Free chapter · Read without an account

Nene da Ayaz suna zaune a dining duk sunyi jim tamkar gidan mutuwa sai kallon ju

by HIS HALAL · RAMUWAR GAYYA

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
🩸🩸🩸🩸🩸
🩸🩸🩸🩸
🩸🩸🩸
🩸🩸
🩸
RAMUWAR GAYYA 

STORY&WRITING 
       BY 
💍HIS HALAL 💍
🆓
🅿️ 1&2

BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM.

Nene da Ayaz suna zaune a dining duk sunyi jim tamkar gidan mutuwa sai kallon juna suke daya dago ido sai idonsu ya shige cikin na juna ita da Ayaz har dai ya gaji ya sauke numfashi yana neman tashi daga kan kujerar da yake zaune 

Saidai sautin tafiya ya sanya dukkansu suka ɗaga kai a lokaci guda domin ganin wanda ke saukowa.

Azad ya fara saukowa daga kan staircase fuskar shi daure take tamau babu alamun wani rahama akan fuskarsa fari ne dogo bawai chan chan ba yana da kasunba a fuskarsa ba zai wuce 35 years ba

Sanye yake da bakin Court wadda ta ƙara fito da kyawun halittarsa. Hannunsa ɗaya yana cikin aljihun wandonsa, ɗayan kuma yana riƙe da wayarsa. 

Fuskarsa cike take da nutsuwa, sai dai yanayin fuskarsa ya nuna cewa ba ya cikin walwala.

A hankali yake taka staircase ɗin har ya ƙaraso ƙasa wurin dining Da isowarsa ya ɗan tsaya, ya dubi Nene da Ayaz waɗanda har yanzu idanunsu ke kansa.

Good morning, Yaa Azad,

 Ayaz faɗa cikin girmamawa yana ɗukar da kansa 

Amsawa yayi cikin kulawa yana gaishe da Nene dake zaune ya rike hannunta yayi kissing dinsa tare da jan kujera ya zauna. 

 Nene ta amsa tana masa murmushi dauke kansa yayi yana ma Ayaz kallo daya ya sake dauke idonsa daga garesa ya mayar a abincin da Mama sefiye ta zuba masa tana barin wurin tana fadan a tashi lafiya ta fice daga dining room din

Ayaz kuwa ya gyara zamansa yana kallon Nene ta daga masa gira akan yayi maganar, magana yayi mata ahankali duk yana kula dasu bayason magana yayin cin abinci shi yasa bai ce komai ba sai da ya kammala ya goge bakinsa kafin yasha ruwa ya mayar da hankalinsa akan su Ayaz da ya kula dakwai magana abakinsa.

Ayaz bai kalama cin abincin ba amma ganin ƴaƴan nasa ya mayar da hankalinsa kasan ya sanya ya ajiye spone din hannunsa yana dan shafa kinjinsa 

Daman yaa Azad magana ce akan tafiya ta abokaina suna ta kirana akan tafiyar bude idon da zamuje 

Budar bakin Azad ya furta ba zaka je ba ya fara kokarin mikewa zaune 

Gyada masa kai yayi yana fadan to Yaa Azad 

Kafin Ayaz ya mayar da hankalinsa wurin cikin abincinsa fuskarsa babu alamar fushi ko wani gardama 

Dakatawa Azad yayi yana juyowa ya kalli Nene alamar ina abincin Baffam yake tashi tayi tana ɗan dogara sandar hannunta ta fara kwalama mama safiye kira da ɗan saurinta ta kariso wurin Nene rike da tiren abincin BAFFAM 

Karba tayi tana gyada mata kai wucewa mama safiye tayi tana barinsu a gun matsowa yayi ya karbi tiren abincin BAFFAM ya nufi hanyar staircase din 

Haka ya nufi part dinsa zaune yake akan kekensa a barandar falonsa ya kurawa wuri daya ido ba tare da dauke idon nasa ba 

Shigowar Azad ya nufi wurin mahaifin nasa ya ajiye tiren abincin akan teburin dake gabansa ya matso kusa da shi yana dukawa kasa har zuwa lokacin idon mahaifin nasa bai bar kallon wurin da yake kallo ba zaune kawai yake a kan kekensa amma baya ko iya motsa hannunsa bare yayi magana 

Gaishe da shi Azad yayi mai ce komai ba ya duka kasa 

Towel da mama safiye ta shigo ta kawo masa ya karba tana juyawa ta fice tana mai addu'ar samun sauƙi amsawa yayi cikin zuciyarsa ba tare da ya furta komai ba ya makala  towel din a jikin rigar mahaifin nasa a hankali ya fara bashi abincin nasa mai dan ruwa ruwa dan shi kaɗai ke shiga cikinsa dan baya iya tauna abinci 

Karba yake a hankali yana motsa bakinsa baya ga bakinsa babu abinda yake motsi a jikinsa,wanda ke bin bakinsa yana sanya tissue yana goge masa baki a hankali 

Har ya kammala bashi ya dauki ruwa ya bashi a bakinsa wani na shiga bakin sa wani yana zuba a  jikin towel din dake makale a rigar sa

Ya kamala bashi ruwan ya goge masa bakinsa kafin ya bar wurin 

Saidai Ni abinda na lura da BAFFAM shine dukan jikinsa baya aiki sai bakinsa dake motsi kuma shima baya iya magana hanunsa kansa baya iya ko dagawa idonsa ya kasance a wuri guda baya ko iya motsa kwayar idonsa sai dai duk abinda zaka fada to tabbas zai jika amma ba zai iya mayar da komai ba.

RAMUWAR GAYYA 

Kenan BOOK 1 iS for FREEEE😹🤌🏻

KU KASANCE A CHANNEL NAMU DOMIN SAMUN POSTING A KAI AKAI

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol