani."
"To kar ka damu ba sosai ba ne."
"Wallahi ba ki yadda nake ji ba idan kina faɗin rashin lafiyar nan ba komai ba ne."
"Ni fa jaruma ce zan iya yin komai."
"Takamar ki ke yar jarida ce,to ki tuna yanzu ba lokacin aiki ba ne,magana ake yi ta rashin lafiyar ki."
"Zan je asibitin Captain."
"Ki yi min alƙawari."
"Ha! Captain bana so ka daina min haka ni fa ba budurwar ka ba ce."
"Eh ƙawata ce Aminiya ta ce wadda bata son airport."
"Na ji. Na yi alƙawarin."
"Yauwa na ji daɗi sai anjima."
"To na gode." Ta faɗa da sauri don wayar ta gundure ta.

Bayan ya kashe wayar ya kalli wayar be san dalilin da ya sa muryarta ta dame shi haka ba. Wataƙila saboda a cikin ɗan lokacin da suka kasance tare ba ne ya saka ta zama daga cikin mutanen da ya damu da su ba. Ya kalli agogon hannunsa.lokacin tafiyarsa ya kusa
Rayyan bai yarda cewa zata je asibitin ba. Gani yake yi ta amsa ne don ta samu sarari daga nacinsa. Ya ajiye wayar a kan tebur bayan wasu daƙiƙu kuma ya sake ɗaukar ta. Ya sake shiga wurin kira ya yi ƙoƙarin sake kiranta sai kuma ya fasa ya tambayi kansa .
"Me yasa na damu haka?" Ya sa hannu ya sosa hancinsa kaɗan. Ya sauke numfashi. So yake ya gayawa kansa Rania ba matarsa ba ce, Rania ba yar'uwar sa ba ce,Rania ba budurwar sa ba ce ba. Haduwa suka yi a airport kawai.
Duk da haka,tun da ya ji muryar ta ya kasa samun nutsuwa,hankalinsa ya ƙi kwanciya.
Ya sake ɗaukar wayarsa ya kira wani daga cikin mutanensa.
"Hello,sir."
"Hi! Zan aiko maka da wani adireshi da room number tare da lambar waya ka je can ka kai mara lafiyar asibiti."
"Sir,amma...."
"Kai! Cewa nayi ka je ka kai ta asibiti."
"To Sir."
"Idris ka tabbatar ta je asibitin,an duba ta,an bata magunguna ka mayar da ita hotel ɗin da ta sauka."
"Yes sir."
Ya katse kiran.
Rayyan ya koma kallon ƙofa. Ya girgiza kai a hankali. Ya sake faɗa a fili "Abota ce kawai." Kokawa yake yi da zuciyarsa ya yarda cewa iya abotar ce amma ina zuciyar sa ta kasa ba shi haɗin kai.

*

Da ƙyar ta samu tayi wanka ta saka wasu kayan. Wando ta saka plazo da riga mai ɗan girma irin oversize ɗin nan. Tana shan tea da aka kawo mata daga ƙasa.
Ƙofar ɗakin aka ƙwankwasa sau biyu kuma ta ji amma sai ta ƙi ɗauka saboda bata da wani angedar haɗuwa da wani ko wata. Sai ta ƙi motsawa. Can kuma wayarta ta soma ƙara bata ma duba ba ta tashi a hankali zaton ta wataƙila Daniel ne.
Buɗewa tayi ran nan a haɗe a murtuƙe kamar bata taɓa yin dariya ba.
"Rania?"
"Eh."
"Captain Rayyan ne ya aiko ni."
Fuskarta ta canja tace "Captain?"
"Eh,aiko ni ya yi wurin ki,ya ce na kai ki asibiti."
Ta yi shiru. Mutumin ya ƙura mata ido ta ji kamar zata fadi ta soma gajiya.
"Ban ce masa ya aiko kowa ba."
"Ni ɗan aike ne Hajiya don Allah ki zo mu je."
Ta soma tunanin me yasa Captain ya damu da ita haka ba.Casual haɗuwa ce fa kawai. Kulawar ta yi mata yawa.
Komawa ciki tayi ya yi saurin cewa "Hajiya..."
Ta juyo tace "Ka jira ina zuwa." Ta kulle ƙofar. Wayarta ta ɗauko ta kira shi.
Tun kan ya ɗaga kiran yace "Rigima ta kira ya isa kenan yanzu zata ce min Captain Ba na so." Ya faɗa yana sakin murmushi sai kuma ya amsa kiran.
"Me ka yi haka?"
Ya ɗaure fuska shi ma yace "Me na yi?"
"Ya za ka aiko min mutum ya kai ni asibiti?"
"Saboda ba ki da lafiya."
"Capt..."
"Ki je asibiti."
"Amma me ya sa ka damu da ni haka?"
Ya yi tsit,tambayar ta zo mata a bazata. Ta sake ce masa "Bana so."
Ya saki murmushi kalmar da yake ta jira ta ambata kenan "Bana so."
"Ina magana kana dariya."
"Yi haƙuri Mass.Airport na ji na miki laifi amma ba zan sake ba yanzu dai ki shirya ki je ya kai ki a duba ki."
"Zan je."
"Good."
"Amma Captain."
"Me ne kuma?"
"Na gode."
Ya yi shiru bai bata amsar godiyar ba kawai yace da ita "Sai kun dawo."
Ta buɗe baki tana kallon wayar da ya katse tun kan ta ce komai again.
Bayan sun isa asibiti suka samu ganin consultant ɗin. Ya yi mata tambayoyi ta amsa ya gaya mata maleria ce sai kuma stress ta samu ta huta, ya rubuta magunguna ya sa aka mata allura.

Bayan sun fito zata shiga cikin motar wayarta tayi ƙara ko da ta duba sai ta ga lambar Daniel. Ta ɗan saki huci ta kalli ɗaya ɓarin.
Abdul yace da ita "Lafiya Hajiya?"
Ta kalle shi kawai ta gyaɗa masa kai ta ɗaga kiran.

Tun kan tayi magana ya riga ta yace "Ki zo akwai matsala."

Sai da gabanta ya faɗi ta ji kanta ya sara mata. Ta ɗan sa hannu a ƙirji kafin ta ce da shi da ƙyar "Me ya faru Daniel?"

"Ba maganar waya ba ce wani wuri zamu je da ke amma kina ina na zo na ɗauke ki don a reception an gaya min kin fita."

"Daniel asibiti na je bani da lafiya."

"Sannu. Ki min sharing location zan zo na ɗauke ki an samu wani clue ne a kan Hamza Bello."

Wani irin sarawa kanta ya yi. Tuni ta ji kamar an sauke mata ciwon ta sauke ajiyar zuciya tace "Bara na yi maka." Daga haka suka ajiye wayar.

"Lafiya Hajiya?"

Ta kalle shi kamar tana son karantar wani abu a cikin idon shi. Wayar ce dai ta sake neman agaji. Ta duba sai ta ga Captain ne.

"Captain."

"Ya jikin na ki?"

"Da sauki."

"Ba abin da yake miki ciwo."

"Ba komai. Na gode da ɗawainiya."

"Ɗawainiya kuma? Ke fa ta musanmman ce a wurina."

"Na gode. Ina da wani aiki ne zan kira ka."

"Shikenan.Ni ma ina sa ran zuwa Jos yau ko gobe ki kula da kan ki."

"In sha Allah."

Ta ajiye wayar a cikin aljihun wandon ta.  Ta sake gyara zaman mayafin ta.

"Ka je na gode za a zo a ɗauke ni."

"Zan iya mayar da ke Hajiya."

"Kar ka damu za a zo ana ma hanya wani aikin zan je."

"To na gode sai anjima Allah Ya ba ki lafiya."

"Amin."

Tana kallon yadda ya yi ma motar key a hankali ya yi reverse ya fita daga harabar asibitin tana kallo har ta daina ganin motar. Wani kebantaccen wuri ta koma ta zauna kan wata kujera irin ta ginin nan wurin akwai sanyi. Tana kallon yadda ruwa ke zuba (waterfall) ga korayen ganye da ciyayi. A zahiri su take kalla amma a baɗini ba haka ba ne a ranta wata kalar faduwar gaba ke damunta tunda Daniel ya ce an samu clue na Hamza Bello Hamza babban abokin ta ,Hamza da ya iya karantar fuskarta,Hamza da suka yi karatu tare suka san damuwar juna, lokaci ɗaya aka ɗauke shi yanzu kuma an ce an samu wani clue a an shi.

"Ko kowa baya tare da ke,ni ina tare da ke ba zan bar ki ba, kuma har kullum ina tare da ke a duk rigimar da za ki ɗauko we are together."

"Me yasa ka ce duk rigimar da zan ɗauko?"

"Saboda na yarda da ke na yarda ba za ki bari wani abu ya same ni ba."

Wannan hira ce da sukan yi da Hamza a mafi yawan lokuta. Hakan nan wata guntuwar ƙwalla ta zubo mata ta ji jikinta ya yi sanyi a kan leɓɓenta tace "Hamza Bello ka na ina?"

Horn ɗin din mota ya saka ya juyawa. Daniel ne sai wani a gefen sa da sauri ta tashi bata gane waye ba amma sai zuciyar ta tace da ita ƙila Hamza ne aka gani da sauri ta tashi har tana haɗawa da gudu ta isa ɗaya ɓarin ta buɗe da sauri ta ce "Hamza ka kada min zuciya ina ka ɓace....." Maganar ta tsaya cak ganin wanda bata yi zato ba, ta zata wasa Daddy yake yi mata.

Yana kallonta da murmushi a kan fuskarsa. Har wani lumshe idanu yake yi. Ya ziro da ƙafarsa ɗaya waje ya karyar da wuyansa yace "Raniata." 

A hankali tace "Sajid..."

"Shhhhh! Na san me za ki ce amma kiyi saving ɗin maganar ki. Ki shiga cikin motar ki zauna mu tafi station."

Ta kalli Daniel ta kalle shi tace "Station kuma? Ban gane ba?"

"Ki shiga za ki ji ko ma mene ne."

"Sajid ka gaya min me ya faru?"

"Abin da yake haɗa ni da ke kenan tambaya ba kya amsar umarni amma kina son a amshi ta ki."

Babu yadda ta iya haka ta buɗe baya ta shiga.
Ba wanda ya ce komai har suka yi nisa ganin sun mata shiru ne ya saka ranta ya sake ɓaci ta buɗe baki duk da yadda kanta ke ciwo tace "Bana son irin wannan abin ya za ayi ku zo ku ɗauke ni ba zaku min bayanin komai ba?"

Sajjid ne ya juya yace "Ba wani abu ba ne mun samu kira ne daga station ƙanwar Hamza ta kai ƙara dan'uwanta ya ɓata tana son a nemo mata shi yan'sanda suna son ganin ki."

Sai a lokacin ta samu relief a ranta, ta sauke ajiyar zuciya. Suna daidai bakin ƙofar station ɗin ne kira ya shiga wayarta. Ta duba bata san lambar ba kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka.

"Salamu alaikum!"
"Rania Sulaiman bana son ki ce komai, kawai so nake ki saurare ni. Magana ce zan gaya miki kuma tana da muhimmanci a wurin ki. Na san kina tare da mutane kuma kuna hanyar zuwa wurin yan'sanda ko na ce ma kina ƙofar har kun shiga."

Da mamaki ta soma juye-juye bata ajiye wayar ba. Ta lashi leɓɓenta. 

"Zan aiko miki da wani adireshi,ki zo kuma ke kaɗai za ki zo za ki samu amsar tambayar ki game da abokin aikin ki Hamza Bello."

Bai bata damar cewa komai ba ya kashe wayar. Ta bi waya da kallo. Ta kasa ma yarda da duk su biyun da Daniel ɗin da shi Sajjid ɗin.

"Mene ne?" Daniel ya faɗa.

"Ba komai." Ta faɗa hannunta na rawa,ta sa yatsa a baki wani irin ciwon kai ya sake saukar mata ta sa hannu biyu ta dafe kai ta koma da baya ta kwanta a jikin kujerar. 

Sajid ya juya,ya kalle ta yace "Ya dai?"

Ta girgiza masa kai kawai. 

Daniel ya kalle ta ya kalli Sajid yace "Koma mene ne a wayar da aka yi mata ne."

"Na ga alama."

"To, ya za ayi mu shiga ciki?"

"Mu shiga."

Da sauri ta masu alama da hannu ta yiwa Sajjid inkiya da hannu ya bata wayar sa. Da farko bai gane ba sai da Daniel ya masa sannan ya bata. Ta saka yatsanta a kan leɓɓenta. Alamar suyi shiru kar su ce komai.

Ta shiga inbox ta yi masu typing.

"Kar ku nuna komai a fuskar ku ina son haɗin kan ku, za mu je da yan'sanda amma ku za ku je."

Ta ba shi wayar ya duba ya sake neman ƙarin bayani.

"An samu bayanai a kan Hamza,sun ce na je amma ni kaɗai suna bibiyata kuma ba zan iya zuwa ni kaɗai ba sai dai dole ne na je ina son ku sa ido ku biyo ni ku shiga ciki ku haɗa da yan sanda saboda sheda."

Suka sake karantawa. Sajid ya gamsu ya ajiye wayar ya fita Daniel ma ya fita su suka shiga ciki ita kuma ta fito daga cikin motar ta nufi waje. 

Ta soma tafiya a hankali tana juyawa bata ga alamar su Sajjid ba sai ta rage sauri har ta kusa main road sannan ta ga motar su ta wuce suka kalli juna a faƙaice suka wuce ta da  kaɗan ta masu alama da babban yatsanta su uku ne kenan an basu alibai.
Ta sauke ajiyar zuciya.

Tun kan ta tsaya wata mota fara ta tsaya a gabanta. Tayi mata horn ta ɗan raɓa gefe ta juya ai kuwa motar ta sake mata horn sai ga waya ta duba wata lambar ce ta daban ta ɗaga.

"Ki shiga cikin motar."

Ta ajiye wayar ta shiga cikin motar.

Ko sakan bata yi da shiga ba ya ja motar da mask a fuskar sa bata ga fuskar sa ba, suka dinga tafiya suna ratsawa ta titi har suka soma shiga daji. Ta dinga juyawa dai bata ga motar su Sajid na bin su ba gabanta ya faɗi ta kalli wayar ta ta ajiye kan cinya ta kuma kallon waje bata ga kowa ba.

Gabanta ya tsananta faɗuwa ba wai tana tsoron rasa ranta ba ne kawai zuciyarta na gaya mata wani abu ya faru da Hamza.
Ba yau ta saba fita operation mai hatsari ba,amma yau tsoron da take ji ya wuce misali.

*

Sajjid da Daniel da suka wuce ta zuwa suka yi suka sauya wata motar daban a maimakon wadda suka fita sai suka ɗauko wata motar saboda su badda kama.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol