Free chapter · Read without an account
Chapter 14
INUWAR JIYA
NA
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
Littafi ta ke karantawa. Ƙarar Bus ne ya sa ya ɗaga kai ta kalli agogon hannunta,sannan ta mayar da dubanta kan sauran ɗaliban da suka fara taruwa a wurin atisayen. Yau ya tayi wa kanta alƙawarin ba za ta sake bari tsoro ya hana ta yin abin da ta zo yi a London ba. Juya ta yi kuka a gaban Captain har ya bata hanky ɗin shi, kunya ma take ji yanzu.
"Maisalati."
Ta juya ta kalle shi, shi kaɗai ne yake kiranta da wanann sunan.
"Good morning Captain?"
Captain ne tsaye a gabanta,sanye da Kayan horonsa. Hannunsa ɗaya yana riƙe da ƙaramin fayil,ɗayan hannun kuma yana cikin aljihun wandon sa.
"Good morning."
"Me yasa kike murmushi?"
"Ba komai."
"Allah Ya sa yau kin shirya ɗaukar darasin yadda ya kamata."
"Am ready."
"Good." Ya nuna mata hanyar zuwa filin horon. "Mu gani ko za ki iya tabbatar da hakan."
Ta miƙe da sauri,ta ɗauki kayanta,ta bi shi.
Tana son ta dinga bin bayansa.Duk.lokacin da take bin bayansa ,tana ƙoƙarin hana kanta kallonsa amma duk lokacin da ya juya don ya tambaye ta abu sai ta ji kamar ya kamata tana aikata wani babban laifi."
Da kanta tace da kanta "Yasmin,ki nutsu. Captain malamin ki ne fa." Ta faɗa har tana dukan goshinta da littafin hannun ta.
Ba a ɗauki wani lokaci ba horon ya fara,Rayyan ya rarraba ɗaliban kashi-kashi. Ya bayyana musu aikin da za su yi,sannan ya nuna musu yadda za su gudanar da shi cikin aminci.
Yasmin ta tsaya tana sauraren sa da kyau. Yau bata son ta sake maimaita kuskuren da ta yi jiya.
Lokacin da ya basu damar gwada aikin, ta yi numfashi mai ƙarfi,ta tuna da abinda ya koya musu,sannan ta fara.
A karo na farko ta yi kuskure bata yi daidai ba. Ta tsaya,ta sake duban abin da take yi, sanann ta gyara a karo na biyu sai ga shi ta gane ya yi daidai yadda ya dace ayi.
"Da kyau!" Ta ji Muryar Captain daga bayanta. Ta juya bakinta ya kasa rufuwa.
"Much better,Yasmin. Me ya canja?"
Tayi murmushi tace "I stopped panicking,sir."
Rayyan ya gyaɗa kai.
"Exactly. Wani lokacin, matsalar ba wai baka san abin ba ne tsoro ne yake sakawa kake manta abinda ka riga da ka sani."
Kalaman na shi sun shiga zuciyar ta.
"Na gode Captain."
Bai ce mata komai ba har ya juya sai kuma ya sake juyawa yace "Don't thank me yet. You still have more work to do."
Tayi murmuashi tace "Na san dama haka zaka ce."
Rayyan ya yi murmuashi ya gyaɗa kai ya juya ya koma sauran wurin ɗalinan don ya ga na su aikin su ma.
Ta bi shi da kallo. A karon farko tunda suka fara horo yau ta ji a ranta cewa zata iya yin nasara ita ma."
Bayan sun kamalla aikin safe,ɗaliban suka tafi hutu. Wasu suka nufi wajen shan ruwa,wasu kuma suka zauna suna tattauna yadda horon ya gudana.
Yasmin na zaune a ƙarkashin wata rumfa tana rubuta wasu muhimman bayanai a littafinta lokacin da Captain ya zo ya tsaya kusa da ita.
"Yasmin ko zan iya ganin notes ɗin ki?"
Ta miƙa masa littafin.
Ya karanta a nutse sannan ya sa biyo ya nuna wani wuri da alƙalami yace da ita "Your observations are good , but you need to be more precise here."
Ta matsa kusa kaɗan don ta ga inda yake nuna mata.
"Kamar haka ,Captain."
"Haka."
Ya mayar mata da littafin. "keep it up. I can see the improvement."
Yasmin ta yi murmuashi mai cike da farin ciki.
Rayyan ya tattara takardun horon ne wani abokinsa ya tsaya.
"Rayyan,kwana biyu na ga kana kula yarinyar can."
Rayyan ya daga kai ya kalle shi yace "Wacce?"
"Yasmin."
Rayyan ya mayar da takardun cikin file ɗin shi.
"Kawai taimako take nema ba wani abu ba ne."
"Ai ban ce komai ba."
"To me yasa kake murmushi?"
"Saboda yadda ka ɓata rai daga tambaya. Just a simple question."
Rayyan ya girgiza kai.
"Ba haushi na ji ba, kawai ina yin aikina ne."
Ya ɗaga hannuwansa sama yace "Alright instructor. Na yarda da kai."
Ya juya ya tafi yana dariya a hankali. Rayyan ya bi bayan shi da kallo saboda bai san da akwai wadda ta riga ta sace zuciyar sa ba. Kawai sai ya zaɓi ya gyaɗa kan sa.
Adnan ya tsaya a wurin yana duba inda Yasmin take a zaune. Tana magana da wata ɗaliba,tana murmushi yayin da take nuna mata wani abu a cikin littafinta.Ya tuna yadda ta kasa yin aikin jiya har tana kuka,da yadda yau ya dage har ta samu nasara.
Ya yi murmushi kaɗan. Abin da yake ji shi ne farin cikin ganin ɗalibar sa tana samun ci gaba. Ya san cewa akwai iyaka tsakanin mai horo da ɗaliba. Ya juya ya tafi ofishinsa. A bakin ƙofa ya ji muryar Yasmin a bayansa.
"Captain."
Ya juyo.
Ta zo kusa da shi rike da littafinta.
"Ina son na tambaye ka abu."
"Ina ji."
Ta yi masa tambayar shi kuma ya amsa mata dala-dala,sannan ya tabatar da ta fahimta kafin ya bar ta ,ta koma wurin sauran ɗalibai. Yasmin ta bi shi da kallo har ya shiga cikin ofis ɗinsa. Ta san har yanzu tana da abubuwan da yawa da za ta koya. Kuma wataƙila,a cikin waɗanan abubuwan,akwai buƙatar ga koyi yadda zata sarrafa zuciyarta idan tana kusa da mutumin da ta fara girmamawa fiye da yadda ta yi tsanmmani.
Washegari,Yasmin ta tashi da wuri fiye da yadda ta saba. Ta yi sallah ta shirya kayanta na training ta zauna a gaban mudubin tana gyara gyallenta. Ta kalli fuskarta,sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"Yasmin yau dai ki tsaya a iya aikin ki, ba wai kina tunanin Rayyan ba."
Ta yi murmushi ganin zata zama sauna tana magana ita kaɗai.
Saƙo ya shigo mata.
*Sofy*
_Madan Pilot kin shirya kuwa?_
Ta maida mata da amsa.
_Na gama._
*
Cornflask ya haɗa ya sha , ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin kayansa na pilots kayan da yake matuƙar so kuma in ya sake su suna masa kyau. A maimakon ya fita sai ya dauko wata diary ɗin sa wadda yake rubutu a ciki musamman in yana cike da kewar Rania.
Ya koma ya zauna a kan kujera a gaban tebur ya ɗauko biro dan siriri.
Sai ya kasa rubuta komai kawai ya sa littafin a cikin aljihun wandon sa ya miƙe kamar an tsikare shi, ya fita mota ya hau ya tafi saboda ya ma fara makara. Yana zuwa ba tare da ɓata lokaci ba ya bayar da horonsa bai ma shiga harkar Yasmin ba yau don baya son ta shiga jikin shi tunda har an fara lura da kusancinsu.
Bayan ya gama na shi ya koma wani wuri ya zauna akan wani benci, a ƙarkashin wata rumfa, hularsa ya ajiye a gefe ,yayin da ma'aikatan ke kai-komo wajen shirya jiragen da zasu tashi.
Kamata ya yi yana nazarin bayanan jirginsa na yau, amma tun da ya zauna hankalinsa ya sake karkata ga abin guda tunani ɗaya wato Rania.
Ya zaro diary ɗin da ga cikin aljihunsa ya ɗauko biron ya buɗe sabon shafi ya saka date ɗin.
"Rania." Ya rubuta ya furta sunan sai kuma wani murmushi ya ƙwace masa.Murmushin da babu wanda zai fahimci dalilinsa sai shi kaɗai da kansa. Ya sunkuyar da kansa ya ci gaba da rubutu.
"Yau ma na tashi da tunaninki. Ban san ko yaushe wannan tunanin zai gaji da ni ba. Na yi ƙoƙarin shagaltar da kaina da aiki,na cika lokacina da abubuwan da ya kamata su ɗauke min hankalina daga tunanin ki amma abu ya ci tura da zarar na samu sarari sai ki fado min ya mamaye min komai da ko ina. Wani lokacin na kan yi mamakin yadda mutum zai iya kewar wanda ba ya kusa da shi har ya ji kamar akwai wani abu da ya rasa a jikinsa.Rania,da ace ina da damar gani ki a duk lokacin da na ji kewar ki,da wataƙila na saba da kasancewar ki. Amma yanzu,ko tunanin fuskar ki ya zame mini abin da nake riƙewa saboda ban san lokacin da zan sake ganin ki ba." Yana kai wa nan ya ɗan dakata ya kalli sama yana kallon wani jirgi da ma'aikata suke shirin fitarwa daga hanger. Jirage za su tashi,za su ketare ƙasashe,su kai mutane wuraren da suke son zuwa. Shi kuwa, yana nan ya rasa yadda zai yi ya kai kansa gurin wadda yake so. Ya sake kallon diary ɗin ya kuma rubuta "Rania... Idanun ki na rasa yadda zan yi bayani a kansu. Ba don ban san kalmomin da zan faɗa ba ,sai don duk kalmar da na zaɓa ina ganin kamar ba zata isa ba. Idanuna sun saba ganin abubuwa masu ban mamaki daga sama, na ga giza-gizai suna taruwa kamar duwatsu,na ga fitilun birane suna haskawa cikin dare ,na ga fitowar rana tana tuna sararin samaniya da launuka masu ban sha'awa. Amma babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da ya sa na kasa samun kalmomin bayyana abin da nake ji kamar yadda tunanin idanunki suke min." Ya murmusa ya ɗan girgiza kai. Idan kuna kallona,Rania,na kan manta da abin da nake son faɗa. Wani lokacin na kan ji kamar ban lura da kallon ki ba,alhali kuwa ina lura da komai. Yadda kike ɗan ɗaga gida idan wani abu ya baki mamaki, ko idan na takura miki da magana ki harareni yadda kike cewa Captain...huh! Ya Allah! Na san ya kamata in daina waɗannan tunane-tunanen ƙananun abubuwan a raina. Amma ta yaya zan manta da abin da zuciya take maimaitawa ko da ba na son tunawar?" Ya ajiye biron na wani ɗan lokaci, ya kalli sama yana kallon sararin samaniya. Sai ya ji wata waƙa ta faɗo masa kawai ya ɗauki biro ya sake duƙufa rubutu.
"Idanunki,idanunki Rania,su ne wurin da tunanina yake komawa,ko da jikina yana can nesa. Su ne hoton da nake gani,ko da na rufe idanuna.
Da ace kewar mutum tana da murya,da kun ji suna ki a cikin shirun safiyata.
Da ace zuciya tana iya aika saƙo,da tuni taki ta san abin da nake ɓoyewa.
Domin ina kewar ki ne ba don na rasa ganin fuskarki kaɗai ba,sai don na rasa damar sanin yadda kike, ko kina farin ciki, ko kina murmushi,ko kuwa akwai wani abu da ke damunki. Ina kewar abubuwan da ban taɓa mallaka ba,ina son kusancin da ban san ko zan samu ba,ina riƙe da tunani wanda ban san ko kina da shi kaina ba,idanunki Rania Sulaiman da ma ace zan iya kallon su sau ɗaya kawai,ba don komai ba,sai don in tabbatar wa zuciyarsa cewa abin da take nema tun tsawon lokaci ,har yanzu yana nan."
Ya tsaya ya karanta ya saki wani irin murmushi hatta da dimples ɗin sa sai da suka shige ciki ya sa hannu kamar mace ya rufe fuskar sa yace "Na shiga uku,ni da nake ganin kamar na iya tafiyar da rayuwata yadda nake so,mace ɗaya ta gama rikita ni."
Sai aka kira shi a waya ya daga wayar ta aikinsa ce sai da ya gama ya sake yin rubutu.
_Wata ƙila wata rana zan iya gaya mata komai. Wataƙila kuma zan ci gaba da ɓoye waɗannan kalmomin a cikin wannan littafin har su zama shaidar soyayyar da ban taɓa samun ƙarfin bayyana ta ga mai ita ba. Amma,ko wacce safiya zan tashi in yi aikina,zan shiga jirgi,in yi murmushi ga waɗanda suke tare da ni, in yi magana cikin nutsuwa kamar mutumin da babu abin da ke damunsa. Idan jirgi ya tashi ,idan na kalli sararin samaniya,zan san cewa akwai wani wuri a duniya da tunanina yake son komawa.Wurin nan shi ne inda Ranka take._
Ya rufe diary ɗin,ya sanya shi cikin aljihunsa,sannan ya ɗauki hular shi ya saka.
Daga nesa aka kira shi "Captain Rayyan Zayd lokaci ya yi."
Ya miƙe ya masa alama da babban yatsan sa ya shirya.
*
"Daddy!"
"Baby kin ga ban zo ba ko?"
"Eh."
"Ki yi haƙuri na so na zo sai kuma na ga ya dace na baki dama da lokaci ki sauko da kan ki daga fushin da kika ɗauka da mijin ki. Na baki dama ne don ki gyara gidan ki da kan ki da kuma tsakanin ki da mijin ki. Ƙila da na zo a wancan lokacin ba za ki saurare ni ba burin ki zai zama ki biyo ni saboda kina fushi da shi. Amma yanzu daga jin yanayin muryarki na yarda kin sami sulhu da mijin ki.
Na san Sajjid ba perfect ba ne ke ma kuma ba perfect ba ce a zaman aure sai ana haƙuri da juna kuma sai ana ganin mutuncin juna. Haƙuri shi ne yake kai ga nasara rashin sa ba ya bayarwa. Bana so na san me ya miki amma ina son na gaya miki cewa ni mahaifin ki Sulaiman ina tare da ke da duk wata shawara da za ki yanke zan goya miki baya kuma ba zan taɓa kin sauraren koken ki ba."
Jikinta ya yi sanyi kuma gaskiya ya faɗa yanzu bata jin haushin Sajjid hasalima tausayi yake bata don duk ta ga ya yi laushi. Sai ya lashi leɓɓenta tace "Daddy na haƙura Wallahi."
"Na sani my girl. Ki yi hakuri kin ji ina alfahari da ke saboda ke me biyayya ce na san kina da dreams ɗin ki amma ki ka bi magabata kika yarda kika auri Sajjid ina roƙon Allah da Ya baki kema 'ya'ya masu yi miki."
"Ameen Daddy." Ta faɗa hawaye na zubo mata. Ko don wannan bawan Allahn ta yarda za ta yi haƙuri ta sake bawa Sajjid dama ta ba adadi.
Ɗakin ya buɗe ya shiga kuma yana jin wayar ta da Daddy sai jikinsa ya yi sanyi ya san wanann bawan Allahn yana son yar shi da ita.
Sai da ta gama ya rungume ta ta baya ya matseta kamar zai mayar da ita cikin shi.
"Am sorry wifey. Don Allah ki yi haƙuri da ni da halina ki yafe mini."
Bata ce masa komai na saboda in ta buɗe baki kuka ne zata saka sai ta zaɓi gyaɗa masa kai kawai.
Ya sake matse ta jikin shi ya kai bakin sa kan wuyanta ya sakar mata sumba ta lumshe ido.
Ya cire kai yace da ita "Tashi ki shirya muje shopping."
Ta ɗan juya ta kalle shi ba wai ba sa zuwa ba amma ana jimawa ba a je ba.
"Da gaske nake miki. Cin hanci zan baki."
Ta miƙe ta shige banɗaki. Kafin ta fito ya ɗauko mata wata abaya milk ce ta daku ta ji kuɗi. Da undies da takalmi da wata jaƙa yar ƙarama duk ya ɗauko mata. Tana fitowa ta gani tayi murmushi don ta ji daɗin yadda ya yi ɗin. Ya sumbaci goshinta ya shige banɗakin kan ya fito ta gama duk wasu shafe-shafen ta har ta saka kaya. Ya taya ta fake gashin kan ta.
"Na gode."
Ya sumbaci leɓɓenta yace "Ba wani thank you."
Basu wani ɓata lokaci na suka fita. Shi ya yi tuƙi har suka isa wani babban super market ya yi parking suka shiga tare. Hannunsu cikin na juna. Suna tafe suna hira da ka gan su ka ga mata da mijin da ke ji da junansu.
Shi ya taya ta ɗiban duk abinda take so bai damu da nawa aka kashe ba. Sun je section ɗin chocolates ne tana zaɓa idanunsa suka sauka akan wata budurwa cikin matsatsiyar riga ta yi masa kyau dirin ta ya burge shi gata yar duma-duma ya sauke wata ajiyar zuciya cikin ikon Allah budurwar nan ta juyo idanunsu suka haɗu da juna ga mamakin sa sai ya ga ta sakar masa murmushi har tana ɗaga masa hannu. Ya juya da sauri sai ya ga hankalin Rania baya inda yake.
Ita ma budurwar sai ta leƙa inda yake kalla sai ta ga mace a gefen shi.
Yana son ya je baya son Rania ta gan shi ko ta gane shi. Shi fa idon sa idon yar kyakkyawa baya iya ɗauke kai sai ya tanka. Haka ya sa da sauri ya juya yace da Rania.
"Babe, ga key je ki ɗauko Atm ɗin nan na manta shi." Bata kawo komai ba ta amsa ta bi hanyar fita ta fita daga cikin supermarket ɗin.
Da sauri ya isa wurinta yace "Hi! Sunana Sajjid."
"Hello. Sunana Ni'ima
"
Ba zan ɓata lokacina ba kar matata ta dawo bani lambar wayar ki zan kira ki sai muyi magana da ke a waya."
Tana yauƙi da iyayi ta karanta masa lambar ya kirata tayi saving sannan suka rabu.
"Sajjid,ban gani ba a ina ka ajiye kar dai ka yi halin ka manta a gida?"
"A'a kin gan shi ma a aljihun gaba ashe."
Ta ɗan harare shi tace "Kai kam baka da dama."
Ya yi dariya ya kama hannunta suka yi gaba. A wurin biyan kuɗi suka sake haduwa da Ni'ima ta sakar mai murmushi haɗe da yi masa fari da ido ya yi saurin ɗauke kai kar Rania ta gan shi ya yarda kuma ya gamsu,yar hannu ce wanann ba zata ba shi wahala ba zata ba da kai bori ya hau.
"Sajjid me kake kallo ne?" Rania ta tambaye shi haɗe da haɗe rai.
"Ba komai me zan kalla kuwa?"
"To ka sa pin mu tafi mana."
Ya biya aka tattara komai suka fita a bayan mota aka zuba musu ledojinsu. Suka shiga suka ɗauki hanya. A hanya ma sai da ya sai musu tsire mai zafi da yogurt sannan suka tafi.
Bai samu lokacin kiran Ni'ima ba sai biyun dare shi ma da Rania tayi nisa a bacci. Ya salallaɓa ya fita waje can harabar gidan ba ma a ciki ba saboda baya son a samu matsala ma don tana da jin motsi kamar me ba zai yi aune ba za ta fito bare kuma yau ya samu ya shawo kanta ta sake ganin wanann kuma gagarumar matsala za a samu ba ƙarama ba.
Ni'ima da ta mato da Sajjid ta yi zaune zaman jiran kira daga Sajjid. Tana sane ta bi su tun shigowar su a babbar mota da suka fito ya mata da ta ga yadda yake wa matar kuma ya kwaɗaita da shi, cikin ikon Allah kuma sai ga shi irin ta ne ba ta wani sha wuya ba da kan shi ya kawo kan shi.
Tana taunar cingum kira ya shigo mata sarai ga gani amma sai tayi jan ajin nan na mata. Sai da ya sake kiranta sannan ta ɗauka.
"Hello."
"Hello yan'mata. Fatan kin koma gida lafiya?"
"Lafiya ƙalau amma ban gane ka ba."
"Babu laifi girman kujerar ki ne Hajjaju. Sajjid ne."
"Oh! Ya kake?"
"Lafiya ba lafiya ba."
"Mene ne?"
"Kece kika sace zuciyata daga kallo ɗaya."
Tayi dariya haɗe da cewa "Sharri ina abin yake?"
Ya mayar da wayar daya ɓarin yace "Babu sharri yan'mata wani abin ma ba zan iya faɗa ba. Baki ga na kasa bacci ba na fito na bar Madam na zo sake jin muryar ki."
"Har kasa na ji kunya."
"Duk ba wannan ba an taɓa gaya miki muryarki na da daɗi kamar busar sarewa?"
Ta saki dariya da gaske ya bata nishaɗi irin shi take so kuma.
"Yau dai an gaya min, na ji daga bakin Sarkin iya magana."
"Sunan da aka bani kenan?"
"Babu wai."
"To na karɓa. Ba tare da ɓata lokaci ba ina son gobe mu haɗu mu keɓe na san kin gane karatun?"
"Girman ka ne Yallaɓai duk yadda kake so haka za ayi."
"To muyi waya da safe kawai sai ki bani adireshin."
"Baka da matsala."
Yana buɗe ƙofar shiga ciki ya ganta a tsaye hannunta naɗe da ƙirjinta ta ƙura masa ido. Amma da yake namijin duniya ne sai ya fuske yace "Ba dai na tashe ki ba?"
Ta taɓe baki tace "Um'um ba ka tashe ni ba amma ban taɓa ganin kana waya da dare haka ba."
'wallahi business call ne dole ne ya sa na ɗaga wayar."
Da yake shi expert ne a waskiya sai yace da ita "Babe,anya kuwa kin yarda da abin da na gaya miki?"
"Ba haka ba ne kawai ban san kana waya da dare ba ne."
"Ga wayar ki duba. Ki gani."
Ta masa wata harara sannan tace "Da ma ina amsar wayar ka ne?"
"To ai na ga kina min kallon rashin yarda ne."
Ya ja hannunta suka shiga cikin daki ya kalallame ta ya samu ya more ta kafin suka yi bacci.
*
Washegari kan ta fita ma ya riga ta fita. Saboda haka bata tsaya ma yin wani girki ba. Tea kawai ta sha ta haɗa da wainar ƙwai. Yau tana da ayyukan yi sosai a ofis.
Tana parking suka haɗu da Nadiya suka kalli juna suka saka dariya haɗe da tafawa.
"Idon ki kenan?"
Ta kama haɓarta tace "ke rabani da wahala haka yake wai?" Ta faɗa ta fashe da dariya.
"Ke kam anyi matsoraciya."
"A'a ina lallaɓawa Sukooni kaina kawai wannan mutumin ya zo ya make ni kawai. Ai ni da gidanki har abada yar nan."
Ta fashe da dariya tace "To ya za ki yi da ni?"
"Mu dinga haɗuwa a ofis da waya ba dai a gidan Sajjid ba."
"Yanzu kika zo?"
"A'a airport dai zan je."
Airport da ta faɗa sai da ta ji wani abu ya dawo mata har ta soma tunanin sunan hakan nan ta saki dariya a hankali tace "Captain Ray,once upon a time."
"Na ga kina dariya."
Ta girgiza mata kai tace "Ba komai wani abu na tuna da ya shuɗe."
"Ya yi. Bari na tafi kar ayi ta jirana covering za mu yi."
"To sai kin dawo."
"Ahan."
*
Wata aniyar rigar bacci ta saka baƙa mai shara-sahara duk da rana ce ba duhu ba amma haka ta zage ta bayyanar masa da surarta.
Tun da ta buɗe masa ƙofa ya ganta a haka ya haɗiyi wani kalar yawu ya ɗauke kai sai kuma ya yi murmushi ya matsa kusa da ita sosai kamar sun saba daman. Cafka ɗaya ya yi mata ya ji wani irin fitinannen ƙamshi ya doki hancinsa har ya soma shinshinar wuyanta kamar wani tsohon maye. Da yake ita ma irin shi ce sai ta saki jiki suka haukace da ƙyar ta iya rufe ƙofa suka shiga ciki.
"Ha! Wato mai sai da diamond shi ya san darajar diamond. Kallo ɗaya nayi miki na ji kin shiga raina ashe kuwa nayi zaɓen daidai kin ji ki kuwa?"
Ta yi wata dariya irin ta yan duniya amma bata ce da shi komai ba. A kan ƙirjinsa ta lafe tana wasa da gashin da yake ƙwance a kan ƙirjinsa.