Free chapter · Read without an account

18. The Engagement

by Zainab · TSAƘANINMU

TSAKANINMU

_Abuja, Nigeria,._

     _Three Weeks Later._

Khalil and Jawahir had 5 dates in her home before Khalil brought up the issue of sending his family to seek her hand in marriage. And Abba gave his consent and all of her brother's. 

Jawahir ta amince wa Khalil ta yarda dashi kuma ta yarda tayi zama na aure tare dashi. He always makes her fall in love with him everyday and she's happy about it. Ita ba zata damu ba idan aka ce yau ɗaurin auren su ko kuma idan aka zo nema a ɗaura aure. Shine take gani wanda ya zama 'man of her dreams' and she talks about him to Ashraf all day. And Ashraf gets a little annoyed whenever she mentions him saboda yanda take kiran sunan yayi mishi yawa akai. 

Ranar da za'a taho neman auren, ta kira Ashraf domin ta faɗa mishi 

"Hey, Ashraf"

"Yes, Jawahir. Ya kike ya gida?"

"Alhamdulillah, kufa?"

"Alhamdulillah, muna lafiya" ya amsa, kuma kafin tayi magana yace "Kinga kuwa na mance inaso na kira na faɗa miki ina son cake guda biyu, single layer da carrot cupcake. And please Jawahir, ki sa min oat flour nan da kike sakawa instead of refined white flour"

"Yaushe kake so?" 

"Gobe , kaman irin wannan time ɗin, karfe biyar"

"Okay, zan maka. Carrot cupcake box nawa za'a yi?" 

"Kiyi guda uku" yace "Yeah, 2 boxes is okay"

"Cake din fa me za'a rubuta?"

"Umm Ayman na Yaya Farida ce zata yi bday. She's clocking 6, so choose the best for her"

"Okayyy. Kuma kace asa oat flour, Ashraf? Kar taƙi ci fa?"

"Yaya Farida tafi son oat flour. Tace tafi so yaranta suna healthy eating tun suna yara"

Murmushi Jawahir tayi tace "That's nice. Zaka samu goben"

"Nawa ne kuɗin na turo"

"Ka bar shi, ya zama B'day gift nawa"

"Ni kuma ya zama me na bata kenan?" Ashraf yace

Dariya Jawahir tayi tace "Ka samu abinda zaka bata"

"Kina ji Jawahir? Na gane kina so ki bada kyautan B'day, amma kinga yayi yawa. Kuɗin zasu yi yawa ki faɗa price se na tura miki koda baki faɗa duka ba"

"Nace ka bar shi, daa bani da kuɗi zan ce zanyi ne? Ai kasani kaima"

"Kinga matsala na dake ko? Kina sana'ar ki, passion naki, amma idan nace ki min se kice kyauta. Idan kika cigaba min a kyauta ai ni ne zan karya miki jarin ki. Idan kuma kika cigaba da cewa kyauta, zan dena sayan kayan ki gabaɗaya"

"To naji masoyina Ashraf, me ƙaunar duk abinda nake ƙauna wanda kuma yake son cigaban Jawahir"

Dariya suka yi su biyu yace "Nawa ne?"

"Ka turo 20k"

"I'll send 50k"

"A'a Ashraf. Wane 50k kuma? Don't"

"I'm gonna send 50k Ma'am. Idan baki so ki zuba sauran a shara"

"I'm not happy about this, you know"

"Ki fashe to"

"Bani fashewa gobe za'a yi neman auren fa" tace mishi cikin kunya 

Wani irin abu Ashraf yaji ya haɗiye. "Gobe za'a yi neman auren? So soon, Jawahir?"

"Yes"

"Are you so sure about him?"

"100%, Ashraf. He's a nice man"

"Alright. I wish you the best. Yanzu kenan ba zan samu kayan gobe ba tunda ke amarya ne?"

"A'a, zan maka"

"A'a , ba ze yiwu ba gobe za'a yi neman auren ki kiyi aiki. Ki bar shi zan nema wata me pastries"

"No, don't mind about it Ashraf. Ba wani taro za'a yi ba. It's going to be lowkey Abba ba ze faɗa ba se an taho aure tukunna"

"Okay, since you insist"

"Yeah, talk to you later"

"Yeah, later"


 
               ***



Saboda nema ne za'a yi, ba wani taro akayi a gidan nasu ba kuma ba'a faɗa wa mutane dayawa ba Abba yana amfani da neman aure a ɓoye idan aka tashi aure a bayyana. 

A few people ne a gidan nasu harda Aunty A'isha ta taho da sisters-in-laws na Jawahir. 

Karfe goma sha biyu akayi neman harda sadakin su sun bada dubu ɗari. 

Jawahir bata fara aikin Ashraf ba se ƙarfe ɗaya. Ƴan uwanta na mata magana akan wa ake yiwa aiki yau da baze yi haƙuri ba har gobe. Murmushi kawai Jawahir tayi ba tace musu komai ba. 

Ƙarfe biyar kaman yanda tace mishi ze samu kayan, ya taho ya amshe kayan shi yana mata godiya sosai tare da yi mata congratulations akan engagement nata. 

Tsayawa tayi dashi tana magana har lokacin da Ahmad ya shigo cikin gida. 

"Ba kin bada kayan ba? Me kike yi a waje kuma?" Ahmad ya faɗa yana kallon ta yana tafiya ze shiga cikin gidan. Ba tace mishi komai ba kuma bata wuce ba. 

"Yaya Ahmad ko?" inji Ashraf yana kallon Ahmad

"Eh, shine, wannan me faɗan"

Dariya Ashraf yayi yace "Yanzu idan kika yi aure shikenan kuma"

"Khalil fa ya sanka. Ba har gaisawa kun taɓa yi ba?"

"You're still a young girl, Jawahir"

"Da gaske zamu cigaba da friendship namu har bayan aure na, Ashraf" tace mishi ita da gaskiyar ta "Ni ina zan iya rayuwa babu kai" ta faɗa da wasa

Dariya Ashraf ya ƙara yi yace "Har sadakin ki fa an bada, kenan an kusa auren"

"Yaya Hamdan ne baya so ana irin wannan dating a jima anayi, nima kuma ban damu ba"

"Saboda kina ƙaunar shi har cikin ranki ne shiyasa"

"Yes, i love him. He's my prince in shining armour"

Dariya suka yi su biyu yace "Indeed, prince in shining armour"

"Exactly"

"Ina miki fatan alheri a kodayaushe"

"Nagode sosai, Ashraf and we are supposed to get married on the same day"

"You snitched on me and started dating without telling me" Ashraf yace da gaske, da Jawahir ta tsaya zata gane irin abinda yake faɗa amma da yake sun saba wasar su, dariya tayi tace "I didn't, Ashraf. It happened.....I didn't even know how it happened"

"You liar!"

Wani dariya ta ƙara yi "Da gaske nake maka fa"

"Na yarda dake" ya faɗa cikin wasa "Zan wuce kar nasa suyi latti"

"I wish Umm Ayman a very happy Bday"

"Thank you, Jawahir. Thank you"


Se bayan Ashraf ya wuce tukuna itama Jawahir ta wuce. 

A chan cikin gida, ɗakin ta ta wuce. Tana shiga se ga kiran Khalil. Murmushi me faɗi ya zauna akan fuskar ta ta ɗauka. 

"My wife" taji yace. Murmushi tayi me ƙara 

"I got you, yeah?"

"You got me, Khalil. We got each other"

"I'm the most happiest man alive today"

"Really?"

"Really, Jawahir"

Murmushi suka yi a tare yace "You have no regret choosing me. I'll be the best husband to you and the best father to our kids"

Kunya Jawahir taji tace "Zamu yi magana anjima" 

Kashe waya tayi bata jira abinda ze faɗa ba. 

Ahmad taga ya leƙo ta ɗakin ta saboda a buɗe yake bata rufe ba. 

"Yaya Ahmad?"

"Eh, ni ne. Ɗazu da wa kike magana?"

"Yaya yaushe?"

"Da ina tahowa na gan ki da wani kuna magana bayan kuma kin gama sallamar shi"

"Yaya saƙon shi na bashi"

"Shine nake faɗa miki bayan kin sallame shi, wane irin magana kika tsaya kina yi dashi?"

"Ina mishi bayanin yanda cakes ɗin suke" tayi ƙarya 

"Ba kina rubuta ingredients naki a card ba? Shi takkwali ne da ba ze iya karantawa ba? Kar na ƙara ganin wani ya taho amsar kaya kuma ki tsaya kina surutu dashi. Akan dalilin me? Have class, girl"

Shiru tayi har ya gama fadan shi ya wuce. 

Yana tafiyar shi ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta shiga bathroom.


~~~~


ohhhh these people! you're not even leaving a like or a comment...oh ni marubuciyar nan 🤣😭 ku yiwa Allah ku bar min koda comment ne idan akwai masu krntawa. i take God beg una

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol