Free chapter · Read without an account

8

by Zainab Amzah · Nour Ayn



A ranta ta ce “Ashe dai da gaske ne da aka ce idan an yi aure wasu na rabuwa da azababben ciwon nan? Daman Farha ta sha faɗa mini haka. Ashe dai da gaske ne? Da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga Google ta fara searching. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama karanta bayanin. Ta ce, “Allah ya sani ina shan wahala sosai ma ba kaɗan ba. Ni kaɗai na san irin azabar da nake ji a jiki na har tsoro nike in ga an shiga sabon wata. Amma duk da haka, ka yi haƙuri ya Fahad, ba ni da burin yin aure a yanzu. Karatu shine gabana. Allah ya sani ina sonka, zuciyata bata san kowa ba sai kai. Kai na buɗe ido na fara gani. Kai ne komai nawa. Amma kayi haƙuri, ba zan iya ba, ba zan iya amincewa da bukatarka a yanzu ba.” Ta daɗe zaune tana tunanin. Horn din da ta ji ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta yi nisa a cikin sa, da sauri ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta sauko. A hankali take saukowa daga staircase ɗin, wani sassanyan kamshi ne ke tashi a parlor tare da sanyin AC da ya haɗe gabaɗaya ya ƙara wa kamshin daɗi. kitchen ta wuce ta ɗauko tsadaddun food warmers ɗin da ta ajiye. Ta yi setting table gwanin ban sha’awa, sai da ta tabbatar ta ajiye komai da zasu buƙata sannan ta fita zuwa taro Daddy. Tana fitowa ba tare da ta lura ba ta buge Faruk da ya shigo parlor ɗauke da kayan daddy a hannunsa. Sosai ta ji gabanta ya faɗi, cike da fargaba ta Ɗago kai ta kalleshi, shi ma kallonta yake a lokacin fuskarsa a daure. Muryar ta na rawa ta ce, “I’m.. I’m sorry yaya.” Wani irin kallo ya yi mata da ya hana ta ƙarasa faɗin abin da ta yi niyar faɗa. Suna tsaye a haka, ita bata wuce ba shi kuma bai bata hanya ba, gaban ta sai duka yake saboda yadda Faruk ya tsare ta da ido, suna a haka daddy ya shigo tare da Nadiya dake bayansa tana riƙe da hannunsa. Dawowarta kenan daga school. Malam TK na gama parking sai ga horn ɗin Ya Faruk da ya ɗauko daddy daga airport. Tun kafin Faruk ya gyara parking ta nufi motansu. Daddy na fitowa da gudu ta je ta rungume shi, sai da suka gaisa sannan suka shigo gidan tare. Faruk ya zagaye ta ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba. Da sauri Mimi ta ƙarasa wurin daddy ta ba shi side hug itama, sunyi missing din Daddy sosai, bai taba tafiya ya dade sosai kamar wanna ba. Ta ce “Daddy welcome.” Ya ce “Thank you mamana, ya kuke?” “Lafiya lau daddy barka da dawowa.” Suna cikin gaisawa sai ga Ammi tana saukowa da murmushi mai kyau a fuskarta. Wani irin sanyi ta ji lokacin da suka yi four eyes da daddy, shi ma daga wurinsa hakan ya ji. Allah ya sani ba ƙaramin kewar mijinta ta yi ba. Three months ai ba wasa ba. A hankali ta ƙarasa kusa da shi, ta ƙasa haƙura ta rungume shi tana murmushi. Faruk ya ɗan shafa kansa yana murmushi tare da ɗauke idonsa. Nadiya ta yi sauri ta ɗauki wayarta ta fara masu pictures ba tare da sun lura ba. Mimi ta ajiye kanta a ƙasa tana murmushi. Nadiya nata washe baki, tana dagowa su ka yi four eyes da Faruk, da sauri ta daina dariyar da take ta sunkuyar da kanta kasa, zaune suke gabadayan su a dining table suna dinner cike da kauna da tattalin juna. Bayan sun gama dinner sunyi sallah isha’i, suka zauna suna yin hira da daddy. Kowa na nuna irin yadda ya yi missing ɗin sa. Musamman Mimi, sun jima suna hira har sai da dare ya yi nisa sosai sannan daddy ya yi masu sallama ya tafi sama ya huta. 

Washegari gabaɗayansu suka ta fi school saboda morning lectures gare su. Ga CA test da zasu fara next week. Bayan su Mimi sun fito daga lecture suna zaune a dai dai spot ɗin da suka saba zama Ita da friends dinta. Zeezee na ta yi mata magana amma mind dinta na wani wuri daban. Zeezee ta ɗan taɓa ta, sai a sannan ta dawo daga tunanin da ta yi nisa a kai. Tace “Mimi, tunanin me kike yi haka? Munata magana har ba ki ji ba?” Mimi tayi shiru kamar baza tayi magana ba. After some seconds ta ce, “Farha, ina da ɗan damuwa ne amma ba da yawa ba.” 
“Subhanallah! Wace irin damuwa?” Zeezee ta tambayeta. Bata boye masu komai ba, ta kwashe duk maganar da sukayi da Fahad jiya a waya ta faɗa masu. Farha ta yi dariya, tace, “To ke yanzu Mimi minene abun damuwa a ciki? Naga ɗan’uwanki ne kuma kuna son junanku. Kuma abin da ya gaya miki gaskiya ne. Mun sha faɗa miki hakan amma sai kike ganin kamar ba haka ba ne. Bari in ba ki labari, step sister na Ya Ikram, wallahi haka take fama da azababben ciwon nan. Ita fa har suma take wani lokacin. Amma wallahi tunda tayi aure bata sake yi ba.” Mimi ta sauke ajiyar zuciya, sannan tace, “Ba zaki gane ba Farha. Bawai ban yarda da abin da kuke faɗa ba ne. Kawai auren ne ban shirya yin sa yanzu ba. Ina da burin yin karatu mai zurfi sosai.” 
“Amma dai kin san Ya Fahad ba zai hana ki ci gaba da karatunki ba. Kuma aure bai hana karatu Mimi. Matan aure nawa kika sani a school ɗinnan? Ko a department ɗinnan namu matan aure nawa kika sani? Su Mommy Ayman da Mommy Rafeeq. Waye zai gansu ya ce ma suna da aure idan basu suka faɗa ba? Kuma Lafiya lau suke karatunsu ba tare da wata damuwa ba. Kin ganni nan Mimi. Wallahi idan da ina da tsayye wallahi aure na zan yi. Kinga Ishaq, parents ɗinsa sunce ba yanzu za suyi masa aure ba. Sai nan gaba saboda yayansa bai yi aure ba. Don haka ba zasu barshi ya riga yayansa aure ba. Sannan yayansa kuma ba auren ne a gabansa ba yanzu. To da ace sun amince masa wallahi da tuni na tura shi wurin daddy. Ke ki gode wa Allah kina da mai son auranki a wannan era ɗin da maza sun baci na Allah basu da yawa, bare irin su Ya Fahad. Ki zauna nan kina wani shirme naki, wallahi kina nan zaune sake da baki wata za ta yi miki wuff da shi.” Wani uban dundu Mimi ta sakarwa Zeezee a baya. Duk da maganar da wasa ta fade ta amma ta dakar mata zuciya, don Mimi nada kishi sosai ma ba na wasa ba. Ta ce, “Insha Allah hakan bazai taɓa faruwa ba, muguwa kawai.” Zeezee ta kwashe da dariya ita da Farha, ta ce, “Kece muguwa ai da zaki karya mini baya da wannan uban dundu da kika sakar mini, ni wallahi rabon da ayi mini dundu har na manta, kuma wallahi ba shi kika ci, don sai na rama ko ba yanzu ba. Ana so ana kaiwa market.” Dariya suka yi gaba ɗayansu har da Mimi. Farha tace, “Zeezee Allah ya shirya ki wallahi.”

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol