Free chapter · Read without an account
9
by Hijjart Abdoul · SALMA ELM
*********Jinjina masa kai Abbahn ya yi, hakan yasa shi miƙewa yana jin kan sa yana sara masa sosai. Wai Alhaji ne ya tafi ya barshi, mutumin da ya riƙe hannunsa ya koya masa tafiya, mutumin da baya son fushinsa, mutumi da yake tsananin son shi da ƙaunarsa? Shin zan sake samun wata soyayyar kuwa? Ko da ace za'a nuna masa soyayya ba kamar yarda Alhaji zai yi ba.
Riƙe kan sa ya sake yi sosai da ya ji yana juya masa sosai. Rayuwarsa da ta Salma yake ganin tamkar suna kamanceceniya, domin duka kakannin ne suka rene su. Shima jin daɗi da walwala ba wacce ba'a bashi ba. Bambanci kawai shine inda suka ta so. Su sun taso a wurin da kowa yana cikin gidan ne baka fita sai makaranta. Sannan shi ba mutum ba ne mai faɗa da neman magana shi yasa be sangarce ba. Duk da ita ana yi mata kallon sangartacciya amma akwai wani haske mai girma dake tattare da ita. Akwai kuma tarin ƙuruciya da suka yi mata yawa uwa uba kyakkyawan gatan da take so samu. Inda ace Alhaji yana nan shi da Inna gatan da za su bata ya tabbatar sai ya yi mata yawan da kullum sai ta zubar da ƙwallar farin ciki. Amma a yanzu basa duniyar ma gaba ɗaya bare ya ba su labarin ya haɗu da Salma. Salmar da yake so, wacce yake bashi labarin yadda ta taimake shi. Ita ce ta sa Yayanta ya bashi jini. A sanda aka ya faɗi da ciwon sa ya tashi, yana jinta tana roƙar da da Allah da ya taimaka masa. Harda cewa idan ta girma zata biya shi kuɗinsa. Duk da yana cikin ciwo sai da ya yi dariya. Daƙyar ya yarda ya bada jinin amma yace a dominta idan ba dan ita ba haka kawai ba zai bada jini ga wanda be sani ba. Kuma ta sa ya biya kuɗin asibitin a account ɗin Daada. Ta ƙi zuwa makaranta ta zauna da shi har ya farfaɗo. A lokaci take tambayarsa shi waye ne? Me ya ke damunsa? Sai ya je ya mutu ko kuwa baya da kowa ne da zai fito haka? Ya ce mata ya zo gidan Dan sa ne ya zo exercise ne ziyara shine ya fito domin ya yi tattaki, kuma idan jikinsa ya ji zai yi faɗa, aikuwa ta balbale shi da masifa, kawai ya tsaya yana kallonta akan be da ce ba da sace yanzu ya mutu ba? Ya za su yi su samu iyalansa? Bama wannan ba kada ya sake fitowa batare da wani a tare da shi ba. Da kuɗin makarantar ta je ta siyo masa fruit ta bashi ya sha. Zata tafi yace su yi hoto. Shine suka yi domin ta shiga zuciyarsa, kuma gata yarinya ƙarama sosai amma akwai hankalin taimako. Tana tafiya shikuma yana zuwa a lokacinne ya bashi labarinta harda faɗan da ta yi masa da irin yarda ta kula da shi. Kafin ya ce a duba idan akwai Camera a ɗakin yana so yake ganinta dan Allah dan babbar asibitine suka kawo shi, domin shine mafi kusa dasu. Abinda ta yi masa ya zauna a cikin zuciyarsa sosai. Bayan wannan taimakon ta sake taimaka masa, shima ya fito shi kadai wannan kuma asthma din sa ce ta tashi ya je cafe ɗin ta, inhaler ɗin sa na mota, ta sake kai shi asibiti, ta taimake shi ko da ya farfaɗo faɗa ta ringa yi masa akan me yasa ba zai ke tafiya da inhaler ba da yace mata tana cikin mota, kamar ya rufe shi da duka ai ba'a mota ake ajjewa ba, tun daga nan sai ya zamana duk idan ya shigo Kano zai je Café ɗin ta su haɗu ko ya je makarantarta, har suka fara gaisawa da Daada har yake zuwa gidansu, sau ɗaya Inna ta taɓa zuwa, amma shi Mufeed be taɓa zuwa ba, ta shiga zuciyar Alhaji yarinyar fiye da tunanin mai tunanin, haka duk haɗuwa idan taga zai ci ko zai sha wani abun da ciwonsa so musamman diabetes bata bari, ta iya kula da marar lafiya sosai da kuma lafiyar duk wanda take tare da shi, domin shima, Sai da ya haɗu da ita ne ya san dalilin da yasa ta shiga zuciyar Alhaji ta zauna. Har ya yi mata kyauta mafi girman daraja saboda abinda ta yi masa. Alhaji yana ce masa She’s wonderfully different and She stands out from the crowd
Amma shi a yanzu ya tabbatar da She’s in a league of her own, sannan yace she's a rare gem.
Wani murmushin takaici ya yi sosai yana jango frame din hotan ta da Alhaji da uniform ɗin makaranta, duk a cikin wannan shekarar nan kenan tunda wannan shekarar ta kammala makarantarta. Gata nan yarda take haka take ba abinda ya sauya a tattare da ita. Ko idan Alhaji yana neman soyayyar shi ko wanne irin farin ciki zai ji? To shi yana son ta ne? Ko da baya son ta, ya yi alƙawarin zama da ita ko dan saboda Alhaji. Amma gashi a yanzu Alhajin baya nan sannan ya haɗu da ita. Duk sanda yake da rai, yace masa ya je ya yi mata godiya amma sai yace a'a ba yau ba zai je. Sai da ya rasu sannan ya samu time ɗin zuwa ya ganta?
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miƙe tsaye yana jin kan sa na sara masa sosai. Yau duka be samu hutu ba. Be samu wani isashen bacci ba da zai ce yau ɗin ya yi har ya gaji.
Kwanciya ya yi yana daura akan sa a pillow ƙafarsa a ƙasa ya ji wayar sa yana ƙara. Idan sa rufe ya ɗaga wayar batare da yace komai ba.
"My Trial boyfriend ya ka ke? Ka yi wanka? Ka ci abinci?
"Ohh ni baka san wanne nake yi ba, kafin na yi bacci. Wanka nake fara yi idan anyi Isha. Sannan sai na ci abinci. Sai na yi kallo. Idan na yi kallo sai na yi karatu, idan na yi karatu kuma sai na yi bacci shikenan. Amma idan na tashi a dare ina sake cin abinci".
Ta faɗa tana dariya.
"Kar fa ka ce min na fiye ci. Ko ka ce ci ba ƙi na faɗa maka tohm".
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana cigaba da sauraronta batare da ya bude idan ba.
"Uhm".
"Wani abu ya faru ne? Ko wani ya ɓata maka rai? Na ji ka wani sama-sama. Ohhh sorry be kamata ace na ji ba ko? Tohm. Sai ka yi ta bari ina surutu ko?
"Kina da abin faɗa shi yasa. Ni kuma banda shi".
Dariya sosai alamar tana jin daɗi hirar na su.
Khadijah ce ta yi sallama ta shigo.
"Yaya Mama tana kiran ka".
Ta faɗa tana komawa. Shikuma ya miƙe tsaye yana kashe wayar.
A zaune ya same su, kowa da system a gabansa yana aiki banda su Khadijah da suke kallo. Abba kuma yake danna waya yana lissafi.
"Sannu da gida Mama".
Kallon sa ta yi sannan ta nuna masa kusa da ita ya zo ya zauna.
"Me ya faru kai da Barrister? Bana son wannan abubuwan da ka ke yiwa mutane".
"Bemun ba".
Gaba ɗayan su kallonsa suka yi, ya sake haɗe fuskarsa sosai.
"Bemaka ba?
Maman ta faɗa cike da mamaki sosai.
"Tunda Alhaji yana da rai kawai na ce bana son sa. Mutumin da ya taɓa cin amana ba buƙatar a sake bashi wata damar. Har sai na sake wani Lawyern da kai na".
Murmushi Abbah ya yi a hankali yana kallonsa kafin ya ce.
"Maman Khadijah barshi kawai".
Zata yi magana ya jinjina mata kai. Kafin ya kalla Mufeed ya ce.
"Babana zaka iya tafiya".
Be ce komai ba ya miƙe yana tsuka shi kaɗai. Shifa ba'a takura masa be saba sam.
**********Ƙarfe biyun dare yau ma ta sake kiran shi. Ya kurawa wayar ido yana kin amsawa sai de ya kasa komawa bacci har sai da ta yi masa kira uku a ukunne ya ɗaga.
"Haka ka ke da nauyin bacci?
"Assalamu alaikha. Ina kwana. Ya ka tashi? Idan ba zaka yi addu'a ba. Ka tashi ni ka yi min. Idan kace baka da buƙata. Ni ka min ina da tarin bukatuna".
"Sannan jiya ka kashe min waya. Baka kira ba, sannan baka ce min komai ba. Ban ji dadi ba. Naji ance Mama tana kiran ka. At least sai ka ce min dan Allah yi hakuri ina zuwa. Idan ba sai ka ce min Mama tana kiran ka ba. Ko baka ce komai ba, da ka kashe wayar idan ka dawo sai ka kirani ka ce yi hakuri Mama ce ta kirani".
"Meye a ciki, amma Allah banji dadi ba. Dan Allah kar ka sake ka ji?
Yarda ta faɗa cikin kwantar da murya ba hayaniya ko ɗaya kuma ta faɗa masa eh ya yi laifin, sai ya ji ta burge shi sosai da sosai. Kowaye yake son zaman lafiya zai ji hakan ya yi masa. Gashi de ya yi mata laifi amma ba ta yi fushi ba. Sannan harda take faɗan laifin sam bazaka ce ta yi fushi ba.
"Ki yi haƙuri".
Ya faɗa mata a hankali yana jin kan sa na wani ciwo.
"Na gode. Ka yi haƙuri kai ma idan ka ji haushi".
"Ka tashi to ka yi sallahr ka yi min addu'a dan Allah".
Sai ta kashe. Girgiza kan sa ya yi kawai yana miƙewa daƙyar. Ƙarfe uku ta kira shi.
"Kana jin yunwa?
"Ni yunwa nake ji gani zan haɗa abu. Byeee".
Ta kashe wayar. Girgiza kan sa ya yi kawai yana kallon hotan da ya ɗauko jiya.
"Alhaji ba dan kai ba, da tuni na jima da ajjeta a shara".
Sai ya yi dariya.
"But she's unique".
Ya faɗa tana sakin ƙaramin murmushi......
***********"Ya Ibrahim Allah ya kiyaye. Allah ya dawo min da kai lafiya yasa ka samu wannan aikin".
Ta faɗa tana riƙe masa jakarsa. An kai shi zai hau mota.
"Kasan me? Zan yi kewarka sosai".
Murmushi ya yi kaɗan yana shafa kanta.
"Nima zan yi kewarki".
Sai ta saki dariya kaɗan kafin ta rungume shi. Shima rungumeta ɗin ya yi.
"Dan Allah banda rashin ji. Ki kula da kan ki sosai".
"Na dena. Sai ka dawo zaka kaini na je na yi registration ko?
"Allah ya dawo dani lafiya".
Sake rungume shi ta yi ta ce, "Ameen ya rabb. Allah ya baka sa'a".
"Baka min peck ba, irin abin larabawa kasan fa nuna ƙauna ne ko?
Be kulata ba, haka yasa ta ita ta yi ɗage ta yi masa a kuncinta. Gogewa ya yi ya na jan tsuka.
"Bana san ƙazanta".
Ya faɗa tana harararta. Zumɓura baki ta yi tace.
"Ai de ba kazanta ba ce. Na ga nuna soyayya ce kuma sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ce".
"Zan make ki kike zumɓura min baki".
Jakarsa ta ajje masa tace, "Ga jakar nan kuma sai na faɗawa Daada".
"Ki faɗawa Baban Daada ba Daada ba. Marar hankali kawai".
Bala ya ce, "Kai kuma ka yi ta biyeta bayan ka san waye ce Ummu ko?
"Bana son kayan haushi ne wallahi".
Gefe ta ja ta tsaya tana harararsa ta naɗe hannu sai kumbure kumbure take yi ita kadai.
Bala ya ce, "Ka ga kuke kallonta kafin yanzun nan mu nemata mu rasa, kai kuma ka fasa tafiya".
"Idan ta tafi ma ta dawo".
Munir ya ce, "Iskancine yake damunta, wallahi ba inda zan je. Nemata kuma sai na kama ta na ci ubanta".
Dake ba jin su take ba amma ta san akan ta suke maganar, kawai ta koma cikin mota ta zauna. Duk da haka Bala be rabu da ita ba ya bude kusa da ita ya zauna, dan har ga Allah yana tsoron Allah yana tsoron Allah hali irin na Salma. Sai da suka ga motar Ibrahim ta tafi sannan suma suka tafi. Ta zo za su shiga layin su taga motar Mufeed zai yi new turn shi kuma. Hakan yasa ta bude ƙofa ta fita.
"Ni zan je gidan su Maryam kuma ga saurayina can, zan je mu gaisa".
Ai bama ta kira cewarsu suka ga ta tsallaka titi.
"Da da hali wallahi yarinyar mugun mutuwa zan yi mata, bana san abinda take yi. Ka duba ka gani, yarinyar ƴar firit da ita sai shegen samari?
Dariya sosai Bala ya yi yana kallon Munir.
"Kuna so ku ɗaurawa kan ku damuwa. With time zata dena. Ku rabu da ita, duk wannan abubuwan da take yi watarana aka ce ta yi ba zata yi ba. Kowa da irin ta sa yarintar".
"Mtsww".
Ya ja tsuka shikam.
Bala ya sake cewa, "Idan aka ce ba zata yi ba, to zata ke yi ne a ɓoye. Ka ga gwara a barta ta yi duk abinda take so. Sannan hakan ba zai janyo take ɓoye abinda yake ran ta ba. A wannan stage ɗin aka hanata za'a iya samun matsala. Shi yasa kawai ka barta ta yi".
Taɓe baki kawai ba yi, ba dan be gamsu ɗin da abinda ya faɗa ba sai dan abin da ake kafa musu akan ta ya yi yawa......