Free chapter · Read without an account

1

by Hijjart Abdoul · SALMA ELM

**********University of Cambridge. 

Fitowar sa daga hall kenan ya kammala yiwa dalibai lecture suna tajin daɗi haka shima yana jin daɗin yarda yake koyar da su suna ganewa, yana murmushi ya fito zai wuce office ɗin sa dake kusa da inda suka yi lecture, sai kuma a hankali ya ja ya tsaya daga inda yake kafin ya tsaya yana ƙarewa wata yarinya kallo. Kafin ya kai ga duban ga mutanen dake wurin. 

Kowa ka duba zaka ga zallar farin ciki ce a tare da shi. Domin kyakkyawan labarin da aka ba su bayan fitowar su daga hall ɗin. Ba iya su wanda suka fito ba, kowa na arean yana cikin walwala da farin ciki. Basa tare da wata damuwa Kowa yana harkar gabansa. Sanann kusan kowa dake wurin yana tare da abokinsa suna tattaunawa, masu tafiya kuma sun tafi. Yayin da wata yarinya mai kimanin shekaru ashirin da uku ke zaune da documents a hannunta,amma ita fuskar ta sam babu alamar farin ciki a tattare da ita. Fuskarta fayau babu ko ɗigon kwalli, baƙin ta a bushe ƙayau babu alamar ana shafa masa lipgloss. Amma hakan be hana ta yi kyau ba abinta, Sam inda farin ciki yake bata kalla ba. Kasancewar ana sanyi yasa ta ɗaura babbar jacket a saman rigarta ta atampha yayin da tafa mayafi a saman ɗankwalin dake kan ta. 

Ƙaramar yarinya ce ta taho da gudu tana bin abin wasan ta ci karo da ƙafarta dake a harɗe, ko kaɗan bata ɗaga kai ta kalli yarinyar ba, bare ace wai ko saboda ita ne yasa yarinyar ta faɗi. Yarinyar har ta gurje saboda faduwar da ta yi amma hakan be sa ta ɗago ta kalle ta ba ko ta san da wani abu a wurin. Har sai da Maman yarinyar ta zo ta ɗauke ta sannan ta yi shiru.

Kansa ne ya yi bala'in ɗaurewa sosai hakan yasa shi sake kallonta a tsanake yana sake karantar yanayin ta, tabbas ita ce, wacce ya sani ce, a sanda ya haɗu da ita ya haɗu da ita ne a lokacin tana shekara sha shida a duniya, sannan ya barta tana sha takwas, duka duka rayuwar shekara biyu suka yi. Amma a cikin wannan shekaru guda biyu babu abinda be sani ba na dangane da rayuwarta. Ya san komai, ya san komai dangane da ita, duk a yanzu ta sake girma amma hakan be sa ya kasa gane ta ba, domin ba yarda za'a yi ya ganta yace ba ita bace. Ba iya ita kawai ba kowa dake cikin gidan su zai iya gane su. Ta kasance wani babban gibi a cikin rayuwarsa....

Office ɗin sa ya koma yana haɗa coffee da kan sa kafin ya bude ƙofar sa ta baya da zai sa shi ganin school ɗin, daga inda yake tsaye a saman building ɗin sa hawa na uku yana iya hangenta da take zaune an a jarabar cafe ɗin an kawo mata coffee amma bata ɗauka ba tana duba abu a babban littafinta. Yana shan coffee din sa yana tuno duk wata rayuwarta ta baya.....

Sunanta Ummusalma, ana kiran ta da Ummu, yayinda wasu ke ce mata Salma, hanyar inda ji yake bata haɗa ba, sai inda tsokana da faɗa yake. Mahaifinta ya kasance mutum ne da baya san hayaniya da husuma, amma dake tana da Kaka wanda take kira da Daada, sannan akwai Kakarta da take ce mata Dadda. Wannan mutane biyun suka ɗaure mata gindin yin duk abinda take so. A gidan su take, haka sune suka yaye ta. Rayuwarta rayuwa ce mai cike da farin ciki, duk da ƙin ji irin nata, tana matuƙar so ta ga wani farin ciki. Ko da ace ta yi faɗa da mutum bata iya gaba da shi, labarin su ya fara ne a sanda ya zo unguwar, ya dawo gidansu da zama sakamakon hatsarin da kakansa ya yi shi da matar sa suka rasu......

***********"An kawo wani Malami mai kyau amma baya dariya". 

Cewar wata yarinya tana zama a kusa da Salma. Yayin da Salma dake zane a littafin ta ce. 

"Kamar ya baya dariya? Maryam Shi azara'ilu ne da za'a ce baya dariya? 

Taɓe baki Maryam ta yi ta ce, "Wallahi be dariya, sai kin gan shi ma, abin tsoro". 

"Tunda Malamin be zo ba zo ki rakani na gan shi". 

Da toh ta tashi suna ficewa daga aji zuwa inda Malamin na su yake. Yana bayan staff ɗin Malamai dake makarantar ma ta islamiyya ce kuma ba wani babba ba ce. Wayanci anan Malamai suke zama saboda inuwar wurin. Leƙa shi suka yi babu kowa a wurin. Yana zaune duk yana karatun Qur'ani, fuskarsa cike da gargasa haka ma akwai suma akan sa, sanye da kayan sa ƙanana fuskar nan a ɗaure tamau. 

"Kin gan shi ko? 

Maryam ta faɗa suna laɓewa. 

"Kaii to shi haka fuskar sa take a ɗaure? Sai ka ce azara'ilu? 

Sai ta kuma ta sake leƙawa tana dariya. Kafin ta sake dawowa taga ba Maryam. Hakan yasa ta sake leƙawa domin ta ƙare masa kallo. Tana leƙawa suka haɗa ido da ita, da sauri ta koma da baya tana ƙifta ido kafin kuma ta galagala da gudu ta shige ajin su tana sauke ajiyar zuciya. Zata yi magana kuma Headmaster ya shigo yana cewa. 

"Malaminku na Quri'ani baya nan, dan haka wani Malamin zai zo ya yi maku ƙari, dan Allah banda rashin ji kun ji? Ku nuna masa ku yara ne masu basira da tarbiyya uhm?!

"To Headmaster". 

Cewar Salma tana sakin kyakkyawan Murmushi. Sai ga shi nan ya shigo fuskar nan a ɗaure sosai, haɗa ido suka yi da Maryam suna ƙwalalo ido. Sai kuma Salma ta guntse bakinta da hannunta alamar dariya da kuma mamakin shine zai yi musu karatu?

Ba wanda ya kalla a cikin su hakan yasa su shiga hankalin su yana fara biya musu karatu ba tare da ya tambaye su ba. Yana karatu yayinda Salma ta yi tagumi ta sa Quri'ani a gaba kawai tana ƙare masa kallo yana da kyau amma gashin da ya bari a fuskar sa sun hana a gane kyan nasa. A cewar ta sun yi yawa da yawa. Sannan ga sumar sa nan be askewa. Bakinsa kawai take kallo yarda yake karatun cike da ƙwarewa dakyau. Haka nan ya ji ana kallon sa hakan yasa shi ɗagowa suka haɗa ido. Da sauri ta maida kan ta ga Qur'aninta, yana maida idan sa kan nasa Quri'ani ta sake kallonsa. A haka ya yi musu karatun tana satar kallon sa. Ya yi ya fice.

Da sallama ta shiga gida tana ajje jakarta akan tabarmar da ke waje. Gidan ɗan ƙarami amma ne mai ɗauke da ɗaki biyu sai kuma ɗakin Yayanta dake zaure. Dake yamma ce lis sai aka shimfida tabarmar a tsakar gidan wanda al'adar gidan ce haka, muddin ba sanyi ba ake ba, to ba zaka same su ba a cikin parlour. Suna tsakar gidansu dake shimfida da sumunti, ko ina ƙal kal, a share babu alamar ko da datti ne alamar akwai tsafta sosai a cikin gidan.

"Dadda har Daada ya fita ne? 

Ta faɗa tana zare hijabinta. 

"Yana bayi yanzu zai fita". 

"To ina yini Dadda? Sannu da gida". 

"Yauwa yarinyar kirki, ya makarantar?!

Darwaje baki ta yi tana matsowa kusa da Dadda tace. 

"Yau aka kawo mana wani Malami. Dadda baya dariya, shi ko faɗar sunansa be yi ba. Aikuwa gobe muka je da safe sai na tambaye shi sunansa na ji". 

"To ki yi a hankali, ba ruwanki da shi. Kin ga sabon Malaminne baki san halinsa ba. Ni kuwa aka taɓa ki sai inda karfina ya ƙare". 

Sake darwaje baki ta yi. Daada ya fita daga bayi yana alwala tana bashi labari. Tsaf ya kammala alawar ta je ta ɗauko masa babbar rigarsa da rawaninsa da yake naɗawa akan sa yana sa mata albarka. 

"To Yar Daada sai na dawo". 

"Ka taho min tsire ka ji? 

"Toh in sha Allah". 

"Ka dawo lafiya". 

Kallon Dadda ta yi ta ce. 

"Kin san me Dadda? Yau Auwalu yace zai zo da daddare. Idan ya zo rashin mutunci zan kar ta masa....

"Amma idan bana gidan nan ko? 

Cewar Yayanta yana fitowa daga parlour zai je masallaci shima. Ɓata baki ta yi cike da sakalci. Aikuwa yasa hannu ya buge bakin. 

"Wallahi sai na saɓar maki kina yiwa mutane rashin mutunci ko? 

Dadda ta ce, "To beyi mata ba, ko ana so dole ne? Wanda suka yi mata ai tana kula su". 

"Wallahi Ibrahim ka fita daga ido na, na rufe, kada ka yarda haɗa ƙafar wando ɗaya da kai"..

Buta ya ɗauka ya ya shiga bayi sai da ya fito ya ce. 

"Indai ƙafar wando ce Dadda ai mun jima da sawa ni da ke. Kawai ku bar yarinya ƙarama tana kula samari. Da wanda suka kai da wanda ba su kai ba, kowa ya zo yace yana son ta. Daga kammala secondary school? Duka nawa take? Da wasu shegun samarinta ƙwailaye kamar ita". 

Sosai yake faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ba wanda ya ce masa komai har sai da ya kammala tas ya wuce ya dauko ruwa a fridge ɗin su dake parlour Ya fito Ya ƙara da cewa. 

"Ƙwailar banza ƙwailar wofi". 

Dadda ta ce,"To so ka ke yarinyar ta zauna a gida taƙi yin aure? Ko kuwa so ka ke sai ta ga ƙarshen biro da takarda? 

Salma tace, "Dadda so yake ya ga na zauna a gida ba aure. Ni kuwa auren nan so nake na yi shi. Da zaka ce min Ƙwaila kuma ai na jima da balaga tunda tun ina ss1 na fara al'ada ko yanzu aka min aure zaunawa zan yi har na haifi yaro....

Kan ta yi hakan yasa ta tashi da gudu tana shige parlour tana kullewa.

"Da kin tsaya da na ƙarya ki...

Dadda ta ce, "Ibrahimu wallahi ka fita a idona na rufe, ka kiyayeni idan ba so ka ke na saɓar maka ba, idan kana taɓa wannan yarinyar tamkar ka ci mutuncina ne, ko uban da ya haifeta be isa na taɓa ta balle kuma kai". 

Be ce komai ya fita yana ɓacin rai, indai zance ne na Ummu bata taɓa ganinsa, shi wannan son be san wanda iri ne ba gaba ɗaya yarinya bata jin magana ta addabi kowa a unguwa........

Turo baki ta yi cike da sakalci tana fitowa daga parlourn bayan ta tabbatar ya fita ɗin. Wurin Dadda ta dawo ta zauna ta zabga tagumi tana tuno fuskar sabon Malamin su, kawai ta saki murmushi. 

"Allah mai iko shi haka ake, halittar mutane. Gashi da kyau amma fuskarsa a cunkushe". 

Dadda da ta idar da sallah ta ce. 

"Tashi ki ɗauko ki yi karatunki, kinga kin kusa kammalawa Quri'aninki. Ki bawa ƴan uwanki kunya ke har yanzu baki gane ba". 

Ɗan murmushi ta yi tana susa kai. Dadda cike da hikima gami da dabara ta ce. 

"Duk sanda bakya sallah ina mai yawan faɗa maki, indai lokacin sallah ya yi musamman na magriba ki riƙe azhkar, kin ga Azhkar yana matuƙar tasiri, ba abinda zai samu mutum, kinji ko? 

Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa. 

"Shi yasa ban so ace kina wannan baccin asubar, idan kina yi zaki ga ina tashinki kina karatu sannan ki yi Azhkar kin ji ko? 

Sake jinjina kai ta yi..

Dadda ta sake cewa. 

"Kinga kowa gani yake, bana koya maki komai, basu san ko su yayun na ki da suke zaune a gidan miji ba wanda ya isa ya koya maki tsafta da girki da kula da miji. Barsu su cigaba da maki kallon shashaha". 

Darwaje baki ta yi sosai cike da gamsuwa da maganar Dadda tana tashi ta wuce ta ɗauko jakarta ta fara hardarta. Yayin da Daada ya shigo da tsirenta, sai da ta kammala hardar sannan suka yi zamna cin abinci su dukan su ukun kafin Ibrahim ya shigo shima aka zuba masa daban, Daada yana yiwa yar sa nasiha cike da hikima dan sam basa yiwa mata faɗa.....





Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol