Free chapter · Read without an account
Chapter 49
BIYU A ƊAYA
Book 2
Page 49
~***~
***
Turo ƙofar ɗakin Mommie Dr Waahab ya yi tare da yin sallama, ya shigo Angel ta bi bayansa, Suhaima dake zaune ta amsa, Mommie ta ɗan tashi ta zauna tana kallon matar Dr Waahab, ta kura mata idanu Angel ta sudda kai ƙasa cike da kunya ta ce
"Barka da dare"
"Amarya barka dai, taso ki zauna anan mana kya zauna a ƙasa"
Ta nuna mata bakin bed, Angel ta ce
"Ba komai nan ma ya yi"
"Mommie na kawo miki ita"
"Ai kuwa barakallah amarya sannu"
Bilqees ta kasa yin magana, mommie ta ce
"Suhaima ba ki ganin matar yayanku ne?"
"Ina wuni"
Ta faɗa ba tare da ta kalli Bilqees ba, ta amsa da
"Lafiya"
"To sai ki kawo mata ruwa ai"
Dr Waahab ya ce
"A'a Mommie bata da ƙishi"
"Ba kai na tambaya ba, da amarya nake"
Murmushi ya yi, ya ji daɗin yadda Mommie ta tarɓi matarsa ya ji sanyi cikin ransa, Suhaima ta fice, Mommie ta ce
"Ya sunan ki"
"Bilkisu"
"To Yarona ka ce me sunan Mamie ka auro, to madallah, wannan ba za ta wuce sa'a da Suhaima ba kaga ta samu ƴar'uwa"
"A'a Mommie Suhaima za ta fi ta a shekaru sai dai Teemah za su iya sa'anni"
"Duk ɗaya ai yanzu ba a duba shekaru"
Angel ta ɗago suka haɗa ido da Mommie ta yi sauri ta sudda kanta ƙasa, shiru Mommie take dubanta ta sauke numfashi ta ce
"Aiki fa ya same ki, kin ga yarona ba ya son cin abinci, kullum cikin aiki yake"
Murmushi Angel ta yi, Dr Waahab ya ce
"Mommie bar tona min asiri"
"Bari na faɗa mata halin ka"
Ya yi murmushi ya ce
"To ki yabe ni"
"Ba a gabanka"
Su ka yi dariya, sun jima suna hira Dr Waahab ya manta da damuwar da yake tare da da shi sannan suka tashi, suka yi wa Mommie sai da safe suka fito, ya bi wata hanyar da ba wacce su ka zo ba, ganin ya tsaya a bakin kofar wani ɗaki ya sa ta tsaya ba tare da ta ƙaraso ba, ya buɗe ƙofar da key sannan ya iso inda take ya riƙe hannunta yana tafe tana biye da shi a hankali zuwa ƙofar ɗakin ya tura ƙofar suka shigo ɗakinsa, ya rufe kofar ya juyo suna kallon juna, ya sakar mata da murmushi ya ɗan ɗaga kafaɗa ya sauke a nutse ya nuna mata cikin ɗakin da hannu ya furta
"Ɗakina ne nan"
Idanunta suka sauƙa kan makeken hoton Yallaɓai likita da yake sanye da kayan likita, ya yi kyau duk da hoton ya kwan biyu, tana ƙarewa ɗakin kallo tsaf da shi sai ƙamshi ke tashi, saukar hannayen sa ta ya kewaye mata ciki, ya rungumeta ta baya ta sudda kai ƙasa, ya sanya kansa a gefen wuyanta, a hankali ya sauke numfashi ya ce
"Ɗakin ya yi kyau?"
Ta ɗan gyaɗa masa kanta alamun eh, ya juyo da ita suna facing juna, ya riƙe hannunta yana kallon lallenta tare da murza yatsunta a hankali ya ce
"Ina me baki hakuri akan abin da Mamie ta yi miki?"
"Wacece Mamie?"
Ya sauke numfashi a hankali ya ce
"Mamata"
Ganin damuwa a kan fuskarsa yasa ta ɗan kawar da nata ta danne damuwarta ta ce
"Ni ma ai mamata ce"
Ya ji daɗin maganar ta har cikin ransa, farin ciki ya mamaye zuciyarsa tabbas ya yi dacen mata, ya shafa gefen fuskarta ya ce
"Ki duba ɗakin duk abin da bai yi miki ba sai a sauya"
"A'a komai ya yi"
"Ki dai duba"
"Ta ɗan ɗago suna kallon juna ta ce
"Da gaske"
"Anan za mu zauna amma in sha Allahu za a gyara miki wancan bangaren"
Ta sudda kanta ƙasa, ya zaunar da ita bakin bed, ya komai cloth set ya rage kayan jikinsa, sannan ya faɗa toilet tana zaune har ya fito, ta sudda kai, ya ƙaraso kusa da ita ɗaure da towel a kugu sai ɗan ƙaramin towel a hannunsa yana goge ruwan dake kwance cikin gashin kansa.
Ganin ta sudda kai ƙasa yasa ya zauna tare da cewa
"Yau ke za ki shafa min mai"
Ta kasa ɗagowa duk kunya ta lulluɓe ta, ya ɗago da haɓarta ya ce
"Ba ki son lada"
Zuciyarta na bugawa, ta runtse idanunta a lokacin da ta yi arɓa da jikinsa ba riga, ya janyota jikinsa, ya ɗago da haɓarta ta kasa haɗa idanu da shi, ya sauke numfashi a hankali ya ce
"Zan raba ki da wannan kunyar ai"
Yana shafa bayanta, jikinta na rawa ta ce
"Zan koma wajen ALAJA"
"Za ki yi nesa da mijinki?"
Ta ɗago tana kallon fuskarsa idanunta sun ciko da ƙwalla ta ce
"A'a amma...
"Sheeet"
Ya ce ya ɗaura yatsansa kan laɓɓanta yana girgiza mata kansa alamun kada ta yi magana, yana jin yadda zuciyarta ke bugawa, ya zame mata gyallenta ya ajiye tare da cire ɗankwalin kanta, ya kurawa gashin kanta idanu yana kallo, ya zame ribon ɗin, duk ta rikice ta kasa nutsuwa sai sudda kai take yi a hankali ya yi magana
"Ba ki yi kitso ba"
"Bana kitso"
"Don me sa?"
"Masu yin kitso sun ce ya yi laushi ba zai yu ayi kitso ba"
"Gaskiya kam ba zai yi ba, ya yi laushi da yawa, wanke wa za ayi dinga yi miki ana gyarawa"
"To"
Ta faɗa a hankali duk ya cika ta da ƙwarjinsa da kuma abin da yake yi mata, yana kallon yadda take ta kame jikinta, ya ɗan zaunar da ita yana nannaɗe bakin gashin kanta da yatsansa ɗaya ya ce
"Bacci kike ji?"
"Eh"
Ta faɗa, a hankali ya ce
"Shikenan"
Ya tashi ya iso gaban mirror ya shafe jikinsa da mayyuka da turaruka masu ƙamshi ya sanya jallabiya, ya dawo inda take zaune ta maida ɗankwalinta da mayafinta ta tashi tsaye. Ya ɗan yi murmushi ya ce
"Shikenan sai da safe"
Ta yi shiru don ba za ta iya gane side da suke ba, ya yi baya sosai ga shi ɗakuna sun yi yawa, ya riƙe hannunta ya ɗan janyota kusa da shi ya ce
"Da gaske tafiya za ki yi?"
"Maa tana jirana"
"To mu je"
Yana riƙe da hannunta ya kawota har ƙofar shiga bangaren baƙi sannan ya ɗan sumbace ta a goshi ya ce
"Sai da safe"
Ta ɗan shigo sannan ta ce
"Allah ya tashe mu"
Ta rufe ƙofar, ta tadda babu kowa a palour, ta shigo ɗaki ta tadda ALAJA tana shirin kwanciya ta zauna shiru ALAJA ta ce
"Na yi tunanin kwana za ki yi da mijinki"
Ta yi sauri ta sudda kai ƙasa ta ce
"A'a ya kai ni wajen Mamansa ne"
"Allah ya sa ba ta wulakanta ki ba?"
"A'a ba ta yi ba"
"To ya fi mata, mutane sai shegen kabilanci, don Allah ya wadata su ki godewa Allah mijinki bai gado halinsu ba"
Ita dai ba ta ce komai ba, ALAJA ta ce
"Sai ki tashi ki watsa ruwa ai"
"To"
Ta faɗa ta mik'e ta shige toilet ta watsa ruwa sannan ta yi shirin kwanciya ta kwanta.
Dr Waahab da ƙyar ya iso ɗakinsa ɗan zaman da su ka yi na mintina har ya ji tana kewarta, ba don kada a ce ya yi rashin kunya ba, da ba zai bari ta tafi ba. Yana wannan tunanin ne bacci ya yi awun gaba da shi...
*********************
A daddafe ta shirya za ta wajen aiki, duk jiki a sanyaye, bata runtsa ba har gari ya waye, sanye da riga da wando na suit ta sanya after dressing akai, ta shafe jikinta da turare ta juyo suka haɗa ido da Ammie ta sauke numfashi tare da cewa
"Na shirya zan tafi"
"A dawo lafiya"
Ta fice zuwa ɗakin su, Ammie ta girgiza kanta tausayi Ashfat ta bata, ta jiye mata ba daɗi da ta rasa miji kamar Dr Waahab.
Ashfat tana shigowa ta tadda su Hauwa suna shan kunun tsamiya ta zauna tare da cewa
"Ku bakwa gajiya da ci da sha ne?"
"Me ya fi ranmu matar Yaya"
Cewar Hauwa, Ashfat ta ce
"Raba ni da wannan sunan, ki je cen an kawo miki Aunty"
"Allah ya sawwaƙa wannan ƴar yarinyar ce Aunty na"
Hauwa ta ce tana haɗe fuska, Suhaima ta ce
"Mommie har da sanya ni na gaisheta, takaici duk ya kashe ni"
"Kika gaishe ta, tab"
Cewar Ashfat, Teemah ta ce
"Bata da laifi don bata san komai ba ai Ya Waahab shi ne me laifi"
"Kada ki ga laifinsa like masa ta yi"
Cewar Ashfat bata so a ce Dr Waahab ya yi laifi, sai kare shi ta ke yi har ta kusa makara ma, sannan ta fito ta wuce wajen aiki.
******
Suna dining suna cin lafiyayyen breakfast, hira suke yi hankali kwance babu abin da ya sha musu kai, a kwana biyu da su ka yi har sun wani canza musamman ma ALAJA da ta samu hutu, Laraba dake yagar gashashiyar kaza ta ce
"Oh ni Laraba har ban son barin nan"
"To ko ya zame miki dole ki bar nan ɗin"
Cewar ALAJA, Jummai ta ce
"Ni ina ga ma zama zan yi don naga waje"
Dariya ALAJA ta yi ta ce
"Ai ko ba ki ga waje ba don yadda naga ƴan gidan nan daidai suke dake"
"Ni fa in zan ci daɗi ba abin da ta shille ni, sai su yi ta yi kansu ake ji"
Laraba ta ce
"Gwanma dai mu tafi, Angel kuma sai ki iya zama da su"
Ita dai Angel jinsu kawai ta ke yi, tana shan kunun gyaɗa ta yi mata daɗi, ta barwa Allah komai ya kawar da duk wani abin da zai cutar da ita, ta gama sha, ta tashi ta dawo kan kujera, ta ɗan kishingida, tana jin suna hira har bacci ya ɗauke ta, jin ƙamahin turare har cikin kwanyarta ya sa ta buɗe idanunta suka sauƙa cikin nasa, suka kurawa juna ido, zata tashi ya maidata ta kwanta tare da yi mata alamar kada ta tashi ta hanyar girgiza mata kansa, ta lumshe fararen idanunta ta buɗe su ta ji ya ɗaura hannunsa bisa wuyarta yana taɓawa a hankali ya ce
"Zazzaɓin ne?"
"A'a"
"Ke kaɗai a palour maimakon ki shiga ciki ki kwanta"
"Bacci ne ya ɗauke ni ban sani ba"
"Kin yi breakfast?"
"Eh na yi"
"Good, zan fita sai na dawo ko?"
"Allah ya dawo da kai lafiya"
"Amin"
Ya sauke mata hot kiss a ƙuncinta"
Ya mik'e ya fice....
****************
Shirye-shiryen kai Bilqees ɗakinta ake yi, babu laifi Dr Waahab ya yi ƙoƙarin duk abin da zata buƙata ya sanya mata a ciki, bai fara fita office ba an ƙara masa hutu. Mamie ba ta sake shiga lamarin Dr Waahab da Bilqees ba, amma yakan shigo ya gaida ta kamar kullum ya koma ba laifi tana sakar masa da fuska amma bata tambayar matarsa, hakan kuma bai yi masa daɗi.
ALAJA ta sanka su Laraba suka sake gyara dakin Bilqees, ya sake yin kyau, sannan suka kawo mata kayanta, yawancin ƙananan kaya ne bata da manya basu fi huɗu ba, su ma saboda biki ALAJA ta din ka mata, sauran kayan ta barsu a Ghana.
Dr wahaab da kansa ya jera kayan Angel a wardrobe, ganin basu da yawa ya ce zai saya mata wasu.
***********
ALAJA ta shirya Angel tsaf, ta yi kyau sai ƙamshi take yi, suka zauna a palour suna shirin kawo ta ɗakinta, Aunty Nazeefa ta shigo, ta taɓe baki tana cewa
"Ah maa shaa Allah amaryar mu me kama da larabawa"
Alaja dake gyara sarƙar wuyar ANGEL ta ce
"Faɗi ki ƙara, don kun kusa samun kyakkyawan jikoki"
Aunty Nazeefa ta taɓe ba ki ta ce
"Don ma gidan kyau ku ka shigo"
ALAJA bata bi ta kanta ba, su ka yi wa Bilqees rakiya ɗakinta har dasu Aunty Nazeefa ganin an sauya wasu abubuwan ɗaki ya matuƙar yin kyau ya sa ta ce
"Iyeee yaro ya gyara komai"
Babu wanda ya kulata, a ƙasan carpet Bilqees ta zauna ALAJA suka zauna Teemah ta shigo musu da ruwa ta ajiye musu tana kallon Angel da ta sudda kanta ƙasa, ta fice, Aunty Nazeefa ta ce
"To a ina za ta dafa abinci?"
ALAJA da ta mik'e ƙafafunta daman kiris take jira Aunty Nazeefa ta taɓota ta ce
"Wa yasan muku, ko ko kun tanadi mata masu aiki n"
"Haram mu gidan nan bama ɗaukan ƴan aiki, zagewa za ta yi ta shiga kitchen ta yi girki"
"A wane kitchen ɗin?"
Cewar ALAJA, Aunty Nazeefa ta ce
"Main kitchen mana sai ta gwamutsu da sauran mutane ta yi aikinta"
"To Allah shi kyauta, amma dai ayi haka?"
Cewar ALAJA, Aunty Nazeefa ta ce
"Ai an gama ma"
Angel tana jin su Aunty Nazeefa, ta fahimci gidan ba a ɗaukan ƴan aiki, hakan yana nuni da ita za ta din ga girkawa Yallaɓai likita abinci. Sun jima suna ta ya ta fira sannan aka fara ficewa Alaja na ƙoƙarin tafiya Angel ta riƙe hannunta ta ce
"Maa ina za ki je?"
"A'a zama zan yi sai na kwana tare da ku"
Ta sudda kai ƙasa, hawaye suka ciko idanunta, ta ce
"Maa to ki ɗan zauna mana"
"Kin ga fita a idona in za ki zauna ki jira mijinki to ki zauna don ni bacci nake ji, kin ga tafiya ta"
Ta fice, jikin Angel ya yi sanyi ta dawo ta zauna kan carpet tayi tagumi, tana tuna irin rayuwar da za ta yi da Yallaɓai likita kamar Mamie bata son auren, ko me yasa?...
Da sallama Ango ya turo ƙofar ya shigo, ta amsa a hankali, ya ɗan tsaya tare da rufe ƙofar, bata ɗago ba kanta na ƙasa ya ajiye ledan hannunsa ya tako zuwa inda take zaune, ya ɗan ajiye gwaiwarsa a ƙasa ya sanya hannu ya ɗago da haɓarta yana kallon kwalliyarta, sai yaga ta yi kyau sosai fiya da kullum, ya kurawa siririyar sarƙan dake wuyarta ido yana kallo, ya yaye mata mayafinta a hankali ya ce
"Na barki ke kaɗai ko?"
Gani ta yi ya yi mata kwarjini, ta kasa yin magana ta rasa me yasa take jin haka game da Yallaɓai likita, babu shiri sai hawaye, ya sauke numfashi tare da cewa
"Subhanallah kuka kuma amarya ta"
Hannunta ya riƙe suka tashi tare, ya zaunar da ita bakin bed ya ce
"Yau ranar farin ciki ne ba na kuka ba"
Zata sudda kai ƙasa ya sake cewa
"Ba ki sona?"
Kai ta girgiza, ya ɗan kyaleta ya faɗa toilet ya ɗauro alwala ya fito ya ce
"Baby je ki yi alwala"
Jiki a sanyaye ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tadda ya yi musu shimfida za su gabatar da raka'a biyu wanda ma'aurata ke yi, ya miƙa mata hijabi ta karɓa ta sanya suka idar da sallah, ya juyo sosai yana kallon ta, ya ɗaura hannunsa bisa kanta yana jero addu'oin da ya sanya Bilqees farin ciki da alfahari na samun miji kamar Yallaɓai likita, a nutse yake addu'a har na neman tsari daga dukkanin sharri sannan kuma ya yi na samun farin ciki da kwanciyar hankali na har abada ya jima yana yi har ta fara hamma, ya cire mata hijabinta, yana kallon kwayar idanunta ya ce
"Yunwa nake ji"
Ta ɗan waro fararen idanunta waje, ta ce
"Ga shi ba abinci, me zan girka?"
Ya lakuci hancinta cike da ƙauna ya ce
"Kusan ƙarfe goma shi ne za ki hura wuta, na zo da abin taɓawa"
Ta ɗan yi murmushi tare da jingina kanta, ya mik'e ya ɗauko leda ya ajiye ta, kaza ce da youghout haɗe da makulashe, ya buɗe tare da ɗauko ya kai mata ba ki ta sudda kanta ƙasa ta ce
"Na ƙoshi"
"To shikenan ni ma ba zan ci ba sai na kwana da yunwa"
"A'a Yallaɓai likita"
"Eh mana in kuma ba ki so na kwana da yunwa sai ki ci"
Ya kai bakinta ta buɗe ya saka mata tana ci a haka ta ɗan ci, shi ya ci sosai, sannan ya bari don tun safe bai nutsu ya ci abinci ba. Ya dube tare da cewa
"Zan watsa ruwa"
Ta gyaɗa masa kanta alamun to, ya mik'e ya faɗa toilet ya jima yana wanka sannan ya fito ya shirya cikin riga da wando marasa nauyi na bacci, Angel ta haɗe jikin garu bacci ya fara ɗaukanta ta ji sauƙan sanyayyen hannun kan fuskarta ta dube shi sai ƙamshi yake yi, ta sauke numfashi ya ce
"Ta shi ki watsa ruwa"
"Ni na yi wanka"
Murmushi ya yi ya ce
"Na sani ki sake yi za ki ji daɗin jikin ki"
Ta yi shiru ya ce
"Ko na yi miki?"
"A'a"
Ta faɗa da sauri ta tashi ta tsaya, ya miƙa mata wata baƙar riga ya ce
"In kin watsa ruwa sai ki saka ta"
Da ƙyar ta karɓi rigar ta shige toilet yana ji ta sanya ki ta rufe ya yi murmushi ya kwanta kan bed ta jima a cikin toilet ɗin sannan ta buɗe ƙofar ta kasa ƙarasowa, da ƙyar ta iya fitowa saboda rigar dake jikinta, ta fito da shapes nata kunya take ji Yallaɓai likita ya ganta a haka, da ƙyar ta ɗan fito ta tsaya bakin kofa, yana ganinta ya shagala da kallon, tashi ya yi ya zauna, ya sauke numfashi tare da cewa
"Ƙaraso"
Ta kasa tashi, ya miƙe a hankali ya nufi in da take, yana kallon yadda rigar ta amshi farar fatarta, wayarsa ta yi ringing ya dawo da baya ya ɗauka ganin sunan Mamie ne ya ɗauka cike da tashin hankali ya ji tana yi masa magana
"Kana ina?"
"Ina ɗakina"
Ina neman ka"
"To"
Ya faɗa jiki a sanyaye, ya riƙe hannunta Angel ya zaunar da ita bakin bed ya ce
"Zan je kiran Mamie"
"To"
Ta faɗa, ya sanya jallabiya kan kayan baccinsa ya iso side nata, sai ya ji hankalinsa bai kwanta ba, yana ta tunanin Allah ya sa lafiya, da mamaki ya ƙaraso ɗakin ya yi sallama bata amsa ba, tana kaɗa ƙafarta ɗaya, ya zauna tare da cewa
"Mamie gani"
"Da gaske ne a gidan karuwai ka auro matarka"
Ya matukar razana da jin abin da Mamie ta ce, take ya haɗa gumi bai taɓa jin irin bugun zuciyar da ya ji a wannan lokacin ba, ya rasa ta yadda zai fara yi mata bayani, ta daka masa tsawar da duk jarumtar sa sai da jikinsa ya yi rawa, da ƙyar ya furta
"Mamie ba haka zancen yake ba ita da mahaifiyarta mutanen kirki ne"
"Eh ko a'a shi ne kawai amsar da nake so"...
___________________
Ayi hakuri da typing errors
Comment and share fisabilillah