Free chapter · Read without an account

Chapter 15

by Asmeetah Writer · WASAN ƘADDARA 1

╔══════════════════════╗
        🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝

_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_

> ✍️ BY ASMEETAH WRITER

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

🌟 Under:

THE SHIDORIA WRITERS TEAM

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 CHAPTER ___29 and 30

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━


Washegari da safe, bayan likitoci sun duba lafiyar Zaitun tare da rubuta mata takardar sallama daga asibiti,

Tun sassafe ɗakin da take ya cika da ƴan uwan mijinta dake ta shirye-shiryen tafiyarta zasu rakata. Kowa fuskarsa na ɗauke da murna da farin cikin ganin ta samu lafiya, amma ita kanta Zaitun, gaba ɗaya zuciyarta ba ta gama samun nutsuwa ba...

 Chief Ahmed Mansur ya mayar da ita babban gidansa domin ta ɗan huta na wasu sa'o'i, kafin daga bisani a shirya komawarta gidan mijinta.

★★

Tana zaune a tsakiyar katafaren falon mahaifinta, sanye da wata tsadaddiyar doguwar atamfa mai launin ruwan madara da ta karɓi fatarta. Hannunta riƙe da kofin shayi dake ta tururi, amma ko ɗigon shayin bai kai ga shiga bakinta ba... Idanunta sun lula cikin zurfin tunani.

Chief ne ya fito daga sashensa, cikin shigar manyan mutane, ya tsaya a saman matakalan falon yana kallon ɗiyar tasa na wasu daƙiƙu, fuskarsa cike da tausayinta, kafin daga bisani ya ƙarasa kusa da ita ya zauna.

"Princess..." ya ƙira sunanta cikin murya mai taushi da sanyaya rai.
Ta ɗago kai a hankali, ta tilasta wa fuskarta fitar da wani murmushi mai cike da raɗadi,  "Daddy..."

Ya kalli kofin shayin hannunta sannan ya dawo da idonsa kan fuskarta, "Me kike tunani haka?"

Ta sauƙe wani numfashi mai nauyin gaske, ta ajiye kofin shayin a hankali a kan teburin gabanta.

 "Daddy... Zan iya tambayarka wani abu?"

Chief ya gyara zamansa, yana fuskantar ta, "Ki tambaya, Princess."

Ta yi shiru na wasu daƙiƙu tana haɗiye wani ɗaci a ranta, sannan ta ce,
 "Daddy... Me yasa duk lokacin da wani abu ya same ni, ko na farin ciki ko na baƙin ciki... Babu wani ɗan uwanmu da yake zuwa?"

Tambayar ta bugi ƙirjin Chief, amma ya daure bai nuna a fuskarsa ba. Ya yi shiru yana sauraron ta.

Zaitun ta ci gaba, muryarta na rawa, "Ranar aurena... Ban ga wani yayanka ba... Ban ga yayyun Mommy ba... Ban ga ƙannenta ba... Babu kowa Daddy." Hawaye masu ɗumi suka cika idanunta, suka shiga zubar mata a kumatu. "Yanzu ma zan koma gidan mijina... Kamata ya yi a ce akwai yayyun Daddy ko na Mommy da za su yi min nasiha, akwai ƴan uwa mata da za su raka ni gidan miji, akwai ƴan uwanmu da za su yi min dariya su taya ni murna..."

Ta girgiza kanta cikin takaici, "Amma ni... Ni kullum kai kaɗai nake gani. Daddy... Wai mu ba mu da kowa ne a duniyar nan?"

Wannan tambayar ta sauƙa kamar kibiyar da aka harba ta daidai saiti, ta ratsa tsakiyar zuciyarsa. Ya runtse idanunsa da ƙarfi na wasu daƙiƙu, yana jin yadda ƙirjinsa yake wani irin zafi...

A take, wasu tsofaffin hotuna na shekaru da dama da suka gabata suka shiga dawo masa daki-daki a ƙwaƙwalwa...
Yana rungume da Zaitun a ƙirjinsa tana ta kuka tana neman mahaifiyarta...
Da hotunan ƴan uwansa.
Da ƙyar ya tilasta wa kansa buɗe idanunsa da suka kaɗa suka yi jawur. Ya kamo hannun Zaitun ya matse a cikin nasa,

 "Zaitun..."

Ta amsa masa tana zubar da hawaye.
"Muna da ƴan uwa..."
 Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, muryarsa ta yi ƙasa-ƙasa, "Amma ƙaddara ce ta raba mu da su tun shekaru masu yawa."

Ta ƙara matsowa kusa da shi, cike da matsanancin fatan ji, "Ba za mu taɓa samun su ba?"

Chief ya haɗiye wani abu da ya tsaya masa a maƙoshi, ya daure ya ce, "In sha Allah... Idan Allah Ya ƙaddara."

Jiki a sanyaye ta kwantar da kanta a kan kafaɗar mahaifinta, tana fitar da numfashi mai zafi, "Daddy..."

"Na'am Princess."

"Wani lokacin ina jin kishin mutanen da suke da yayyu da ƙanne. Ni ban taɓa sanin yadda hakan yake ba." Ta share hawayen fuskarta ta ci gaba, "Ka san abin da ya fi ciwo? Duk lokacin da wani abu ya same ni, sai na ji kamar ni kaɗai ce. A ranar aurena ma, da na ga dangin Arman sun cika gidan suna ta dariya da nasiha, na yi ta kallon ƙofa ina fatan ko zan ga wani ya shigo ya ce, Ni yayan Daddy ki ne, ko Ni ƙanwar Mommy ce. Amma babu kowa Daddy... Sai kai kaɗai."

Kowace guda ɗaya daga cikin kalmomin Zaitun tana ƙara cusa wa Chief kafaffen takobi ne a zuciyarsa,  A hankali ya shafa kanta cikin rarrashi

"Allah Shi ne Mai tsara ƙaddara, Princess...Ki je ki ɗan huta a ɗakinki, zan yi baƙi yanzu..."

Ta ɗago kai ta dube shi, "Ƴan uwan Arman ne za su zo ɗauka na?"

Chief ya girgiza kai, "A'a, abokan aikina ne za su zo, akwai wani ƙaramin meeting da za mu gudanar. Zuwa dare in sha Allah, ni da kaina zan kai ki gidanki."

Murmushin jin daɗi ya subuce mata, ta gamsu da bayanin mahaifinta. Ta tashi ta yi masa sallama, sannan ta nufi matakalar da za ta kai ta upstairs.

Tana shiga cikin ɗakinta, ta tura ƙofarta ta rufe. Kai tsaye ta nufi bangon gaban gadonta, inda hotunan mahaifiyarta suke a manne a jiki.
Ta ƙarasa kusa da babban hoton mahaifiyarta da yake tsakiyar bangon. Hawaye masu ɗumi suka sake kwararo mata a fuska. Ta kai hannunta ta shafi fuskar hoton, tana magana a fili cikin muryar kuka.

"Mommy... I miss you so so so so much..."

Ta tsaya tana kallon fuskar mahaifiyarta na ɗan lokaci, kafin daga bisani ta matsa zuwa kan wani babban hoton daban dake kusa da shi. Hoton ya kasance na Daddy ɗinta ne da Mommy ɗinta a zaune suna farin ciki. A lokacin, Mommy tana ɗauke da ƙanwarta a hannu, wacce a lokacin ba ta wuce ƴar watanni ƙalilan ba a duniya. Ita kuma Zaitun dake ɗan girma, tana zaune a kan cinyar Daddy tana dariya...

Ta zuba wa hoton ƙanwar tata da mahaifiyarta idanu, tana jin yadda kewarsu yake ƙara rurruka a can ƙasan zuciyarta...

"Baby... da ace kina raye da yau muna tare. Allah Ya jikanki ke da Mommy."


Chief ya rage shi kaɗai a cikin katafaren falon. Ya jingina kansa da kujera, yana jin wani irin nauyi a ransa. A hankali ya zaro wayarsa daga aljihunsa, ya shiga gallery.
Yana dubawa, ya tsaya a kan wani kyakkyawan hoton matarsa Sadiya lokacin da ta tafi Makkah... Hoton ya nuna ta tana sanye da fararen kaya, tana yi masa wani murmushi da ya bayyana tsararren haƙorinta na Makkah, wanda ya ƙara fito da asalin kyan fuskarta...

A hankali, muryarsa ta karye, ya furta
"Sadiya... Duk da ban ga gawarki da ta ƙaramar ƴarki ba, amma ina muku fatan samun rahamar Ubangiji... Allah ya muku rahama... Da ke da sauran ahalinmu gaba ɗaya."

Ya sake zubar da wani hawayen, sannan ya matsa zuwa kan wani bidiyo dake ƙasan hoton. Wannan bidiyon shi ne last video call na ƙarshe da suka yi da ita kafin komai ya tarwatse... 

A lokacin ya ɗauki screen record na maganganunsu ne domin yana tunanin zai ajiye shi a matsayin tarihin hidimar auren ahalinsu da ake gudanarwa... Sai gashi tarihin ya zama na rashinsu ne na har abada...

Ya danna bidiyon, nan take sautin muryar Sadiya ya cika falon cikin murmushi da nuna masa mutanen dake gurin.

"Hubby, wallahi ka yi missed da yawa! Kalli yadda ƴan uwa suka zo kowa da kowa amma banda kai... Kalli yadda gurin bikin nan ya tsaru sosai"

A cikin bidiyon, Sadiya tana ta juya kyamarar tana nuna masa harabar babban gidan taron, ta nuna masa Amarya da Ango dake zaune cike da farin ciki, da sauran ƴan uwa kowa yana hidimar gabansa cike da annashuwa.
A lokacin, sautin muryar Chief Ahmed na baya ya fito a bidiyon yana cewa,

 "Kaii Beb, na gaji da kallon mutanen nan haka, ai duk na san su... Yanzu dai ina Ambaby na?"

Sadiya ta gyara goyon dake bayanta, sannan ta nuna masa fuskar wata kyakkyawar ƴar yarinya dake goye, ta ce cikin shagwaba,

"Gata nan, ta ishe ni da kuka shiyasa na goye ta. Kuma ba ta yarda kowa ya ɗauke ta ba tsabar ƙiwa... Uhmmm, gashi na sha kwalliyata amma ta ɓata min ita yanzu da goyo..."

Ahmed ya yi dariya a cikin rikodin ɗin, "Sorry Beb. Tunda Allah ya ba ki dole ki yi rainon kayanki... Ina kuma Baby na?"

Sadiya ta ɗan taɓe baki, "Uhmmm, wannan rigimammiyar ita ma, na tura ta makaranta."

Chief ya zaro ido a cikin bidiyon, "A ranar bikin ahalinsu na musamman za ki tura ta school? Amma ba ki da kirki Beb."

"To, to, to! Da wanne zan ji? Ga wannan ga wancan duk sun sa ni a gaba... Sun hana ni rawar gaban hatsi... Yanzu dai gaya min, yaushe za ka dawo? Gaskiya kana jin daɗin ƙasar Italian nan, wannan aikin naku sai a slow..."

ya amsa mata, "Kar ki damu na kusan dawowa. Daman wata shida za mu yi ai, na yi uku sauran uku... Kin san sojojin nan aikinsu ba wasa..."

Daidai lokacin, aka ji ana ƙiran sunan Sadiya daga nesa. Ta juyo tana kallon kyamarar, "Ka ga Hubby ana ƙirana za mu shiga kitchen..."
Daga nan, bidiyon ya tsinke...

Chief ya runtse idanunsa, zafafan hawaye dake ɗauke da tsantsar baƙin ciki da raɗaɗi suka wanke masa fuska... ya kashe bidiyon a hankali, hannunsa na rawa. Ya jingina kansa da bayan kujera, ya lumshe idanunsa. Hawaye suka ci gaba da gangaro masa ba tare da ya damu da goge su ba...

A hankali ya ɗaga hoton Sadiya dake wayarsa ya sake dubawa.

"Sadiya..." ya furta da ƙyar.
"Na yi iya ƙoƙarina... Amma har yau na kasa cike gurbin da kika bari."

Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ya ci gaba cikin muryar da ta cika da rauni,

"Zaitun ta girma tana neman amsoshin tambayoyin da ban taɓa samun ƙarfin halin ba ta su ba... Ban san ranar da zan iya gaya mata gaskiyar sanadin mutuwarku ba..."

Ya sauƙe wani nauyayyen numfashi.
"Ya Allah... Ka ba ni ikon jure wannan jarabawa..."

★★★


A tsakar gida, Amira tana tsugune a gaban babban baho tana ta faman wanke-wanke.

 Uma kuma tana zaune a kan ƴar kujera ta tsakar gida, ta ajiye faranti a cinyarta tana tsintar tsakuwa a cikin shinkafar da za su dafa na abincin rana.

Uma ta ɗago kai ta kalli Amira, "Ambaby... Yi maza ki je ki ɗebo mana ruwa a can famfon layi mana. Kinga ba mu da ruwa ko kaɗan a gidan nan, ko na sha babu shi yanzu."

Amira ta saki murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana. Ta lura idan dai Uma za ta sanya ta wani aiki na wahala ko na a fita waje, to sai ta ƙira ta da wannan sunan na  Ambaby.
 Amma duk da haka, har can ƙasan ranta tana jin wani irin daɗi da murna idan ta ji sunan ya fito daga bakin mahaifiyar tata..

Amira ta juyo tana kallon Uma cikin zolaya, "Uma... Me yasa kwanan nan kike yawan ce min Ambaby? Kuma ma sai idan za ki sanya ni aiki kike tunawa da sunan."

Uma dake zaune ta ɗan harare ta ta bayanta cikin wasa, "Kawai mafarkin sunan na yi... Sannan naga sunan ya dace da ke sosai. Amma tunda har kin canfe ni cewa sai zan sanya ki aiki nake ƙiranki da shi, shikenan na daina."

Amira ta yi saurin cewa, "A'a Uma, wallahi ina son sunan sosai. Kuma ma gaskiya, ni ma zan canza miki suna, wannan Uma ɗin gaba ɗaya bai dace da ke ba."

Uma ta tsayar da hannunta na tsintar shinkafa, "Iye? Saboda me?"

"Kalle ki fa Uma!" Amira ta ajiye kofin da take wankewa tana nuna mahaifiyarta da hannunta dake ɗauke da kumfa. "Wallahi inda za a ce za ki yi kuɗi ki zama wata Hajiya, ba ƙaramin canzawa za ki yi ba. Kina da kyau, kuma ba ki tsufa ba fa... Wani da zai gan ki a waje, ba zai taɓa cewa ke kika hafe ni ba. Kai, indai kika ci kwalliya kika yafa gyale, wallahi budurwa za a dinga kallon ki."

Uma ta yi dariya mai sauti, "To ƴar iyawa... Wani suna ne to ya dace da ni a lissafinki?"

Ta ɗaga gira tare da faɗin "Mommy... Or Mom"

Uma ta zaro idanuwa da sauri tana kallon Amira, "Ban da ko sisi a ɗakina, amma za a dinga ƙirana da sunan ƴan gayu?"

Amira ta taɓe baki, "Ai kyan fuskarki ne ya baki sunan, Mommy."

Suna cikin wannan hirar, sai ga Malam ya turo ƙofar gidan ya shigo da sauri. Yana takowa yana kwala wa Uma ƙira cikin ɗaga murya,

"Halima!... Halima!!... Halima!!!..."

Uma ta turɓune fuska, ta kalli yadda yake ta rawar ƙafa tace, "Haba Malam, sai kace wanda na yi bulaguro... Idan ka fara ƙira yadda kasan makaho."

Malam ya saki baki yana kallon Uma cikin mamaki, "Zagi na za ki yi Halima? Amma dai kin san uwata ce makahuwar ko?... To dai ba wannan ba."

Uma ta sauƙar da idonta akan ƙafafunsa waɗanda suka yi datti kamar wanda ya shiga kwata, ta ce 
"Meye to ya faru?"

Malam ya canza murya, ya fara washe baki yana sosa ƙeya,

 "Dan Allah aron dubu ɗaya za ki ba ni mana? Wallahi wani Ojatili abu ne ya taso min yanzu-yanzu."

Uma ta watsa masa harara ta gefen ido, "Ni wallahi Malam kana ba ni kunya da irin waɗannan ƙaryar turancin naka... Urgently ake faɗi, ba wani Ojatili ba."

Malam ya dafe ƙirji, "Yo ke ma Halima yaushe kika yi karatun boko har da za ki yi min gyara? Ni dai ba ni kuɗin na tafi, jirana ake yi a waje."

Uma ta kaɗa kai, "Ni ban da shi."

Ya matsa kusa, "Haba dai! Ba za ki rasa ba Halima, binciko min mana a cikin tsofaffin tsumman dake ɗakinki."

Uma ta taɓe baki, "Eh, dake ka ba ni jarin sa'a a baya, shi yasa dole kace na binciko maka kuɗi duk sanda kake so."

Ya juyo ya nuna Amira dake tsugune tana wanke-wanke amma duk hankalinta yana kansu, ya ce, 

"Gata can... Wancan yarinyar mai farar ƙafa! Duk ita ce ta talautar da ni a rayuwa. Amma da a ce ba ita ba, da yanzu na kai ki aikin Hajji Makkah..." Ya ƙarasa maganar yana yi mata wani irin dariyar soyayya...

Ta ce, "To na ce maka ban da shi ɗin"

Malam ya fusata, ya ce, "Allah ya raba mu da babu...Kullum haka kike cewa idan na tambaye ki abu. Haba Halima, yanzu ki dubi irin dukiyar dake manne a jikin haƙorinki, kullum sai tauna shi kike a baki, amma kin bar mu cikin wahala da azabar talauci tsabar mugunta."

Uma ta canza fuska, muryarta a ɗaure ta ce,
 "Malam na sha gaya maka ka cire idonka a kan haƙorin Makkan nan nawa ka ƙi ko? Wallahi babu mai sa na cire shi...Ko ba talauci ba? To ya kashe mu idan zai kashe..."

Malam ya matso gaba ya ce,  "Yanzu don taurin kai ba za ki cire wannan dukiyar a je a siyar ba mu sami kuɗi?"

"Ba zan bayar ba" Inji Uma cikin tsawatarwa...

Malam ya juya baya yana ƙwafa, "To shikenan, ki riƙe tsiyar taki... Ni kaina ban ma san lokacin da kika je Makkah ɗin ba ballantana har kika sanya haƙorin... Tsabar munafurci irin naki, kin samo haƙorin jabu kina yaudarar mu."

Yana gama faɗar haka,  ya shiga ɗakinsa tare da bugo ta..
Uma ta ja tsaki ta girgiza kai, sannan ta juyo kan Amira dake ta faman murmushin kallon wasan kwaikwayon da suka yi.. 

"Ke kuma... Ki tashi kije ki ɗebo mana ruwan da na saka ki"

Amira ta tashi tana goge hannunta a jikin zaninta, ta ce, "To Mommy na..."

Uma ta harare ta tare da faɗin "Mommyn uwarki... Dallah je ki samo min ruwa, ki bar wanke-wanken nan zan zo na ƙarasa da kaina."

Amira ta yi dariya, ta ɗauki babban bokitin roba ta nufi hanyar fita waje. Tana tafiya tana gunguni ƙasa-ƙasa.

"Wai Uma duk sanda mutumin nan ya ɓata miki rai... Sai ki dawo ki huce a kaina..."

Ta tura ƙofar gidan ta fita...
Uma tana nan zaune a kan kujerarta tana ci gaba da tsintar shinkafar, tana tunanin kalaman Amira da kuma tsohon haƙorin Makkah dake manne a bakinta wanda ta kasa gane asalin yaushe ta sanya shi, sai ga wata sallama ta ratsa tsakar gidan.

"Assalamu alaikum..."
Muryar mace ce mai cike da natsuwa da kamala. Uma ta ɗago da sauri ta kalli ƙofar waje. Wata mata ce sanye da tsadadden leshi da babban gyale mai kyan gaske, fuskarta ɗauke da murmushi. Matar Alhaji ce dake babban gida na farkon layinsu.

Murna ta cika Uma, ta ajiye farantin shinkafar gefe guda ta tashi tana maraba, "A'a! Hajiya... Yau kece a gidan namu? Lallai yau gidanmu ya ga babban baƙo."

Hajiya ta shigo tana murmushi, "Wallahi kuwa Halima. Fatan na same ku lafiya."

Da sauri Uma ta shiga ɗaki ta ɗauko wata sabuwar taburma ta shimfiɗa mata a inuwar tsakar gidan, "Bismillah Hajiya, zauna a nan wurin ya fi sanyi."

Bayan Hajiya ta zauna, Uma ta zauna a ƙasa kusa da ita suka shiga gaisawa cikin mutunci. Uma ta gyara zamanta, fuskarta cike da damuwa ta ce, 

"Hajiya, wallahi rannan da abun nan ya faru na gobarar gidan ku, hankalinmu ya tashi sosai. Allah ya kiyaye na gaba, ya mayar muku da mafificin alheri. Kuma aka ce min kun tafi Abuja gaba ɗaya kafin a sake gyara gidan."

Hajiya ta sauƙe numfashi, "Haka ne Halima, abun ya faru babu zato. Kuma lokacin hankalinmu ya tashi da firgicin da muka shiga, shi yasa aka kwashe mu zuwa Abuja. To amma kuma abin da ya fi damuna..."

 Ta buɗe jaka ta ciro wasu damun kuɗi guda biyu na dubu hamsin hamsin sababbi,  "... Haƙƙinki na ladan aikin da kika yi mana a gidan kafin wannan tsautsayi ya faru...kuɗin ki dubu hamsin ne sai na ƙara miki hamsin domin kinyi mana ƙoƙari wallahi..."

Daidai lokacin da Hajiya ta fito da damin kuɗin, sai ga Malam ya turo ƙofar ɗakinsa ya fito saboda jin maganar kuɗi. Yana ganin damin kuɗin a hannun Hajiya, sai kawai ya tsaya cak, idanunsa suka zaro tamkar za su fito waje, baki kuma ya washe har kunne yana leƙen kuɗin ta gefe. Ya ɗan yi taku a hankali ya zo ya raɓe a jikin wata kujerar dake gefe ya zauna yana ji...

Hajiya ta miƙa wa Uma kuɗin tana faɗin, "Halima, wallahi ko da yaushe ina kwana ina tashi da tunanin kuɗinki dake kaina... Ai yau muna dawowa garin nan nace bari na zo da kaina na ba ki hannu da hannu. Kin san mutanenmu na yanzu babu amana, shi yasa ban amince na turo muku da wani ya kawo miki ba, dake kuma na san ba ki da account na banki."

Uma ta kalli kuɗin, sannan ta kalli hannun Hajiya. Wani abu ya motsa mata a rai, amma saboda tsantsar wadatar zuciya da fargabar karɓar abin da ta ji a ranta bai dace ba yanzu, ta girgiza kai tare da tura hannun Hajiya baya a hankali.

"A'a Hajiya... Ba za a yi haka ba. Dan Allah ki bar shi kawai, na yafe muku tun a lokacin. Gobara fa kuka yi, babban rashi kuka yi, ta yaya zan biyo ku ina karɓar kuɗin aiki bayan an shiga cikin wannan ƙunci? A'a wallahi ki bar shi."

Malam dake gefe, jin kalaman Uma ya kusa faɗowa daga kan kujerar da yake zaune. Ya shiga hararar Uma, yana mata ishara da ido da baki cewa ta karɓa, amma Uma ta yi banza da shi.

Hajiya ta ɗaure fuska, "Haba Halima! Me yasa kike magana haka? Wannan ai ladan gumi ne na aikin da kika daɗe kina yi mana kafin gobarar ta afku. Haƙƙinki ne na halal, me yasa ba za ki karɓa ba?"

Uma ta ƙeƙashe ƙasa, "Hajiya na gode ƙwarai, amma dai gaskiya zuciyata ba za ta ba ni ikon cin waɗannan kuɗin ba bayan na san halin da kuka shiga a lokacin. Ki bar shi kawai, Allah ya saka da alheri."

Malam ya kasa daurewa, ganin dukiya tana shirin kuɓuce musu a yau ɗinnan. Ya matso kusa yana shafa gemu, ya dube Hajiya yana wani buɗe haƙora..

"Hajiya, babban barka da dawowa... Ya mai gidan a Abuja?"

 Sannan ya juyo kan Uma cikin faɗa da magiya, "Halima... Ke wace irin mutum ce ne? Yanzu a gaban babban baƙo za ki dinga nuna irin wannan taurin kan naki? Hajiya ta taho da ƙafarta tun daga Abuja don ta sauƙe nauyin dake kanta, ke kuma kina nuna mata rashin kunya na ƙin karɓa?"

Uma ta kalli Malam cikin takaici, "Malam wa ya saka ka a cikin wannan maganar?"

Malam ya haɗe hannaye biyu guri ɗaya yana yi wa Uma magiya a gaban Hajiya, "Halima dan Allah... Dan darajar iyayenki, dan darajar wannan babban rashi da muka daɗe muna yi na talauci, ki mika hannu ki karɓi kuɗin nan! Kar ki sa mu kwana da yunwa yau bayan Allah ya aiko mana da abincinmu har gida."

Hajiya dake zaune ta yi murmushi, ta sake tura wa Uma kuɗin, "Halima, kalli yadda maigidanki yake roƙon ki. Dan Allah kar ki sa na koma gida da nauyinki a kaina. Ki karɓa don Allah."

Duk da magiyar da Malam yake yi har yana kusan zubar da hawaye, da kuma rarrashin da Hajiya take yi... Sam Uma ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi karɓa. Zuciyarta ta ƙi yarda ta karɓi kuɗin, tana ganin kamar cin amana ne da rashin tausayi ga wanda ya yi babban rashi na dukiya a gobarar da ta gabata.

Ganin cewa Uma ta ƙi ba da ƙafa kuma ran Hajiya ya ɓaci idan ta nace za a iya samun matsala, Hajiya ta sauƙe ajiyar zuciya ta mayar da kuɗin cikin jakarta.

Ta tashi tsaye tana murmushi mai cike da mutuntawa, "Lallai Halima kina da wadatar zuciya ta musamman. Allah ya saka miki da alheri, ya bar zumunci."

Uma ta tashi tana yi mata godiya, "Amin amin Hajiya, har za ki tafi? A gaishe da mutanen gidan."

Malam kuwa yana ganin kuɗin sun koma cikin jaka, sai kawai ya dafe kansa ya koma gefe yana sambatu, gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi tamkar an zuba masa ruwan ƙanƙara.
Hajiya ta yi musu sallama ta fita. Uma ta bi bayan ta don ta raka ta har ƙofar gida.

Uma tana dawowa daga rakiyar Hajiya, fuskarta a murtuke ta nufi tsakar gidan. Ba tare da ta ko kalli inda Malam yake zaune yana dukan kafaɗa ba, ta sunkuya ta naɗe tabarman, ta shiga da ita ɗaki ta ajiye ta.
Malam dake zaune yana huci kamar tsohon kurege, ganin Uma ta shiga ɗaki kuma babu kowa a tsakar gidan, ya san idan ya tsaya a nan, ba zai taɓa samun ko sisi na waɗancan kuɗaɗen ba. Cikin zafin nama ya faki idon Uma, ya ranta ana kare ya fice...

Hajiya ta riga ta yi nisa sosai a layin, har tana shirin isa gidan da suke, sai kawai ta ji an biyo bayanta da gudu ana kiranta da sauri-sauri.

"Hajiya!... Hajiya!... Hajiya dan Allah tsaya!..."

Hajiya ta tsaya cak ta juyo cikin mamaki, tana kallon yadda Malam yake ta faman gumi har da tuntube yana isowa gare ta.
Ta ɗan haɗe girar sama da ta ƙasa,

 "Lafiya kuwa, Malam?"

Malam ya washe lalatattun haƙoransa, ya dafe gwiwarsa yana huci, "Lafiya lau Hajiya... Wallahi na zo ne a guje don na sanar miki da wani babban sirri... Na sanar miki cewa, Halima ba ta da lafiya"

Hajiya ta zaro ido, ta dafe ƙirji, "To pah! Na shiga uku, amma me ya same ta? Kuma me yasa ba ta sanar da ni ba?"

Malam ya yi ƙasa da murya, yana dube-dube kamar mai shirin tona asirin ƙasa, "Ai Hajiya, ita kanta ba ta san ainihin me ke damunta ba balle ta sanar miki. Ciwon hauka take fama da shi na. Kwanaki ma haka ciwon ya tashi aka dinga ɗaureta da igiyoyi da kaca, wai za ta fita gari tsirara... Haka muke ta shan wahala dare da rana gurin yi mata magani. Gaba ɗaya ɗan abin hannunmu ya ƙare a gurin neman magani da yawo garuruwa. Yanzu haka ma muna so mu koma gurin wani babban mai magani amma ko sisi babu a hannunmu..."

Hajiya ta cika da matsanancin tausayi da firgici, "Allah sarki! Wayyo Allah, ai ban sani ba ko kaɗan. Ashe abin ya kai haka?"

Malam ya ƙara haɗe fuska yana nuna damuwa, "Wallahi taɓaɓɓiya ce yanzu haka, shi yasa duk sanda za ta yi magana ba a ɗaukar zancenta da gaske. Yanzu kuɗaɗen nan da aka kawo, da a ce ta karɓa, da tuni gobe za mu koma gurin mai maganin nan..."

Hajiya ta gyada kai, "Gaskiya ne kam! Babu damuwa, tunda kai ne mijinta kuma kake jinyarta, bari na baka kuɗin ka kula da ita."

Ta buɗe jakarta ta ciro damin kuɗin dubu ɗari ɗas-ɗas ɗin nan, ta miƙa wa Malam.
Malam ganin kuɗi sun shigo hannunsa, bai san sanda ya zube a ƙasa har ƙasa ba, yana miƙa jera mata godiya kamar zai mata sujjada. "Mungode Hajiya! Allah ya ƙara arziki, Allah ya saka da alheri ya kiyaye hanya!"

Hajiya tace, 
"Allah Ya ba ta lafiya. Da zarar kun dawo zan sake zuwa na gan ta."

ta yi masa sallama ta wuce abun ta cikin damuwa.

Daidai lokacin da Malam yake karɓar kuɗin a hannun Hajiya yana durƙusawa, Amira dake tafe ɗauke da bokitin ruwan da ta samo a famfo ta zo wucewa ta kusa da su.
Ta tsaya cak tana kallon yadda Malam yake ta zazzare idanu yana karɓar kuɗin, sannan kuma ta jiyo ɓangaren kalaman da yake yi wa Hajiya a kan mahaifiyarta. Duk da ba ta ji dukkan zantukan ba saboda nisan da ta ɗan yi da su, amma kalma ɗaya ta fito fili ta daki kunnenta, wato kalmar "...taɓaɓɓiya ce..."

Gaban Amira ya faɗi. Ta gane lallai akwai makirci da yaudara a gurin.
Malam yana karɓar kuɗin, bai tsaya ko kallon Amira ba. Ya karkace hula ya nufi hanyar cikin gari...

Amira ta shiga gida da sauri. Tana shiga tsakar gida, ta iske Uma tana ƙarasa wanke-wanke. Ta ajiye bokitin ruwan da ƙarfi, ta ƙarasa kusa da Uma fuskarta cike da fushi da mamaki..

"Uma... Ke kuwa kin san abin da Baba ya yi yanzu?"

Uma ta ɗago kai tana kallonta, "Meye ya faru kuma?"

Amira ta sa hannu a ƙugum, "Yanzu haka ina tafe a hanya bayan na ɗebo ruwa, na tarar da shi a wurin Hajiyar nan wanda kika yi aiki a gidansu. Yana ta faman yi mata bayani a kanki, ban ji duka maganar ba amma na ji yana ce mata wai ke taɓaɓɓiya ce. Kuma naga sanda ta ciro kuɗaɗen ta ba shi, shi kuma ya karɓa ya durƙusa yana mata godiya. Yanzu haka ma ya nufi hanyar cikin  gari da kuɗin a hannunsa"

Uma ta saki baki tana kallon Amira cikin matsanancin mamaki da takaicin halin irin na Malam. Ranta ya gama ɓaci....

Ganin yadda idanun Amira suka kaɗa sukayi jajur saboda takaicin halin da Malam ya nuna, Uma ta sauƙe numfashi mai nauyi, ta kasa cewa uffan...

Ta kalli mahaifiyarta cikin tsananin son jin ƙarin bayani, "Amma Uma, shin ta zo gidan nan ne?"

Uma ta gyara zamanta, ta fuskanci ɗiyarta tana cewa, "Hajiya ce, matar Alhaji dake can farkon layinmu. Kin san na daɗe ina yi musu aiki a gida kafin gobarar nan ta afku shekarar da ta gabata har muka rabu basu biya ni haƙƙina na kusan dubu hamsin ba. To yau ta dawo daga Abuja ta kawo min kuɗina hannu da hannu. Shine na ce mata na yafe mata, tunda sun tafka babban rashi a baya... Amma ban san Malam zai bi ta a baya ya yi mata wannan ƙaryar ba."

Haushin da Amira take ji ya ninke fiye da na baya... Ta zabura ta zauna a kan gwiwoyinta tana kallon Uma cike da takaici...

"Yanzu Mommy, dan Allah don me zaki ƙi karɓar haƙƙinki? Kalli yanzu abin da ya faru! Da kika ƙi karɓa, ai gashi nan ya zamo rabon wani, Malam ya je ya karɓe... Kuma kinsan muna da tarin matsaloli a gidan nan da suke jiran kuɗi"

Uma ta sunkuyar da kanta tare da faɗin 
"Amira, ai hakan bai dace ba..."

"A'a Uma, ya dace mana" Amira ta katse ta cikin muryar kuka-kuka. "Yanzu idan muka rubata JAMB. Idan Allah ya sa na ci jarrabawar nan kuma na samu scholarship kyauta, shin shopping ɗin da zan yi na tafiya makarantar wa zai yi min shi? Da siyan littattafan karatu, da kuɗin abinci na yau da kullum fa? Ga bani da wasu suturu wasu kyau, balle hijab ko takalmi...Ke kanki kin sani, jami'a akwai kashe kuɗi sosai, ba duka abubuwa ne za a dinga yi miki kyauta ba koda kin sami gurbin karatu kyauta."

Ta goge gefen idonta dake shirin zubar da hawaye, ta ci gaba da cewa,

"Kullum kina cewa mu zauna mu daure da talaucin nan. To gashi yanzu kin daure, amma shi Malam ya je ya kwashe kuɗin da za su rage mana rabin raɗaɗin rayuwarmu, ya tafi abunsa kuma kinsan ba dawowa zai yi da ko sisi ba. Me yasa kullum kike cutar da kanki da ni a kan abubuwan da suke haƙƙinki ne?"

Uma ta kalli Amira, idanunta suka cika da ƙwalla. Ta san duk kalaman da yarinyar take faɗa gaskiya ne, amma tana tsoron karɓar kuɗin da zuciyarta ba ta kwanta da su ba. Ta sa hannu ta dafo kafaɗar Amira tana cewa.

"Ambaby, ki yi haƙuri. Allah yana nan kuma ba zai taɓa barin mu mu lalace ba. Idan karatun naki ya zo, Allah da kansa zai buɗe mana hanyar da ba mu taɓa tunani ba..."

Amira ta kauda kanta gefe guda tana turo baki, tana jin zafin abin da ya faru, amma ƙaddara ta riga fata...

★★★

Bayan sallar isha'i, dare ya tsala sosai a lokacin da Zaitun ta kammala shirye-shiryen ta na komawa gidan mijinta. Chief Ahmed Mansur, wanda shi da kansa ya yi alkawarin kaita, ya shigar da ita cikin tattausar motarsa ta alfarma suka ɗauki hanyar gidan Janar Zarkhan...

Bayan isar su, ba a tsaya a ko'ina ba aka wuce da su zuwa babban falon gidan na alfarma.
A nan, manyan iyayen duka biyu sun hallara domin sasanta wannan saɓani da ya kusa kai auren ga mutuwa...

Janar Zarkhan yana zaune a kan kujera ta alfarma, kusa da shi kuma matarsa Hajiya Mairos ce zaune fuskarta babu yabo babu fallasa. Arman yana zaune a gefe ɗaya cikin shigar ƙananun kaya ta natsuwa, yayin da ita kuma Zaitun take zaune a ƙasa a kan lallausan kafet ɗin falon, kanta a sunkuye cikin ladabi da nadamar abubuwan da suka faru...

Kowa a gurin ya san asalin tushen matsalar. Ba wani katoton abu ne ya raba su ba, illa rashin bincike da kuma zargi na fito-na-fito...

Janar Zarkhan ne ya gyara zamansa, ya dube Zaitun cikin sanyin murya mai cike da kwarjini da faɗa..

"Zaitun... Kin san abin da kika yi ko? Zargi shi ne babban makamin da shaiɗan yake amfani da shi gurin ruguje farin cikin ma'aurata. Kishi ya zama dole a gurin mace, rashinsa ma a jikin mace aibi ne... Amma kishi idan ya tsallake gurbinsa ya koma na hauka da rashin hankali, to zai koma hauka ne wanda zai halaka miki miji da rayuwarki baki ɗaya. Kin biyo yarinyar da ba ta san hawa ba ba ta san sauƙa ba kin ci mutuncinta, wanda hakan zai iya jawo muku abin kunya a idon duniya.."

Janar ya sauƙe numfashi, ya kalli fuskar abokinsa Chief kafin ya dawo da idonsa kan Zaitun,

"Sannan kin san da matsalar dake tare da ke, kina da ciwon zuciya... Me yasa kike barin fushi da zafin kishi yana mamaye miki zuciya? Kula da lafiyarki shi ne abu na farko. Kiyi haƙuri, ki rage zafin rai, kin ji ko?"

Zaitun ta gyada kai a hankali, hawaye ya cika idonta, "Na ji Abbah, zan kiyaye in sha Allah."

Hajiya Mairos ta gyara zamanta, ta kalli Zaitun cikin tattausan murya na natsuwa,

 "Zaitun, zaman aure zaman haƙuri ne. Ki zauna a ɗakin mijinki lafiya, ki zauna da kowa lafiya. Arman mijinki ne, ba abokin gabarki ba ne... Idan kika ga abin da ba ki gamsu da shi ba, tambaya ta dace ki yi masa cikin lallashi, ba wai ki yanke hukunci da kanki cikin fushi ba."

Daga nan, Chief Ahmed Mansur shima ya kalli ɗiyar tasa da ita ce kaɗai farin cikin sauran rayuwarsa. Muryarsa ta yi sanyi sosai,

"Zaitun... Ki dubi maraicin ki, ki dubi yadda kika girma ba tare da dangi a kusa da ke ba. Idan kika lalata gidanki na aure, wa kike da shi bayan ni? Ni kuma yau ina raye, gobe ba na nan... Ki zauna lafiya da kowa, ki riƙe mijinki da amana, ki daina barin fushi yana sanya ki yanke hukuncin gaggawa."

Kalaman mahaifinta sun ratsa ta sosai, ta fashe da kuka a hankali tana roƙon gafararsu.
Daga nan Chief ya juyo gurin Arman, fuskarsa cike da ban haƙuri,

 "Arman... Ina sake baka haƙuri akan duk abubuwan da suka faru. Ka ci gaba da haƙuri da ita, ka san halin nata. Allah ya yi muku albarka."

Arman ya sunkuyar da kai, "Babu komai Daddy, na gode ƙwarai. Zan ci gaba da haƙuri da ita."

Janar Zarkhan ya juyo kan ɗan nasa Arman cikin gargaɗi,  "Kai kuma Arman, ya zama dole ka rage wannan aikin naka da yawan fita... Ka dinga baiwa matarka lokacinka sosai. Ba koda yaushe za a neme ka a gan ka a kan aiki ba, mace tana buƙatar kulawar mijinta a kusa da ita."

Hajiya Mairos dake gefe ta taɓe baki a hankali, ta ɗan harari mijinta Janar ta gefen ido. A ranta tana faɗin,

 'Kaima ai haka kake a da, yaushe kake bawa gidan nan isashen lokaci a baya? Banda yanzu da kayi ritaya a aikin sojan kake da lokacin zama a falo muna gaisawa...' Amma ta daure ba ta fito da maganar fili ba don kada ta ɓata zaman.

Bayan an gama wannan zaman na sulhu, kowa ya fito da kyawawan manufofi a ransa. Chief ya yi musu sallama cikin jin daɗin yadda aka karkare maganar, ya shiga motarsa ya koma gida. Janar da Hajiya Mairos ma suka wuce sashensu don su huta...

Arman ya kalli Zaitun dake ta faman goge hawayenta, ya matsa kusa da ita ya kama hannunta a hankali,

 "Tashi mu tafi ko, my beautiful first lady?"

Ta ɗago ta dube shi da jajayen idanunta, ta gyada kai, tare da sakin murmushin jin daɗi...

Suka juyar da takunsu suka nufi matakalar da za ta kai su babban sashensu na sama, wanda babban gida ne mai zaman kansa cike da alfarma da kyan tsari. Suna shiga ciki, Arman ya tura ƙofar ya rufe, kowannensu yana jin sabon yanayi da kuma kewar juna...


MA SHA ALLAH...

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol