Free chapter · Read without an account
6
by Hijjart Abdoul · SALMA ELM
**********Yana zaune ya ji Abban su na cewa.
"Fahad ina budurwar ka? Ko ka dena son nata kwana biyu ba'a zo anyi maka warning ba".
Fahad da sauri ya ce, "Abbaaaaaa".
Dariya suka sa gaba ɗayan su.
Mama ta ce, "Ina ruwan Ummu da Kakanninta".
Khadijah ta ce, "Ai kai ma kasan wa ka ɗauko. Taya za'ai ka ce kana son ta? Bayan irin faɗan da kuke yi da ita, ai ka rena mata hankali ma".
"Wallahi Khadijah ana min magana kina sa baki sai na ci....
Mama ce ta zuba masa kyakkyawan ranƙwashi a kan sa ta ce.
"Ban hanaka wannan zagin ba? Baka da aiki sai zagi a cikin gida?
Tsuke baki ya yi yana muzurai.
Ya ce, "Kuma sai take shiga abinda ba ruwan ta?
"Ta shiga ɗin, tunda kai baka da hankali a rayuwarka".
Cin magani ya yi yana ɗauke plate ɗin sa ya tashi ya sauka daga kan kujerar ya koma wurin Mufeed.
"Yaya Mufeed, Ummu ta kira ka? Jiya ta ce na turo maka numbern ka? Did she? Ko tana son ka ne? Shegen son maza ne da ita. Nima na ce ina son ta, baka rashin mutuncin da ta min ba. Wai ban yi mata ba, ni ba ajinta ba ne. Shegiya mai kama da aljanu".
"Ta kira ka?
"Who is she?
Mufeed ya faɗa kamar irin be san waye ce ita ba.
Aikuwa ya zage ya shiga bashi labarin Ummu.
"Tana da kirki idan ta so amma fa".
Kawai jin sa ya yi amma be ce masa komai ba.
"Yau ku samu mai ɗauko ku daga makaranta. Abbaaaah".
Ya kwala kiran sunan Abbah.
Abbah ya ce, "Na'am Babana".
"Dan Allah a nemo mana driver, wallah na gaji da kai wannan masu kama da magunan na je na ɗauko su".
Abbah ya ce, "Mufeed ka kai su ka ɗauko su".
Idris ya ce, "Abbahh....
Kallon da ya yi masa ne yasa shi yin shiru kawai. Mufeed uffan be ce ba, ya kalla Fahad alamar ya bashi key ya kuwa bashi ɗin.
"Na dauka machine ɗin ka?
Be yi masa magana ba sannan be ce masa a'a ba. Ya fita waje.
Mama tace, "Ku tashi ku fita, kun san ba magana zai yi ba".
Tashin suka yi suka fita suka same shi a
cikin mota. Sune suka sanar da shi inda makarantar take dan ba sani ba ya yi. Ya kai su ya je ya dawo kenan ya ga Ummu a tsakiyar titin da zata sa da su da layin su ta ci uwar ɗamara tana cacar baki da wasu maza. Ya jima yana kallonta ganin yarda take zazzaga masifa. Wasu suna bata haƙuri wasu kuma suna faɗan da su.
Tana ganin Baban ta kwasa da gudu, zata shige layin su sai kuma ta dawo da baya ta kalli Mufeed, kafin ya zagaya da gudu ta buɗe motar ta shiga tana sunkuyar da kai gabanta, sai faduwa tana sauke ajiyar zuciya. Ga wani irin haki da take yi na tsananin tsoro da tashin hankali. Sai ƙifta ido take yi.
"Ya tafi? Wani mutum mai fararen kaya, fuskarsa a ɗaure baya dariya?
Ta faɗa tana kallon sa, ganin ya rabu da ita be kula shi ba, ta sa hannu ta mintsine shi.
"Magana nake maka".
Sai kuma ta leƙa, taga ba kowa kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana zama a kujerar motar ta sa hannu ta zuge glass ɗin.
"Kafin ya ganni ya sake cin ubana. Jiya dukan mutuwa ya yi min. Baka ji jikina ba zazzaɓi sosai".
Ta faɗa a hankali tana taɓa jikinta. Sai kuma ta kalle shi.
"Yi hakuri. Ina kwana? Ka tashi lafiya? Ya ka tashi? Ka tashi cikin daren ka yi min addu'ar?
Kallonta ya yi sannan ya nuna mata windown ta
"Ga mutumin nan a baya ki".
Da sauri ta juya taga Baba ta ƙwalalo ido sai kuma ta sunkuyar da kan ta ƙasa.
"Shikenan na mutu na lalace. Yau kasheni zai yi. Ya tsaneni, tsana mai tsananini wallahi. Daman ni tsintoni ya y, Babansu ne ba Babana ba".
Gajeren murmushi Mufeed ya saki yana girgiza kan sa ya kawar da kan sa.
"Ya tafi?
Sai kuma ta ɗago a hankali tana kallon wurin taga ba kowa sannan ta kalla glass ɗin taga ashe fa tinted ne.
"Kasan de tsorata musulmi ba kyau ko?
Ta faɗa tana kumbura fuska tare da hararansa.
"Uhm".
Ya faɗa a hankali yana kallonta.
"Ka yi kyau".
Kallon jikin ita ya yi, daga ita sai doguwar riga ta atampha sai uwar damarar da ta ci. Da hula da kan ta kitsonta ya fito ta ƙasan hular.
"Kai ne ka ke wannan ƙamshin ko kuma de motar ce?
"Kai ne?
"Allah akwai daɗi".
"Mu je ka kaini shagon saurayina zan siyo abu, sai na yi masa rashin mutunci kuma. Ni dai yaudara ya kalle ni yace be so na".
Ta yi ƙwafa. Dan girgiza kan sa kawai ya yi yana jan motar.
"Ka ga Babansu, ka ga gidansu".
Ta faɗa tana sakin dariya ganinsa a kofar gidan da motar sa shi kuma yana gaisawa da wasu.
"Ni Babansu be taɓa min dariya ba, kullum fuskarsa a murtuke sai de naga dariyarsa daga nesa nesa be so na ai".
"Kuma wai shine ya haifeni wai fa a hakan? Dan Allah sai ka ke bugun wacce ka haifa?
"Tsaya tsaya tsaya".
Ta faɗa da sauri hakan yasa shi jan burki da sauri yana kallonta.
"Ga gidanmu bari na kira Dadda ta zo ku gaisa".
Bata ma jira cewarsa ba ta fita a guje tana shiga gidan nasu. Gidan ya bi da kallo, ga bishiya nan a kofar gidan, sai ɗan dakalin da ake zama. Ƙaramsr kofar ya bi da ido inda Ibrahim yake fitowa da machine ɗin sa. Sai ga Dadda harda Daada sun fito. Da sauri ya fito daga cikin motar dan wallahi be zaci za su biyewa shirmen tasu fito ba. Kawai hijabinta ta ajje a motar da ta yi damara da shi shi yasa be ja motar ba ya tafi.
"Ina kwananku".
Ya faɗa a hankali yana russunawa ita kuma daga baya tana washe baki ta maƙale a bayan Yaya Ibrahim, Shi kuma Ibrahim kamar ya yi bindiga tsabar takaici da abin haushi, ita kuma wai kunya take ji. Karo na farko a rayuwarsa da ya ji wasu ahali sun burge shi sama da nasa. Kuma ya ji yana so ya shiga jikinta dominta kawai. Dan bazaka iya taɓa yakice wannan yarinayr da take so ta samar masa farin ciki ba. Ko waye ta yi maka haka sai ka ji wani abu na musamman a tattare da ita.
Hannu Ibrahim ya miƙa masa yana masa murmushi suka gaisa.
"Malam Mufeed dan Allah a riƙe ta da amana ka ji ko?
Dadda ta faɗa tana komawa dan shi daman Daada ya koma suna gaisawa. Jinjina kai kawai ya yi.
Ibrahim harara kawai yake aika mata a kaikace gashi ta riƙe masa riga sai squeezing take yi masa da riga daga baya wai kunya. Shi Mufeed kunyar ce take bashi dariya sosai.
"Zaki iya saki na na tafi?
Ya faɗa mata yana juyawa ya kalleta ya zabga mata harara. Yanzu ya taɓa ta duniya ta ji shi, shida su Dadda. Ƙwafa ya yi mata yana jinjina kan sa, ya ja machine ɗin sa ya wuce.
"Ga su Daada da kuma Dadda ko?
"Yaushe zaka zo zance? Yau da daddare? Ko mu haɗu a cafe ɗina?
"Uhmm?
Ta faɗa innocently tana sakin kyakkyawan Murmushi. Sai kuma ta fara wasa da hannunta tana ɗan kumbura baki tana ƙasa ƙasa ita a dole an zo wajen ta. Kawai jingina ya yi da mota yana ƙare mata kallo.
"Na gama zaka iya tafiya, na fasa zuwa shagon na yi rashin mutunci. Amma kuwa zai sani wallahi".
Ta yi ƙwafa kawai ta na sake sakar masa wani irin kyakkyawan narkakken murmushi.
"Until next tiiimmmmmeee".
Ta wani ja time ɗin tana masa waving da hannunta. Ta shige cikin gidan yana jiyo ta ƙwalawa Daada kira. Wato aiken ta fasa ikon Allah......
**********"Daada ina kwana".
Haɗe fuskarsa sosai Daada ya yi yana juyar da kan sa tamkar ba shi Baba yake gaidawa ba. Yayin da Baba ya sunkuyar da kan sa ƙasa kafin ya ɗago cikin alihinin da yake damunsa yace.
"Daada dan Allah ka yi haƙuri. Tun jiya baka min magana ba, dan Allah ka yi haƙuri".
Sake juyar da kan sa wani gefen Daada ya yi yana zumɓura baki da kaɗa ƙafa na tsantsan rigimar tsofaffi.
"Ka yi haƙuri".
Ya sake faɗa masa a hankali cike da sanyin jiki.
"Daada tunda ka ke da ni, baka taɓa min faɗa ba, sai akan Ummu Baba. Zuwan Kuma ne zai sa muke sa mun matsala da kai?
"Dan Allah Baba ka yi haƙuri".
Daada ya ce, "Ehh saboda na ce ka yi abinda na ke so baka yi. Baka cikawa, akan me zaka ke samun yar mutane kana bugu. Akan me?
"Dan Allah ka yi haƙuri".
Ya faɗa masa a hankali. Tunda de mahaifinsa ne amma ba yarda ya iya da shi.
"Shi wancan yaron ɗin ka tura masa kuɗin makarantar ko na je na tura masa da kai na?
"Na tura masa sati biyu da suka wuce".
Jinjina kai ya yi kawai ya ce, "To sai kuɗin registration ɗin yarinyar itama. A biya mata, bana so ace mun gaza ta kowanne fanni ne. Bari ubansu ya zo na ji shi ko yana ba su ko baya ba su din".
Ana haka sai ka ga Kawu Mudan ya shigo wanda ya kasance kawu ne a wurin su Ummu. Kana ganinsa ka ga mutum mararsan hayaniya da husuma san beyi kala da masu tashin hankali ba. Kamar su daya da Baba.
"Daada lafiya? Naganka a haka?
Ya faɗa a hankali yana zama a kusa da shi. Tsuke baki Daada ya yi ya ce.
"Yoo ba dole ka ganni a haka ba, ya samu yarinyar mutane ya jibgeta, yanzu har gori ya yi min wai shi ne ubanta, na komar masa da ƴar sa".
"Dan Allah ka yi haƙuri, Shalelenka yarinyar ka ce, kuma mai sunan Hajiya ka ga kuwa ai babu wannan maganar".
Taɓe baki ya yi kawai yana kaɗa kai.
"Ka yi haƙuri".
Shima Kawun ya faɗa. Sake taɓe baki ya yi kawai be ce komai ba.
"Batun yaran nan, kana kula da su yarda ya kamata ko?
Sunkuyar da kan sa ya yi, kafin ya ɗago ya ce.
"Daada ina so su dawo wajemmu, bance ta gaza ba wurin ba su tarbiyya, amma kamar na so na raina kula da su da take yi. Neman kuɗi kawai ta sa a gaba. Bata da wani buri da ya wuce kuɗi?
Daada ya yi murmushi.
Ya ce, "Ai tun ran gini tun ran zane. A yanzu karɓar yara ba zai iyu ba, suna da damar da za su zaɓi wanda zai su zauna da shi. Walau uba ko mahaifiyarsu. Balle kuma su da Babansu ya rasu, Bana jin kuma za su zaɓemu tunda gani take bama iya yin komai, alhali Allah ya gani muna iyakacin ƙoƙarinmu akan su".
Jinjina kai kawai ya yi. Shi de Baba be sake cewa komai ba yana jin su suna zancen su.
"Babansu ina kwana? An tashi lafiya?
Cewar Kawun yana miƙa masa hannu.
"Sai de Baban na su kam".
Daada ya faɗa yana jinjina kai, abinda ya yiwa Salma ya kasa barinsa, wai duka? To ita jaka ce da zaka kama yake zabga ko kuwa meye ne?
Ƙwafa kawai ya yi yana jinsu suna zancen be shiga ba har sai da goma ta yi sannan suka yi masa sallama shi da Dadda kowa ya wuce wajen aiki....