Free chapter · Read without an account
19. The Rain and the Roses
by Zainab · TSAƘANINMU
TSAKANINMU
_United States of America._
_Bethesda, Maryland._
Tunda ya dawo daga masjid na Sallah Isha ya lura da yanda sama yayi duhu alamun kowane irin lokaci ana iya yin ruwa amma kuma yasa wa ranshi zuwa inda Madina su dawo gida tare.
Yana sanye da casual outfits nashi ya sanya jacket a sama koda anyi ruwa kuma dai ga yanda weather'n garin yake suna samun ruwa sosai.
"Take care of the house while I come back home with your Maama"
Ya sanar da Gumsu, ta mishi peck a cheeks shima ya maida mata tukuna ya wuce a ƙafa.
A hanyar shi na zuwa nan down the street akwai me saida flowers, su marigold, jasmine ne da Roses, flowers kala daban daban. Deep red roses ya siya sannan ya taka da ƙafa daga nan zuwa Suburban Hospital.
Koda ya isa ƙarfe tara daidai anan parking lot ya tsaya daidai motar Madina yana jiran ta.
Tsayuwar shi da minti biyu se ga Madina ta fito. Tana ganin Hamdan ta sauke wani irin ajiyar zuciya kafaɗun ta na sauka ƙasa tayi murmushi, duk gajiyar ta na fita daga jikin ta.
"Tun yaushe kake nan?"
"Ban jima da zuwa ba" ya faɗi mata
"Okay. Ya aiki?"
"Alhamdulillah. Ya naki?"
"Tiring amma dole wahala na ya gudu da ganin ka"
Murmushi Hamdan yayi ya amshe medical bag nata da doctor's coat da packing box yasa mata a cikin motar ta.
Deep red roses dake hannun shi ya bata "I love you"
"I love you too, my Hamdan" ta faɗi tare da kai roses ɗin a hancin ta tana jin ƙamshin da suke
"You're a good man, Hamdan" tace tana kallon shi cikin idanu.
Mijinta Hamdan yana da haske irin caramel skin, he's tall jikin shi daidai irin na mazan da suke not slim and not fat but middle. Beard nashi ya fara zama grey irin grey ɗinnan da zaka duba kasan mutum baya cikin wahala ko kaɗan. Lokacin da suke Nigeria, caramel skin nashi daidai yake caramel especially fuskar shi amma da suka dawo nan States, fatar jikin shi tayi haske especially a hannuwan shi daidai wrist nashi zuwa fingers. He has a pointed nose and beautiful eyes da yake sakawa glasses saboda ciwo.
"You're a good woman too, Madina"
"Ban kai naka ba" tace tayi hugging nashi.
Sun jima a hugging juna kafin taji yace "We're going to trek down to Bradley Hills from here so we better go"
Da sauri ta tashi daga jikin shi "Trek, Hamdan?"
"Ba zaki iya bane?"
Dariya tayi "A'a zan iya. Amma da motana gashi lafiyar ta ƙalau but again, yeah, it'll be one of those memorable moments for us to trek down to Bradley Hills. So, let's go amma bari na faɗawa securities motana na nan"
Nodding Kai Hamdan yayi ta matsa gaba kaɗan tayi wa securities magana.
Dawowa tayi riƙe da deep red roses nata da ya bata suka fara trekking.
Shiru ne a tsakaninsu, hadarin sama yana ƙara haɗuwa ga iskan da ake yi yana kaɗa manya manyan itacen dake garin.
Gari yayi shiru shima, babu mutane dayawa se wasu dake tafiya tare da karnensu da kuma mutane dake cikin manyan-manyan kyawawan motoci saboda yanda unguwar take na masu kuɗi.
"Gumsu is having problem with her eyes" ta sanar dashi
"I'm afraid she has to start using glasses in her teens" ya faɗa
"Tayi gadon Dad nata kenan"
"It was during my late teens that I started using it"
"Gashi har ya maka wuri a hanci" tace tare da kallon hancinsa da sa glasses ya raba ta sama chan wurin idanun shi.
"Kuma ya maka kyau" tace tare da yin murmushi
"Ke ma idan kika fara sawa ze miki kyau"
"Ni lafiya na lau"
"Mu kuma bamu da lafiya ko?"
"Like father like daughter!" Madina tace tare da yin murmushi
"Like mother like daughter ake cewa"
"Amma ni lafiya na lau, so za'a amfani da mahaifin Gumsu"
"Yanzu kin bar min ita?"
Wata dariya Madina ta sake yi tana tuna lokacin da ta haifa Gumsu. Hamdan yana kusa da ita ta haihu he was holding her hand.
"You have been a very good man, Hamdan"
"Dalilin da yasa shine kema kin kasance mace me kirki a wuri na"
Murmushi tayi ta riƙe hannun shi suka cigaba da tafiya.
Yayyafi aka fara ahankali kafin a zubo ruwa da ƙarfi. Saboda yanda akwai manya manyan itace yasa idan ruwan ya dake itace se ana jin loudness sosai.
Cire jacket nashi yayi ya sawa Madina yace mata "Run" yana ɗaga murya ta yanda zata ji sosai
"What?" Madina ta faɗa tana dariya sosai tana riƙe da deep red roses nata.
"I said run"
Dariya take sosai tana saurin tafiya tayi tsaye a tsakiyar titi tana mishi magana with a loud voice domin yaji, ga wandon scrubs nata duk ya jiƙe, fuskar ta shar da ruwa.
"I love you very much, Hamdan. Ours will be even after death. And it'll forever be for better and for worse because you're my heart, my Hamdan"
Murmushi Hamdan yake yana kallon ta and he catches her by the hand and he pecks her knuckles.
"You promise?"
"I always promise" tace da murmushi akan fuskar ta
A jikin shi ya sata yace "I'm afraid you'll be down with cold"
"And I don't mind, Hamdan. I won't mind getting sick again and again and again just doing this with you"
Kanta yasa a chest ɗin shi suka cigaba da tafiya. Ruwa suka cigaba da zubowa with a few people on the road going home as them.
"Are you listening?"
"Yes, Madina"
"Wanan engagement na Jawahir yayi sauri dayawa, Hamdan. Ka gaji da ita ko so kake ayi sauri ayi mata aure saboda wani dalili naka? Kar kaga kaman maganar da nake na banza ne, eh duka mun yarda idan namiji yana son mace kuma ya shirya, sun amince da junansu, ba'a jimawa sosai manya zasu shigo cikin lamarin su ayi maganar aure. Na yarda da na Jawahir amma inaso ka ƙara dubawa, Hamdan. Ku sake yin bincike akan mijin da zata aura kafin ku aura mata shi. Nasan wani bincike yayi yawa amma wannan maganar aure ne. You ask a few different people to know about him, Hamdan. Jawahir is a small innocent girl bana so ta shiga damuwa akan auren da take tunanin zata samu zaman lafiya"
"Kina tunanin muna sauri akan zancen auren Jawahir?"
"Ba saurin ba, Hamdan, binciken da kuke yi. Ina ganin wannan binciken be isa a kira shi da bincike ba"
Tunani yayi kuma da gaskiyar ta, ya kamata shima yasa a mishi binciken Khalil. Yasan halin yaran yanzu yanda suke yin abubuwa, mutum se ya nuna yana son yarinya ze riƙe ta amana amma da anyi aure kuma komai ya chanja na halayyar shi.
"I'll assign a trusted person for it, Madina"
"Yes, talk to Mustapha. I trust he'll be open with you concerning everything that has to do with Khalil"
"I'll talk to him. Thank you for your care"
"Jawahir kaman ƴa ce a wuri na fa" tace tana tuna zaman da suka yi da ita chan lokacin baya
Murmushi yayi suka cigaba da tafiyar su.
Har sun kusa isowa gida tace "What'll happen if I die, Hamdan? Will you forget me?"
"Me ya kawo wannan maganar kuma?"
"Gwara na faɗa kafin wani ya faɗa ko, tunda mun san da akwai mutuwa inda ke rayuwa"
"Ta ya za'a yi na mance dake? Kuma waya ce ke zaki mutu ki bar ni?"
Dariya tayi "Babu wanda ya sani amma ni ba zan taɓa mancewa da kai ba. Zan cigaba da zama dakai a cikin zuciya ta ina maka addu'a a kodayaushe. Ina fatar haka a wurin ka kuma"
"Mu dena wannan maganar, Madina, saboda ni ban taɓa tunanin rayuwar da babu ke ba"
Murmushi tayi tace "Koda na ma riga ka mutuwa, inaso ka kasance wanda zaka min last bath nawa kuma kayi min sutura. Ka kula muna da yarinyar mu, Gumsu"
Ran Hamdan ne ya ɓaci sosai ya tada kanta a gefen chest ɗin shi yace "Wannan wace irin magana ce kike yi?" Ruwan dake kan fuskar shi ya share "Dan Allah mu dena irin wannan maganar. Naji ya isa"
Murmushi Madina tayi ta riƙe hannun shi suka cigaba da tafiya basu ƙara cewa komai ba har suka isa gida suna shivering hardai ita.