Free chapter · Read without an account
Chapter 7
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA..,.....
Kusan qarfe hud'u da wani abu na yamma '
Rafi 'a ta takure a can dungun d'akin ,,
Tun safe batasa ko ruwan kunu a cikin ta ba .
Ga d'akin ya d'au zafi sosai domin ko silim babu ,
Gashi ko ta ina a jikin rufin d'akin a 'bule gashi ana rana sosai tsabar rana har wani irin qara saman kwanon yakeyi "
Tunanin irin sabuwar rayuwa me cike da qalubalen da ta shigo takeyi '
Wani irin dad'i ne ya kamata saboda jin muryar Ajimal.
Duk da taji canji sosai a tattare da muryar ,,
Muryar sa ta fashe sosai ta qara kauri da girma '
Duk da taji kamar baya cikin hayyacinsa amma hakan be hana ta gane muryar sa ba "
Da sauri ta fito tana mur mushi sede ganin Ajimal ya canza mur mushin ta zuwa hawaye '
Domin bata ta'ba tunanin akwai ranar da ko da a mafarki zataga Ajimal cikin irin yanayin da ta ganshi ba.
Idanunsa sunyi jazur se layi yake kamar babu qarfi a jikinsa,
Kallo d'aya zakayimasa kasan baya cikin hayyacinsa "
Da gudu ta qaraso ta rungumeshi tana kuka ,,
Yaya Ajimal meye wannan?
Me ya sameka haka naga gaba d'aya ka canza meyasa kakeson lalata rayuwar ka ka tarwatsa goben ka da kanka?
Ke babu komai fah.
Ya fad'a yana jan hannun ta suka shiga d'akin ,,
Rafi 'a.....
Wannan shine d'akin da aka kawoki?Kamar gidan bredi '
Dan Allah ki qara haquri Rafi 'atu inaji a jiki na kamar wahalar ki ta kusa qarewa,
Ajimal yayiwa Rafi 'a fad'a sosai'
Sannan ya tambayeta ko tanada wata matsala,,
Batada za'bi haka ta fad'a masa gaskiya domin idan ta 'boye masa batasan a ina zata dinga samun abinci har na tsawon wata guda ba .
Sosai ya bata haquri ya sayomata kayan abinci ya ajiye mata yace '
Kiyi haquri kinji Rafi 'a ba iya na wata d'aya ba kawai ko zuwa yaushe ne inde be baki abinci ba kar ki sake ki tambayeshi "
Babu ruwanki da tambayansa komai inkin samu kici idan kuma baki samuba ki haqura ,
Sannan ya ciro dubu goma ya bata yace ta dinga sana a da su dan ta dinga samun abunda zataci Kuma ta biyawa kanta buqata.
Sosai Rafi 'a taji dad'in zuwan yaya Ajimal tayita masa godiya,,
Taliya da manja ta dafa taci sannan ta tashi ta shiga maqota ta nemi yarinya ta aiketa kasuwa '
Kayan miya ta saro mata da madarar yin alawar madara.
Tass........ Tass.......
Momi ta d'auke umai ma da wasu kyawawan maruka wad'an da suka haifar mata da ganin taurari a idanun ta,
umai ma ashe bakida hankali?
Duk mazan duniya ki rasa wanda kikeso a matsayin miji se Muazzam '
To bari na fad'amiki gara ma ki cire a ranki tun cirewa na da sauqi ,,
Dan wallahi ko maza sun qare a duniya bazan ta'ba bari ki auri Muazzam ba.
Momi wallahi inason yaya Muazzam kuma bazan iya rayuwa babu shi ba "
Moni wallahi shi kad'ai ne farin ciki na banajin zanyi farin ciki idan ba tare da shi ba '
Sanin kanki ne munada target sosai a kan Muazzam '
Idan kika aureshi kamar kin 'bata duk wani shirin da mukeda shi a kansa na tsawon shekara da shekaru ,,
Saboda haka inaso ki gaggauta cire soyayyar sa a ranki kuma sunansa ya fita daga bakinki.
Bazan iya ba Momi.....
Wallahi bazan ta'ba iyawa ba"
Inason yaya Muazzam ,
Kuma wallahi sena aureshi ko ta yaya ,,
Duk dunuyar nan babu wanda ya isa ya hanani mallakar sa a matsayin miji.
Se a lokacin dady da ke zaune yana kallon su yace '
Kar ki damu umai ma inde Muazzam ne kamar kin mallakeshi "
Inade kina son shi?
Eh dady..,....
umai ma ta fad'a babu alamar jin kunya a tare da ita.
Shikenan zamusan abun yi kije zanyi magana da Momi nnaki Kuma itama nasan zata amince ,
Toh dady.....
umai ma ta fad'a tana mur mushin jin dad'i sannan ta juya ta fice daga d'akin.
Haba Alhj '
Ya zaka biyemata kawai saboda farin cikin ta ka rusamana shirin da mukayi shekaru munayi?
A kan Muazzam fa ake magana kuma kabata tabbacin auren shi "
Duk da kasan hakan dede yake da wargaza mana duk wani shirin mu,
Haba Alhj.......
Taya zaka 'bata mana shiri lokaci d'aya kawai saboda umai ma tanason Muazzam?
Seda dady yayi dariya ya zare glass d'in fuskarsa sannan yace '
Babu wani abu da ze 'batamana shiri,,
Kinfi kowa sanin nafi kowa son shirin nan ya tafi dede bazan ta'ba bari ya lalace ba .
Na amince ne saboda naga cewar ta hakan zamufi cimma burin mu da wuri akan Muazzam.
To ta yaya kenan Alhj?
Dariya yayi sannan yace ,
Zan fad'a miki shirin da dare idan na dawo yanzu ina sauri"
Amma kada ki qara cewa umai ma bazata auri Muazzam ba '
Domin aurensu shine matakin cin nasarar mu ta farko.
Qarfe sha d'aya na dare '
Ruwa akeyi sosai da iska me qarfi ,,
Bacci Rafi 'a takeyi akan katifar ta gaba d'aya ta takure saboda sanyi,
Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un........
Ta fad'a a gigice saboda wani lafiyayyen mari da taji an sauqe mata a cinyar ta '
Da qarfi zuciyar ta ta buga lokacin da idanunta suka sauqa a kan Gaddafi "
Kwalbar giya ce riqe a hannunsa yana layi ,
Ga wata yar tsigigiyar budurwa a gefen sa sanye da wata matsatssiyar T . Shirt pink color da baqin wando,
Ta zuba wani uban atach a kanta se wani faman taunar cingam take"
Kana ganinta kaga cikakkiyar yar zaman kanta,
Domin kallo d'aya zakayimata kasan tacecciyar yar bariki ce.
fita ki bamu guri....
Gaddafi ya fad'a cikin tsawa ,,
Na fita kuma?
Ina zan je a cikin ruwan nan?
Dan Allah kuyi haquri idan yaso idan ruwan ya tsagaita se na fita na baku gurin.
Rafi 'a tayi maganar tana she sheqar kuka "
Yanzu zaki fita nace muna buqatar hutawa ni da samsy ta.
Rafi 'a ta kalle ta tana hawaye '
Baiwar Allah kiji tsoron Allah dan Allah ,
Kema fa mace ce bazakiso shiga irin wannan halin a cikin gidan ki ba "
Bance ku fasa abunda kuka zo yi ba '
Amma dan Allah kuyi haquri ku bari ruwan ya tsagaita se na baku gurin dan.
Da sauri ta saka hannu ta dafe gefen fuskar ta had'i da sakin wani irin ihu ,,
Saboda sauqar belt d'in da taji a gefen fuskar nata .
Gaddafi ya shiga zuba mata belt d'in ta ko ina a jikin ta tana ihu '
Seda yayi mata duka sosai har seda ko ina a jikin ta ya fashe,
Ya kamota ya wurgata qofar d'akin sannan ya koma ya rufe.
Haka ruwan nan ya qare a kan Rafi 'a ,,
Se rawar sanyi take.......
Wata iska me sanyi ta dinga ratsa har cikin qashin ta.
Haka har kayanta suka bushe a jikinta tana takure waje d'aya '
Se da asuba Gaddafi ya bud'e qofar "
Bacci ya d'auki Rafi 'a tana zaune a qofar d'akin '
Qafarsa ya saka ya shureta da qarfi ,
Ke maza tashi ki d'aura mana ruwan wanka.
Wani abu me kama da mashi ne ya taso ya soki qirjin ta "
Dak'yar ta had'iye wani busasshen yawun takaici .
Ta tashi tana rawar sanyi ta hura wuta ta d'aura musu ruwa '
Haka rayuwar Rafi 'a taci gaba da kasancewa cikin qunci a gidan Gaddafi ,,
Zagi cin mutunci walaqanci babu irin wanda bata gani.
Wataran idan ya shawo giyar sa haka ze zo yayimata dukan tsiya seta suma,
Wataran dak'yar maqota suke zuwa su kwace ta .
Matan banza kuwa kala kala babu irin wacce baya kawowa gidan,,
Wata har marinta se da ta ta'ba yi ,
Wai saboda me ta bari ruwa ya jiqa mata takalma.
Haka ze koro Rafi 'a ta kwana a waje cikin tsoro da far gaba '
Wani lokacin ga sanyi ko ruwa har gane gane takeyi wasu lokutan a cikin gidan,
Abincin ma baya kawowa da ribar kayan miyan da take sayar wa da alawar madara take cefanen kayan abinci ,,
Haka idan yazo babu ruwansa da inda ta samu abinci ze d'auke ya cinye koda itad'in bata ci ba.
A hakan wataran har qorafi yake yimata akan wani abun bejiba a cikin girkin,,
Bayan wata shida......
Rafi 'a na kwance a tsakiyar d'aki tana fama da zazza'bi saboda qaramin cikin da take da shi na wata biyu '
Gaddafi ya shigo tare da wata karuwa yace ta fita ta basu d'akin.
Saboda tace batada lafiya yayimata dukan tsiya ya tattaka cikinta "
Ganin bata motsi ga jini yana bin qafar ta ne yasa suka gudu suka barta kwance cikin jini bata motsi .
Rufaida yarinyar maqotansu ne ta shigo ta ganta a kwance a tsakiyar d'aki cikin jini ta koma ta fad'a a gida akazo aka kai Rafi 'a asibiti,
Dak'yar likitoti suka samu nasarar ceto rayuwar ta '
Sede cikin jikinta ya zube saboda dukan da ya sha '
Gashi jininta ya hau sosai saboda damuwa da yawan tunani ,,
Ko da ta dawo gida bata ishi Gaddafi kallo ba balle har yace mata ya jiki.
Tana kwance a d'aki tana kuka saboda matsanancin ciwon marar da yake damunta ,
Tunda Gaddafi ya daketa matar take ciwo "
Ga wata matsananciyar yunwa na damunta '
Kwana biyu kenan batasa ko da ruwan kunu a cikin ta ba,,
Domin d'an jarin da ta dogara da shima gaba d'aya Gaddafi ya kwashe ya kashe lokacin da take asibiti.
Sosai take kuka idanuwan ta sun kumbura suntum sunyi ja"
Cikinta nayimata qugi saboda yunwa ,
Ajimal yayi sallama...
Dak'yar ta amsa domin ta riga ta galabaita sosai ,,
Har ta fara fita a hayyacin ta saboda yunwa da ciwo.
Ajimal ya qaraso cikin d'akin '
Dak'yar ta yunqura ta tashi ta zauna,,
Sannu da zuwa yaya Ajimal.......
Me yake damunki Rafi 'a?
Naga gaba d'aya kin rame kin canza '
Babu komai yaya kawai na d'anyi rashin lafiya ne.
Qarya kikeyi Rafi 'a......
Idan ba wani abu ne yake damunki ba meyasa kike kuka?
Mara tace kemin ciwo.
Ta fad'a cikin son kawar da maganar domin batason fad'awa Ajimal gaskiya ,
Saboda ranar ma da Gaddafi ya daketa ta fad'a masa haka ya shawo k'waya ya d'auko wuqa yace seya kashe Gaddafi "
Dak'yar mutanen anguwa suka hanashi.
Kin tabbata ba wani abu yake miki ba?
Eh"
Na tabbata babu wani abu lafiya nake zaune.
Shikenan ba komai tunda kince haka '
Amma dan Allah idan wani abu na damunki ki sanar da ni.
Toh ,,
Seda ya bata dubu uku kafin ya tafi sannan ta nemi abunda zata ci.
Bayan shekara guda......
Rafi 'a ta idar da sallar magrib kenan ta miqe zata nad'e sallayar ,
Gaddafi ya shigo ya sameta "
Naji ance yayarki Naja 'atu ta kwaso abun kunya tayi cikin shege koh?
Kamar kwanaki naji ance an kamata a d'akin saurayi ma '
Ko da yake dama ai kinsan tana zuwa tunda dama tare kukeyi kika samu na rufa miki asiri na aureki ,,
Hawaye suka cika Ido Rafi 'a '
Amma bata ce masa komai ba "
Dama ai nasan da walakin goro a miya,
Haka kawai baza a tashi auramin ke da gaggawa cikin sati biyu ba '
Dole nasan akwai abunda ake 'boyemin game da ke ,,
Wato kinje kin gama gantalinki da bin mazan ki shine akayimin rufa rufa aka auramin ke koh ?
Kodayake ai ba abun mamaki bane dama ai barewa bazatayi gudu d'anta yayi rarrafe ba '
Dama naji ance ke d'in ma shegiya ce shiyasa kema bakya gudun abun kunya,,
Har lokacin kan Rafi 'a na qasa tana hawaye '
Ko da yake ba lefinku bane ,
Lefin wannan tsohon kwanon da ya taraku a gida yana kawalci da ku d'in ne"
Se ya dinga nuna shi na Allah ne alhali kuma mun riga munsan komai dama.
Tass....
Be qarasa ba Rafi 'a ta d'aukesa da mari,
Kafin ya farga ta qara d'aukeshi da wani marin ta d'ayan gefen '
Kul wallahi ahir d'in ka ,,
Zan jure duk wani abu da zaka fad'a a kai na' amma kar ka sake ka fad'i maganar banza akan baffa na '
Idan ka kirani da shegiya babu lefi domin suna na ne amma duk sanda ka sake kiran baffa da tsohon banza sena baka mamaki wallahi ,
tana gama fad'ar haka ta juya tabarshi a tsaye a gurin kamar an dasashi mamaki ya hanashi koda iya jan numfashi me kyau.
Momi gani umai ma tace kina nemana '
Eh Muazzam ,,
Zo ka zauna magana nakeso nayi dakai "
Toh Momi.......
Muazzamu kaga yanzu kai ba yaro bane aqalla ka mallaki hankalin kanka ,
Saboda haka ya kamata ace ka mallaki iyali zuwa yanzu"
Shiru Muazzam yayimata yana saurarar ta.
Muazzam inaso naga kayi aure ka zama cikakken mutum domin inaso naga ka samarmin da jika,
Sanin kankane kaine babba a cikin gidan nan '
Saboda haka yanada kyau ace zuwa yanzu kanada mata.
Mata kuma Momi?
Ni da ban ta'ba yin budurwa ba taya za ayi nayi aure?
Wallahi Momi bansan yadda ake soyayya ba ban ta'ba sanin yadda so yake ba ,,
In fact ma de ni soyayya bata ta'ba burgeniba '
Kuma ban ta'ba sha awar yinta ba.
Shikenan Muazzamu kaje zanyi magana da dadyn ku se musan abun yi ,,
Okay"
Ya miqe ya fice daga d'akin,
Momi tabi bayansa da wami shu umin mur mushi me d'auke da ma anoni kala kala da ita kad'ai tasan ma anar su.
Gaddafi yana fita ya nufi mashayar su zuciyarsa na tafasa '
Kwanciya kawai yayi yanata huci kamar wani kumrci ,,
Qanin mace ne yace masa '
Wai me yake faruwa ne Gadda?
Na eh ga yau gaba d'aya kamar baka cikin wal Wala "
Waye ne ya ta'ba ka muje mu qaddamar masa?
Gamawa ne wallahi ba tsoron uban kowa mukeji ba semu 'barar da eh koma waye dan wallahi munci dubu se ceto bama gudun magana .
Kabari kawai qanin mace wallahi yau se yarinyar nan ta baqunci qiyama "
Yaushe nayi lalacewar da har mace zata saka hannu ta mareni?
Wace yarinyar kake magana ne kam?
Wannan shegiyar Rafi 'atun mana,
Wallahi yau lahira zatayi baquwa ba a halicci wanda ze saka hannu ya mari Gadda ya kwana lafiya ba.
A huce haka mutumina yanzude cafke wannan na eh lura akwai yarinta a tare da wannar barun taka haquri zakanayi '
Kar kace zaka sakamata kaifi ba girmanka bane,,..
Idan kaji bazaka iya haquri ba kawai taci na jakuna ka yankamata Red cart ta koma gidan su .
Se lokacin ajali yace '
Haba sanyi mana Gadda ya kake nema kayi yawa ne kana nema ka 'batawa kanka rai akan qaramar yarinya?
Kawai ka kar'bi kayan caji kayi caji zakaji zam zam .
Gaddafi be shigo gidanba se qarfe d'aya da rabi na dare,
Rafi 'a tana kwance amma ta kasa bacci domin se daga baya ta gane tayi kus kuren marin Gaddafi da tayi,,
Yana shigowa ya fara dukan Rafi 'a yana tattakata,
Wani irin ihu ta sake ta suma saboda yadda ya gwara kanda da bango.
Har ta far fad'o yana masifa "
Yarinya se rashin tarbiyya har zaki saka hannu ki mareni a matsayina na mijin ki saboda bakida kunya,
To wallahi bazan lamunci haka ba maza ki tashi ki barmin gida na na sakeki saki uku kada ki sake ki qara koda minti biyu ne a cikin gidan nan tunda gida na ne ba gidan ubanki bane .
Saki uku kuma na tafi yanzu?
Na shiga uku......
Dan girman Allah kayi haquri kabari na kwana koda a tsakar gida ne da safe se na tafi.
Wallahi ko a qofar gidan nan bazaki kwana ba tunda bakida mutunci ,,
Shegiya marar tarbiyya kawai duk inda iyayenki suke wallahi nasan ba mutanen kirki bane .
Babu irin roqo da magiyar da Rafi 'a batayimasaba amma yayi burus '
Haka ta fito qarfe biyu na dare tana kuka "
Ita kad'ai a layin anguwar banda kukan karnuka babu abunda take ji ,
Gashi duk jikinta yayimata tsami saboda dukan da Tasha.
Har ta d'auki hanyar gidan baffa se kuma ta juya ta canza hanya ,
Domin tanajin gara taje ko ina ta rayu akan ta koma gurin Amo,,
Har kusan qarfe hud'u tana tafiya sannan ta samu gindin wata bishiya ta kwanta.
Da safe ta tashi da wata muguwar yunwa amma batada abunda zata ci '
Haka taci gaba da tafiya ba dan tasan inda zataje ba"
Har yamma batasaka komai a cikin ta ba kuma batasan inda zataje ba.
Cikin nitsuwa Muazzam yake tuqa motar,
umai ma na gefensa Momi kuwa tana zaune a baya '
Daga gurin gaisuwan rasuwa suke,,
Qanin mijin hajiya Rahama aminiyar Momi ne ya rasu a hatsarin mota.
Sauri suke domin akwai hadiri sosai a garin da alamar an kusa fara ruwa ma "
Da sauri ya taka burki saboda ganin Rafi 'a a gabansa ,
Kad'an ya hana ya bugeta.
Sannu baiwar Allah.
Dan Allah kiyi haquri wallahi ban ganki bane,
Malam dan Allah ku temakamin bansan kowa ba '
Kuma tun safe babu komai a ciki na ,,
Dan Allah ku temakamin koda da abunda zanci ne.
Rafi 'a tayi maganar idanunta suna qoqarin kawo ruwa,
Cikin tausayawa Muazzam yace '
Ayya sannu baiwar Allah idan bazaki damu ba zamu iya,,
Kul Muazzamu....
Kada ka sake kace zamu temaki yarinyar da bamu sani ba,
Yanzu duniya babu yadda wanda ka temaka idan kayi wasa wataran shine ze zama silar rushewar rayuwar ka har abada .
Momi ta fad'a cikin sauri da son dakatar da Muazzam abunda yakeda niyyar fad'a Amma Momi macece fah "
Dan Allah mu temaka mata kada rayuwar ta ta lalace,
Wallahi wannar daga ganinta ba muguwa bace Momi.
Kayimin shiru Muazzam ka wuce mu tafi"
Ai kai har yanzu yaro ne bakasan me ze iya cutar da kai ba.
A'a "
Dan Allah Momi......
Wallahi Muazzam idan baka wuce muka tafi ba zan sa'ba maka,,
Haka Muazzam ya ja motar gaba d'aya ransa babu dad'i '
Kafin su isa gida aka fara ruwa me qarfi dan haka suna isa kowa ya wuce d'akin sa ,,
Sede Muazzam har yanzu ya kasa nitsuwa yanajin tausayin yarinyar sosai '
Saboda haka ya d'au key d'in motar ya shiga ya fizgi motar a guje .
Ya dawo gurin amma ko alamar ta be ganiba ,
Saboda haka ya fito a cikin ruwan yana nemanta amma be ganta ba "
Har ya fara gajiya da nemanta yana shirin shiga mota ya tafi se ya hangota ra'be a cikin wani kango ruwa yayimata duka se kar karwa take.