Free chapter 路 Read without an account

Chapter 31

by Gidan Iko 路 GARWASHI

_GARWASHI_
       
   *Hadiza Bara'u Gidan iko*


..........Ciwon Kai ya matsa min irin me Azabar Rudarwar Nan don ji nake tamkar Kan zai dagargaje na Kuma sani ba komai ne silar ciwon ba sai kwalbar da Amaka ta jefo min aka duk maganin da nasha banji ya sauka ba  Dole nake kwance Ina dafe da Kan

Ina kwance naji Rutu tana yiwa su Amaka da Maazi Nkem barka da zuwa inda Kuma naji gabana yayi masifar faduwa na Kuma ji kaina ya Kara daukar wani ciwon fiye da Wanda yakeyi na Mike zaune inajiran inji shigowar Amaka ko Maazi Nkem Amma banji Wanda ya nufo dakin nawa ba. Duk da na kasa fitowa ko sannu da Zuwa nayi musu saboda tsoro da Rudani Haka na kasa komawa na kwanta duk jikina na bukatar hakan Amma na kasa.

Na Mike da kyar juwa na diba ta da nufin na fita nayiwa su Amaka sannu da Zuwa don na gano wautata ta kin fitowa yi musu barka da zuwa Amma Kuma jiri ya kwasheni ya zube akasa Ina dafe kaina Wanda ke gana min Azaba abinda ya Hana Ni fita kenan na kwanta Ina dafe kaina Ina Runtse idanu saboda wahala

Can da Dare ne naji shigowar Sony da Emmanuel inda Kuma na jiyo tashin muryar Amaka tana fada tana karawa duk da ban San ko wa take wa fadan ba Kuma Akan me take ba sai na Mike a hankali na nufi Fallon  wajen inda nake jiyo muryar Amaka tana fada

Na fito a hankali saboda ciwon Kai don Basu San na fito ba don ko karar taku banayi 

Tun daga nesa nake jiyo muryar Amaka Sai da na matso naji abinda take wa fada wato Sony Wanda duk ya firgita da fadan Amaka har ya koma kalar tausayi cikin kumfar Baki Amaka ke fadin


"Wato kaima ka Zama munafuki ko? Har Ni zaka munafunta ko? Tanayi Kuma tana zaro ido tana nuni da yatsan ta manuniya

"Ni da kaina na Kira ka na tambaye ka Justina tazo Nan ? Kace min Bata Zo ba Ashe Kai munafuki ne? Yaushe ka zamo munafuki? Har Ni zakayiwa munafunci? Kai ke Goya mata baya ko ? Kai ke daure mata kugu ko? To Zan hada har Kai in la ance ku tunda har kake Goya mata baya........

Sony ya dubi Amaka Yana fadin Wallahi banyi Miki munafunci ba ban San komai Akan abinda Justina tayi Miki ba don Allah kiyi hakuri .........

"Ehen Ehen inyi hakuri kake cewa ? Kai dubi idona kace inyi hakuri? Kana son kace min baka San abinda tayi ba? Yace Wallahi ban San abinda tayi ba 


Amaka ta dubi Emmanuel tace kaima har da Kai ake min munafunci ko? Yayi saurin kada kanshi Yana fadin
A a banda Ni Amaka ban San komai ba Wallahi ya fada fuskar shi da tsananin tsoro

"To Bari kuji dama na Kira ku NE in fada muku Ni da uban ku mun cire Justina daga cikin Ya'yan da muka haifa har mun la ance ta Kuma duk shegen da naji yayi Mata ko magana sai na hada na la ance ku duka babu mu babu Justina har abada kunji abinda na fada muku? Ta fada tana Rike kunnen ta Alamar dai su San kashedin da take musu suka amsa da sunji amma Kuma Sony sai ya tambaye Amaka wane irin laifi Justina tayi Wanda suka yanke Mata wannan hukuncin?

Sai kawai Amaka ta fashe da kuka har tana tsigar gashin kanta Alamar bakin ciki ya sameta dama idan har Bakin ciki ya sameta haka takeyi tayi ta cirar gashin kanta.

Emmanuel ne ya Ruko ta daga tsigar gashin kanta Yana bata hakuri shi Kuma Sony ya dauko mata Ruwan faro ya Bata a Baki kafin ta Soma share hawayen ta ta Kuma Soma Basu labari

"Ba na fada muku maganar Auren ta da yarima Gibson ba Dan gidan igwai? Suka ce Eh haka ne

Sai tace Kuma ai na fada muku Ciwon da Uban ku yayi a can gida imo har muka kwanta Asibiti ko? Suka sake cewa Eh haka ne

"To shegiyar yarinyar Nan Justina ta fita daga addinin mu ta koma cikin hausa man yanzu salla takeyi Kuma har komai na masu salla takeyi shine take sanar wa Dan gidan igwai Wai  shima zata mayar dashi me Salla Ni kuwa me na kuskure da na haifo me salla a cikina? Sai ta Kara Rusa kuka tana Kara tsigar gashin kanta inda Suma Sony da Emmanuel sukayi Duff kamar Ruwa ya cinye su

Amaka na ta Rusa kuka su Kuma suna cikin jimami don hatta Emmanuel baiji dadin hakan ba don su a wurin su canjin addini shine karshen abin kunya..
Sony ya watsowa Amaka tambayar wadda ta fusata ta inda yace yanzu kenan yarima Gibson ya fasa Auren ta? 

Sai kawai Amaka ta kwasa mishi Mari tana fadin
"Don ubanka ta Yaya Dan Gidan igwai zai Auri me salla?

Ina tsaye Ina Jin takaddamar dake faruwa Ina Kuma kallo 

Kalmar da tafito daga bakin Sony ita ta firgita Ni don kuwa cewa meye amfanin Rayuwa ta tunda na canja addini? Amaka tayi saurin fadin 
"Babu amfani Wallahi babu Amfani don ita tana kunyar kawayen ta da Yan uwan ta idan sukaji yarta ta canja addini

Emmanuel dai baice komai ba sai tagumin da ya zuba inda Amaka tace duk su tashi su tafi dama abinda zata fada musu kenan Kuma duk Wanda ya Kuma yi min ko magana ce zata la ance shi in sun kiyaye to sun tsira idan kuma tsautsayi ya kaisu kusanta ta to zasu ga abinda zai faru

Suka tafi jiki a sanyaye Ni Kuma na koma daki tunda nayi sa ar Amaka Bata ganni ba bata Kuma zaci naji wannan magana tasu ba

Na kwanta HAWAYE na bin idaniya ta Ina tausayin kaina duk da a zuciya ta bana nadamar kasancewa ta musulma Amma Kuma Ina nadamar batawa iyayena Rai musamman idan na tino so da kaunar da suka nuna min da gatantawa Amma nice na zamo sanadin hawayen su to ya zanyi? 

Babu Wanda ya leko dakina tun daga Amaka zuwa Maazi Nkem bare su CE min kanzil

Na fito da safe na nufi dakin Amaka don na Roke ta gafara in Kuma Roki ta yafe min laifukan da nayi Mata Amma dakinta a kulle na koma dakin Maazi Nkem shima bashi dakin a kulle Dole na tambaye Mai Aikin mu Rutu inda Amaka ta tafi Rutu ta fada min ai Asibiti suka kwana gabana yayi masifar faduwa na tambaye ta waye ba lafiya? Tace min ai Maazi Nkem ne jikin shi ya tashi bayan sun dawo gida 

Nayi shiru inajin Rashin Dadi a Raina ko wannan ciwon kadai da ke wahalar da Maazi Nkem alhakin sa fa Yana kaina to Amma ya zanyi ?

Nacewa Rutu ta kawo min Ruwan zafi don Rabo na da abinci tun jiya gara ko shayi nasha na warware Yan hanjina

Rutu ta sunnar da kanta kasa tana bani hakuri Alamar tana Jin kunyar fada min wata magana
Na dubeta nace me kikayi min ne Rutu da kike bani hakuri? Tace madam CE tace  idan na sake ko Ruwan gidan Nan Kika Sha abakin Aikina don Allah kiyi min Rai Kar na Rasa Aikina tace komai Kika nema Kar na Baki 

Nayi turus Ina kallon Rutu da sakon Amaka gareni  Dole na bi umarnin Rutu don Kar ta Rasa Aikin ta Domin ko gari ya gari aka kawowa Amakar ita don tayi aiki a sallameta ta Kuma Tara abin Duniya

Ciwon zuciyar Maazi Nkem ne ya Tashi Wai don kawai ya dawo gida aka sanar dashi Ina Nan don Haka suka kwasa suka koma Asibiti Amaka na jinya 

Kwana Biyu ko Ruwa ya gagare Ni Dole na fito da kudi na siyo abubuwan bukata na dawo daki na zauna Ina tunanin indai Haka su Amaka suke nufi lallai Rayuwa zatayi min tsanani da wahala don ko kudin dake hannu na ai daga garesu suke Ranar da suka Kare Kuma sai na yi Yaya?
Na samu ciwon Kai ya yi min sauki sai kadan kadan nakejin shi Amma Kuma yanayin da nake neman SHIGA yafi komai yi min tsanani Amma Kuma har yanzu banji nadamar abinda nayi ba

Na fito a falon Ina shimfida abin salla ta saboda a zuhur tayi na koma dakina na dauro Alwala nazo na saka hijabina Rutu tana kallo na cikin mamaki da Al ajabi har tana Rike Baki Wai duk cikin mamaki take Ni kusa da Naga irin kallon da take min sai nayi kamar ban San Allah yayi tsiron halittar ta a wurin ba na zura hijabina na tada kabbarar harama 


Nayi Raka a biyu Ina zaune Ina tahiya naji kugin motar Amaka inda na tabbatar kafin na karasa sallar ta shigo Kuma naji kamar na katse sallar amma Kuma na ci gaba da salla ta inda suka shigo Kuma naji su kamar ba su kadai ba Kuma ga Alama tsayawa sukayi suna kallo na don naji hakan a jikina Ni Kuma hankalina kwance na ciko sauran Raka a biyu nayi tahiya Kuma na sallame har na daga hannu ina ADDU A duk banji motsin kowa ba har na shafa ADDU AR na juyo muka Kuma yi ido Hudu da Amaka da Maazi Nkem har ma da Yan uwana Sony da Emmanuel duk suna kallo na cikin wata fuska da ke nuna Alhini da jimami kafin Amaka ta nufo Ni a fusace..........


Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran


Gidan iko shine sunana kecewa saduwar ALHERI馃グ馃拑馃徔

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol