Free chapter · Read without an account

Chapter 16

by Asmeetah Writer · WASAN ƘADDARA 1

╔══════════════════════╗
        🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝

_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_

> ✍️ BY ASMEETAH WRITER

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

🌟 Under:

THE SHIDORIA WRITERS TEAM

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

📞 ***

📚 BOOK 1

📖 CHAPTER ___31 and 32

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━

Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━



Kamar kullum, dare ya tsala. Kowa yana zaune a tsakar gida, yayin da suke jiran shigowar Malam wanda har zuwa lokacin bai dawo gida ba tun bayan guduwar da ya yi da kuɗin..

Amira tana zaune akan tabarmar waje, tana ƙiran sunan Uma cikin kulawa, "Mommy... Ina man kaɗanyar nan da aka siyo na shafa miki a bayanki"

Khadijah dake zaune a gefe tana kwasar tuwon dare, ta tsagaita cin tuwon, ta kalli Amira da mamaki dake bayyana a fuskarta,

 "Iyeee! Sabon salo, gemu a kafaɗa... Wannan sunan kuma na Mommy daga ina yake?"

Amira ko kallon gefenta ba ta yi ba, ta kuma dawo da hankalinta kan Uma, "Mommy, dube ni mana..."

Khadijah ta fara waige-waige a tsakar gidan na su, sannan ta taɓe baki, "Gaskiya kam banga wata Mommy da ta shigo gidan nan ba sai dai idan dai aljanun gidan ne suka canza miki kamanni."

Amira ta juyo ranta a ɓace, "Ke... Ki shiga taitayinki da ni fa"

Khadijah ta zaro ido, "Wai fa... Uma ce ta dawo Mommy" Ta tintsire da dariya ta cigaba da faɗin, 

"To pahh! Dan ma dai ba a riga an tafi jami'a ba, da abun sai ya fi haka girma."

Amira ba ta biye mata ba, ta tashi ta shiga cikin ɗaki gurin Uma dake tsaye riƙe da kunkuminta, fuskarta cike da zurfin tunani da fargaba. Kafin Amira ta ce uffan, Uma ta yi saurin janyo hannunta ta matso da ita kusa, tana magana ƙasa-ƙasa cikin sanyin murya yadda su Khadijah ba za su jiyo su ba...

"Ke... Kin san me nake so da ke yanzu?"

Amira ta gyada kai cikin sauraro, "Meye, Uma?"

Uma ta leƙa ƙofa ta dawo, "Ina so idan Malam ya shigo ya huta a ɗakinsa, ni zan fito da shi waje ta hanyar jawo da hankalinsa... Ke kuma sai ki faki idonsa, ki sulale cikin ɗakinsa ki binciko mana kuɗaɗen nan da ya karɓa gurin Hajiya."

Amira ta zaro ido cikin tsoro, "Amma Uma... Kin san fa ban taɓa shiga ɗakinsa ba. Kuma ma... Allah ya sa bai riga ya kashe kuɗin gaba ɗaya ba."

Uma ta ƙarfafa mata gwiwa da faɗin, "Mu gwada dubawa kawai..."

★★★

Can wajajen ƙarfe 10, Malam ya turo ƙofar gidan ya shigo. Ko kallon gefen ɗakin da Uma take bai yi ba, balle ya yi mata albashirin cewa ya karɓi kuɗin gurin Hajiya... Ko magana bai yi ba, ya nufi ɗakinsa kai tsaye ya shige ya tura ƙofar.
A lokacin kowa a gidan ya kwanta barci, ban da Uma da Amira dake jiran dacewar shirin...

Uma tana jin shigarsa ɗaki, bayan wasu mintuna ta fito da sauri. A can cikin ɗakin kuwa, Malam yana jin motsin tafiyarta, ya firgice... Cikin hanzari ya shiga daddafa kuɗin dake hannunsa, ya tura su ƙarƙashin tabarma ya ɓoye su..

Uma ta shigo ɗakin da gudu, fuskarta cike da firgici, tana nuna waje kamar za ta yi kuka,

 "Malam! Malam dan Allah ka fito kazo! Wani abu na gani yanzu can tsakar gida kamar ɓarawo ya shigo... Yanzu haka naga ya shige cikin banɗaki!"

Malam ya zaro ido, "Innalillahi! Ɓarawo dai a gidan nan? Meye zai sace?"

Ba shiri ya miƙe, ya nufi ƙasan gadonsa ya zaro ƙaton addarsa da yake ajiye ta, ya karkace hula, 

"Mu je mu gani, yau sai na ci ubansa a gidan nan!"
Ya turo ƙofarsa ya rufe ta, sannan suka nufi hanyar banɗakin da sauri. Suna tsaka da tafiya, Uma ta yi firgikit ta nuna hanyar waje,

 "Innalillahi! Malam gashi can yayi hanyar ƙofar waje"

"Haba! Yau sai dai shi ko ni" Malam ya ranta da gudu ya nufi ƙofar gidan da addarsa a hannu ya fice waje.
Yana fita da gudu, Amira dake fake a ɗakin Uma ta fito a guje, ta tura ƙofar ɗakin Malam dake a ɗan tura ba tare da an saka sakata ba, ta shige ciki da sauri.
Ita kuma Uma, tana ganin Malam ya fice waje, ta bi bayansa ta tura babbar ƙofar gidan, ta sanya sakata ta garkame ta...

A can cikin ɗakin Malam, Amira ta shiga dube-dube cikin sauri da fargaba. Ta duba ƙasan matashin kai, ta duba ƙasan katifa, can ta kai hannu ta ɗaga tsohuwar tabarmar baccinsa... Nan take idanunta suka haska.. Ta hangi damin kuɗi a dunkule. Ba tare da ta tsaya sanin nawa ba ne ko nawa ya kashe, ta kwashe su duka 

A waje kuwa, Malam ya fara buga ƙofar gidan da ƙarfi yana haki, "Halima!... Halima ya zaki rufe gidan kuma? Wato kina so ɓarawon ya kashe ni a waje ko?!"

Sai da Amira ta fito daga ɗakin Malam a guje ta koma ɗakin Uma sannan Uma ta taka a hankali ta buɗe ƙofar tana zazzaro idanuwa a firgice.

"Malam, tsoro nake ji sosai! Da naga ka fita waje, na ji tsoron kar ɓarawon ya dawo mana ciki shi yasa na saka sakata. Idan ka dawo sai na buɗe maka..."

Malam ya duba hagu da dama da addarsa a hannu, ya ce, "To muje ciki, ban ga kowa ba a waje."

Suna shigowa tsakar gida, Malam ya ajiye addarsa yana hamma, "Je ɗakinki Halima, ni zan shiga nawa domin na gaji sosai yau."

Uma ta tare shi, "Haka za ka kwanta ba tare da ka yi wanka ba, Malam? Gaskiya ka ɗan watsa ruwa ko za ka ji daɗin jikinka."

Malam ya harare ta, "Haba Halima, ya kike so kiyi da ni ne? Jiya na yi wanka, yau ma sai na yi? Gaba ɗaya kin mayar da ni namijin agwagwa... Kin san yawan sa ruwa a jiki yana da illah ko?"

Uma ta canza salo, ta yi murmushi, "To shikenan mu shiga mu kwanta..."

Malam ya yi turus, ya tsaya yana kallonta, "Wai me yake damunki ne yau? Ki koma ɗakinki mana"

Ta shige gaba tana turo baki, "Gaskiya ni a gurin mijina zan kwana yau saboda kewa."

Malam ya zaro ido, "A wurina kuma?"

"To, haramun ne don na kwana a inda mijina yake?" Uma ta faɗa tare da gilfawa ta shige cikin ɗakinsa.

Malam ya bi bayanta a zabure, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi. Ya nufi gurin da ya ɓoye kuɗaɗen a ƙasan tabarma ya tsaya cak a kai. Ba tare da ya duba ko suna nan ko ba sa nan ba, ya kwanta a gurin da sauri ya loda duka tsofaffin kayayyakinsa a kai saboda tsaro...

Uma ta kwanta a gefensa a kan tabarmar.
Malam ya kalli katifarsa ta soso dake gefe, ya ce, 

"Ki hau kan katifar mana Halima."

Uma ta ce, "To ai sai muje mu hau tare..."

Malam ganin ba shi da zaɓi, kuma yana tsoron kar ta gano abin da yake ɓoyewa idan ya matsa sosai.., suka tashi suka hau kan katifar. Uma ta matso kusa da shi, ta kankame shi sosai ta rungume shi ta yadda duk lokacin da zai yi yunƙurin motsawa ko sauƙa daga kan katifar dole ta ji motsinsa.

A ɗayan ɗakin kuma, Amira tana shiga ta tura ƙofarta ta saka sakata. Ta tsaya cikin sanyin jiki tana sauraron numfashin Khadijah dake barci.
Sai da ta tabbatar su Khadijah sun yi nisa a cikin barcin nasu sannan ta ciro kuɗaɗen a hankali ta zauna a ƙasa ta shiga ƙirgawa guda-guda cikin farin ciki.
Idanunta suka zazzaro cikin tsananin murna da annashuwa!
A cikin dubu ɗarin nan, dubu ashirin da biyar kawai Malam ya taɓa ya kashe a ciki. Ragowar saba'in da biyar ɗin duka suna nan!
Ba tare da ta ɓata lokaci ba, ta nemo wata kyakkyawar leda ta zuba kuɗaɗen a ciki ta ƙulla ta sosai. Sannan ta nufi wani ɓoyayyen lungu na ɗakin wanda ta tabbata ko da Malam zai yi haukan bincike na shekara ɗari, ba zai taɓa iya gano inda kuɗin suke ba...

Ta kwanta a kan katifarsu tana murmushi, tana jin cewa aƙalla yanzu sun sami mafita na kuɗin tafiyarta makaranta...

★★★

Sanyi mai ratsa jiki na gabannin asuba ya ratsa ɗakin, amma kuma sanyin bai hana gumin dake jikin Malam tsiyayewa ba. Uma tana jin ƙiran sallah na farko ya ratsa ko'ina, ta zame jikinta a hankali daga jikin Malam wanda har lokacin yake baccin-biri idanunsa biyu amma yana tsoron ko motsawa. 

Ta gyara ɗaurin zaninta, sannan ta taka a hankali ta fice daga ɗakin kamar ba abin da ya faru, ta nufi randa ta debo ruwan alwala.
Malam yana jin sautin takunta ta fita daga ɗakin, ya zabura ya tashi kamar wanda wutar lantarki ta taɓa.

 Bai ko tsaya shafa addu'ar tashi daga barci ba, ya faɗa kan tsohuwar tabarmar dake shimfide a kasa. Hannunsa na rawa ya bayyana tsoron dake zuciyarsa...
Ya kwashe kayayyakin da ya loda a kai, sannan ya tura hannunsa ƙasar inda ya tura damin kudin.

Hannunsa ya taɓa daskararriyar ƙasa mai sanyi. Bai ji alamun komai ba balle takardar kuɗi mai kauri... Malam ya shiga sosa ƙasar kamar mai neman gwal, ya sake ɗage duka tabarmar gaba daya, ya duba karkashin katifar soso ko ya fura ya je can, amma wayam. Babu ko sisi, babu ko alamar an taɓa ajiye kuɗi a gurin...

Ya dafe kansa da hannu biyu, idanunsa suka zazzaro kamar zasu fito, ya saki wani uban ihu a gigice,

"Wayyo kura ta ci min dukiya... Wayyo kuɗinaaaa! Kudina sun tafi"

Uma dake tsakar gida ta gama alwalar, ta shigo ɗakin da gudu fuskarta ɗauke da tsananin mamaki na bogi, tana salati.

"Malam! Malam lafiya kake wannan irin ihu kamar wanda aka zarewa laka da asubanci haka? Ko mafarkin tsoro kake yi?"

Malam ya shiga rikicewa, jikinsa yana karkata, yana nuna ta da yatsa yana kakar muryar kuka..

"Halima! Ke ce... Ke kaɗai ce kika shige min ɗaki jiya da daddare, kuma tare muka kwana a ɗakin nan! Ina kuɗina da na ajiye a nan? Bani kuɗina tun kafin in saɓa miki"

Uma ta tsaya tsayin daka, ta haɗe girgiza cikin natsuwa da nuna ɓacin rai, "Ni, Malam? Kuɗin me kake da shi da zan dauka? Kuma ma ai tare muka kwana sannan banga lokacin da ka tashi ko na tashi ba balle na ɗauki wani abu. Sannan tambayarka nake... Kuɗin me kake dashi da zaka fara wannan mitar da asubanci haka?"

Malam ya daskare a tsaye. Kwakwalwarsa ta shiga lissafi da sauri-sauri. To ko dai ɓarawon ne ya shigo bayan ya fita? Ko kuwa dai aljanun gidan ne suka kwashi kuɗin? Ko kuma dai kuɗin ne suka ɓace da kansu?
Babban abin da ya fi komai tsaya masa a wuya shi ne. Bai isa ya buɗe baki a cikin gidan nan ko a gaban kowa ya ce,  "Na karɓi kuɗin Hajiya dubu ɗari ba, kuma an sace su.."
 Idan ya faɗi haka, ai asirinsa ya riga ya tonu a gurin matarsa.

Ya runtse ido, ya haɗiye wani ɗaci dake maƙale a maƙogaronsa, ya ɗauki butarsa ya fita waje yana tangal-tangal kamar mashayi zai nufi masallaci, amma zuciyarsa tana can tana tafasa...

Gari ya waye, hasken rana ya gauraye ko'ina. Amma ga Malam, wannan rana ta waye masa da duhu. Ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai zarya yake tayi a tsakar gidan, yana faɗin maganganu marasa daɗi..

"Wannan wane irin ɓarna ne? Gida ba amana, mutum ya ajiye abu a gidansa amma ya neme shi ya rasa! Ai wannan ba karamin bala'i ba ne"
  ya riƙe kunkumi yana tafe yana mita.

Khadijah dake share tsakar gida ta kalli yayarta Amira dake zaune ta taɓe baki, "Wai ke kuwa Aunty Amira, me yake damun Baba ne yau tun safe yake ta wannan faɗan?" Amira ta girgiza kai a hankali, ta ɓoye murmushin dake son suɓuce mata.

Malam ya sake dawowa gaban ɗakin Uma, ya tsaya yana huci..

"Halima, kuɗin ajiya ne fa aka bani... Kusan dubu hamsin ne na wani abokina, yanzu gashi sun ɓace" 

Uma ta kalle shi tun daga sama har ƙasa, ta taɓe baki tana zuba abun karyawa wa yara, ta ce

"Yanzu Malam, a wannan zamanin da kowa yake kukan babu, wa zai ɗauko kuɗin ajiyarsa ya baka a matsayinka na mai son abun duniya, in banda tsautsayi irin na mai kudin? Ai ko wanda ya baka ya yi kuskure."

Malam ya ji maganar ta soke shi har cikin jijiya. Jikinsa ya shiga rawa, gumi mai ɗumi ya shiga yarfo masa ta goshinsa da wuyansa, yana goge shi... Ya tabbata cewa yau idan bai nemo kuɗin nan ba, tabbas ya tabka babban asarar da bazai taɓa mantawa ba, kuma lissafin da ya yi na abubuwan da zai saya da kuɗin ya rushe gaba daya...


Haka aka wuni a gidan ranar cikin wani irin yanayi. Malam kansa duk ya fita a hayyacinsa, sai faman rarraba idanu yake yi kamar wanda ya tafka babban laifi, yayin da a ɓangare guda kuma Uma da Amira suka gudanar da nasu sirrin lissafin cikin kwanciyar hankali. Sun tsara yadda za su yi amfani da waɗannan kuɗaɗe domin inganta rayuwarsu da kuma shirye-shiryen karatun Amira dake tafe...

Babban abin farin cikin kuma shi ne, washegari ita ce ranar da Amira za ta rubuta jarrabawar JAMB, jarrabawar da take da babban tasiri a kan makomarta...

Kashegari da asuba, tun kafin hasken rana ya warware, Amira ta tashi cikin shirinta na musamman. Bayan ta yi salla, ta fito sanye da kyakkyawar doguwar rigarta da ta sha guga, fuskarta ɗauke da fargaba da kwarin gwiwa. Uma ta raka ta da addu'o'i masu yawa na samun nasara...

Kuɗin abun hawa zuwa can cibiyar da aka tura ta don rubuta jarrabawar ya yi tsada sosai saboda nisan gurin, duk da cewa yana cikin garin Kaduna ne. Amma albarkacin dabarar da suka yi wa kuɗin Malam, ba su sami matsalar kuɗin motar ba...

Tana isa gurin, ta tarar da ɗalibai da dama sun riga sun hallara. A gurin ne ta hango ƴan makarantarsu su goma, waɗanda duk aka tura su guri ɗaya. Suka taru a gefe guda suna ta hira cikin sanyaya gwiwar juna yayin da suke jiran a fara tantance su ta hanyar ɗaukar hoton yatsa domin tabbatar da kowace ɗaliba ta yi rijista da kyau...

Bayan an kammala tantancewar, aka fara buɗe musu CBT Hall...

 Shigar Amira cikin ɗakin ke da wuya, ta ji kamar ta shiga wata duniyar daban. Wurin ya kasance tamkar aljanar duniya, asalin duniyar zamani ta zamani wadda hukumar JAMB ta amince da ita ɗari bisa ɗari. Sanyin na'urorin sanyaya daki yana kaɗawa ta kowane gefe, kujeru ne da kwamfutoci a jere cikin tsari mai ban sha'awa...
Kowace kwamfuta tana ɗauke da lambar zama ta ɗalibi. Amira ta duba nata lambar, ta ƙarasa ta zauna a kan kujerarta. Murmushi kawai take yi tana kalle-kalle cikin girmama tsarin gurin.

 Tana zaune tana shafa jikin kwamfutar tata a hankali, duk da cewa ba a ba da damar farawa ba tukunna.
A gefenta, akwai wata kujerar da take kusa da ita wadda mai ita bai zo ba tukunna.

Bayan wasu ƴan mintuna, sai ga wani kyakkyawan saurayi ya zo ya zauna a kan kujerar gefen Amira yana turo baki cikin ɓacin rai... Wannan saurayi kuwa ba kowa ba ne illa Ahan.

Asalin abin da ya jinkirta shi kuwa shi ne, jiya bai kwanta barci da wuri ba domin ya tsaya kallon wasan ƙwallon ƙafa na dare. Yana yin sallar asuba kuwa ya koma barci mai nauyin gaske. Bai jima da kwanciya ba, mahaifiyarsa Hajiya Mairos ta shigo ɗakinsa tana ta ƙoƙarin tashi amma ina! Barcin nasa ya yi nauyi kamar an dasa shi...
Ganin cewa lokaci yana tafiya kuma yana iya makara gurin rubuta wannan jarrabawar ta JAMB, Hajiya Mairos ta fito cikin sauri ta nufi sashen sama gurin babban ɗanta Arman. Tana shiga ta sami Arman da Zaitun, ta shaida masa cewa Ahan ya ƙi tashi kuma yana da jarrabawa yau.
Arman, wanda kowa ya san shi da tsauri da rashin wasa, bai ɓata lokaci ba. Ya sauƙo daga can sashensa sanye da farar jallabiya mai kyan gaske. Ya nufi sashen Ahan kai tsaye. Yana shiga ɗakin na Ahan, bai ma tsaya ƙira ba, ya shige banɗaki ya ɗibo ruwan sanyi a cikin bokiti, ya dawo gaban gadon ya kwarara masa shi a fuska baki ɗaya...

"Wayyo Allah" Ahan ya zabura ya tashi a guje yana rarraba idanu cikin tsananin firgici.
Arman ya tsaya ya zuba masa idanu cikin gargaɗi, "Na ba ka minti goma ka shirya ka same ni a mota. Idan na sake dawowa na iske ka a ɗakin nan, to kashinka ya bushe."

Tsoron yayansa Arman dake ransa ya sanya Ahan ya tashi shaf-shaf ya shirya cikin sauri, jikinsa duk yana ɓari...
A lokacin, shi ma Arman ya canza shigarsa zuwa ƙananan kaya na jeans da baƙar riga mai dogon hannu wadda ta ƙara fito da jaruntakarsa, rigar ta matse shi sosai...

 Zaitun ta fesa masa turarensa na musamman mai daɗin ƙamshi, sannan ta rako shi har ƙasa zuwa babban falon gidan.
Ahan yana fitowa, Arman ya kalle shi a taƙaitaccen bayani,

 "Ka je ka jira ni a mota."
Sannan ya biya ta gurin iyayensu tare da Zaitun suka gaishe da Janar Zarkhan da Hajiya Mairos cikin girmamawa, kafin daga bisani ya fito ya nufi motarsa. Shi da kansa ya yanke shawarar kai Ahan gurin jarrabawar, domin akwai wani muhimmin al'amari na musamman da shi ma yake son gudanarwa a gurin.
Wannan ya sanya Ahan ya iso gurin jarrabawar a daidai lokacin da kowa ya riga ya zauna, ya shigo ɗakin yana faman turo baki domin har yanzu akwai sauran ragowar barci a idanunsa, ya zauna daidai kujerar da take gefen Amira.

A daidai lokacin da kowa ya zauna sanyin na'urar sanyaya ɗaki yana ratsa jikinsu, sai aka fara jin wasu ma'aikatan gurin da malamai suna raddi a tsakaninsu cikin ɗoki..

"A.Y.Z ne ya zo..." Inji wani malami yana leƙe ta tagar gilashi...

"Haba? Wallahi kuwa shi ne! Ya kamata mu je mu gaishe shi ko kuwa zai shigo nan..." Wani ya amsa masa da sauri.

Ɗaya daga cikinsu ya girgiza kai, "Ina kuma zai shigo nan? Ai ba lallai ya shigo cikin hall din nan ba..."

Wannan sunan na A.Y.Z da aka ambata, kamar an watsa wa ɗaliban dake zaune wutar lantarki ne. Nan take kowa ya fara miƙa wuya, ana dube-dube cikin zumuɗin son ganin babban mutumin da sunansa yake tashe a gari, musamman ma Amira. Idanunta suka zaro, zuciyarta ta shiga dukan uku-uku.
Ba tare da tunanin komai ba, ta zabura ta miƙe tsaye tana shirin nufar kofar fita domin ta leƙo shi. Amma da sauri wani mai kula da ɗakin ya tare ta,

 "Hey! Ke ina zaki je? Duk wanda ya riga ya shigo baya fita."

Amira ta ciza leɓe,  ta ce, "Zan yo fitsari ne..."

Ma'aikacin ya dube ta cikin ɗaure fuska, "Meyasa baki yi a gidanku ba sai da kika zo nan zaki ce wani fitsari? Oya, sit down!"

Haka ta dawo ta zauna jiki a sanyaye, tana gunguni. Ko da ta zauna ɗin, zuciyarta ba ta daina bugawa da ƙarfi ba...

Mutane biyu kawai take muradin gani, daga wannan A.Y.Z sai kuma mijin Zaitun..duk da bata san sunan Zaitun ba har yanzu...

"Shin da gaske ne... A.Y.Z yana nan a waje?" Ta tambayi kanta a ɓoye..

Ahan dake zaune a gefenta ya lura da yadda take ta faman zare ido da leƙen ƙofar shigowa. Ya ɗan yi murmushin gefen baki, cikin zolaya ya ce,

"Ke ma kin shiga sahun masu son ganin babban yayana kenan?"

Amira ta juya da sauri ta dube shi, fuskarta ɗauke da mamaki, "Kana nufin... da gaske ne ɗan uwanka ne ko kuwa dai sharri ne irin naka kake son kayi kalan dangi..?"

Ahan ya murtuke fuska ya ɗaga gira, "Ban sani ba... To ke wani munafurci ne yasa kike son ganinsa in ba kwaɗayin tsiya ba? Ko ma hala sonsa kike yi ko?"

Amira ta zaro idanuwa baki buɗe, "Me?!"
Kafin ta samu damar mayar masa da zazzafan martani, sai muryar jami'in JAMB na gaba ya dakatar da kowa...

"Silence please! Kowa ya zauna ya natsu. Examination is about to begin."

Nan take ɗakin ya yi tsit, babu abin da ke tashi sai sautin sanyin A.C da bugun zuciya..

A daidai wannan lokacin kuwa, a filin ajiye motoci na harabar wurin...
Wata baƙar motar alfarma ƙirar AMG mai sheƙi tana ajiye cikin nutsuwa...

 Arman ya fito daga ciki bayan zaman da ya ɗan yi a ciki,  ya sanya baƙar glass a idanunsa, sai agogon zinare dake haskawa a tsintsiyar hannunsa...
 Tsayinsa da kyakkyawar tafiyarsa suka sa kowa dake harabar gurin ya maida hankali gare shi.
Ko kallon gefen da mutane suke bai yi ba. Amma duk da haka, duk inda ya taka, idanun ma'aikata da jami'an tsaro dake gurin suna bin sa ne cike da matsananciyar girmamawa da fargaba..

"Assalamu alaikum, Ogah A.Y.Z..." Wani babban jami'in tsaro dake gurin ya ƙaraso cikin girmamawa ya miƙa masa hannu...

"Wa alaikumus salam," Arman ya amsa a takaice, tare da miƙa wa  jami'in hannu..

Daga ɗan nesa kuma, wasu sabbin ma'aikata da aka turo duba jarrabawar ne suke ta magana a tsakaninsu, 

"Wai shi ne A.Y.Z ɗin?"

"Kwarai kuwa, shi ne."

"Subhanallah... ai ya fi kyau a zahiri fiye da yadda ake faɗa.."

Wasu ma'aikatan JAMB har sun yi yunkurin takawa su je su gaishe shi, amma saboda kwarjinin aikinsa da kuma irin natsuwarsa, sai suka tsaya daga nesa kawai suna kallonsa.
Arman ya duba tsadadden agogon hannunsa. Ya ciro wayarsa daga aljihunsa, ya danna ƙiran waya na kusan daƙiƙa talatin yana magana cikin sanyin murya dake cike da umarni...
 Bayan ya gama, ya kashe wayar ya nufi wani tsararren sashe wanda yake can saman bene...

An riga an fara jarrabawar a kwamfutar kowa. Kwamfutocin sun kawo tambayoyin ɗaya bayan ɗaya, kowa ya shiga latsawa cikin natsuwa.
A can gefe guda kuwa, Ahan gaba ɗaya ya ruɗe. Bai san amsar kusan kashi saba'in cikin ɗari na tambayoyin dake yawo a kan kwamfuta ba...

 Cikin rawar jiki ya shiga satar kallo zuwa gefen Amira. Ya fara kaɗa ƙafarsa da hannunsa cikin sigar nuna alamun yana buƙatar ɗauki dake jarrabawar ta multiple choice ce..

Amira wacce duk hankalinta yake kan nata jarabawar kuma ta ga tana da ikon amsa tambayoyin cikin sauƙi, ta lura da yadda jikin Ahan yake rawa. Tausayi da kuma tsoron kar ya faɗi jarabawar ya sanya ta shiga taimaka masa ta ƙarƙashin tebur..

Idan amsar tambayar A ce, sai ta ɗan nuna masa yatsa ɗaya a ɓoye ba tare da kowa ya lura ba... Idan kuma B ce, sai ta nuna masa yatsu biyu. Idan C ce yatsu uku, idan kuma D ce yatsu hudu..

Ahan yana ganin alamar hannunta, sai kawai ya saki ajiyar zuciya ya dinga danna amsar a kwamfutarsa.

A daidai wannan lokacin, a can babban ɗakin kula da tsaro na cibiyar wato Control Room, inda CCTV na kowane lungu da saƙo na ginin suke bayyana...

A.Y.Z yana tsaye kusa da Manager... Suna tsaka da tattaunawa akan tsarin tafiyar da jarrabawar ta bana, sai kawai idanunsa suka sauƙa a kan ɗaya daga cikin manyan fuskokin kwamfutocin dake nuna cikin ɗakin jarrabawar...

Idonsa ya hango Ahan yana ta faman satar kallo da karkata kai zuwa gurin wata yarinya dake gefensa.
Arman ya tsagaita da maganar da yake yi, ya zura wa hoton ido sosai. Ya sake ganin Ahan ya karkace, yarinyar kuma tana ɗan leƙa jami'an sa ido kafin ta yi wasu alamun yatsu a karkashin tebursu...

Manajan dake tsaye kusa da shi ya lura da inda idon uban gidan nasa yake kallo. Ya gyara gilashinsa da sauri, "Sir... These two candidates are communicating."

Fuskarn Arman ta canza lokaci guda. Ya ce cikin tsanani da ba da umarni..

"Pause that camera... Zoom in."

Ma'aikacin dake gaban kwamfutar ya danna ya dakatar da hoton kyamarar, sannan ya matso da fuskar Amira da Ahan kusa sosai. A nan ne komai ya fito fili ras. Sun tabbatar da cewa duka biyun suna musayar amsoshi ne ta hanyar amfani da yatsu...

Amira tana kallon kwamfutarta tana duba tambayoyin, Ahan kuma yana kallonta, ita kuma tana nuna masa yatsu a asirce, shi kuma yana latsawa.. 

Arman ya ɗaure fuska kamar bai taɓa yin dariya a rayuwarsa ba. Ya ɗauki wayar intercom, ya ƙira babban mai kula da dakin jarrabawar..
 
"Candidate Number 028 da Candidate Number 029 suna musayar amsa a cikin ɗakin jarrabawa. Ku je ku raba su nan take. Bayan an kammala jarrabawar, ku tabbatar an rubuta official malpractice report, sannan ku adana dukan hotunan CCTV na wannan lokacin domin a tura wa headquarters na JAMB."

Bayan kusan awa guda Amira ta kammala nata jarrabawar, amma kuma Chief supervisor yana sane da su domin shi AYZ ya ƙira...

 Ta juya kaɗan ta kalli Ahan, ta iske shi cikin tsananin damuwa da ɓacin rai, ya tsaya a kan tambaya ta ƙarshe ta fannin Lissafi wadda ta ruɗe shi... 

Ya ɗan waiwayo ya kalle ta cikin roƙo. Amira, ba tare da sanin abin da ke jiransu ba, ta ɗan nuna masa yatsu uku wato C.. a takaice dai duk amsoshin ita ta gaya masa, idan akayi gaba sosai sai ya nuna kamar ya sani amma ganin lokaci ba jira zaiyi ba sai ya canza fuska kamar zaiyi kuka har sai ta gaya masa a haka dai har ta gama masa exam ɗin...

Da zarar ya danna amsar, sai ya danna Submit.. Amira ma ta danna nata kwamfutar ta yi Submit. Dukkaninsu suka sauƙe numfashi mai nauyi tare, suna masu tunanin cewa komai ya riga ya kammala lafiya lau kuma sun tsallake rijiya da baya...

Suna shirin tashi domin su bi sauran dalibai su fice, sai kawai muryar babban jami'in sa ido ta daki kunnensu.

"Candidate Ahan Y. Zarkhan and Candidate Amira A. Mansur... Please don't leave the hall."

Sauran ɗaliban duka suka fara fita ɗaya bayan ɗaya suna kalle-kalle, har dakin ya rage daga su biyu sai jami'ai...
Gaban Amira ya fara faɗuwa da karfi, jikinta ya ɗauki rawa. Ahan ya ɗan matso kusa da ita ya ce ƙasa-ƙasa,

 "Kada ki damu, ƙila verification ne bai yi ba."

Kalaman nasa basu gama fita ba, sai ga Chief Supervisor ya shigo ɗakin fuskar nan tasa a murtuke, tare da wasu jami'an tsaro guda biyu sanye da kakin hukuma.
Ya tsaya a gaban tebursu, ya ce, "Ku biyo mu."

Suka bi bayan jami'an jiki a sanyaye har zuwa cikin wani ƙaton ofis na gudanarwa...
A cikin ofishin kuwa, A.Y.Z yana zaune a kan kujera ta alfarma ta juyawa, yana danna kwamfutarsa. Ko kallon bangaren da suke bai yi ba, kuma ya juya musu baya gaba daya domin ba shi ne zai yi musu magana ba, shi sauraro kawai yake yi...Don haka basu samu damar ganin fuskarsa ba..

Chief Supervisor ya zauna a kan kujerarsa yana fuskantar Amira da Ahan, jami'ai biyu kuma suna tsaye a bayansu fuskokinsu cike da tsanani.

Supervisor ɗin ya ɗauko wasu takardu, ya ɗago kai ya dube su da ɓacin rai.

"Candidate Ahan Y. Zarkhan... Candidate Amira A. Mansur..."

Dukansu suka ɗago kai a firgice, ofishin ya yi tsit kamar babu kowa. Amira ta ji wani irin sanyi yana ratsa ƙafafunta, gwiwowinta suka fara rawa.
Supervisor ya ɗaura hannunsa akan tebur,

 "An kama ku ta hanyar kyamarar tsaro ta CCTV kuna musayar amsoshi a cikin ɗakin jarrabawa... Duk abin da kuka yi yana nan a rubuce kuma an adana shi."

Amira ta girgiza kai da sauri, muryarta tana rawa tana shirin kuka,
 "Wallahi tallahi banga..."

"Silence!" Jami'in ya daka mata tsawa, ya katse ta nan take.
Sai ya nuna musu wani babban talabijin dake jikin bango. Ya danna na'ura, nan take hoton Amira ya bayyana yana nuna yadda take mika yatsunta karkashin tebur, Ahan kuma yana latsawa..

"Tun daga lokacin da kika fara nuna masa alamun yatsu, kyamara tana ɗaukar kowane motsinku. Rahoton laifinku an riga an kammala rubuta shi, kuma yanzu haka an tura shi kai tsaye zuwa babban ofishin JAMB na ƙasa. Wannan jarrabawar taku gaba daya an  cancelled nashi, sannan kuma za a sanya sunanku a blacklist cikin waɗanda aka haramta wa sake yin jarrabawa gaba ɗaya..."

Kalmar blacklist dake nufin haramta jarrabawa ta daki kunnen Amira kamar tsawa. Jikinta ya yi sanyi sosai...

Take ta tuno da irin wahalar da mahaifiyarta take sha a gida, babu damar shiga jami'a ... Duk wannan mafarkin nata gashi yana shirin rushewa a cikin daƙiƙa ɗaya saboda taimakon da ta yi wa wani da ba ta ma sani ba...
Idanun Amira suka cika da zafafan hawaye, ta fara rarraba idanu tana numfashi da kyar..

"Don Allah... Don Allah ku yi hakuri... Ku taimake mu..."

Numfashinta ya fara ɗaukewa saboda tsananin kiɗima da firgici. Ta kai hannu da kyar domin ta riƙe kujerar gabanta don kada ta faɗi, amma jiri ya kwashe ta, idanunta suka juya sama...

Sai timmm....

Ta zube a ƙasa a sume
Ma'aikatan dake gurin suka firgice, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ahan ya zabura cikin tsananin firgici ya duƙa a kusa da ita,
 "Amira! Amira ki tashi don Allah" Ya yi yunkurin daukarta amma jami'an tsaron suka tare shi da sauri suka raba shi da ita...

A lokacin ne Ahan ya kalli kujerar da take juye ta juyo a hankali, ya hango bayan yayansa Arman. Nan take ya gane shi duk da cewa bai ga fuskarsa ba tun farkon shigowarsu.
Ahan ya ƙarasa gaban yayansa, ya zube a kasa yana kuka mai ban tausayi, idanunsa sun cika da hawaye

"Yaya... Yaya don Allah ka yi hakuri ka taimake mu! Wallahi duka laifina ne. Ita yarinyar nan ba ta da laifi, ni ne na matsa mata kuma na tursasa ta har ta gaya min... Don Allah ka janye wannan rahoton da ka tura..."

A.Y.Z bai ko ɗago kai ya kalle shi ba. Idanunsa suna kan kwamfutar dake gabansa kawai, yana danna ta cikin natsuwa. Bayan kusan daƙiƙa talatin, ya ce cikin sanyin murya

"Ka gama?"

Ahan ya haɗiye yawu mai daci, yana share hawaye, "Eh... Yaya."

Arman ya juyo da kujerarsa a hankali, ya cire gilashin dake idanunsa, ya zuba wa Ahan idanu kai tsaye cikin ɓacin rai.

"Yaushe na sanar maka cewa a wannan cibiyar za ka  iya karya doka saboda kai ƙani ne a guri na?"

Ahan ya yi shiru, ya kasa cewa uffan.. 

"Shin wannan cibiyar tana ƙarƙashin sunan wa?" Arman ya sake tambaya cikin sauti mai karfi.. 

"Na sani... Sunanka ne, Yaya."

"Ka san shekaru nawa aka ɗauka ana gina mutuncin wannan cibiyar a idon hukumar JAMB da ƙasa baki daya?"

"Na sani..."

"To saboda ka rasa amsar tambaya, ka ga ya dace ka lalata wannan sunan...?"

Ahan ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin tsananin kunya da nadama, "Yaya... Don Allah ka taimaka mana... Wannan shi ne karo na farko da na taɓa yin haka. Wallahi ba zan sake ba."

Arman ya zuba masa idanu, ya ma rasa wani irin hukunci zai masa idan suka koma gida,

 "Karo na farko?"

Ahan ya jinjina kai..

Arman ya miƙa idonsa zuwa kan fuskar Amira dake kwance a sume a ƙasa. Ya sake mayar da idonsa kan Ahan

"Kyamarar tsaro ta CCTV ba ta ƙarya. Kuma ni ba alkalin hukumar JAMB ba ne."

Ahan ya ɗago kai da sauri, yana ganin kamar akwai sauran ragowar tausayi a zuciyar yayansa,

 "Yaya... Don Allah..."

Arman ya katse shi, "Ni banga dalilin da zai sa in soke muku jarabawa ba tun da ba ni da ikon yin hakan."

Ahan da wasu ma'aikatan dake ofishin waɗanda tausayinsu ya fara kama su suka sauƙe numfashi na farin ciki, suna tunanin Arman ya sauƙo. Amma sai suka ji ya ɗora da cewa.

"Amma ni ne zan tabbatar da cewa an tura rahoton laifin sata a hukuma tare da bidiyon CCTV ɗin zuwa headquarters JAMB ba tare da an rage ko ɗigo ɗaya ba... Hukunci kuma, su ne zasu yanke muku shi."

Ahan ya girgiza kai cikin tsananin damuwa, "A'a... Yaya don Allah kada kayi mana haka..."

Arman ya miƙe tsaye, ya gyara tsayinsa, "Idan kuna ganin cewa ba ku yi wani laifi ba, to ku je ku kare kanku a gaban hukumar JAMB idan lokacin bincike ya yi...Idan kuma kun san kun yi laifi, to ku koyi darasi tun yanzu. A wannan cibiyar tawa, ba a ɓoye laifi saboda dalilin dangantaka."

Ya juya ya nufi kofar fita domin ya bar ofishin. Kafin ya tura kofar ya fita, ya tsaya ba tare da ya waiwayo ba, ya ƙira babban jami'in gurin..

"Chief Supervisor..."

"Sir!"

"Ku ba su report number... Idan suna da wani korafi, su bi hanyoyin da suka dace na hukuma."

Daga nan ya ɗan juyo kaɗan ya kalli Ahan dake durkusa a ƙasa,

 "Daman ai kai baka damu da yin jarrabawar ba. To sai ka koma gida ka ci gaba da baccin naka."

Yana gama faɗin haka ya tura kofar ya fice..

 Yana fita, Ahan ya duƙa a gaban Chief Supervisor yana kuka yana riƙe masa ƙafa gami da bashi hakuri. Ba ma damuwa yake yi da makomarsa ta jarabawar ba, gaba ɗaya hankalinsa yana kan Amira dake kwance sumammiya a kasa kamar gawa..

Supervisor ɗin ya kalli Ahan, ya ji tausayinsa ya kama shi sosai domin ya san halin Arman na rashin son wasa da aiki. Ya yi murmushi ya ce,

"Ahan, kwantar da hankalinka ka tashi tsaye...In sha Allahu zamu duba hanyar da zamu lallashe shi har ya haƙura kafin a tura rahoton... Kasan halin yayan naka, shi sam baya duba dangantaka idan aka zo kan gaskiya..."

Daga nan, ɗaya daga cikin jami'an ya ɗauko gorar ruwan sanyi, ya shiga yayyafa wa Amira a fuskarta..

Bayan wasu sekanni, Amira ta ja nishi mai ƙarfi tare da buɗe idanunta dake jawur. Tana farfadowa, ta fashe da wani matsanancin kuka mai ban tausayi, ta fara sambatu tana ƙiran sunan mahaifiyarta..

"Wayyo Uma na...Damar mu ya tafi! Karatuna ya lalace... Wayyo Uma me zan ce miki yanzu? Shikenan rayuwata ta lalace..."

Ta dinga surutai kamar wata zararriya saboda tsananin firgicin abin da ya faru gare ta...

★
★
★NEXT

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol