Free chapter · Read without an account
EP____________1️⃣2️⃣
🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️ QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
EP____________1️⃣2️⃣
"Faryal, Fayyad was an armed robber".
"Whattt?". Faryal ta faɗa cikin tsananin tashin hankali, tana miƙewa. "Fayyad ɗin ne armed robber?". Ta sake maimaitawa.
"Yes Faryal, amma Alhamdulillah, Allah ya toni asirinsa kafin ma aje ga ɗaura auren. Sun yi fashi ne a gidan wani attajiri last week, saidai kuma as the saying goes 99 days for the theif one day for the owner. Tunda gashi yau dai an yi nasarar cafke su, ashe dama sun saba y.....". Kafin ya ƙarasa kawai ya ga Faryal ɗin ta yanke jiki ta faɗi.
Ammi da Aunty Mimi, waɗanda Maama ta kira tace su dawo daga gidan Faryal ɗin da suka je karasa shirya mata wasu abubuwan ne suka shigo cikin Parlourn. Da azama Ammi ta riƙo Faryal kafin ta karasa kai wa ƙasa tana faɗin, "Arham, maza ɗauko min ruwa, yi sauri! Faryal! Faryal!". Ta ƙarashe tana tapping kumatun Faryal ɗin, a daidai lokacin Arham ya dawo da ruwan, Hadiyyah na biye da shi.
A hankali ta fara buɗe idanunta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya bayan Ammi ta shafa mata ruwan a fuska. Waro idanunta tayi gabaɗaya, sai kuma ta miƙe zaune da sauri tana riƙo hannun Ammi. Ta ce, "Ammi, Ammi, dan Allah ki ƙaryata abin da Arham ya faɗa min. Ammi, ki ce min ƙarya ne abin da ya faɗa, dan Allah Ammi!". Ta ƙarashe tana girgiza Ammi, wadda ita ma Arham ɗin take kallo cikin rashin fahimtar abin da ke faruwa.
Aunty Mimi ce ta ce, "Arham, me ka faɗa mata?".
Sunkuyar da kansa ƙasa yayi, yayin da Aunty Mimi ta daka masa tsawa, "Kai, ba da kai nake magana ba? Me ka faɗa mata nace?".
"Mimi, whl ita ta matsa min sai na faɗa mata abin da ke faruwa".
Aunty Mimi ta kalli Ammi kafin ta mayar da dubanta ga Arham ta ce, "Mu ma Aunty Sharmila ce ta kira mu ta ce mu dawo gida. Me ke faruwa ne a gidan? Mun dawo mun tarar taro ya watse kowa na ta tafiya".
Ba bata lokaci Arham ya kwashe duk abinda ya faru ya faɗa musu. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un²". Shi ne abin da Ammi da Aunty Mimi suka shiga maimaitawa a tare.
Maama ce ta dawo falon, har lokacin fuskarta ɗauke da bacin rai. Ta kalle su ta ce, "Me ke faruwa kuma a nan?".
Faryal ce ta miƙe da sauri ta nufi mahaifiyarta ta. Ta riƙo hannunta tana faɗin, "Maama, na san ko da kowa zai yi min ƙarya, ke za ki faɗa min gsky. Dan Allah ki faɗa min, da gsk an kama Fayyad? Da gsk Fayyad armed robber ne?".
Cike da tausayin ƴar ta ta, ta ce, "Haka ne Faryal, duk abin da kika ji gaskiya ne. Amma mun godewa Allah da ba a ɗaura auren ba lokacin da aka kama shi. Da a ce an ɗaura auren, da mun shiga uku. Faryal ki gode wa Allah da ya tseratar da ke daga faɗawa irin wannan mugun hannun".
Zamewa Faryal tayi ta zube a wuri, ta fashe da kuka me tsanani. "Is this how destiny is always attacking her? Today, the happiest day turned into the darkest day of her life. Shin ita ba ta da sa'a ne a rayuwa? Shin ba ta cancanci samun farin ciki me ɗorewa ba ne kamar kowa?".
Daadee, wadda ta shigo falon, ta ƙarasa ta riƙo hannun Faryal ɗin ta miƙar da ita, sannan ta jata zuwa kan kujera two seater, ta zaunar da ita sannan ita ma ta zauna a gefenta. Saidai kafin ta samu damar magana, Appa da Uncle Junaid sun shigo suna sake tattauna abin da ya faru a masallacin.
Tsayawa sukayi ganin yadda kowa yayi jugum jugum a falon. Sai kuma suka karasa suka zauna su ma. Appa ya kalli Faryal cikin tausayawa ya ce, "Zo nan Faryal".
Ba musu ta miƙe ta isa gare shi ta zauna a gefen ƙafarsa.
"Faryal, ke ba ƙaramar yarinya ba ce, kuma ke ba jahila ba ce. Ya kamata mu ɗauki wannan a matsayin taimakon Allah. Ki yi tunani, da a ce sai bayan mun aura miki shi, har kun fara samun zurriya sannan aka gano ainihin halinsa da wani irin tashin hankali zamu shiga daga mu har ke? To amma yanzu Alhamdulillah, sai mu godewa Allah, muce Allah yasa hakan shi yafi alheri kinji".
Daadee ta ja numfashi kafin ta ce, "Hafiz, a gsky idan da akwai me laifi a wannan lamari, to kai ne. Hakkin ka ne fa ka binciki mutumin da za ka aura wa yarka, ka binciki halinsa, addininsa, asalinsa da kuma cancantarsa a bangaren aure. Amma ka faɗa min, tsakanin ka da Allah kayi bincike akan mutumin nan yadda ya kamata?".
Appa ya sunkuyar da kansa ƙasa, dan bai san abin da zai ce ba. Saboda ana yin engagement ɗin ya yi tafiya, lokacin da ya dawo kuma he was busy receiving what he ordered. Shiyasa bai samu lokacin yin binciken ba, dan ya ma manta akwai wani abu wai shi bincike kafin aure.
"Ka gani ko Hafiz, komai yana da iyaka. Yaranku ba ilimi kawai suke buƙata ba. Dukkan ku kai da Sharmila akwai buƙatar ku saka idanu akan yaranku, ku haɗa hannu wurin basu tarbiyya. Saboda bayan ilimin zamani da na addini, akwai wani ilimi na rayuwa da ba a koyarwa a makaranta. Kamar yadda ake cewa, charity begins at hime, amma dukkan ku biyun ba ku da lokacin yaranku.
Ibn Umar (Radiyallahu Anhu) reports that he heard the messenger of Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) say: Dukkaninku makiyaya ne, kuma dukkaninku za a tambaye ku game da abin da aka ba ku kiwo. Hafiz, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Duk wanda yake da ya ya mata guda uku, kuma ya yi haƙuri da su, ya ciyar da su, ya shayar da su, ya kuma tufatar da su, za su zama kariya a gare shi daga wutar Jahannama.
To amma Hafiz me ya sa za ka ɗauki wannan babbar damar da Allah ya ba ka a matsayin abin wasa? Idan dan dukiya ne, ka tara, you have enough, me za ka yi da ita? Duk fa arzikin da mutum ya tara, a wannan duniyar zai bar shi. Babu wanda zai tafi da dukiyarsa, kyawunsa, girman kansa, iliminsa, matsayinsa ko wani abu makamancin haka zuwa lahira. Ya kamata ka ɗauki abin da ya faru da Faryal a matsayin darasi, ka gyara kuskuranka".
Daadee ta ƙarashe tana miƙewa ta bar falon. Maama da Appa sukayi shiru, jikinsu a matuqar sanyaye. Can Appa ya ɗago ya kalli Maama, realizing the mistake he almost made.
"Faryal, Hadiyyah, ina kuke n...". Maganarta ta maqale Saboda idanunta da ya sauka akan mutanen da ke falon, da kuma yanayin dake kan fuskokin su.
Maama ce ta ɗago ta dubeta da faɗin, "Manira, ki koma ciki ki sallami ƙawayenku, ki faɗa musu an ɗage bikin zuwa wani lokaci".
"Maama, me ke faruwa ne?".
"Zo ki rufe mu da duka sai mu faɗa miki". Ammi ta faɗa tana yi wa Manira kallon gargaɗi.
Juyawa tayi ta koma ciki, tana waiwayen su har ta bar falon.
Tashi Appa yayi ya shige ciki, Maama ma ta bi bayan shi.
Uncle Junaid ne ya ci gaba da yi wa Faryal nasiha, wadda har lokacin sheshekar kuka take kasa ƙasa.
Yana gamawa, shi ma ya musu sallama ya tafi. Faryal ta miƙe ta nufi ɗakin mahaifiyarta, dan ta san nan ne kaɗai wurin da za ta iya samun damar kaɗaicewa yadda take buqata.
Ko da ta shiga ɗakin, akan rug ta zube tana yi wa kanta tambayoyi. "Shin wai su mugayen mutane ba su da wata alamar da ake iya gane su ne? Domin da ba don abin da ya faru ba, da za ta iya rantsewa da Alƙur'ani cewa babu wani mutumin kirki sama da Fayyad, amma sai gashi ya bata mamaki.....".
Kafin Faryal ta gama saƙa da warwarar da takeyi, gabaɗaya tsanar maza ta dabaibaye Zuciyarta. Zuciyarta ta yi nauyi da baƙin ciki yayin da take tunanin yadda aka yi ta bari Fayyad ya yaudare ta da kyawawan halayensa na zahiri.
"Wai kowa fuska biyu ne dashi? Kenan bai kamata a riƙa yankewa mutum hukunci akan halayyar sa ta zahiri ba? Shin su duk mazan haka suke ne?". Girgiza kai tayi, her thoughts consumed by bitterness. "No more excuses for men, they are all betrayer's, cheaters, and evils like the brothers of shaytan". Ta faɗa cikin ɗacin rai.
Tashi tayi ta wuce bathroom, ta wanko fuskarta sannan ta fito, ta haye gado ta kwanta, ta lumshe idanunta, duk da cewa ba barcin take ji ba.
*** *** ***
A haka kwanaki biyu suka shafe, yau ta kama litinin, cibiyar aiki. Faryal ce tsaye a gaban mirror tana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunta. Fuskarta ba alamun walwala, ta yi wani fayau kamar wadda ta kwanta ciwo, ɗaura agogon take kamar marar lakka a jiki dan yau hatta da yanayin ta ya nuna rashin kuzari da walwala a tattare da ita.
Maama ce ta shigo ɗakin, amma sai ta dakata ganin Faryal ɗin tsaye a gaban mirror cikin shiri.
"Faryal, kar ki ce min fita za ki yi aiki?".
Faryal ta yi murmushin yaqe kafin ta ce, "Eh Maama, gani nayi gwara na fitan maybe aikin ya ɗauke min hankali ko zan dan samu nutsuwar zuciya".
Cikin damuwa Maama ta ce, "Amma jiya da dare da ciwon kai kika kwanta, ina ganin da kin huta yau ɗin gobe ba sai kije ba, komai fa ɗan haƙuri ne Faryal".
"Haka ne Maama, amma karki damu yanzun na ji sauƙi ne. Shi yasa ma na shirya ɗin, zan iya zuwa". Faryal ɗin ta amsa tana kallon mahaifiyarta ta.
"To Shikenan, amma kar ki je ko'ina daga Company. Ki kuma kula da kanki". Ta faɗa tana juyawa ta bar dakin.
Faryal ta bi bayanta da kallo, cike da mamakinta, dan sai taji abun banbarakwai. But her mind was preoccupied, sai kawai ta ɗauki jakarta ta nufi waje.
Tea kawai ta sha a matsayin breakfast, ta ce wa Maama sai taje Company za ta ci wani abu. Haka dai ta samu ta zille ta bar gidan.
Sai da ta zauna a cikin motarta sannan ta ciro wayarta daga cikin jaka ta kira wata number. Ko da aka ɗaga, shiru ta yi tana sauraron wanda ke magana ta cikin wayar kafin can ta furta, "Okay". sannan ta kashe wayar.
Within a minute, wayarta ta yi ƙara, alamar shigowar saqo. Ta ɗan kalli screen ɗin wayar na wasu daƙiƙu kafin ta mayar da ita cikin jaka. Ta kunna motar, ta sa reverse, sannan ta danna hon, mai gadin ya buɗe mata ta fice.
A cikin harabar police station ta faka motarta ta, ta fito sannan ta nufi ciki.
A bakin kanta ta tarar da wasu yan sanda su uku. Bayan sun gaisa, ta ce, "Da Allah nan ne station ɗin da aka tsare Fayyad Adam?".
Ɗaya daga cikin su ne ya amsa da, "Eh nan ne, amma yanzu basa nan, an yi gaba dasu".
"Zuwa ina please?".
"Gsky ba mu sani ba".
Faryal ta ciji yatsanta kafin ta ce, "Zan iya ganin DPO ɗinku?".
"No, he's busy right now". Ɗayan jami'in ya amsa mata.
Ɗan shiru tayi, can kuma ta saka hannu cikin jakarta ta ciro wasu kuɗi tana faɗin, "To, babu matsala. Ga wannan ba yawa, ko recharge card a saka. Nagode, sai anjima".
Kallon juna sukayi, kafin ɗayansu ya dakatar da Faryal, wadda ta yi waje. "Dawo Hajiya, let me go and ask permission from him first".
Faryal ta yi murmushi kafin ta dawo da baya. Bayan mintuna biyu, sai gashi ya dawo ya ce, "Muje in raka ki".
Da "To". ta amsa sannan ta bi shi zuwa office ɗin DPO. Gaishe da DPO ɗin tayi bayan sun shiga office ɗin, ya amsa yana nuna mata kujera ya ce, "You can have a seat".
Zama tayi shi kuma ɗan sandan da ya rakota ya fice. Kallon sa tayi ta ce, "Na zo ganin Fayyad Adam".
DPO ya mata kallon tsanaki kafin ya ce, "Are you from the investigation office or somewhere else?".
"No not at all sir, I'm his sister".
"Kina sane da abin da ake zargin ya aikata kuwa?".
"We just recently found out".
"Alryt, mun tattara bayanansu mun miƙa su kotu a safiyar yau".
"Dan Allah ko zan iya sanin wace kotu ce?".
"High Court". Ya bata amsa a takaice.
"But sir could you provide more details about it?".
"A halin yanzu case ɗin na gaban kotu ne. Za ki ji komai ne in kinje can".
"Okay to na gode sosai". Ta fada tana zaro kuɗi shi ma ta ajiye masa kan table ɗin tana faɗin. "Ga wannan sir, a sha ruwa".
Kallon kuɗin yayi, sai kuma ya ɗan yi murmushin gefen baki, tare da dakatar da ita sannan ya ce, "Zan yi miki uzuri saboda ke yarinya ce, amma ki kiyaye bayar da cin hanci a ko'ina. Ba dukkanmu ne muka taru muka zama ɗaya ba, akwai mutanen kirki akwai kuma akasin haka. Kin aikata babban laifi na ƙoƙarin ba ni cin hanci da kikayi, amma na yafe miki. Just be careful next time, ba'a haka kinji ko".
Faryal ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗauki kuɗin ta mayar da su cikin jakarta kafin ta ce, "Na gode sosai ranka ya daɗe. Allah ya ƙara girma". Jinjina mata kai yayi, ita kuma ta fice daga office ɗin. Kai tsaye ta nufi motarta ba tare da ta yiwa na bakin kantar sallama ba.
Kotun ta nufa direct, ko da ta isa Fayyad da abokan aikinsa suna can tsare a cikin cell kafin a kira shari'arsu.
Dan haka ta tambayi ɗaya daga cikin custody officers ɗin game da wanda ta zo gani. Suka yi mata wasu tambayoyi kafin su bata izinin zama a wani empty office kafin a zo dashi.
Fayyad, wanda yake tsaye a cikin cell ɗin ko riga babu a jikinsa ba, ya harari custody officer ɗin da ya gama faɗa masa cewa yana da baƙo dake san ganinsa. Ya ce, "Ba zan ga kowa ba".
Nan jami'in ya yi ƙoƙarin shawo kansa, amma ya nace kan cewa ba zai je ko'ina ba har sai an kira shari'arsu. Haka custody officer ɗin ya koma ya faɗa wa Faryal yadda sukayi da Fayyad ɗin.
Faryal ta miƙe da sauri tare da fadin, "Ni zan je in gan shi da kaina as long as it's permissible".
"No you can't". Ya faɗa yana girgiza mata kai.
"To, dan Allah ka faɗa masa Faryal Hafiz ce ta zo ganinsa. Ina son mu yi magana ne kawai, ko da mintuna uku ne, dan Allah".
Custody officer ɗin ya sake kare mata kallo kamar zaiyi Magana sai kuma ya fasa. Ya juya ya fita.
Cell ɗin ya koma, tare da faɗin, "Kai, Faryal Hafiz ce ta zo ganinka".
"Faryal Hafiz?". Fayyad ɗin ya maimaita da mugun mamaki, sai kuma ya ɗauki rigarsa, wadda ta yi duqun duqun, ya rataya a wuya.
Custody officer ɗin ya buɗe cell ɗin ya fito, sannan ya tisa shi gaba zuwa office ɗin da Faryal take.
Suna shigowa, Faryal ta miƙe da azama, idanunsu suka shige cikin na juna. Fayyad ne ya fara kawar da nasa, saboda wata kunya da nadama data rufe shi a karon farko na rayuwarsa.
Faryal ta yi ƙoƙarin controlling kanta, na ganin bata fashe da kuka, kafin ta ce, "Fayyad...".
"Me ya kawo ki nan, Faryal?". Fayyad ɗin ya katse ta.
"Fayyad, zuwa nayi in ji dalilin da ya sa ka ci amanata, ka yaudare ni. Dalilin da ya sa ka sa na kamu da sonka, dalilin da ya sa ka sake juya rayuwata upside down".
Ɗaurewa yayi ya ɗago ya kalle ta, cikin wani irin yanayi ya ce, "Faryal, duk abin da zan faɗa miki a yanzu ba zai canza komai ba. Na san ina ɗaya daga cikin ƙasurguman armed robbers, amma tunda na sa niyyar auranki, i tried hard to leave my past behind. Sai dai abokan aikina sun rinjaye ni, a cewar su mu yi wannan aikin tare ko da shi ne na ƙarshe da zanyi, da haka suka shawo kai na na amince. And that's how everything happened".
Faryal dake girgiza masa kai ta ce, "Fayyad me ya sa ka amsa min da bakinka cewa ka aikata wannan laifin? Me ya sa?". Faryal ta faɗa tana gunjin kukan dake tasowa daga kasan zuciyarta, dan ba ƙarya whl tana mugun son Fayyad.
"Kiyi haƙuri Faryal. Ban yi niyyar cutar da ke ba. Ba ki cancanci duk wannan ba, amma son kai na ne ya jawo komai".
"Fayyad, dan Allah ka faɗa min cewa ba ka sona. Ka faɗa min cewa ka tsane ni. Ka faɗa min wani abu mai zafi, wanda zai sanya ƙiyayyar ka a zuciya ta. Fayyad, na kasa, duk yadda nake ƙoƙarin dasa ƙiyayyarka a cikin zuciyata ko zan samu sassaucin abinda ke damu na, whl na kasa".
Fayyad ya yi murmushi me ciwo, cike da matsananciyar damuwa kafin ya ce, "Ba na son in ƙara yawan laifin da ke kaina. Faryal ba zan iya yi miki ƙarya ba. Ban taɓa shiga soyayya ta gaskiya ba sai a kanki. Infact, aikina bai taɓa ba ni lokacin da zan iya yin kowacce irin soyayya ba.
Bari kiji, i was a master manipulator . Na kasance ina zaɓar yan mata da suka fito daga gidan masu hannu da shuni ko kuma wani sanannen family, inyi amfani da charming side dina wajen jan hankalinsu har su yarda da ni, su amince min ni kuma sai nayi amfani da wannan damar wurin gano duk wasu sirrikansu, daga nan sai mu shirya robbery a gidan ko kuma mu sace yarinyar mu nemi kuɗin fansa daga iyayenta. Amma daga lokacin da na haɗu da ke, komai ya rikice min, kin sauya tunanina gabaɗaya".
Ai Faryal ji tayi baza ta iya ci gaba da sauraron maganganun nasa ba, dan haka ta nufi ƙofa da sauri domin fita.
Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa, "Idan kika bar nan Faryal, bansan lokacin da zan sake ganin ki ba. Dan haka ina roqonki dan Allah, find a place in your heart to forgive me. Dan Allah kar ki fita daga nan ba tare da kin yafe min ba".
Faryal ta juya ta sake kallonsa. Ta girgiza masa kai tare da faɗin, "Na yafe maka Fayyad. Na yafe maka...". Kasa ƙarasa tayi, sai kawai ta juya da gudu ta fice tana kuka.
Motarta ta shige ta kifa kanta kan steering ta cigaba da kuka mai tsanani. Sai da ta yi kuka fiye da yadda ta yi a ranar da abin ya faru. Kusan awa ɗaya ta ɗauka kafin ta iya kunna motar ta bar harabar kotun.
Ko da ta isa Company, sanar wa Aysah tayi ba ta son ganin kowa yau, daga nan ta shige office ɗin nata ba tare data jira amsar Aysah ɗin ba.
Haka ta zauna ta sake faɗawa duniyar tunani, bata san iya adadin lokacin data kwashe ba a haka, sai da ta ji knocking. Ta kalli Tv ɗin da ke opposite da ita kafin ta ce, "Yes".
Aysah ce ta shigo tare da faɗin, "I'm sorry Ma'am. Hamdan ne a waje, yana son ganinki".
Cikin tsananin ɓacin ran da Aysah bata taɓa gani ba a tare da ita, ta buga table ɗin gabanta da ƙarfi tare da faɗin, "Gate out Aysah! Shin ban fada miki cewa ba na son ganin kowa ba? To kar ki sake shigo min nan in har bani na neme ki ba".
Jikin Aysah ne ya fara rawa, saboda ba su taɓa ganin CEO tasu cikin irin wannan yanayin ba. Dan haka cikin sauri ta ce, "Yi haƙuri Ma'am". Sannan ta juya ta fita da sauri.
Hamdan ta samu ta sanar da shi cewa Faryal ɗin tace ba ta son ganin kowa yayi haƙuri ya tafi. Miqewa yayi tsaye ya nufi ƙofar office ɗin yana faɗin, "Ba ki dai faɗa mata Hamdan ba ne".
Aysah ta jinjina kai kafin tayi murmushi, ta ce, "Yau kai ma za ka samu naka rabon, dan daga yadda na ga Ma'am, she's not easy today".
Yana shiga, Faryal ta ɗago kai ta kalle shi ba tare da ta ce komai ba.
"Daga gidanku nake, mai gadi ya sanar min kina wurin aiki".
"Eh, ina nan. Amma dan Allah, I'm not up for a discussion today. Can we catch up another time?". Ta faɗa fuskarta ba alamun walwala.
"No, ba wani abu ba ne ba ma, dama na zo ne in jajanta miki abin da ya faru. Gsky na ji miki ba daɗi. It's not easy to end up with an armed robber, but that's the consequences of a betrayer".
"Cin amana, Hamdan? Idan akwai wani maciyi ai bai wuce kai ba. Macuci, wanda ya ɓata min lokaci. Wallahi, ba zan taɓa yafe maka ba. You have ruined my life".
"To yanzu da kika yi amfani da lokacinki, me kika samu? Ɗan fashi da makami?". Ya faɗa yana dariya, kafin ya ƙara da faɗin, "Look Faryal, ni na riga dana faɗa miki ban shirya aure yanzu ba, amma kika ce za ki jira ni, to miye laifina? You are the one who saw fit to waste your time not me. There's no way you can call me a betrayer".
"Amma kai kuwa ka kira ni da hakan?". Ta faɗa a zafafe. "To ai abinda kika yi yafi kama dana mayaudara, sau nawa ina kiranki? Okay wato a lokacin kina jin kin samu wanda ya fini shine zaki min wulakanci ko?".
Faryal ta saki baki tana kallonsa kawai cikin tsananin mamaki. Mutumin da ta sadaukar da lokacinta saboda shi, wanda ta ba zuciyarta gabaɗaya, ta nuna masa soyayya ta gsky, yau shi ne tsaye a gabanta a matsayin maƙiyinta, dan wadannan maganganun nasa sunfi kama da na makiyinta wanda yake neman chance a kanta, tunda gashi yanayin sa ya nuna jin daɗin musibar da ta faɗa ciki ma yake.
Numfashi ta sauke kafin ta miqe tsaye ta nuna masa kofa ta ce, "Fita Hamdan! Get out of my sight".
"Miye a cikin Company da har za ki kore ni daga office ɗin ki? Oh noo, na fahimce yadda kike ji a halin yanzu. A dinga haƙuri ana kai zuciya nesa, bani na kar zomon ba, rataya ma ban ansa ba". Ya faɗa cikin sigar tsokana.
"Kai, kar fa kayi tunanin za ka zo har inda nake, kace zaka iya faɗa min duk abin da kake so. Ka gane ko?".
"And so?". Ya faɗa cikin sigar rainin wayo. Nan fa suka shiga musayar kalamai marassa daɗi kamar wasu abokan gaba. Duk da cewa Faryal ba ta yi niyyar biye masa ba, amma ya riga ya hasala ta ne, dama kuma a cikin ɓacin rai da damuwa take. A ƙarshe dai sai securities ta kira suka raka shi waje.
Riqe kanta dake sara mata tayi bayan sun fita, tana jin kamar tayi ta ihu ko zata ji saukin halin da take ciki. Wucewa tayi ta ɗauko robar ruwa me sanyi ta buɗe ta sha.
Shuru ta ɗan yi a tsayen, can kuma ta wuce ta ɗauki jakarta ta bar Company, ta nufi gidan su Shenal domin ta samu ta ɗan warware, kafin ta koma gida.