Free chapter · Read without an account

LOKACI CHAPTER 40

by Rabi'atu kabiru Fulani · LOKACI

***

⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳ 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

 YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

UNDER TEAM YOTA'S AMAZING PEN'S.

SADAUKARWA A GAREKI AN KARIME KARIME NA ❤️
   

FULANI ❣️ 
***


     PAGE 4️⃣0️⃣

Tana idar da sallar asubah ta shiga kitchen, ta na gab da kammala abin da take taji tsayuwarsa a bayanta.

"Sannu da aiki Baby"

Sunan da ya kirata da shi, sai da ya sata dakatawa daga kan abin da take, ba tare da ta juyo ba tace.

"Me wani Baby kuma sai kace yarinya"

"Baby ce mana ai gaskiya na faɗa"

Da sauri ta juyo tana masa wani irin kallo. Murmushi ya saki ya haɗe tazarar dake tsakaninsu.

"Baby"

Ya faɗa yana hura mata iskar bakinsa.

Lumshe idonta ta yi ta buɗe akan fuskarsa.

"Bana so"

Ta faɗa ƙasa_ƙasa.

"Me?"

Ta fahimci tsokanarta yake son yi sai ta girgiza kanta, hannunta ta saka guda ɗaya ta turasa baya, amman ko gezau baiyi ba.

"Ka matsa na gama aikin toh"

Maimakon ya matsa kamar yanda ta buƙata, sai ya sakata a ƙirjinsa gaba ɗaya.

"Babu gaisuwa babu komai taya zan matsa?"

Zame jikinta tayi ta miƙa masa hannunta suyi musabaha. Baya ya yi da hannunsa.

"Ba irin wannan gaisuwar nake so ba, anyi ɗaya sauran ɗaya"

Ya faɗa yana nuna mata bakinsa.

Da sauri ta juya masa baya, tana murmushi cikin jin kunya. Dariya ya yi kaɗan ya jingina da loker kitchen ɗin yana kallonta.

"Ko ki zo ki yi min, ko kuma ni nazo nayi"

"Muhan ka tafi nayi aikina"

"Sai fa anyi zan fita"

Takun tafiyarsa da taji ne ya saka ta juyawa babu shiri, ajiyar zuciya ta sauke ganin tray ɗin data haɗa kayan breakfast ya ɗauka.

"Ina bin ki bashi yarinya"

Ya faɗa yana fita daga cikin kitchen ɗin.

Kanta ta girgiza tana kallonsa har ya bar kitchen ɗin, tabi bayansa da wani irin murmushi da ya kasa ɓoyuwa akan fuskarta, wanke kayan da ta ɓata tayi, bayan ta gama fita tayi daga kitchen ɗin, ganin baya nan sai ta faɗa ɗakinta ta saka key, wanka tayi bayan ta fito ta shirya cikin atamfa mai gold, a wajen ɗaurin ɗankwali ne ta kasa dole kawai ta rufasa a kanta, ta buɗe ƙofar ta fito.

Ƙofar ɗakinsa taje tayi knocking, daga ciki ya bata izinin shiga, handle ɗin ta tura ta shiga da sallama a bakinta, shima har yayi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya, sosai ta tsaya tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi, dan yayi mata kyau, sun jima suna kallon juna fuskarsu ɗauke da murmushi.

"Kinyi kyau Besty"

"Nagode"

Ta faɗa a hankali tana ɗauke kanta, so take ta ce masa shima ya yi kyau, amman ta kasa.

Hannunsa ya miƙa mata, suka yi musabaha, sai a lokacin suka gaisa, ba tare da ya sake ta ba suka fita daga ɗakin, kan dining suka je kujera ya ja mata ta zauna, shi yayi saving ɗinsu, sannan ya zauna suka karya.

"Muhan ina son zuwa wajen Ammie kafin mu tafi please"

Ta faɗa tana kallonsa.

"Ina tunanin yau ya kamata kije idan har zaki je ɗin, tafiyarmu gobe ce in sha Allah"

Kanta ta gyaɗa masa cike da jin daɗi, bayan sun gama ya yi mata sallama akan zai je duba restaurant, daga nan kuma zai biyo ya ɗauketa su wuce. Yana fita ta shige cikin kitchen kayan da suka siyo ta fara dubawa, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara aikin cikin nishaɗi, ta daɗe rabon da ta shiga cikin kitchen da sunan haɗa kayan snacks, dan haka take aikin da kazar_kazar kafin kace me har taci fin ƙarfin aikin, bayan ta gama ɗakinta ta koma, wanka tayi ta saka doguwar riga, ba tayi kwalliya ba, kuma bata cika turare ba, dan tasan idan tayi ɗaya daga ciki za'a iya fasa fitar, duk da bai taɓa fitowa ya faɗa mata, amman bata manta zuwansu gidan Inna ba.

Tana rolling ya shigo ɗakin da sallama a bakinsa, jingina yayi da jikin mirror ya zuba mata ido, ta cikin madubin suka haɗa ido, murmushi ta sakar masa.

"Sannu da dawowa Best friend"

Hannunsa ya buɗe mata, cikin nutsuwa ta juyo ta tako gabansa, ɗan tsayawa ta yi sai kuma ta faɗa jikinsa tana murmushi, hannayensa ya saka ya zagayeta da su, tana jin ajiyar zuciyar da ya sauke.

"Kinyi kyau Besty"

Ya faɗa yana ɗago fuskarta. Gemunsa taja tana murmushi ba tare da ta ce masa komai.

"Na shirya mu tafi Muhan"

Ta faɗa da zumuɗi a muryarta, baiyi mamaki ba saboda shi ya san yanda Zahra take son Ammie, yayi tunanin gidansu zata ce zata je, amman yaga wajen mahaifiyarsa take son zuwa, shiyasa a kullum take ƙara samun matsayi mai girma a wajensa.

"A bari nayi wanka ko?"

"Uhm uhm" 

Ta maƙale masa kafaɗa kamar ƙaramar yarinya. Babu yanda ya iya haka ya bita ba tare da yayi wankan ba, abubuwan da tayi ta ɗakko a kwando a kitchen sannan ta fito, karɓa yayi yana tambayarta menene wannan. 

"Babu kyau saka ido Muhan"

Amsar da ta bashi kenan ba tare da ta basa amsar tambayarsa ba, shima ƙyaleta ya yi suka shiga mota ya bar unguwar, suna tafiya suna hira jefi-jefi a haka har suka ƙarasa, lokacin da suka je gidan babu kowa a haraba, dan haka ya ɗauki kayan duk yanda yaso riƙe hannunta bata yarda ba, dan ba za ta bari ayi abin kunya a gidan sirikai ba.

Fitowar Ammie daga kitchen kenan suka shigo da sallama, da sauri ta ware wa Zahra hannunta tana sakin murmushin jin daɗin ganinta.

Da ƴar sassarfa ta faɗa jikinta tana dariya.

"Ammiena nayi kewarki"

Ta faɗa kamar zata yi kuka.

"Nima nayi kewarki daughter"

Ta ce bayan ta riƙo hannunta sun zauna akan kujera.

"Ammie baki ganni bane?"

Zay'd ya tambayeta ganin ta Zahra kawai take.

"Au yaushe ka shigo?"

Rasa abin da zai ce mata yayi kawai ya ajiye mata kwandon a gabanta. Zahra ce take masa dariya, hararar wasa ya yi mata sannan suka gaisa da Ammie, bayan sun gaisa itama ta gaisheta ta amsa.

"Ammie ina yaran gidan?"

Ya tambayeta jin tsit ɗin ya yi yawa.

"Princess tana ɗakinta, Khaleel kuma yana office"

Ta basa amsa tana kallon Zahra.

Tashi ya yi ya ce zai je ya dawo. Bayan fitarsa hira suka ci gaba dayi da Ammie hankali kwance, anan take faɗa mata sallama tazo yi mata zasu tafi Abuja.

"Shine kuma baki min waya ba, a haka za ki bisa, kai babu kitso, hannu fari kamar nasa?"

Ammie ta faɗa tana ƙara kallon Zahran.

Itama kallon jikin nata tayi sai dai bata ga komai ba, sai ma ganin yanda fatarta take ta ɗaukar ido, kuma jikinta ya murje sosai. Jin Ammie na buga waya ne yasa ta mayar da kallonta kanta. Bayan ta gama ta ci gaba da mata magana, sosai ta nuna mata muhimmancin gyara dan kana da kyau ai ka ƙara da wanka, suna nan a zaune suka shigo su uku, waɗanda suka yi mata gyaran jiki da lalle da kitso ne, lokacin da za ta koma gidanta.

 Bayan sun gaisa Ammie ta kaisu sama, dan tasan Zay'd zai iya dawowa, zani ta bata bayan ta ɗaura ta fita ta basu waje, dan danan suka fara abun da ya kawo su, ba zai yuyu ayi mata ƙananun kitso ba, saboda yamma tayi hakan ya sa ta yarfa mata ibira sosai ya kwanta yayi kamar ta saka hula a kanta, sai da aka gama mata gyaran jiki, sannan a kayi mata lallen mixt aka mata me ja da baƙi, hannu da ƙafa, kafin kace me ta fito a amaryarta sak.

Doguwar rigar da Ammie ta bar mata ita ta saka bayan anyi mata kabbasa, suna gyara wajen ta fito ta bar musu ɗakin, tun kafin ta sakko take jin tashin muryar Princess da Khaleel, kusan a tare duk suka juya suna kallonta, banda shi daya lumshe idonsa.

"Ammie an gama"

Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi tana zama a wajen ƙafarta.

"Ma sha Allah daughter dawo nan ki zauna"

Ta ɗagota ta zaunar da ita a kusa da ita, kusa da ita princess ta dawo ta zauna, gaisheta tayi, ta amsa sannan ta juya suka gaisa da Khaleel.

"Gaskiya Ammie nima aure zanyi, yaushe za'a je nema min aure?"

Khaleel ya tambayeta, yana kallonta.

"Idan har ka samo matar zan maka aure Khaleel"

Ta faɗa tana dariya, dan dai tasan bashi da wata budurwa.

"Ai Ammie duk kun santa Autah nake so, Big sister ai dai ba za ki hanani ba ko?"

Kafin ma ta basa amsa Ammie ta tare numfashinsa.

"Ma sha Allah na fi kowa farin ciki da wannan haɗin, aikam dole Abhie ya koma gidan Baffa nema maka aure"

A take parlown ya kaure da hayaniya tsakanin shi da Princess, shi dai gogan bai ce komai ba, sai murmushin da yake ta saki, itama Zahra a ɓangarenta wani irin farin ciki ne yake ratsata. Bayan sun gama ganin magriba ta kusa suka yiwa Ammie sallama, har bakin mota suka rako su, sannan suka koma, tayi tunanin gida zasu wuce amman taga ya ɗauki wata hanyar daban, bata kawo komai a ranta ba, sai da taga dagaske hanyar gidansu ya ɗauka sannan tayi magana.

"Muhan"

Idonsa da ya ɗan shige ciki ya ɗago ya zuba mata.

"Uhmm"

Ya ce yana maida hankalinsa kan tuƙin da yake. Har suka zo ƙofar gidan bai yi magana, ba ta san tayi kewar gidansu ba, sai da ta ganta a ƙofar gidan, bama ta tsaya sunyi sallama ba ta buɗe ƙofar ta fice, ƙofar gidan ba'a datse take ba, dan haka ba ta tsaya knocking ba ta shiga da sauri.

"Autah! Mahmah! Autah!!"

Babu ko sallama ta shiga tana ƙwala musu kira, da wani irin gudu Autah ta fito ta rungume ta, itama rungumeta ta yi suka fara juyi a tsakar gidan.

"Oyoyo Big Sister"

Take ta faman maimaitawa. Mahmah tana tsaye a ƙofar ɗakinta tana kallonsu, cike da farin cikin ganin Zahran. Gaban Mahmah suka ƙarasa hannunta riƙe dana Autah.

"Mahmah"

Ta kira sunanta tana faɗawa jikinta.

"Na yi kewarki"

Tana riƙe da ita tace itama tayi kewarta, gaisheta ta yi, ta amsa sannan ta ce.

"Ke kaɗai ko kawo ki a kayi"

Da sauri ta zaro idonta waje.

"Autah je ki ce Muhan ya shigo yana waje"

Hijabi Mahmah ta saka akan kayan jikinta, suka koma ɗakin. Babu jimawa Salmah ta shigo da ledoji a hannunta, yana biye da ita, har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da Mahmah, bayan sun gaisa ya ce zaije ya dawo bayan magriba su wuce, godiya Mahmah ta yi masa sannan ya fice, kamar ba Mahmah ba haka suka zauna suna ta hira cikin nishaɗi, ko da Mahmah bata furta ba tabbas taji daɗin ganin Zahra, sun daɗe a ɗakin Mahmah sannan suka wuce ɗakinta na da ita da Salmah jin ana kiran sallar magriba, bayan sun idar da sallar zama suka yi suna hira su biyu.

"Autah"

Ta kira sunanta ƙasa_ƙasa.

"Na'am Big Sister"

Itama ta amsa mata a yanda ta kirata. Dariya sukayi a lokaci ɗaya, sai Zahra ta girgiza kanta, a fili ta ce.

"Allah ya shiryaki Autah, kin san me?"

"Sai kin faɗa"

Ta faɗa tana matsowa kusa da ita har da ɗora hannunta a kan cinyar Big Sistern.

"Abuja za mu je da Muhan"

Wani irin ihu ta fasa, da sauri ta toshe mata baki, tana harararta, sai da taga ta nutsu sannan ta cire hannunta a bakinta.

"Yaushe za ku tafi?"

Ta tambayeta cike da farin ciki.

"Gobe"

"Wayyo Allahna!"

Magana suka ci gaba da yi a kan tafiyar, sosai Zahra ta tattauna abin da ko mahaifiyarta bata yi maganar da ita ba, anan kuma suka yi magana akan alaƙar Khaleel da Autah, bayan sun gama magana suka fito suka koma ɗakin Mahmah, anan Salmah take ce mata sallama Big Sister ta zo yi mata za su tafi Abuja, suna cikin maganar tafiyar Baffa ya dawo.

"Mamana ya ki ka bar mijinki a mota yana jiranki"

Ya katse mata gaisuwar da take masa.

"Bansan ya dawo ba Baffa"

Ta faɗa cikin jin kunya.

"Toh maza tashi ku tafi"

Haka ta miƙe Mahmah ta ce ta jirata, ɗakinta taje ta ɗakko mata wata yar jaka ta bata, sannan ta ce komai akwai bayaninsa a jiki. Har bakin mota Autah ta rakota, sannan ta koma cikin gida, suna tafiya babu mai magana a cikinsu, can ta katse shirun.

"Wani abu ya faru ne Muhan?"

Murmushin gefen baki ya yi mata, dai-dai lokacin da ya tsaya a inda ake siyar da gasashiyar kaza. Da ɗan mamaki ta kallesa saboda suna da ita a gida a cikin firiza, amman ba ta yi magana ganin kamar baya son magana ne, daga nan kuma ya tsaya ya shiga rufaidah ya siyi yughurt sannan suka wuce gida, bayan sun shiga ɗakinta ta wuce bai hanata ba, abubuwan da Mahmah ta bata ta duba, kusan duk magunguna ne, ba tare da tunanin komai ko bin ƙa'idarsu ta kwankwaɗi zuma, sai kuma gumba itama ta ci daga zaune, sunyi mata daɗi hakan ya sa ta zauna tana ci kamar ta samu abinci, kitchen ta shiga ta fasa madara ta ruwa guda uku ta zuba garin magani tana daga tsaye ta shanye tana siɗe baki, sai da ta gama ta fito ta shiga wanka, turaren wanka da aka bata tayi amfani da shi, sannan ta shirya cikin rigar bacci iya gwiwarta, bata saka hula ba saboda tana son yaga kitsonta, ita da kanta tasan tayi kyau a iya yau ɗaya kuma ta canza, sosai maroon ɗin rigar ta haskata.

Tasan ba zai wuce master bedroom ɗinsu ba, dan haka ta nufi can a gaban mudubi ta samesa shima cikin kayan bacci yana fesa turare, ta cikin madubin ya tsaya yana ƙare mata kallo, ɗan ƙaramin murmushi ya yi ya juyo ba tare da ya kalleta ya fice daga ɗakin. Sak ta yi tabi bayansa da kallo a ranta tana tunanin ko dai tayi masa wani laifi ne, saboda yanda yake ta shareta abin ya fara damunta. Tana tsaye ya dawo da flate a hannunsa da cup, da hannunsa ya kirata tazo kusa da shi ta zauna, kazar ya juye a flate sannan ya cika mata cup da yughurt, da kansa ya bata a baki sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan shima yaci, kwashe kayan ya yi ya mayar da su kitchen sannan ya shigo ɗakin.

Hannunsa ya saka ya ɗauketa ya zaunar da ita akan cinyarsa, kitson da ake mata yake shafawa a hankali, can kuma ya cusa hancinsa a wuyanta, sosai yake shinshinata, dan ƙamshin da take gaba ɗaya tun a gidan Ammie ya gama birkitasa, hakan yasa yake ƙin kallonta gudun a samu matsala, tana jikinsa ya tashi ya kashe hasken ɗakin. 

Atoohh ina ganin haka ni ɗiyar baba Achadu na tattara ya nawa_ ya nawa na ƙara gaba.

Wata iriyar wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke, ta wanda yaci kuka ya ƙoshi, tabbas ta sha wahala a hannunsa, ta yi tunanin abin sauƙi garesa, sai da ta shiga hannunsa sannan ta gane ba haka bane, sai dai duk wahalar da ta sha ba ta kai wancan, yafi awa ɗaya yana faman rarrashinta da wasu irin kalamai masu tsada, amman kukanta yaƙi tsayawa, har wanka shi yayi mata, sannan suka dawo suka kwanta, gaba ɗaya ta lafe a jikinsa tana masa ƴan ƙananun koke koke, shi da kansa yasan ta sha wahala hakan yasa ya ɓuge da rarrashinta, sai da ya tabbatar tayi bacci sannan ya zare jikinsa daga nata, hasken ɗakin ya kunna kaɗan yana ƙarewa fuskarta kallo, bakinta da yayi jajir ya zubawa ido, a hankali ya lumshe idonsa, zai iya cewa wannan shine dare na biyu da ba zai taɓa mantawa da su ba, a cikin rayuwarsa, darensu na farko, sai kuma wannan daren, wancan komai ya faru a gaggauce ne. Wannan kuma cikin nutsuwa da soyayya, duk da a farko ta bada haɗin kai daga baya ne ta nemi turjewa, amman ta riga da ta makara, bai san sanda shima bacci ɓarawo ya ɗaukesa ba.

Kiran asubar farko suka tashi kusan a tare, shi ya kaita har cikin toilet, bai biye mata ba yayi alwala ya tafi masallaci, itama sallar tayi ta zauna a kan daddumar tana azkar, tashi ta yi da jan ƙafa ta shiga ɗakinta, ruwan zafi ta haɗa ta gasa kanta, sannan tayi wanka ta fito ɗaure da towel tana fitowa yana shigowa ɗakin. Ƙasa tayi da kanta ta gaishesa bai amsa ba, sai hugging ɗinta da yayi, hannunta ta saka ta zagaye ƙugunsa.

"Ya jikinki?"

"Ni lafiya ta ƙalau"

Ta basa amsa muryarta a dishe.

"Dagaske?"

Ya tambayeta yana ƙare mata kallo. Ba tare da ta kula da irin kallon da yake mata ba, ta gyaɗa masa kanta, ai kuwa sai da tayi danasanin ce masa ƙalau take. Bayan ya samu nutsuwa ya mayar da ita toilet ɗin wanka yayi mata shima yayi, sannan ya fito da ita ɗauke a hannunsa, goge mata jikinta yayi ya zura mata doguwar rigar da ya gani akan gadonta, kwantar da ita yayi shima ya kwanta bayan yaja musu bargo.

"Matar Muhan"

Ya kirata ƙasa_ ƙasa, amman muryarsa na ɗauke da wani irin shauƙi da ya gaza ɓoyuwa a cikinta.

"Uhmm"

"Sannu kinji"

Ba ta iya amsa masa ba, dan ji take hatta da bakinta ciwo yake, gaba ɗaya jikinta yayi mata tsami, tana kallonsa ya tashi ya fita, bai jima ya dawo da cup ɗin tea da magani, bayan tasha ya bata maganin sannan ya mayar da ita ta kwanta, shima ya kwanta ya janyota jikinsa, Allah ya taimakesa jirgin sha biyu zasu bi, da sai dai a ɗaga tafiyar da ta safiya ce, ya na jin yanda take ta sauke numfashi da ajiyar zuciya.

FULANI
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol