Free chapter · Read without an account

Yar mai gadi Chap8

by Quenneriya · Yar mai gadi

Dady ya shiga falon gidan tara Baba ali don su ci abinci.. direct dining suka huce dan komai is ready !!!
bayan sun gama cin abincin Dady yace bari na kiran mutanan gidan ku gaisa dan nasan gobe da sasafe zaka tafi….
ha haoura sama ya kira bilkisu sanan yace ta leka dakin anifa ta kirata …. Yana fita momy ta buka wani uban tsuki…..« tsusssss»  sai kace Kanin shi sai rawar jiki yake bayan mai gadin gidan yayanshi neh…
ita fah bata son haraka da talakawa dan batasan raini…😏😏😏 fita tayi bah yada ta iya amma bah dan haka bah ita bah abinda ze kaita zuwa gaida mai gadi.. ta leka dakin anifa tace ….kai fito zaku gaisa da mai gadin cen na gidan yaya Usman…. Anifa ta dan bata rai tace Momy mai gadi fah kika ce ????
momy tace ehh koh bah mai gadin bane … 
Hakaneh mai gadi neh cewar anifa … Ni Wallahi momy har banson zuwa gaidashi dan banson ya shafa mana talauci…..😏😏😏
momy tace muje kar dadyn koh ya fara mitar mu jima …
suna isa falon momy ta zawna kusa da dady akan kujera daya … bata gaidashi saima kafa data dawra daya kan daya .. tana kwallon TV a fakaice… Anifa koh gefe cen ta samu ta zawna kan kujera… dady yana jira momy ta fara gaisuwa yaji shuru haka Anifa ma ta gum… abinta a cewar ta ayy shineh zai fara gaidasu…
tsawon 1 daya bah wanda yace komai !!! 
Baba koh ya gwara murya yace hadjia bilkisu inna wuni ya gida ya iyali da fatan mun sameku lafiya …
Momy ta amsa ah takaice tace Lafiya sanan ta mike ta huce sama dan bazata iya wanan kaskantar da kan bah …
Dady ya bita da ido sanan ya kwalli Anifa ya mata wata irin harara… ta dan muskuta tace …
baba ina yuni ya gida ???  sai kuma tayi shuru tace toh baba sai anjima …
itama ta kama gabanta …
Dady duk jikinshi yayi sanyi
koh ba’a fada mishi bah yasan Ali yaji ciwon abun nan ganin yadda fuskarshi ta dan cenza bah kamar yadda suke dazu bah …🫩🫩🫩 
Baba yace bari na kwanta kar na makara gobe insha’allah… ya dan jiyo yace nikam bangan Uzeif bah 🫴 Dady yace ayy shi bah zaka ganshi yanzun bah yana cen tun da yama nayi waya dashi yacemin za’ya kwana gidan abokinshi suyi karatu gobe sunada exam…
Baba yace Alalh ya taikama 🙏 Toh ya wajan Abdul da aikin nashi..??? Ah alhamdulilah 
sukayi salama ya huce ban garan da aka sawkeshi .. yayi alwala ya kwanta yana mike kafafunshi da bayan ah zuciyarshi sai mita ciwon bayan da yaji yake…..
Dady koh yana komawa cikin direct dakin Anifa ya huce ya bulbuleta da fada har saida ta fara kuka 😭😭😭…. sanan ya ja kunanta da karta sake ta kuma abinda tayi yau .. da sam ta tarbiyar kware bace , ya fuce yana tunanin yadda yar tashi take cenza halayan daya santa da su kuma yacen bah kowa ne silar wanan cenjin bah face momy… ta dawki wasu halayan da basu kamata bah ta dawrawa kanta … Rashin son na kasa da ita d yulakanci wanada ada cen bah halayenta bane  … 
Tana dawra ya’yan akai wanda kaff babu daya da suka dawka amma ta riga da taci nasara akan Anifa dn baki daya duk abinda momy keyi yoh anifa copy take kaway!! 
Ya karasa dakin tare da rufo kofar ya tarar da momy na waya da kawarta hadjia salame.. dan yaji tana kiran sunanta lokacin da yake shigowa… kwallan ta kaway bece komai dan yanzu ya daina bata yawun bakinsa akan halayar nan tata…. 
haka ya kwanta ita gashi ba wanda ya nemi dan uwansa dan kowa naji haoushi kowa…




Washe garin Rana bata ma gama fitowa bah bayan sallar asuba …. Baba ya kamo hanyar kano… bayan yin sallama da Alhj Habib !!!
karfe 11h cikin garin Kano tayiwa Baba dan yayi gudu sosai… sauda ya fara euwa kamfani ya aje motar sanan ya huce gida….
Mama na zawne tana zuba kunun aya da tayi a wani jock dan ta kaiwa ina Baba ya shigo da sallam…. Mama tayishi sanun sa zuwa tana ta murmushi da washe hakora sai kace yayi wata daya bata ganshi bata kwana 1 kaway yayi…
suna shiga tace bari na kaii maka ruwan wanka dan tun dazu na dawra na ruwan zafi , bayan ta kai ruwan wanka ta huce ta dawki kunun aya tahu bangaren Inna sai sawri take taje ta dawo ta zubawa Baba abinci dan taga kamar ya dan fada… maybe ma koh kari beyi bah tasan wanan sawri zuwa da yayi be tsaya yin kari bah ..
tayi sallam ta shige falon tace ..Assalamu Alaikum Inna kwana kin tashi lafiya ya karfin jikin ???? Inna tace lafiya lau zara’u ya gidan … nikam gadagan har yanzun be shigo bah san nayi magana dazun da usman yake cemin ya baro abuja !!  
mama tace ayy  Inna shigowarshi kenan gidan … Inna tace Toh Masha’Allah ace ina mishi sanaun da zuwa … mama insha’allah sanan ta aje jock din tace bari na tafi inna toh …
Har mama ta mike sai ta lura da Inna kayan Asiya ne gabanta take likewa harda su pent 👙da brezia saida mama taji yar kuwa 
sanan tayi kamar bataga komai dan bata ma son  ganin …
tana fita ta kudurta ah ranta idan Asiya ta dawo daga school saita maka fada meya sa zata bar inna da  wanan aiki harda wanan kayan kunya tsussss…. tayi tsuki tana shiga falon … 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol