Free chapter · Read without an account

78

by Halima Zakariyya Haruna · LULLUƁIN BIRI

Hasken fitilun compound ɗin suka haske mata shi tarr, tana kallon yadda ya kai hannu ya shafo wuyansa, kamar dai yadda yake a ɗabi'arsa. 
Wannan side view ɗin nasa da take gani, sai ya bayyana mata yadda hancinsa ya ƙara tsayi. 

Ya rame da yawa! 
Haka ta ji zuciyarta ta faɗa mata. 

Ba ta san sunan ainihin abin da ta ji a lokacin ba. Amma dai ya yi kama da tausayinsa. Wani irin tausayi da ta ji ya taso mata daga can cikin zuciyarta, ba tare da ta kira shi ko ta gayyace shi ba.

"Shi wannan ciwon nasa, har yanzu yana tare da shi? Ba zai bar shi ba kenan? Ba a samun warkewa daga gare shi gaba ɗaya?"

Wata ƙaramar murya a cikin zuciyarta ta yi mata tambayar, kuma kafin ta samu damar zurfafa tunaninta, sai wani ɓangare na ƙwaƙwalwarta ya haska mata abin da ta taɓa karantawa.

"Ana iya warkewa mana!"

Ta tuna da takardar asibitinsa da ta taɓa gani. A cikin bayanan da ke jikin takardar, an rubuta Acute Kidney Injury.
Kuma kamar haskawar farin wata, haka ya haska mata bayanin wani likita da ta taɓa ji, lokacin suna Saudia.
To idan har wannan ne ciwon Turaki, ai yana iya samun waraka. Ba wai duk wanda ƙodansa suka samu matsala ne zai rayu da ita har ƙarshen rayuwarsa ba. 

"Zai warke! Zai samu waraka watarana, in sha Allahu."

Ta faɗa a cikin zuciyarta, kamar tana ƙoƙarin tabbatar wa kanta da abin da take fata. Da wannan tunanin, idanunta suka ci gaba da binsa. Ba ta san dalilin da ya sa ganin raunin da ke tattare da shi ya dame ta ba, har yana neman saka jin ciwo a zuciyarta.
Ta ja dogon numfashi ta sauke a hankali, a daidai lokacin da ƙwayar idanunta suka lumshe. Ta bar su a rufe na ɗan lokaci.
Sakan biyar...
Bakwai...
Minti ɗaya!

Ta sauke dogon numfashin da ta ja. Idanun suka buɗe a hankali. Ba ya wajen da yake. To ina ya nufa? Wurinta ya taho kenan? Me zai ce mata? Ita ma me za ta ce masa?
Masifa! 
Ehh ita ta sani, ta tanadi masifa kala kala da zata zazzage masa kamar yadda ta sha alwashi, muddin aka kawota gidansa.

Amma... masifa za ta yi masa ne a kan ya sake ta?
A'a! Ba saboda sakin ba. Ai dama ita sakin take so. Kuma ya yi mata abin da take so ɗin, ya kamata ma ta gode masa.

To a kan me za ta yi masa masifar?
Tambayar ta taso a cikin zuciyarta, tana jin kamar wani ne a gefenta ya jefa mata ita kai tsaye.

Sai ta buɗe tafukan hannayenta biyu, tana kallonsu kamar za su iya ba ta amsa.
Ba ta sani ba!
Kawai dai za ta yi masa masifar ne saboda tana jin haushinsa.
Haushinsa dai!

Haushinsa a kan me to?
Wannan karon ma sai ta sake buɗe hannayenta, tana kallon su cikin wani irin rashin fahimta. Kamar ita kanta ba ta san abin da take nufi ba. Kuma kawai sai ta tsinci kanta da turo baki gaba, tana hararar wurin da ya bari.

To ma shi idan ya zo wajen na ta me zai ce mata? Ki kwashe kayanki ki tafi.

Ta yi saurin ƙulle idanunta gam, tana so ta hana tunanin nan sake shiga kanta. Kuma ta daɗe a haka kafin ta buɗe su.
A wannan karon, wani motsi da ta hango ta gefen idonta ya ja hankalinta. Ba tare da ta shirya ba, sai ƙwayar idanunta suka karkata zuwa inda yake.

Ganinsa ta yi yana tafiya zuwa wani ɓangare na gidan, ɓangaren da ba nata ba.
Ya gaji!
Haka tafiyarsa ta nuna mata. Ba irin gajiyar wanda ya yi aiki sosai ba, akwai wani abu mai nauyi a tattare da motsin na sa, kamar dai mutumin da ya gaji da komai, har ma da shi kansa.
Kamar ma! Kamar ma ƴar ƙaramar packaging nylon ɗin hannunsa na neman rinjiyarsa ne ta kayar da shi.

Ta zuba masa ido, tana bin tafiyarsa da kallo. Akwai wani abu a wannan tafiyar tasa da ya ƙara tabbatar mata da cewa Turaki ba shi da ƙarfi kamar yadda ta saba ganinsa.
Ƙofar part ɗin da take iya hangowa sosai ta buɗe. Tana kallon yadda ya murɗa handle ɗin, sannan ya tura ƙofar a hankali.

Ba ta iya gane yadda ya sa ƙafafunsa cikin ƙofar ba. Domin kuwa daidai lokacin da ƙofar ta buɗe, zuciyarta ta buga da wani irin ƙarfi, sannan ta matse, har hakan ya jawo mata ɗaukewar ganinta na ɗan lokaci.

A take ta yi saurin kai hannu ta dafe saitin zuciyarta, kamar hakan zai hana abin da ke faruwa a cikinta bayyana a fili.
Ta sake runtse idanunta.
A wannan karon, ba wai kamar ba ta son sake buɗe su ba ne. A zahiri, ba ta son buɗe su ɗin sam. Ba ta son sake kallon wancan ɓangaren gidan. Ɓangaren da Turaki ya shiga yanzu.

Sashen wata...

A'a, ba wata ba.

Sashen matarsa!

Ɗayar matarsa, wadda za su yi zaman kishi da ita.
Kenan ita ba zai zo wurinta ba?
Ba zai zo ya tsaya a gabanta ba, ya yi mata rumfa da tsayuwarsa, sannan ya yi magana da ita cikin wannan ɗaga muryar tasa mai sa mutum ya firgita? Ba zai tambaye ta dalilin da ya sa ta yarda aka kawo ta gidansa alhali ya riga ya sake ta ba? Ko kuwa ba ta san cewa babu aurensa a kanta ba, saboda haka zaman gidansa ya haramta agareta.

"Are you mad?"

Ta ma ji kamar ta riga ta ji muryarsa a kunnenta.
Ai ta san duk haka ne zai ce mata. Zai tsaya gabanta, ya zuba mata manyan idanunsa masu kama da na damisa.

Wannan sanyin da take ji yana ratsata, ba ta san daga ina ya taho ba. Mintuna kaɗan da suka wuce, tana jin ɗumi ne a jikinta, amma yanzu da idanunta ke rufe suna hasko mata Turaki da wata macen, da irin abubuwan da ka iya wakana, sai ta ji kamar an ɗauketa cak an tsoma a cikin ruwan da ake narkar da ƙanƙara.

Taku biyu kawai ta yi ta ja da baya, kafin ta tsinci kanta da barin bakin window ɗin.
Idan ta ƙara wani takun fa, me zai faru?

"Rami ne a bayanki fa, kuma faɗawa ciki za ki yi. Ramin da ba za ki taɓa iya fitowa daga cikinsa ba."

Wani ɓangare na zuciyarta ne ya ba ta amsar tambayar da ta yi wa kanta.
A lokaci guda, sai wani irin sanyi daban ya ratsa ƙirjinta, sanyin da ya zo da wani yanayi da ba zai bayyanu ba. Ta yi ƙoƙarin haɗiye abin da ya tokare mata maƙogwaro, amma kafin ta iya yin hakan, hawayen da ke taruwa a idanunta suka fara gangarowa a kumatunta.

Ta ƙara runtse idanunta sosai. Zafin hawayen na ƙona mata fatar fuska. A hankali ta sulale har ta zauna a ƙasa.
Sai a sannan ta fara fahimtar ainihin nauyin da take ji a ƙirjinta. Wani irin nauyi da ya sa ta yi saurin rungume jikinta, tana ƙoƙarin hana kanta karkarwar da ta fara mamaye ta.

"Ke ni yanzu ne ma na gane dukkan dalilin kukan naki. Muna ta wahalar da kanmu da tambayarki abin da yake damunki. To wallahi ki sauƙaƙawa zuciyarki Sister. Idan kika biye wa zafin kishi tsab zai hallaka ki. Don shi wanda kike yi dominsa, kina ji kina gani, za ki tafi ki bar masa duniyar ya zauna shi da wadda kika ɗaga hankalinki akai, kina ta faman kuka sama da kwana biyar duk akan kishi. Ke kuwa Sister wane irin kishi gare ki haka?"

Haka Raudha ta faɗa mata a safiyar yau. Ita a lokacin tana kuka ne kawai akan takardar sakin da aka bata. Shima kuma ba wai don tana jin zafin rabuwar tasu ba ne. A'a sam! Tun da dama ba sonsa take yi ba. Duk wannan kukan da take yi na tsawon kwanaki bata san na menene ba har ga Allah.
Amma kuma a yanzun da take cikin wannan condition ɗin, sai ta ji tana so ta mayarwa da Raudha martanin maganarta, to amma ta yaya za ta amsa tambayarta ta ƙarshe?

Don ita ma ba ta san kishin take yi ba, balle irin kishin da take yi ɗin. Abin da kawai ta sani shi ne, wannan kishin yana yi mata illa. Yana murƙushe wani abu a cikin zuciyarta, yana kuma ƙara mata wani nau'in ciwo da ba ta san sunan da za ta kira shi da shi ba, amma dai yana da zafi, sosai zafin.

Ta dunƙule hannunta, ta kai duka a kan tiles ɗin.
Don me?
A kan me?
Kawai sai ta riƙa jin wutar kishin mutumin da ba mallakinta ba na balbala a zuciyarta? Ai ya sake ta ko? 
Ita fa ba matarsa ba ce. To me ya sa zata damu da shi da lamarinsa?

Wata ƴar ƙaramar murya ta fito daga can ƙasan maƙoshinta, cikin rauni, da ƙyar take iya ji. "Kuma ai ba na son sa. Ban taɓa sonsa ba."

Ta fitar da maganar tana gamewa da fitar sautin kukan da take ta dannewa tun ɗazu.
Ta kai hannu gefe, da zummar farfashe duk abin da ya zo hannunta. Amma sai ta ji babu komai. Wayam sai iska kawai!

Ashe duk waɗannan abubuwan da take ganin za ta iya ɗauka ta watsar su tarwatse, a cikin duhun idanunta ne kawai suke bayyane. Amma a zahiri, babu komai a kusa da ita.

Yana nufin ita kaɗai za ta kwana a wannan ƙaton wajen?
Fiye da mintuna goma suka shuɗe kafin ta iya buɗe idanunta. A hankali ta ɗago kai, ta zuba wa ɗakin da take ciki ido. Kango ne nan ɗin, kango ne aka barta a ciki, kowa ya tafi ya barta, cikin mamakon sanyin da yake neman hallakata.

Tsoro! Tsoro take ji!

Da ace ta san cewa haka za ta ji, da ta roƙesu su zauna har gari ya waye.
Ba a wannan lokacin ne ta fara jin tsoron ba. Tun kafin a kawo ta gidan nan, tun daga safiyar ranar da za a taho da ita, zuciyarta ta riga ta fara ɗaukar wani nauyin fargaba da ita kanta ba ta san yadda za ta sauke shi ba.

Kishi!
Kishi!!

Wai ita mene ne ma wannan kishin yake nufi? Kamar fa yana yunƙurin kasheta ne lokacinta bai yi ba.

Kuma shi Turakin, ya tafi ya bar ta cikin wannan halin. Ba zai zo ya tambaye ta abin da ke damunta ba, balle ya ba ta maganin da zai rage mata wannan azabar da take ji.

A take sabbin hawaye suka cika idanunta taf. Ba su zubo ba, amma tana jin kamar an zuba mata barkono a cikinsu saboda yadda suke mata yaji.
Ta buɗe idanunta da ƙyar, ta ɗaga kai tana kallon saman ɗakin. Ba fa zata bar hawayen su zubo ba. Zata ci gaba da taresu, dole ma su tsaya.

Sai dai yayin da take ƙoƙarin yaƙar hawayen, wata magana da Ummi ta faɗa mata a safiyar jiya ta dawo mata a cikin kanta.

"Idan ma kina tsoron faruwar wani abu a auren naku ne, ki riƙa ambaton 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un'. Allah zai sanya komai ya zama mafi alheri a gare ki. Ni dai har cikin zuciyata ba na jin wani mummunan abu game da tarewar nan taki. Kullum addu'a nake, ina miƙa al'amarinki ga Ubangiji. Kuma na gamsu da son da yaron nan ya ce yana yi miki."

Haka Ummi ta faɗa mata a ranar da za a taho da ita.
A lokacin, ba ta ce wa Ummi komai ba. Ta dai bita da kallo har ta fice, sannan ta mayar da hankalinta kan Alƙur'anin da ke gabanta. Suratul Yusuf ta buɗe, ta fara karantawa a hankali, tana ƙoƙarin nutsar da hankalinta cikin ma'anar ayoyin.

Kamar yadda Ummi ta faɗa mata falalar karanta alqur'ani, a hankali sai ta fara jin damuwarta tana raguwa. Fargabar da ta mamaye zuciyarta ta fara sassautawa.
Ba wai ta manta da abin da ke damunta ba ne, amma ta samu nutsuwar da ba ta da ita. Kamar an rage mata nauyin da ke kan zuciyarta, ta samu damar numfashi cikin sauƙi.

Tabbas, Alƙur'ani waraka ne ga zuƙata. Natsuwa ne ga wanda damuwa ta mamaye shi. Allah Ya bayyana cewa, da ambatonSa ne zuƙata suke samun nutsuwa. 
Don haka a yanzun ma, sai ta yi ƙoƙarin miƙewa. Da ƙyar ta tashi daga inda take zaune. Ganinta bai gama daidaituwa ba, haka har ta isa gaban madubi. A saman madubin ta hango Alƙur'anin da Inna Falmata ta ba ta shawarar kada ta taɓa ɗaukewa daga wurin. Ta miƙa hannu ta ɗauko shi. Sannan ta koma ta zauna a kan dardumar da ta yi sallah a kai. Ta buɗe Alƙur'anin, ta fara karatu a hankali, cikin nutsuwa da ƙira'a mai daɗi.

A wannan lokacin, babu abin da take buƙata kamar ta samu nutsuwar zuciya. Tana so ta daina jin wannan baƙin zafin da ya mamaye ƙirjinta. Tana so ta daina jin kishin da ba ta fahimci dalilinsa ba, tana so ta daina tunanin inda Turaki yake, da wadda yake tare da ita, da kuma dalilin da ya sa bai zo wurinta ba.

Tana so ta daina tsoron komai. Tana so zuciyarta ta dawo yadda take a da, cikin salama da walwala, ba tare da wani abu yana ta cizon ta daga ciki ba.
Babu wani abu da ke haddasa mata wannan zafin face Turaki. Shi kaɗai.
Mutumin da take ƙara faɗawa kanta cewar ba sonsa take yi ba. Kuma ba zata taɓa son sa ba.

Haka ta kasance cikin kaɗaici a wannan daren. Ta kasa baccin da take ta so ya ɗauketa. Sai dai ta juya ta ƙara juyawa, kuma ba zata iya tashi akan dardumar ba ta hau kan gado, saboda tana jin tsoro. Gani take kamar nan ɗin yafi safe a gareta.
Yatsanta tasa tana ta wasa da shi a saman dardumar. Kuma a hankali komai da ya wakana a ranar jiya yake dawo mata, tana ganinsa tarr kamar an kunna mata TV. Sai ta ƙara jin kewar gida da ta ahalinta, musamman mahaifiyarta.

Tun a jiyan da ta farka take so ta yi wa Ummi bayani akan sakin. To amma bata son ganin Ummin ta shiga damuwa. Babban tashin hankali ne a wurin Uwa ace anyi auren ƴarta kuma kafin tarewarta auren ya mutu. Wanne tunani jama'a za su yi akan hakan? Me za a ce? Turaki dai bai duba mata ba, idan ma da niyyar ya wulaƙantata ya tozartata ya yi mata hakan, ta barshi da Allah.
Sabuwar kewar Ummin ta ƙara kamata. Tunawa da ta yi a lokacin da ta shiga banɗaki ta zauna tana kuka, da ta fito Ummin ce ta zaunar da ita a kan darduma, ta ɗauko Alƙur'ani ta miƙa mata.

"Ki yi ta karantawa. Za ki ji sauƙin duk abin da ke damunki. Tun da dai ni da nake mahaifiyarki ma ban isa ki faɗa min matsalar da ke damunki ba, to ga maganin kowacce irin damuwa nan. Ki yi ta karatu. Da ƙarfe sha ɗaya na ji Daada na cewa jirginku zai tashi."

Hakan kawai tace mata ta fita a ɗakin ta barta. Bata dawo ba sai ƙarfe takwas, hannunta ɗauke da tray ɗin da ke ɗauke da kayan breakfast.
Ta ajiye mata a gabanta, ita kuma ta ajiye Alƙur'anin. Tare da Ummi suka ci abincin, wanda ba zata tuna when last Ummin ta iya sakewa suka ci abinci tare ba tun zuwansu Taraba. Kuma suna ci Ummi ta riƙa yi mata nasihohi game da sabuwar rayuwar da za ta shiga. Tana mata magana cikin tausasawa, tana ƙoƙarin shigar da kowacce kalma cikin zuciyar ƴarta. Sannu a hankali maganganunta suka taimaka wajen rage sauran fargabar da ke tare da ita.

Ita kaɗai ta yi murmushi a yanzun. Da ta tuna abin da su Maijidda suka ce mata da suka shigo, suka tarar tana cin abinci suna hira da Ummi.

"Munafuka Ashe dama so kike a kai ki gidan miji. Shi ya sa kika ishe mu da kuka! Yau ga idonki nan ƙyam, sai ƙyallin amarya yake yi."

Babu wadda ta tankawa a lokacin. Suka sakata a gaba da zolaya. Har Ammi ta shigo ta tarar da su, wadda tana shigowar ta kama hannunta suka bar ɗakin, suka nufi sashen Lamiɗo, zuwa ɗakin matarsa Diyam.
A nan aka zaunar da ita domin a shirya ta.

Daada ta shigo ɗakin tana murmushi.

"Masha Allah! Tubarkallah. Lallai Muhammad Turaki ya yi dace da kyakkyawar Ƴar mu. Ai da na sani na ƙayyade masa sabon sadaki."

Zuciyarta ce buga a lokacin. A hankali ta kai hannu ta dafe takardar sakin da ke maƙale a cikin bra ɗinta.

Yafendo ta miƙa mata gorar ruwa. "Ungo sha wannan."

Ta karɓa tana yatsine fuska. Za ta yi gardamar da ta saba, Yafendo ta tsawatar mata.

"Ke wannan ba magani ba ne. Ruwan tofi ne Dottijo ya bayar a kawo miki. Ki yi Bismillah ki kafa baki ki sha."

Ta yi Bismillah a fili, ta kafa baki ta sha. Ba ta sauke kofin ba sai da ta shanye tas. Yafendo ta dubeta cikin ƙauna.

"Ko ke fa, addu'armu ita ce Allah ya ba ku zaman lafiya. Allah ya yi muku albarka, ya albarkaci rayuwar aurenku. Allah ya ba ku zuri'a ɗayyiba, ya kawar da fitina tsakaninku, ya haɗa kanku ke da abokiyar zamanki."

Dukkan waɗanda ke ɗakin suka amsa da "Amin."

A lokacin ne Daada ta shigo. Ita ma ta ba Fullo wani ruwan addu'a ta sha, sannan ta miƙa mata wani magani da kuma turare da ta fesheta da shi daga kai har ƙafa. Sannan ta sake bata wata ƙaramar kwalba mai ɗauke da turare.

"Karki yarda wannan ya je hannun kowa har sai kin shiga ɗakinki. Ki shafa turaren a lokacin da zai shigo ɗakin. Karki yi wasa da duk abin da muka faɗa miki da kuma abubuwan da muka ba ki. Muna so ki yi zarra, ki zama tauraruwa mai haskakawa cikin gidan mijinki."

Yafendo Mari da Adda Asma suka kama Fullo a tare, suka fito da ita daga ɗakin. Sashen Hajjah suka wuce, inda Ummi take zama yanzu tare da Kaka da sauran Ƴan'uwan Fullo da suke uba ɗaya.
Ummi na ganinta a lulluɓe cikin alkyabba sai ta fashe da kuka.

A hankali aka kawo Fullo gabanta, ta durƙusa. Ummi ta zura hannunta cikin alkyabbar, ta kamo hannun ƴarta ta riƙe shi sosai. A lokacin Fullo ta saki nata kukan, wanda ta daɗe tana dannewa tun safiyar ranar.
Rabuwa tsakanin uwa da Ƴa ba ƙaramin abu ba ne. Fullo ta manne a jikin Ummi, tana kuka mai taɓa zuciya. Ita ma Ummi zuciyarta ta yi da rauni, nan suka shiga kuka tare. An kuwa sha wahala kafin a samu a cire Fullo daga jikin Ummu.

Daga wurin Ummi aka wuce da ita sashen Maudo. Maudo da Dottijo suna zaune a Fadar cikin gidan. Aka zaunar da Fullo, kowa ya fita, aka barsu su kaɗai. Maudo ya ɗora hannunsa a kanta, ya shiga kwaranyo addu'a yana tofa mata. Bayan ya gama Dottijo ma ya yi mata tasa addu'ar.

Kukan Fullo sai ƙaruwa yake yi, musamman da tunanin mahaifinta ya sake taso mata. Sun jima suna yi mata nasiha kafin daga bisani aka fito da ita.  Aka shigo da motar da zata ɗauketa cikin ƙaton tsakar gidan, motar Maudo mai matuƙar tsada ta tsaya a gabanta, sannan aka shigar da ita.

Anata busa algaita da sarewa, kamar wata ƴar sarki. Da alama dai Galadima ya yi lokacinsa a sanda yake raye.
Yafendo Mari, Inna Baraka Yayar Hayyo, da kuma wata cousin ɗin Ummi mai suna Innah Hajar, su ne suka shiga motar amarya. Sauran motocin kuwa, waɗanda ba su wuce uku ba suka ɗauki hanyar Gombe.

Motar Amarya ita ta nufi airport. Inda sauran motocin kuma suka ɗau hanyar Gombe.
A gidan Alƙali aka yada zango. Su da kansu suka tura mota domin ɗauko amarya daga airport. Yafendo Mari da sauran waɗanda suka zo tare da Fullo sun sami kyakkyawar tarba a wajen Hajiya Madina. Sun ga karamci da mutunci sosai.

Lokacin da su Inna Falmata za su miƙa Fullo a hannun Mum, sai ta girgiza kanta, tana nuni da Hajiya Madina.

"Ai ga mahaifiyar tasa can."

Hajiya Madina ta ji wani abu ya tsarga mata. Ta ɗau lokacin tana kallon Hajiya Ramla, kallo mai cike da tarin ƙauna da Rahma. Haƙiƙa tana son kishiyarta, so na tsakani da Allah. Kuma a yau ɗin da tayi mata wannan babbar karar. Sai take jin duk duniya bata da wani abu da zata iya biyan Hajiya Ramla da shi. Matar Ɗanta aka kawo mata gabanta, amma sai ta nuna musu ba ita a madadinta.

Inna Hajar ce ta miƙa hannun Fullo a kan ƙafafun Hajiya Madina, tana shaida mata. "Hajiya ga amanar ƴarmu."

Maama tana murmushi mai faɗi, cike da jin daɗi, ta tabbatar musu cewa sun karɓi amanar. Ta ƙara da cewa, "In sha Allahu Ɗanmu ba zai baku kunya ba."

A zuciyar Fullo, sai take jin komai ya yi mata sabo, kamar baƙuwa take jin kanta. Tana jin kamar a wannan ranar ne ta fara shigowa gidan Alƙali Dikko. Kamar a wannan ranar ne ta fara sanin su Maama.
Hannayenta riƙe cikin tafukan Hajiya Madina. Ƙwayar idonta na sake karanta mata rubutun, wannan rubutun da ke ɗauke da adadin sakin da Turaki ya yi mata. Har tana iya jin muryarsa a kunnenta, tamkar yana sake karanta mata kalmomin sakin ne.

Sai wajen ƙarfe uku na rana, ƴan Taraba da Daada ta zaɓa domin halartar Dinner suka fara isowa. Har da ita kanta Daada. Ta sha wanka na kece raini, kamar ba tsohuwa ba. Less ɗin da ke jikinta kaɗai ya isa ya sa mutum ya tsaya yana kallo.

Ƙarfe takwas na dare aka fara shirin tafiya Dinner. Wannan shirin duk na Hajiya Madina ne, don ce ta yi sai ta rama duk wani shagali da bata yi ba a aurensa da Ilham. 
Faɗin yadda amarya ta yi kyau ya fi ƙarfin alƙalami. Doguwar riga mai matuƙar tsada ta saka, wadda Maama ta sa Samha ta yi order ɗinta daga Europe. Shigar pink aka yi mata, launin da ya ƙara fito da hasken fatarta. Sai dai fa kowa ya ganta bayan yaba kyanta da ya yi, sai ya tanka sirantarta.

Raudha da Maijidda, Ƴan uwa kuma Aminan Amarya, su ne suka mata rakiya har bakin mota. Bello ne zaune a driver seat ya yi musu sannu da zuwa.
Raudha ta buɗe mata motar ta shiga ciki. A take ƙamshin turaren da ta sani ya doki hancinta. Ta ɗaga kai da sauri, sai ta gansa hakimce yana kallon gefe guda, kamar bai san mai ke wakana ba.

Ba wani haske ba ne a cikin motar. Amma ta ɗan hasken fitilun waje da ya ratso zuwa ciki, shi ya haske mata Fuskarsa. Tana ganin yadda sam babu annuri a tare da shi. Tamkar wanda aka yi wa saƙon zuwan mutuwarsa. Sai ya dawo mata sak asalin Turakin da ta fara gani a rayuwarta.

Bata isa ta ce bai yi kyau ba. Domin zuciyarta da ta motsa ta tabbatar mata da kyan da ya yi. Tana jaddada mata babu abun kushe ga wanda shi ɗin mai kyau ne, komai nasa mai kyau ne, kuma komai ya yi kyau yake masa.
Bata san ta ya ba, haka kawai hoton yadda Mata za suke kallonsa suna yabawa idan suka fito daga mota, shi ya haska mata tarr a gabanta. Lokaci ɗaya ta ji sukar wani abu mai kaifi a zuciyarta. Zafin da sai da yasa ta rumtse ido gam. 

Wata arniyar suit ce a jikinsa, baƙa mai ratsin pink irin na kayan da ita ma ta saka.
Tunawa da cewa ita fa ba matarsa ba ce, ya sa ta yi saurin buɗe ido, tare da kore tunanin komai nasa daga ranta.

Idanunta suka ciko da hawaye, amma ta hana su zubowa. Ba ta son ya ga raunin da take ciki, balle ya danganta hakan da zafin sakin da ya yi mata.
Kawai sai ta ƙura wa ƙunshin hannunta ido, tana addu'ar su tafi aje a gama taron, ko zata ta daina ganinsa kusa da ita.

Daga Bello da ke tuƙi, har ita da shi da Raudha wadda ke gaban mota. Kowa da abin da yake saƙawa a zuciyarsa.

Lokaci zuwa lokaci Bello sai ya bugi steering yana jan dogon tsaki.
Ba kallonsa take yi ba, amma jikinta take jin tasirin kallon da ya kafeta da shi. Ta ɗago kai, idanunsu suka haɗu.
Ba tare da ta yi tunanin abin da za ta faɗa ba, bakinta ya suɓuce da cewa.

"Kana da buƙatar ƙara sanin addini da kyau, domin na lura sam ba ka san yadda shari'ar Musulunci ke tafiya ba."

Ta faɗi maganar a ƙasa, yadda Bello da ke gaba ba zai ji ba. Turaki ya zuba mata ido cike da mamaki. Da farko kamar ba zai ce komai ba, daga bisani ya ce.

"Kin fini buƙatar ki koma ki nemi ilimi, ke da kika kasa ba da takardar sallamar da aka ba ki."

Ya faɗi hakan daidai lokacin da suka isa event center. Kuma da wannan tunanin ne ɓarawon bacci mai nauyin gaske ya ɗauketa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol