Free chapter · Read without an account

Chapter 6

by Fatima Usman Abdullahi · UQUBA

‎BY
‎
‎FATIMA USMAN 
‎SHA LELEN TERAWAN GAMJI.......
‎
‎
‎
‎
‎Salati Amo ta sa tana kiran sunan Ajimal '
‎Ajimal.... Ajimal....
‎Kai Ajimal ,,
‎Shikenan na shiga uku malam Rafi 'a ta rabani da d'a na.
‎
‎Shegiya algun guma kawai '
‎Baqar ashana qona gari , y'ar tallen guba y'ar tallen turmi a kasuwa '
‎Allah ya d'aga garinki iska ya kwashe .
‎
‎Haka Amo tayita zagin Rafi 'a tana fad'a mata mugayen maganganu "
‎Ajimal kuwa yana fita ya nufi d'akin abokinsa guduma,
‎
‎Kwanciya kawai yayi ya rasa abunda yake masa dad'i a duniya '
‎Gaba d'aya idanunsa sun kad'a sunyi ja"
‎Zuciyarsa tanayimasa wani irin zogi kamar zata fashe ,
‎Ganin kamar ana qaramasa damuwar ne yasashi miqewa da sauri '
‎Ya miqa hannun ya kar'bi tabar da guduma yakeshe da niyyar kaiwa bakin sa,,
‎
‎Da sauri guduma ya riqe hannun sa ya kwace tabar sannan ya ce"
‎Kai Ajimal......
‎Ka rasa tunanin ka ne?Abunda tunda kake baka ta'ba yi ba shine kuma yau zaka fara da rana tsaka?
‎Ko ka manta kaine kake hanani shan kayan maye kana fad'amin batada fa ida a hankace da lafiyar jiki.
‎
‎A iyakar sanin da nayimaka,
‎Ko a wasa baka ta'ba shan kayan maye ba Kuma ko wani bakaso kaga yana sha kaf anguwar nan babu matashi me hankali da nitsuwa kamar ka dan Allah kada ka canza kanka" 
‎Ka fad'amin matsalar ka Ajimal zamu maganceta '
‎Amma dan Allah kar ka fara shan kayan maye .
‎
‎Kallon guduma yayi da idanunsa da tuni suka kad'a sukayi ja yace,
‎Ka bani dan Allah "
‎Ka bani abunda zan sha na manta da ita,
‎Kabani abunda da zesa na manta da damuwata gaba d'aya,,
‎Guduma dan Allah kabani kar zuciya ta ta fashe '
‎
‎Se a lokacin ne wani kuka me qarfi ya kwace masa,,
‎Bashida iKon dakatar da shi,
‎Saboda haka se ya durqushe a gurin ya saka hannayensa duka biyu ya riqe kansa ya fashe da wani irin kuka me qarfi kamar ransa ze fita .
‎
‎Guduma yayi iya qoqarinsa wajen ganin ya shawo kan Ajimal ya fahimtar da shi amma abu yaci tura '
‎Domin Ajimal baya iya fahimtar komi "
‎Hakan ne yasa dole guduma ya d'auko wata k'waya ya jiqa ya bashi.
‎
‎Aure ya matso sosai gobe za a d'aura akai amarya Rafi 'a d'akin ta,
‎Amma idan ka ganta bazakace itace amaryar ba "
‎Amo ce da kanta ta zauna tayiwa Rafi 'a wani d'an iskan lalle marar dad'in gani '
‎A cewar ta tunda suma sun iya base sun kashe kud'insu ba .
‎
‎Aka kira wata y'ar maqotansu da take koyan dayis ta zauna ta kwa'ba mata hannu yayi baqi qirin ,,
‎Babu gyaran kai....
‎Kitso ma basu wuce guda ashirin ba akayi mata,
‎Gaba d'aya ta rame tayi zuru zuru da ita '
‎
‎Ba Rafi 'a kad'ai ba har baffa kana ganinsa kasan yana cikin matsanancin damuwa da tashin hankali,
‎Alamu sun nuna ransa bayason auren"
‎Amma yana tsoron ja da maganar Amo.
‎
‎Ranar aure ranar da ko wace mace take burin gani a rayuwar ta,
‎Rana ta musamman da tafi kowacce rana a cikin rayuwar duk wata mace '
‎Ta kasance ranar da tafi ko wacce duhu da qunci a cikin rayuwar Rafi 'a ,,
‎Rafi 'a tayi kuka kamar zata mutu '
‎Tun tana iya kukan da hawaye har ta dena iyawa.
‎
‎Rafi 'a naji tana gani aka d'auketa aka kaita gidanta"
‎Wannan ranar ta zama baqar rana a gareta,
‎Ji takeyi inama ace ta mutu kafin wannan ranar' 
‎Tanaji tana gani aka watse aka barta a d'an qaramin d'akin ta kamar zuciyar talaka.
‎
‎Gaddafi be shigo gidanba se qarfe sha d'aya da hamsin da uku '
‎
‎Rafi 'a ta takure a can qarshen tsohuwar katifar da aka sayamata a gidan wata dillaliya ,,
‎Ta had'e kai da guiwa se kuka take,
‎Tanajin shigowarsa se warin wiwi yake yana layi kamar ze fad'i.
‎
‎Wani irin tsoro ne ya kama ta.....
‎Jikinta ya d'au kerma kamar zatayi fitsari a jikinta dan tsoro"
‎Ledar hannunsa ya ajiye ya fad'a kan katifar ba tare da ya cire koda takalmansa ba.
‎Batasan sanda wani sabon kuka me qarfi ya kwace mata ba ,
‎Wayyo Allah na shiga uku....
‎Shikenan rayuwata wayyo ni Rafi 'atu.
‎
‎Wani irin firgita tayi duk jikinta ya d'au rawa saboda wata iriyar tsawa da ya daka mata '
‎Ke dallacan malama kimin shiru kin dameni.
‎Hannu ta sa ta toshe bakinta da qarfi saboda wani sabon kuka da yakeson kwace mata ,,
‎
‎Tashi kije ki d'auko min kwano a kitchen '
‎Ya fad'a cikin tsawar da ta sakata miqewa ta fice daga d'akin da gudu tana kuka"
‎Seda ta d'an jima kafin ta dawo domin batasan Kitchen d'in ba ,
‎
‎A tsorace ta durqusa ta miqa masa kwanon jikinta na rawa.
‎Ledar yasa ta d'auka ta juye abun ciki "
‎Dankalin hausa ne soyayye da quli  ,,
‎Seda ya ja yaci sannan ya miqamata sauran '
‎
‎Ta kar'ba ta koma gefe ta zauna,
‎Amma ta kasa ci se hawaye take .
‎Jiranki fa nakeyi zakici ne ko se ranki ya 'baci?
‎
‎Yadda yayi maganar cikin tsawa ne yasata janyo robar dankalin ta fara turawa jikinta na rawa.
‎
‎Muazzam na shigowa umai ma ta tareshi da sauri '
‎Yaya Muazzam sannu da shigowa ,,
‎Yauwa umai ma.....
‎Yau naganki cikin farin ciki kode akwai labari ne?
‎
‎A'a '
‎Kawai de yau na tashi cikin farin ciki ne Masha Allah dama nafiso kullum naganki cikin farin ciki.
‎Umhm.......
‎Yaya Muazzam yaufa girki nayimaka da kaina  ,
‎
‎Wow"
‎Wallahi kamar kinsan na dawo da yunwa kuwa ,,
‎Me kika dafamin?
‎Tuwon semo da miyar ku'bewa da kunun aya me sanyi.
‎
‎Wow.....
‎Gaskiya bazan iya jira se nayi wanka ba kawai kizo ki zubanin yanzu naci '
‎Bayan ta zubamai ta nemi guri ta zauna a kusa da shi ,,
‎
‎Gaskiya umai ma girkin nan yayi dad'i sosai ,
‎Me kikeso na baki a matsayin tukuici?
‎
‎Duk abunda nakeso zaka bani?
‎Eh gaskiya yau kin cancanci samun duk abunda kikeso domin girkin nan yayi dad'i sosai '
‎Inda Mark za a bada na tabbata sekin cinye dubu bisa d'ari.
‎
‎Har cikin ranta taji dad'in yabon sosai domin tanaso taga Muazzam yana yabon komai nata "
‎Kayi alqawarin zaka bani duk abunda nake so?
‎
‎Yeah"
‎I promise you ,
‎Kede kawai ki fad'amin koma me kike da buqata.
‎
‎Kai nakeso yaya Muazzam ,,
‎Zuciya ta ta jima tana dakon soyayyar ka babu dare babu rana '
‎Babu wata kyauta mafi girma da zakayimin da ya wuce ka mallakamin kanka da zuciyar ka.
‎
‎Ta fad'a a cikin ranta' 
‎Amma a fili se tace ,,
‎So nakeyi ka kaini wajen shan ice cream yau da yamma ,
‎
‎Gaskiya umai ma kin cika son yawo da yawa fah "
‎Kinriga kinsan Momi batason wannan yawon fah  '
‎Amma ke kullum bakida aiki se son yawo ,
‎
‎Kwata kwata bakyason zaman gida kuma nide da bansanki da yawo ba"
‎na rasa waye ya 'batamana ke da yawo .
‎
‎Soyayyar kace ta 'batani yaya Muazzam '
‎Jinakeyi inason kasancewa tare da kai a ko da yaushe "
‎Saboda ina neman abunda ze qara kusantani da kai ne shiyasa kullum nakeson fita tare da kai.
‎
‎Ta fad'a a zuciyar ta sannan tayi dariya tace ,
‎Wallahi yaya zaman gidan ne gaba d'aya babu dad'i "
‎Kullum kana gida ai dole akwai gajiya.
‎Kuma nasan kai kad'ai ne zaka iya shawo kan Momi ta bari mu fita,
‎
‎Okay "
‎To ki shirya ,,
‎Amma daga yau bazan qara kaiki yawo ba '
‎Dan kar Momi tace ina 'bataki da yawa.
‎
‎Tun qarfe hud'u da Rafi 'a ta tashi bata koma bacci ba ''
‎Ta fito ta share gidan tsaf ta gyara ,
‎Ta d'ebo kwanukan da y'an biki suka 'bata ta wanke '
‎
‎Ta d'ebi ruwa tayi wanka ta dawo qofar d'akin ta zauna,,
‎Saboda tana tsoron kar Gaddafi yace ta takura masa yana bacci ,
‎Sanyi takeji sosai ga wani irin yunwa na kwaqular cikin ta.
‎Gashi ba a kawota da ko k'wayar shinkafa gidan da sunan gara ba.
‎
‎Haka taci gaba da zama a qofar d'akin tana jiran Gaddafi ya tashi daga bacci ko ze bata abunda zata dafa ta sakama cikinta"
‎
‎Be tashi ba se kusan qarfe sha biyu da kwata ,..
‎Lokacin Rafi 'a tayi alwalar sallar azahar.Da sauri ta durqusa a gaban sa ,
‎Ina kwana....... 
‎Ko kallon inda take beyiba ya miqe ya shige band'aki '
‎
‎A tunaninta alwala zeyi ya fito amma ga mamakinta yadda ya shiga haka taga ya fito' 
‎Babu alamar yayi wanka ko alwala.
‎Ke ina abinci na?
‎
‎Ban ban dafa ba......
‎Rafi 'a ta fad'a cikin rawar murya kamar zata fashe da kuka ,,
‎Ban gane baki dafa ba me kike nufi?
‎
‎Babu abunda zan dafa ne shiyasa ban dafa ba '
‎Dama ina jira ne idan ka tashi daga bacci se ka kawo na dafa  "
‎Ke tsabar kin renamin wayo me kike nufi da babu abun dafawa?
‎
‎Kina nufin wannan tsohon uban nakin be had'oki da gara ba kenan?
‎Koda yake najima ancefa ked'in shegiya ce ashe bakida uba y'ar tsintuwa ce ko,
‎
‎Amma duk da ke y'ar tsintuwa ce ai ya kamata a kawoki da gara da kayan d'aki tunda ai ba gidan qanin ubanki za a kawoki ba "
‎
‎Sosai maganar tayiwa Rafi 'a ciwo,
‎Dama Amo ce tace tunda kai d'an aminiyar ta ne base an kawo komai ba ,,
‎To se me idan ni d'an aminiyar ta ne?
‎
‎Ai ba ita za a kawowa ke ba tunda ba ita zata ciyar da ke ba,
‎Dan haka bana buqatar ta yankemin hukunci akan gida na.
‎Saboda haka inaso ki saurareni '
‎
‎Akwai wasu dokoki da qa idodi da zan sakamiki "
‎Inde kinason zama a gidan nan dole se kin bisu.
‎
‎Doka ta farko itace,
‎Daga nan zuwa wata guda bazan sayo ko k'wayar abinci na kawo gidan nan ba har se lokacin da naji ya kamata ace gara ta qare.
‎
‎Doka ta biyu '
‎Ko da na fara kawo abinci gidan nan ba kullum zanna kawowa ba ,,
‎Domin nasan ko a gidan ku ba kullum kike ci ba.
‎Sannan kuma koda zan kawo sau d'aya ne a rana"
‎Ko ya isheki ko be isheki ba ai a gidan da ake riqonki ko sau d'ayan bakya samu ,
‎
‎Doka ta uku ,,
‎Idan ina bacci ba a tashi na komai tsananin buqatarki dole ki jira sena tashi kada kiyi kus kuren tashina ko da wasa ,
‎idan kikayi hakan zaki fiskanci mummunan hukunci daga gareni '
‎
‎Doka ta hud'u ,,
‎Duk ranar da na kawo y'an mata na cikin gidan nan,
‎Zaki fita ki barmana d'akin har se mun gama abunda zamuyi.
‎
‎Doka ta biyar ,,
‎Ban yarda ki aihu a gida na ba '
‎Domin bazan yadda na had'a zuri a da wacce bansan asalin ta ba"
‎Sannan Kuma ki sakawa ranki bauta kikazo yi gidan nan saboda haka ki tsaya a matsayinki na baiwa domin zamanki a gidan nan qalilan ne ,
‎
‎Na d'an wani lokaci nekawai idan kin gama yimin amfani dole kibar gidan nan ,,
‎Sannan Kuma ki nemarwa kanki abunda zakici domin na fad'a miki '
‎Bazan kawo abinci cikin gidan nan ba se bayan wata d'aya ,
‎
‎Yana gamawa ya fice ya barta a durqushe a gurin tana wani irin kuka me ban tausayi"
‎Se yanzu ta tabbatar ta shiga uqubar rayuwa '
‎Se yanzu ta tabbatar rayuwar gidan Amo kamar aljannah ce,,
‎
‎Se yanzu ne tasan tashiga asalin wahalar rayuwa ,
‎Wasu hawayen tausayin kanta suka sulalo mata '
‎Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un.
‎

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol