Free chapter · Read without an account
Chapter 13
INUWAR JIYA
Ummulkhair S Panisau
(KHAIRATUP)
MERIDIAN POST
SASHEN RAHOTANNI.
Tun ƙarfe takwas na safe Rania ta iso Ofis sai dai tun zuwan ta bata aikata komai ba har ƙarfe sha ɗaya na safe. Bata yi rabin aikin da ta saba yi ba. Ta zauna a gaban computerta, tana kallon rubutun da ke kan screen ɗin,sai ta ga kamar kalmomin suna mata rawa a ido.
Ta ɗauki shayin da ta saka peon ya kawo mata ta samu ta ɗan gasa cikinta. Ta kai bakinta kuma sai ta ajiye bata iya sha ba. Abinda ya faru jiya ya dawo mata. Tun biyan take ƙoƙarin kawar da tunanin abin da ya faru, amma duk lokacin da ta lumshe idanunta,sai ta ga lokacin da hannun Sajjid ya sauka a kan fuskarta yana mata izaya amma bata taɓa jin zafin irin marin da ya yi mata ba.
Ba iya zafin marin ne ya dame ta ba illa abin da ya karya mata zuciya shi ne mutumin da ya aikata mata hakan wai miji ne a gare ta,abokin rayuwa. Ta girgiza kai haɗe da komawa kan aikinta.
"Rania,za ki shigo meeting ɗin amma?"
Muryar abokiyar aikinta ga katse mata tunanin.
Ta ɗago kai tace da ita "Eh, am coming." Ta ɗauki littafinta da alƙalaminta ta bi bayanta zuwa ɗakin da aka tanada don taro(meeting).
Taron ya fara ne da nazarin rahotannin da za a fitar a wanann makon. Shugaban sashen ya yi bayani a kan wasu muhimman batutuwa,sannan ya bayar da dama don jin ra'ayoyin ma'aikata.
Rania da ke zaune a ɗakin taron ta kurdawa wuri guda ido hasalima hankalinta baya kan taron da abinda aka tattauna a kai. Hankalinta ya yi nisa.
Ogan ya buga tebur yace "Rania,me kike gani game da wanan rahoton?'
Ta ɗago a firgice tace "I'm sorry ,sir. Zaka iya maimaitawa?"
Shugaban ya sake maimaita tambayar. Ta yi ƙoƙarin ba da amsa,amma ta kasa tsara maganganunta yadda ya kamata. Ta rikice a kan wani abu da a da ne ba zai ɗaukar mata mintuna biyu ba ta gama da shi.
Bayan wasu mintuna ta sake yin shiru, tana kallon littafin da ke gabanta. Shugaba sashen ya lura da yanayin ta. Ya rufe file ɗin da ke gabansa,sannan ya kalleta yace "Rania,lafiyar ki ƙalau kuwa?"
"Eh Yallaɓai."
"Kin tabbata? Saboda tunda aka shigo baki ba da wata kwakwarar amsa ko shawara ba, that's unusual for you."
Ta haɗiye yawu.
"Kawai na gaji ne kaɗan sir." Ya ɗan yi shiru kafin ya amsa.
"In haka ne gaskiya na baki hutu ki tashi ki tafi gida za mu ƙarasa naki rahoton gobe."
"Amma Yallaɓai zan i..."
"Lafiyar ki ita ce a gaba,Rania. Ki je ki huta."
Ta gyaɗa kai tace "Thank you sir."
Ta tattara kayanta,ta fita daga ɗakin taron..Da ta koma kan teburinta sai ta ɗauki wayarta domin ta kira motar haya don bata fita da mota ba saboda sauri da ɓacin rai kuma bata son ta gan shi.
Kan tayi wayar sai ta ga sakonnin Sajid rututu. Ta saki tsaki ta soma dubawa.
"Kina ina?"
"Me yasa ba kya ɗaga wayata Babe?"
"At least tell me if you are okay."
Ta kalli saƙonin na ɗan lokaci sai kuma tayi tsaki ya kashe a fili tace"Kamar gaske mtss."
A maimakon ya bata haƙuri ya nuna mata ya yi nadamar abin da ya yi mata ba jiya,shi abinda ya dame shi kawai bata amsa kiran shi ba. Ta ɗauki jakarta ta tashi. Yau bata da lokacin Sajjid ko zantukansa. Daddy kawai take jira.
Tana waje kiran Daddy ya shigo wayarta.
"Salamu alaikum ,Daddy."
"Wa alaikum salam Baby."
Sai ta ji wani rauni a muryarta a hankali tace "Ya kake Daddy?"
"Lafiya lau. Baby ki saurare ni, Ina son na baki haƙuri.Ban samu Flight ba yau."
Sai ya ɗaure fuska.
"Baka samu jirgi ba Daddy?"
"Eh na yi ƙoƙarin na ga na samu amma ban samu na amma gobe in sha Allah zan zo tare da Auntyn ki."
Ta sauke ajiyar zuciya tace "Me yasa zaka zo da wanann matar?"
"Rania."
"Fine am sorry..Allah Ya kaimu goben,ai kamar yau ne ga mai yawan rai."
"Haka ne. Kina ina yanzu?"
"Ina gun aiki amma na gaji na kasa mai da hankali an bani leave na yau na je na huta ina waje."
"To ki tafi gida ki huta..Kar kiyi aiki da yawa sai goben idan Allah Ya kaimu."
"In sha Allah Daddy."
"Rania."
"Na'am Daddy?"
"Duk abinda ya faru,ki tuna za ki iya yin magana da ni Ina tare da ke."
Hawaye ya cika mata ido amma tana ƙoƙarin danne su.
"Na sani Daddy."
"Ina son ki yata."
"I love you to Daddy."
*
Sajjid kuwa ya kalli wayar sa ya fi kuɗin a ƙirga. Yana zaune a ofis ɗin sa. Ya sake duba sakwanin da ya aikawa Rania amma babu amsa. Ya kirata sau biyu amma bata ɗaga kiran shi ba. Ya ajiye wayar ya shafa goshinsa ya jingina da kujerar,ya shafa goshinsa. Tun safe yake ƙoƙarin samun damar yin magana da ita,amma duk ƙoƙarinsa ya ci tura. Ya san ta yi fushi da shi,ya san ta ji ciwon abinda ya mata jiya amma bai yi tunanin za ta iya rufe mai ƙofa ba har ta iya fita bata kula shi ba kuma ta ƙi daukar kiransa ba.
Ya sake buɗe chat ɗinsu ya kalla ya sake tura mata da saƙo.
"Rania, can we talk please?"
Bai tura ba ya sake karantawa sai kuma ya goge shi. Ya sake rubutawa.
"Ki yi haƙuri akan abinda ya faru jiya."
Wanann karon ma ya kasa danna send kawai sai ya ajiye wayar ya saki tsaki ya rufe idanunsa.
A jiya lokacin da ya ɗauki ɗumi ya yi fushi, bai tsaya ya yi tunanin abin da hannunsa zai iya yi wa zuciyar matarsa ba. Yanzu kuma yana son ta ba shi kulawar da ya saba samu kamar dai babu abinda ya hada su. Amma Rania ta fara janye kanta daga gare shi. Ya ja numfashi ya fesar ya kuma gane cewa akwai banbanci tsakanin mayar da ta yi fushi da shi da kuma matar da ta fara jin tsoron sake yarda da shi. Ya zari wayar kamar wani zarare ya sake aika mata da saƙo.
"Babe, I know I hurt you. I'm sorry." Wanann karon ya danna send saƙon ya tafi.
Bata isa gida ba saƙon ya shigo mata ta duba amma bata ce komai ba ta kashe screen ɗin kawai ba don bata ga saƙon ba sai don kawai zuciyarta bata shirya sauraren shi ba."
Kuma a gobe take son ta fayyacewa Daddy abinda yake faruwa a gidan aurenta shin za ta iya ci gaba da zama da shi ko zata tafi tare da Daddy?
*
Da ta koma gida,Rania ta ajiye jakarta da mayafi akan kujera, ta shiga bedroom ta canza kaya,sannan ta fito don ta gyara dakin da ta bari da safe. Ta share ko ina a falo ta yi moooing,ta tattare wasu takardu da suka watse a kan kujera,sannan ta shiga kitchen. Duk da irin damuwar da ke cikin zuciyarta, ba ta yi tunanin kin yin komai ba. Ta shiga kitchen ta fito daga nama daga cikin fridge,ta wanke shi,ta ɗora tukuna a kan wuta. Ta yi miyar da Sajjid yake so, ta dafa shinkafa,sannan ta shirya komai a tsari. Ba don tana son faranta masa rai ba. Ta yi hakan ne saboda ita ce ta saba da kula da gidanta, kuma ba ta son abin da ya faru tsakaninsu ya sa ta daina gudanar da rayuwarta. Bayan ta gama girkin ta zuba abincin a cikin warmer,ta ajiye plate ɗin Sajjid a kan dinning table,tare da ruwa mai sanyi. Ta duba agogo karfe biyar da rabi. Ta san Sajjid zai dawo nan da awa ɗaya ko fiye da awa ɗaya. Ta ɗauki littafin da ta saba karantawa,ta koma falo ta zauna ta ɗauki littafin da ta saba karantawa,ta koma falo ta zauna. Amma shafukan littafin ba sa shiga kanta.
Jim kadan ta ji ƙarar buɗe ƙofa ko ba a faɗa ba ta san waye. Minti biyu tsakani ya shigo ciki da sallama. Don sallama ne shi yasa ta amsa masa. Hannunsa riƙe da jakar aikinsa. Ya rufe ƙofar, ya ajiye takalmansa,sannan ya juya ya kalle ta a tsakar falon.
Idanunsa suka sauka a kanta.
"Rania."
Ta ji muryarsa,amma ba ta amsa masa ba. Ta ɗauki wayarta ta ci gaba da kallonta. Ta tsaya na ɗan lokaci ta yi shiru.
"Barka da yamma." Ta faɗa tana kallon wayarta ba tare da ta kalli inda yake ba.
Sajjid ya sauke ajiyar zuciya. Ya san tana fushi da shi,amma ganin yadda take nuna masa kamar ba ya wurin ya fi daga masa hankali. Ya cire rigar jikin shi ya ajiye kan kujera daga shi sai singlet.
"Yaya kike?"
Ta masa banza.
"Rania ,magana nake yi miki."
Ta ɗago kai a hankali,ta lalle shi na ɗan sakanni,sannan ta mayar da idanunta kan wayarta.
"Na ji ka."
Ya ɗan daure fuska.
"Amma me yasa ba zaki iya amsa min ba?"
Ta ajiye wayar akan cinyarta.
"Me kake so na ce maka,Sajjid?"
Tambayar ta fito cikin sanyin murya,irin sanyin nan na karantarwa wanda zai saka ka ji shakku a amsawa. Ya matsa kusa da ita.
"Kawai so nake yi muyi magana ni da ke."
"Na gaji."
"To, za mu iya magana bayan kin huta?"
Ta kalle shi. "Ba na son magana yanzu."
Ya gyaɗa kai a hankali,yana ƙoƙarin danne rashin jin daɗin da ya fara bayyana a kan fuskarsa.
"Fine."
Ya miƙe tsaye,ya nufi bedroom.Amma kafin ya shiga ,ya sake juyowa yace "Kin ci abinci?"
"Ban ci ba."
"Kin yi girki?"
Ta nuna masa dinning area da ka. Sannan tace "Abincin ka na kan tebur."
Ya bi wajen da kallo.Sai a lokacin ya ƙura da yadda aka shirya masa abinci. Shinkafa ce da miyar ganye da nama a ciki sai ruwa mai sanyi a gefe. Da cokali da komai duk an adana masa.
Ya kalli Rania,sannan ya sake kallon abincin.
"Da gaske ni kika girkawa?"
Ta tashi tsaye tace "Abinci na gida ne,Sajjid ba sai na sanar da kai zan yi girki ba."
Maganar ta zo mai a yadda bai zata ba.
Inda da ne yadda ya dawo ɗin nan zata amshi jakar sa,za ta tambaye shi yadda ranar ya kasance masa a gun aiki,wani lokacin ma tana ba shi labarai musamman na abubuwan da ta yi ,yanzu kuma abincin da ya saba gani a matsayin wani ɓangare na soyayyar su ya zama kamar wani aiki da take yi ba tare da shi a zuciyarta ba. Ya koma da baya kusa da ita.
"Rania don Allah."
Ta ɗaga idanunta "Don Allah me?"
Ya haɗiyi yawu.
"Don't do this to me."
Ta yi murmuashi mara daɗi.
"Do what,Sajjid?"
"Act like a stranger in my own house."
Ta lalle shi sosai wanann karon. "ka tuna da ni a matsayin matarka lokacin da ka ɗaga hannu ka mare ni?"
Maganar ta dake shi sai ya yi shiru. Rania ta kawar da kanta ta ɗauki wayar ta.
"Please,let me rest."
Sajjid ya tsaya yana kallonta. Ya so ya ce wani abu, ya so ya kare kansa,amma bai samu kalmar da za ta iya share abin da ya faru ba. A ƙarshe ya nufi dinning table ya zauna.
Ya ɗauki cokali,amma bai fara cin abincin nan take ba.
Ya kalli kujerar da Rania take zama idan sun cin abinci tare. Ya tuna yadda take yawan ba shi labarin abubuwan da suka faru a wurin aikinta,yadda take dariya idan yana mata wasa,da yadda take yi masa faɗa idan ya manta bai sha maganinsa ba lokacin da yake rashin lafiya. Yanzu komai ya yi shiru. Ya fara cin abincin a hankali.Daɗin miyar ya yi daidai da yadda ta saba yi masa.
Ta yi masa girki,ta shirya masa komai ta bar masa abincinsa a kan tebur sai dai ta cire kanta daga cikin rayuwarsa duk sai gidan ya masa duhu.
Bayan ya gama cin abincin ya tattara plate ɗin da ya ci abincin ya kai kitchen ya dawo falo ya tarar ta fito tana duba wasu takardu. Ya zauna a kusa da ita,wanann karon ya ɗan bada tazara a tsakaninsu.
"Rania don Allah ki kalle ni."
Ta cigaba da duba takardunta, tace "Ina ji."
"Bana son ki ci gaba da yi min irin wanann hukuncin."
Ta ajiye takardun a kan cinyarta,ta juya ta kalle shi.
"Kamar yaya?"
"Kamar yadda kike nuna min halin ko ina kula."
Ta ɗan yi shiru,sannan ga tambaye shi cikin sanyin murya.
"Me kake tsammanin zan yi Sajjid? In rungume ka? In yi maka murmushi? In tambaye ka yadda aiki ka ga kasance? In yi kamar ba ka taɓa marina ba?"
Ya sunkuyar da kansa.
"Ba haka nake nufi ba."
"To me kake nema?"
Ya ɗaga kai ,idanunsa cikin nata yace "Mata ta nake so ta dawo yadda take."
Rania ta ji wani abu ya caki zuciyrta.
"Your wife back? Kamar wife ɗin ce ta tafi,kamar ita ce ta maka komai? Kamar ita ce ta sauya komai? Am still hare Sajjid,ina gidan ka, na maka abinci,na bar maka komai a shirye har ruwan wanka,amma abinda ka yi min ya canja yadda nake ji a kan ka,ba zan iya mantawa ba saboda ka dawo gida kana son muyi magana."
Ya yi ƙoƙarin kama hannunta,amma ta janye nata a hankali. Wannan janye hannun ya sa ya tsaya cak. Ta lura da yadda fuskarsa ta sauya,amma ba ta nemi ta lallashe shi ba.
"Please ,Sajjid. I need some space."
Ta gyaɗa kai a hankali,duk da cewa a fili yake bai ji daɗin haka ba.
"Okay." Ya miƙe ya nufi bedroom. Rania ta koma kan takardunta,amma da ta ji ƙofar ɗakin ta rufe,sai ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Ba ta ji daɗin yadda komai ya kasance ba amma dole ne ta nuna masa ta san wacece ita.
A cikin bedroom,Sajjid ya zauna a gefen gado,ya cire agogonsa ya ajiye a kan bedside table.Ya ɗauki wayarsa ya shiga kallon hoton Rania wanda ya fi so.Hoton da suka ɗauka a wajen wani biki,lokacin da ta jingina da kan shi tana murmushi ,shi kuma yana kallonta kamar ita kadai ce a wurin. Ya daɗe yana kallon hoton. A da ,baya buƙatar roƙon matarsa ta kula shi,kulawar tana zuwa ne da kanta,cikin ƙauna da farinciki.Yanzu kuma duk da suna ƙarƙashin rufin gida ɗaya,ya ji kamar akwai wani bango da ya raba su. Ya rufe idanunsa,ya dafe goshinsa.
"Rania, what have I done?"
Tambayar ta fito a hankali. Sai dai babu mai amsa masa wannan tambayar.
Daga falo ya ji wayar ta na kara kuma ta ɗauki kiran sai dai bai san me take cewa ba saboda a hankali take magana sai ya ji wani abu kamar kishi kamar nadama kamar kuma tsoron rasa abin da ya saba ɗauka a matsayin tabbataccen abu. Bai san takamaiman abinda yake ji ba. Abin da ya sani kawai shi ne,shirun Rania yana damunsa fiye da duk wata gardama da ta saba yi masa. Amma wannan karon dole ne ya fuskanci gaskiyar cewa ba zai iya tilasta mata ta sake yarda da shi ba.
Idan yana son ya gyara aurensa,dole ne ya fara da amincewa da abin da ya yi, ya nemi afuwa ba tare da kawo wani uzuri ba,sannan ya nuna sauyi ta hanyar ayyukansa. Saboda ya lura Rania ba ya buƙatar kalmomi masu daɗi kawai,tana buƙatar ta sake jin cewa ta amince da mijinta. Kuma wanann amincewar ba za ta dawo a dare daya ba.
Har ta kai ƙofa sai wata zuciyar ta hane ta kuma da fita sai ta sauya akalar tafiyarta zuwa cikin kitchen kafin ta shiga ta ajiye jakarta da mayafi a kan kujera, ta zare takalmin ta sannan ta cire takalmin ta ta saka na shiga kitchen. Ta dafa tea ta zuba a tea flask,ta kuma soya wainar kwai ta jera masa a kan tebur. Ta sake shiryawa zata fita kuma sai ga shi ya fito ya ga kam tebur yace da ita "Ba za ki tsaya ki ci abincin ba?"
"Zan ci a ofis."
"Me yasa kike yi min haka Rania. Still kina yi min duk waɗanan abubuwan bayan ba kya magana da ni."
"Saboda ina son in gudanar da rayuwata yadda na saba. Ba ina yin waɗanan abubuwan ne don na nuna maka cewa komai ya wuce ba."
Ta saɓa jaka tayi gaba ya sake tare ta yace "Rania Please tell me what I can do to make this right?"
Ta tsaya amma bata juya ba.
"Ka fara fahimtar cewa abin da ya faru ba ƙaramin abu ba ne ya fi min sauran abubuwan da kake yi min ciwo a da baka taɓa mari na wannan kuma shi ne ya fi zafi. Kuma don Allah ka ƙayale ni ka bar ni na samu lokacin da nake bukata." Ta juya ta fice bai yi ƙoƙarin hana ta fita ba.
*
Ƙarfe takwas daidai ta isa ofis. Ta yi ƙokarin mayar da hankalinta kan aikinta. Ta buɗe computer,ta duba rahotannin da take da su,sannan ta fara gyara wani rubutu ta aika wa editan jaridar.
A yau,tana son ta shagaltu sosai har ba za ta samu lokacin tunanin abin da ke faruwa a gidanta ba. Can kuma saƙo ya shigo wayarta saƙon an Sajjid ne ta buɗe ta karanta.
"Have you arrived safely?" Ta karanta sai kuma ta ajiye wayar.
Bayan mintuna goma wani saƙon ya sake shigowa.
"Please Rania,let me know when you get this."
Ta sauke ajiyar zuciya,ta koma kan aikinta. Ba a jima ba ya sake kira amma har ta gama ringing ta katse bata ɗaga ba. Da ya gaji ma sai ta aika masa da saƙo.
"Please Sajjid aiki fa nake yi."
A ɗaya bangaren Sajjid yana zaune a ofishin sa hana kallon wayarsa. Ya san tana cikin aiki amma yana son ya wanke kansa ne. Shi fa wanann shirun ya sa ya fara tunanin ko dai ta yanke zama da shi ne? Ya karanta sakon ta wai aiki take ya ji babu daɗi da ya ga ba zai iya ba ma kawai sai ya sake aika mata da saƙo.
"I know I can't force you to talk to me. Ina son kawai ki sani cewa ina mai nadamar abin da na aikata miki. I won't make excuses for what I did."
Ta ga saƙon kuma ta karanta. Ba ta ba shi amsa ba amma kalmomin sun sa ta shiga tunani. Ba ta san ko nadamarsa za ta kai ga sauyi na gaske ba. Ba ta san ko zai sake fusata wata rana ya maimaita abin da ya yi ba. Abin da ta sani shi ne,ba za ta iya yanke shawara bisa kaloli kawai ba. Ta ajiye wayar ta sake dake zuciyrta ta koma kan aikinta.
Da yamma,bayan ta dawo gida,ta tarar da Sajjid ya riga ta dawowa. Ta shiga ciki ta ajiye jakarta da takalmanta.
"Sannu da zuwa." Ya faɗa a hankali.
"Thank you."
Ta wuce shi zuwa ɗakinta.
Sajjid ya miƙe tsaye,amma bai bi ta ba ya tuna ta gaya masa ya bata sarari. Ba ta jima ba ta sake fitowa ya nufi kitchen. Ta fara shirya abincin dare tana sa ran a daren Daddy zai iso duk da bai kirata ba har lokacin. Ya zauna saitin kitchen ɗin yana kallon shige da ficen ta.
Da bata fushi da shi shiga zai yi ciki ya taya ta tana yi yana tsokanarta, yana ɗanɗanawa ko ya yanka mata veggies ita kuma tana masa faɗa cikin wasa.
Yanzu gidan ya zame masa kamar kango, ba tsokana,ba dariya,sai shiru kawai. Ya kasa jurewa ya tashi ya shiga cikin kitchen ɗin yace "Can I help you?"
"A'a am fine."
"Rania ba fa sai kin yi ke kaɗai ba."
Ta cigaba da yanka kayan lambu. Tace da shi "Na saba."
Ya tsaya a wurin na ɗan lokaci.
"Don Allah Rania, don't shut me out completely."
Ta ajiye wuƙar ta juyo ta kalle shi.
"I'm not shutting you out to punish you,Sajjid. I'm trying to understand how I feel about what happened."
Ya yi shiru ta cigaba da magana.
"Ko yaushe na tuna ina jin haushi. Kuma ka zo kana damuna dole sai na kula ka, I feel like I'm supposed to make you feel better about something that hurt me."
Sajjid ya sauke kansa kasa yace "Na fahimta."
Ta lalle shi, tana kokarin fahimtar ko da gaske ya fara ganewa.
"Do you?"
Ya ɗaga mata kai.
"Kamar na fara fahimta."
"Yauwa to ka bani lokaci."
Ya gyada mata kai a hankali "Na baki."
Ya juya zai fita,amma kafin ya kai kofar kitchen Rania ta kira shi a hankali.
"Sajjid."
Ya tsaya da sauri ya juyo ya kalle ta.
Ta nuna masa tukunyar da ke kan wuta.
"Abincin zai dahu nan da minti goma. Ka shirya tebur."
Ya kalli ta kamar bai ji daidai ba sai kuma yace "Are you asking me to help you?"
Ta ɗan daga masa gira.
"Idan ba zaka iya ba zan yi da kaina."
"A'a zan iya."
Ya fita da sauri zuwa dinning area.
Rania ta bi bayansa da kallo yadda yake rawar jiki. Ta girgiza kai a hankali. Wani ɓangare na zuciyrta na jin tausayin sa amma wani ɓangaren na tuna mata cewa ba za ta bari tausayinsa ya sa tayi watsi da ciwon da take ji ba. Ta cigaba da juya abincin, ta ji muryarsa daga dinning area.
"Raina,ina kika ajiye wankankun plates ɗin nan?"
Ta ɗan yi murmushi a hankali tace "Cabinet ɗin dama."
"Wanne?"
"Na sama."
"Okay,Okay. Ba sai kin yi ihu ba na ji ki."
Ta kasa hana kanta yin wata yar dariya saboda yadda yake rawar jiki.
Sajjid ya ji dariyar sarai ya tsaya da plate a hannu, da wani irin fata na wata ƙila akwai sauran gyara a tsakaninsu. Ya sani wanann yar safiyar ba tana nufin ta yafe masa ba ne. Yau ta ba shi damar ya taya ta shirya tebur ƙila gobe ta ba shi dama ya nuna mata cewa ya fahimci kuskurensa.Kuma watarana idan ta shirya,zai Saurare ta ba tare da ta nemi ta gaggauta warkeea daga abin da ya yi mata ba.