Free chapter · Read without an account

Chapter 50

by Sayyada barrister · BIYU A ƊAYA

BIYU A ƊAYA 


B2 p50
 ~***~
***
Sayyada barrister



Hankalin Dr Waahab ya matukar tashi, bai yi mamakin Mamie za ta ji wannan maganar ba, amma bai yi tunanin za ta ji da wuri ba, kasa magana ya yi yane neman daidaita nutsuwar sa amma ya kasa. Ya sauke numfashi tare da jingina da jikin garun ɗakin ya sudda kai ƙasa, yasan Mamie ba zata taɓa yarda ba sai ya faɗa mata gaskiya, ya yi mata bayani dalla²...

"Babangida tambayar ka nake yi ka yi min shiru, me hakan yake nufi?"

"Mamie Bilqees marainiya ce, haya suke yi a gidan da aka ce suna ciki"

"Aka ce! Ko suna ciki?"

Ya ɗan lashe lamban sa ya share gumin dake gishinsa, duk ya kiɗeme hankalin sa ya tashi, daman Mamie ba son auren take ba yanzu da ta ji haka bai san me za ta ce ba...

"Babangida"

"Na'am Mamie"

"Baka kyauta min ba, kuma baka kyautawa kan ka ba, yanzu wacce baka san asalin ta ba ka auro, ka ƙi amincewa da ƴar'uwar ka ta jini, ka zaɓi wacce ta taso gidan karuwai"

Ya runtse idanunsa sosai yana jin kalmar ta yi masa ɗaci cikin zuciyarsa, da ƙyar ya numfasa ya ce

"Daddy sun je sun ga gidan, wallahi Mamie kamilalliya ce yarinyar, kuma Mamanta ma tana da kirki"

"Yaushe ka zama haka? Wacce irin zuri'a kake so ka haɗa? To ba zai yi na zuba ido naga abin da ka ke yi ba"

Ƙirjinsa ya sananta bugu, hankalin sa ya tashi, waye yake son raba shi da farin cikin sa, Mamie da Bilqees sune rayuwarsa ba zai iya juriyar rasa ko ɗaya daga cikin su ba. Da ƙyar ya numfasa ya ɗago ya kalli Mamie kamar ya yi kuka ya ce

"Mamie ki yi hakuri, duk abin da kike tunani ba zai faru ba, za ki yi alfahari da Bilqees a rayuwa"

"Ban amince ka haɗa zuri'a da ita ba"

Ji ya yi numfashin sa yana neman ɗaukewa, kada Mamie ta raba shi da farin cikin sa, jikinsa ya soma rawa ya ce

"Mamie yarinya ce bata san komai ba, kuma tana da ibada, don Allah kada ki raba mu"

Takaici da baƙin ciki suka cika zuciyar Mamie, ƴar gidan karuwai ce sirkarta wannan wacce irin tarbiyya za ta bai wa jikokin ta, ta ce

"Ga mata waɗan da kuke yan'uwan juna masu asali ka ƙi ka sallake wata uwa duniya ka auro wacce bata da asali, duk ƴan'uwan ka sun zaɓi matan su cikin dangi amma ban da kai, don haka ban yarda da wannan haɗin ba"

Ya runtse idanunsa sosai yana jin ƙirjinsa kamar zai faso ya fito, ya sudda kai ƙasa yana sauke numfashi...

"Kai ɗaya tilo yarona, wanda nake alfahari da shi, nake ganin za ka zama babban mutum ka riƙe ahali guda, amma ka auro wacce take gidan karuwai me kake so a ce damu? Wane irin tarbiyya kake son baiwa ƴaƴanka, don dole su taso da ɗabi'unta"

"Mamie Allah ya ƙaddara Bilqees ita ce matata, ki yi hakuri ki amshe ta za ki yi farin ciki da wannan auren nan gaba"

"Ban amince ba, ba zai yi ka haɗa zuri'a da ita ba, ban amince mu'amalan aure ya shiga sakaninku ba, ba zan yarda a yi wa jikokina gori ba cikin ƴan'uwana"

Kalmar innalillahi wa inna ilaihir rajiun ne ya fita daga bakin Dr Abdulwahab Waseem KIRAWA, ji ya yi duniyar na juyawa da shi, kamar ya yi ihu yake ji ko zai huce, ya yi wa Bilqees alkawarin bata farin ciki na har abada ga shi Mamie za ta zama silar da zai cutar da ita...

"Na gama magana ka tashi ka fice min"

Da ƙyar ya numfasa ya furta 

"Ki yi hakuri Mamie ita...

"Babangida na ce ka tashi ka fice"

Ya mik'e da ƙyar ya fito ya koma ɗakinsa, ya shigo tare da rufe ƙofar, ganin Angel ya yi ta duƙunƙune a ƙasan carpet bacci ya ci ƙarfinta, da ƙyar ya zauna kusa da ita ya kura mata idanu, tana bacci baiwar Allah me ganin jarrabawa iri daban-daban, a wannan shekarunta take ganin rayuwa, ya ɗauko ta ya kawo ta cikin familynsa don ta ji daɗi ta sami farin ciki sai dai kash har yanzu dai gidan jiya. Bilqees tun da Yallaɓai likita ya fice take zaman jiransa duk jikinta a sanyaye za su kwana bed ɗaya da shi, ta kurawa rigar da ke jikinta ido ba ki ɗaya ta ɗame ta, duguwa ce amma ba ta je har ƙasa ba, hannun vest, tana zaune bacci ke neman cin ƙarfinta ya sa ta sauƙo daga kan bed ta kwanta a ƙasa, bacci ya ɗauke ta.

Hannu ya sanya ya ɗauko ta kamar wata ƙaramar yarinya ya kwantar da ita kan bed yana kare mata kallo wani irin sha'awarta ne ke bijiro masa, da sauri ya kawar da idanunsa daga kanta ya janyo marufi ya rufe mata jiki ya yi sauri ya sauƙo daga kan bed zuwa kan kujera dake kusa da table ɗin da yake ɗaura system nasa, ya zauna tare da jingine bayansa ya lumshe idanunsa yana sauke numfashi...

Ta buɗe idanunta a hankali saboda haske da ta gan, idanunta suka sauƙa kan Yallaɓai likita dake sallah, duk da bata san ƙarfe nawa ba amma ta san sallah dare ya ke yi, bacci ya sake ɗaukanta, a lokacin da ta farka sallah asuba ta yi, Yallaɓai likita baya ɗakin, ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta sanya hijabi ta idar da sallah, har ta komai bacci bai dawo ba.

Sai farkawa ta yi taga gari ya yi haske, ta hango Yallaɓai likita yana kwance kan dardumar sallah tana bacci, ta sauƙo a hankali ta shige toilet ta watsa ta duba wardrobe in da ya jera mata kayan ta, ta ɗauko riga da wando na Dubai, ta sanya sun yi mata kyau ta yafe ɗan ƙaramin matafin, ta juyo taga Dr Waahab ya kura mata idanu, jikinta ya yi sanyi bata san har tsawon yaushe ba, a hankali ta tako zuwa kusa da shi ya rage tsawonta ta zauna tare da cewa 

"Ina kwana Yallaɓai likita"

Yana kallon kyakkyawar fuskarta ta matuƙar ba shi tausayi, ya lumshe idanunsa ya buɗe ya miƙa mata hannu alamar ta sanya nata a ciki, a kunya ce ta sanya, ya riƙe sosai ya janyota kusa da shi yana kallon idanunta masu ɗaukar masa hankali, ya shafa gefen fuskarta a hankali ya haɗe goshinsu ya sauke ajiyar zuciya, yana jinta ta ko'ina, yana jin wani sihirtaccen ƙamshi yana tashi a jikinta, da ƙyar ya iya cewa

"Baby nah kin tashi lafiya"

"Lafiya kalau"

Ta ce a hankali, tana jin yadda yake sauke numfashi akai akai, jikinta ya soma rawa, shiru bai sake yin magana ba, ya sanya dukkanin hannayenta a bayansa alamun ta rungume shi, ta yi yadda yake so, jikinsa zafi sosai, hankalinta ya tashi, bata san lokacin da ta ce

"Mon amour baka da lafiya ne?"

Bai bata amsa ba sai da ya ɗauki tsawon lokaci sannan ya ɗago yana kallon fuskarta ganin yadda ƙwayar idanunsa suka sauya zuwa red yasa ƙirjinta ci gaba da bugawa, ta sauke nata idanun, ya sauke numfashi a hankali ya ce

"Ban jin daɗi baby nah"

Ta ɗago suna kallon juna, tana bin fuskarsa da kallo duk ya sauya kamar ba shi ba, ya yi sanyi sosai, a hankali ta furta

"Sannu"

Ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe su sannan ya sake watsa su cikin nata idanun, ya ɗan riƙe haɓarta yana ɗan shafa wa da babban yatsan hannunta ya ce

"Ina son ki baby nah, ina son ki matata, ke tamkar rayuwata ce, ina jinki kamar numfashina, ke ce farin ciki nah"

A hankali ta runtse idanunta, tana sauke numfashi, ya ci gaba da cewa 

"Na yi niyyar ba ki farin ciki, na ba ki kulawa amma na kasa"

Ta buɗe idanunta ta sauke su cikin nasa, bata fahimci inda kalaman suka nufa ba, amma ta fahimci yana cikin damuwa, ta girgiza masa kanta alamun a'a ya ɗan yi murmushi da ƙyar ya ce

"Ki yi hakuri"

"Ka bani farin ciki Mon amour, baka gaza ba ta ko'ina"

Ya rungume sosai kamar ya yi kuka, cikin kunnenta yake raɗa mata

"Kada ki yabe ni, na gaza, ni nasan na gaza"

Ta fashe da kuka a hankali take yi, jin yadda yake yi kamar me kuka, ta ce

"Me yake damunka?"

Bai bata amsa ba sai da ya ɗauki mintin biyar sannan ya ɗago yana share mata hawaye, ya yi magana kamar baya son yi

"Ki bani lokaci, kada ki tambaye ni dalili, za ki fuskanci wasu abubuwan amma bana tashin hankali ba, don Allah ki jure, zan gyara komai"

Ta shafa fuskarsa tana girgiza masa kanta alamun to. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan ya ce

"Na gode, zan fita wajen aiki"

"To me zan shirya maka na abinci"

"A'a bana jin yunwa, tashi mu je na nuna miki kitchen"

Ya tashi, ita ma ta mik'e yana riƙe da hannunta har suka fito, ya kaita kitchen ba nisa sosai da ɗakinsu suka shiga, ya baya mamaki musamman girmansa da abubuwan da suke cikin sa, ba abin da bai ƙunsa ba. Dr Waahab ya riƙe hannunta yana nuna mata wajen suna zagayawa ya buɗe manya manyan frizzer yana nuna mata ɗanyan abubuwan da za ta yi amfani dasu, sai da ta gane kan kitchen ɗin sannan suka dawo ɗakinsa, ya zaunar da ita bakin bed sannan ya shige toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin fararen suit sun yi masa kyau ya ɗaura wrist watch nasa ya sake feshe jikinsa da turare, tana kallon mijinta tamkar balarabe ya juyo suka haɗa idanu tana iya fahimtar damuwar da yake tare da shi, ya ƙaraso ya zauna kusa da ita tana kallon yadda ya yi kyau, ya ce

"Zan wuce wajen aiki, sai yamma zan dawo"

"Allah ya bada sa'a"

"Amin matata, ki kwanta ki yi bacci ki huta kin ji"

"To"

"Me zan kawo miki?"

"Ba komai"

"Ya ɗan janyota jikinsa ya ɗago da haɓarta ya ce

"Ki furta min, ki ce mijina"

Ta yi saurin rufe fuskarta da dukkanin tafikan hannayenta tana murmushi cikin jin kunya, shi ma murmushi ya yi tare da cewa 

"Shikenan tun da ba za ki faɗa min ba"

"Mijina"

Ta ce tana sake rufe fuskart, ya janye hannayenta a hankali ya sauke mata hot kiss a kan kyakkyawan lips nata sannan ya ce

"Take care my princess"

Ya zaunar da ita ya mik'e ya ɗauki side bag nasa da duk wani abin da zai yi amfani da shi a office ya iso gare ta ya riƙe hannunta ta yi masa rakiya har ƙofa sannan ya ce 

"Sai na dawo"

"A dawo lafiya, Allah ya tsare"

"Amin"

Ya wuce, ta rufe ƙofar ta dawo ta kwanta kan bed, jikinta yana bata akwai abin da ke faruwa, tabbas jiya wani abu ya faru bayan kiran Yallaɓai likita da Mamansa ta yi, tana wannan tunanin ne bacci ya ɗauke ta...

Dr Waahab ya wuce parking space ya shige motar sa ya tadata ya ji ana nocking glass ya sauke ganin Daddy ne ya da yana ƙoƙarin fitowa ya ce

"Ba sai ka fito ba, ina zuwa da safe haka"

"Daddy office"

"Ba ka karɓi hutu ba"

Ya sauke numfashi tare da sosa keyarsa ya ce

"Wani abu ne ya taso"

"To in ka dawo sai mu yi magana"

"To Daddy"

Daddy ya shige ciki, Dr wahaab ya tada motar ya fice daga cikin gidan, kai tsaye hospital ya nuna, yana shiga office nasa ya shiga, ya cire rigar suit nasa na sama ya rataya ya dawo kan resting seat ya kwanta yana sauke numfashi, tausayin kansa da na matarsa yake ji, me Mamie ke ƙoƙarin yi ne? Anya zai iya jure komai? An ya zai iya nisantar matarsa, ga shi bai son kowa ya sani, yana wannan tunanin ne bacci me nauyi ya ɗauke shi, ya jima yana yi ya ji ana tashinsa MD ya gani ya tashi ya zauna tare da cewa 

"Morning sir"

"Bacci kuma likita?"

Ya ɗan sosa keyarsa ya ce 

"Daga kwanciya ya ɗauke ni"

"Sabon shiga ba"

Murmushi kawai Dr Waahab ya yi ya tashi su ka yi magana, sannan MD ya fice, Dr Waahab ya sauke numfashi ya janyo ɗan ƙaramin drower dake jikin tebur nasa, ya fiddo da wasu magunguna ya ɓalle su ya sha sannan ya maida ya rufe, a hankali ya furta 

"Ashe ban rabu da shan ku ba"

Ya ɗan yi murmushi kamar wani sabon zaɓaɓɓe, Dr Faisal ya shigo tare da cewa 

"Ango ka sha ƙamshi"

Ya yi murmushi ya ce

"Kai ba ka rabo da zolaya"

"Kut ramuwar bacci ka yi?"

"Dr Faisal main your business"

Dariya Dr Faisal ya yi ya ce

"Na shigo kawai naga motar ka a parking space, na ce hutun ya ƙare ne mutumina ya fito"

"Bai kare ba, kasan su ALAJA suna nan sai sun koma zan ɗauki hutu"

"Dole fah naje mu gaisa, ko yau da daddare ko gebe za mu je ni da Beb"

"Ba damuwa"

Dr Faisal yana ta sokanarsa har ya tafi, Dr Waahab ya ci gaba da wasu ayyukan...

******

Nocking ta ji ana yi cikin bacci ta tashi ta sauƙo ta buɗe ƙofar su Laraba ne suka shigo suka ajiye mata kulolin abinci suka ce in ji ALAJA sannan suka bata hand bag nata, ta duba ta fiddo wayarta ta kunnta sannan ta maida jakar cikin wardrobe ta duba cikin luggage nata hoton ta da Mamanta ta bata ta gani ta sanya shi ƙasan kayanta dake cikin wardrobe ɗin sannan ta dawo ta ce

"Ina kwanan ku"

"Sai yanzu za ki gaishe mu"

Cewar Jummai, Bilqees ta ce

"Ku yi hakuri"

"To mun amsa hira muka zo taya ki"

Kusan wuni tare su kayi, suka sake gyara mata ɗakinta m, abinci matar Alhaji babba ce take aiko musu har zan su shiga kitchen ALAJA ta kirawo su a waya akan su dakata an kawo musu abinci kuma ya yi yawa, sai da Dr Waahab ya kusa dawowa suka koma side nasu, ta yi wanka  light make up ta yi, ta sanya doguwar riga ta yi kyau sosai, sai ƙamshi take yi, bata da turaren wuta ta feshe ɗakin da room freshener da ta gani a ajiye ta zauna zaman jiran mijinta...

Dr Waahab ya dawo kamar yanda yake yi sai da ya wuce side na Mommie ya gaishe ta sannan ya shigo side na Mamie tana cikin toilet ya zauna har ta fito sanye da hijabi wanka ta yi, cike da girmamawa ya ce

"Mamie ina wuni?'

"Lafiya Babangida ka dawo?"

"Eh Mamie"

"To ya yi kyau"

"Na gode"

Ba ta sake cewa komai ba, yana shafa mai ya sudda kai ƙasa shiru yana kallon carpet, ta juyo ta kalle shi tare da cewa 

"Da wani abu ne?"

"A'a"

Ya ce ya mik'e ya fito, side na Ammie ya shiga, tana zaune a palour ita da Ashfat shigowar ta kenan daga wajen aiki, ya rage tsawonsa tare da cewa 

"Barka da yammaci Ammie"

"Barka likita ya aiki"

"Alhamdulillah"

"Ya Wahaab ina wuni"

Ya ɗan kalli inda take ya amsa da 

"Lafiya Ashfat"

Ta kura masa ido taga yadda ya ƙara kyau dai sheƙi yake yi, a hankali ta ce 

"Ya aiki?"

"Da godiya"

"Ammie zan shige ciki"

"To a huta gajiya"

Bai ji daɗi ba daga ita har Ammie basu tambaye shi Amaryarsa ba, ya fito. Ashfat ta sauke numfashi ta mik'e ta shige cike, Ammie ta girgiza kanta, Dr Waahab ɗan Albarka ne duk cikin matasan gidan babu me zuwa gaishe ta safe da yamma kamar ibada sai shi, in kuma ya ji bata da lafiya ya yi ta ɓakin ƙoƙarin sa ya ga ta samu lafiya. Yaro me ladabi da biyayya tabbas dole ta ji baƙin cikin rasa shi a matsayin sirki...

Dr Waahab ya shigo ɗakinsa da sallama, Bilqees dake zaune ta amsa ta tashi ta karɓi side baga nasa tare da cewa 

"Sannu da zuwa"

Murmushin farin ciki ya yi ya ce 

"To ai ba haka ake tarɓan miji ba"

Ta rataye side bad nasa tana murmushi ta ce

"Ya ake yi"

"Zo na nuna miki"

Ta matso ya nuna mata ƙuncinta ya ce

"Sumbace ni anan"

Ta ware fararen idanunta ta ce

"Yallaɓai"

Tana murmushi ya ce

"Sai gobe"

"Yau dai"

Ta sudda kanta ƙasa ya riƙe hannunta ya rungumeta ya ce

"To ko runguma ai na samu"

Ta yi murmushi ta sanya fuskar ta a ƙirjinsa ya sha bayanta ya ce

"Ina wayar ki?"

"Yana nan"

"Shi ne ba ki neme ni ba"

"Zan neme ka gobe"

Ya ɗago da fuskarta ya ce

"Tom me aka girka min"

"Ban yi abinci ba aikowa aka yi"

Ya bata leda dake hannunsa, ta ajiye side bag ɗin sannan ta ajiye leda, ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya sun yi masa kyau, bai ci abinci sosai ba iya abubuwan da ya sayo kawai ya ci sannan ya fice sallah magriba bai shigo ba sai kusan 9:00 pm, bacci ya ɗauke ta ya iso kusa da bed ya kura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskar ta tausayi take ba shi, ya rufe mata jiki ya dawo kan carpet ya kwanta, ya sauke numfashi a hankali yana jin yanayinsa yana sauya wa, ya miƙe ya ɗauko side bag nasa ya fiddo maganinsa ya ɓalle ya zuba a baki ya kora da ruwa ya koma ya kwanta yana jin yana samun nutsuwa, ya ji muryar Ange 

"Yallaɓai likita"

A hankali ya buɗe ido ya kalleta, tana zaune kusa da shi, ya ɗan tashi ya kishingiɗe tare da cewa 

"Kin tashi?"

"Ka koma kan bed ni zan kwanta anan"

"Ba damuwa ki kwanta

"A'a bai dace ka kwanta a ƙasa ba"

Ya ɗan ja numfashi ya sauke, ya tashi ya zauna ya riƙe hannunta yana kallon cikin ƙwayar idanunta ta deep light ya ce

"Bana jin daɗi ne"

"Na sani, kwanciya a ƙasa zai sanya ka ciwon jiki"

Bai so ta shiga cikin damuwa, ya mik'e ya koma bakin bed ya zauna yaga ta kwanta a inda ya tashi, kamar ya yi hawaye, ta ba shi tausayi, ya ce

"Ta shi ki zo"

Jikinta ya yi sanyi ta kasa tashi, sai da ya maimaita, sannan ta taso a hankali ta iso bakin bed ya ce

"Ki kwanta"

Ta kwanta tare da duƙunƙune jikinta, ta ji ta a takure, first time ta kwanta bed ɗaya da na miji, ganin taƙi sakin jiki yasa ya kwanta ya juya mata baya.....



______________________

Wasa ma da wasanta ban da zagin uwar miji😁


Ayi hakuri da typing errors 


Comments and share fisabilillah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol