Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Fatima Usman Abdullahi · UQUBA

‎Muazzam yanaji har Momi da umai ma suka gama zage zagensu suka tafi '
‎Amma koda Ido ya kasa d'agowa ya kallesu ,,
‎
‎Suna ficewa Muazzam ya kwantar da kansa a kan carpet d'in d'akin ya fashe 
‎da wani irin kuka me cin rai,
‎Meyasa kika kasa fahimta ta Momi? Kinqi ki saurareni balle ki fahimci abunda zan fad'a miki.
‎Why Momi..... Why ?
‎
‎Muazzam yayi maganar yana dukan qasa da qarfi.
‎Rafi 'a kam gaba d'aya ta rasa ma a wace duniya take ,
‎Bazata iya tantace irin yanayin da take ciki ba "
‎Ba kuka take ba domin yanayin da take ciki ya wuce ayimasa kuka,
‎
‎Kallon Muazzam kawai takeyi amma ta kasa furta masa koda kalma d'aya.
‎Haka ya gama kukansa ya tashi dak'yar ya ja jiki ya fice ,,
‎Abunka da farin mutum duk fuskarsa tayi ja kana ganinsa zakasan yaci kuka har ya gaji .
‎
‎Yana dawowa gida bebi d'akin Momi ba ya wuce d'akinsa kai tsaye domin besan da wani ido ze kalli Momi ba '
‎Wanka yayi ya kwanta amma ya kasa bacci se juyi yake ,,
‎Gaba d'aya zuciyar sa ta dagule '
‎
‎Ya rasa me yake masa dad'i babban damuwar sa shine "
‎Da wani ido ze kalli su Momi da Daddy harda umai ma da take qoqrin zama matarsa.
‎Haka ya kwana ransa babu dad'i '
‎
‎Da safe se kusan goma da wani abu ya shigo gaishe da Momi da Daddy ,,
‎Se faman ra'be ra'be yake saboda tsoron kada su tareshi da maganar jiya '
‎Sede ya sha mamakin yadda suka nuna masa babu komai kamar ma ba ayi wani abu ba.
‎
‎Am "
‎Momi nace dama maganar jiya ce ki saurareni Momi wallahi ban aikata komai ba ,
‎Yarinyar nan ni kwata kwata ma ban san taba '
‎Temakonta kawai nayi wallahi Momi dan girman Allah ki yarda da ni ,,
‎D'anki ne ni fah a hannunki na tashi kin riga kinsan duk wani abu da zan aikata da wanda bazan aikata ba '
‎Kinsan halina Momi kinsani bazan ta'ba aikata zina ba "
‎
‎Iyayena basu aikata ba Kuma nima har abada bazan ta'ba aikatawa ba insha Allah.
‎Muazzam ya kai qarshen maganar muryarsa na rawa ,
‎
‎Lahhhh ...
‎Kada ka damu Muazzam wallahi babu komai kayi haquri nayimaka fad'a akan abunda baka aikata ba kuma ni kaina nasan bazaka ta'ba aikatawa ba '
‎Kawai zugar mutane ne da 'bacin rai da kuma sharrin shed'an.
‎Ka kwantar da hankalinka Muazzamu wallahi inde nice komai ya wuce .
‎
‎Sosai yaji sanyi a ransa da maganar Momi Na gode Momi da kika fahimceni ,
‎Wannan yarinyar kawai tausayi take bani shiyasa na temake ta Kuma ai nasan kema zaki iya yin hakan.
‎
‎Allah sarki Muazzam gaskiya ka kyauta ai temako abune me kyau "
‎Da haka yayimata sallama da niyyar tafiya wajen aiki '
‎Momi tabi bayan sa da wata iriyar dariya wacce ita kad'ai tasan ma anar ta.
‎
‎Da fari da Muazzam ya shigo bega Rafi 'a ba yayi tunanin ta shiga toilet ne saboda haka se ya zauna jiranta '
‎Amma se yaga jiran ya wuce misali babu ita babu motsin ta ,,
‎Hakan ne yasa ya shiga k'walamata qira amma shiru babu amsa '
‎
‎Toilet d'in ya bud'e be ganta a ciki ba ,
‎A rikice ya shiga aikin nemanta a cikin gidan babu inda be duba ba amma babu ita babu alamar ta.
‎
‎A guje ya fito ya nufo wajen me gadi "
‎Ina Rafi 'a ta shiga? Ina ka bari ta tafi?Kode taje sayo wani abun ne bata gayamin ba?
‎Dan Allah ka fad'amin ina ta shiga' 
‎
‎Gaba d'aya Muazzam a rikice yake har idanunsa sun fara kawo ruwa ,,
‎Domin ko kad'an be shirya yin nisa da yarinyar ba.
‎
‎Magana nakeyimaka fah '
‎Ka fad'amin ina Rafi 'a ta shiga? Wallahi ban saniba ranka ya dad'e "
‎Jiyade da dare kusan qarfe goma naga hajiya da umai ma sun shigo,  
‎sun d'an jima kafin su fito amma basu jima da fitowa ba naga itama ta fito riqe da jaka tana kuka ,,
‎To wallahi bayan wannan ni bansan komai ba.
‎
‎Momi da umai ma sunzo kuma?
‎Wayyo Allah na shiga uku, Rafi 'a ina kika shiga?
‎Dan Allah kada ki barni ina qaunarki ban shirya rasaki yanzu ba wallahi '
‎Da gudu ya fita yabi titi kamar mahaukaci wai ko ze ganta ,,
‎Amma bega ko da alamar qurar ta ba. 
‎
‎Wayarsa ya ciro daga aljihunsa ya fara kiran layin Momi amma bata amsa ba '
‎Da gudu ya dawo ya shiga motarsa ya fizgeta ya nufi hanyar gida ,,
‎
‎umai ma da Momi suna hira sunata dariya umai ma tana cewa "
‎Wallahi Momi munyi maganin shegiya gara da mukayimata haka bazata sake dawowa ba ,.
‎
‎Muazzam ne ya fad'o kamar an jefoshi  '
‎Ina kuka kaimin Rafi 'a? Momi me kuka yiwa Rafi 'atu?
‎Ina kuka kaita?
‎
‎Kai Muazzam kada ka sake ka kawomin maganar banza "
‎Wacece kuma Rafi 'a?
‎Ka bamu ajiyar ta ne da zakazo kana tambayarmu inda take ,
‎Wallahi idan kasakemin maganar yarinyar nan se ranka ya 'baci .
‎
‎Okay Momi "
‎bazan sake tambayar ku ba domin ban baku ajiyar ta ba ,
‎Amma maganar aure' na da umai ma nan da sati d'aya na soketa har se ranar da na samo' Rafi 'a ,
‎Kunga idan ban samota ba har abada hakan yana nufin bazan ta'ba zamowa mijin umai ma ba har abada.
‎
‎Yana kaiwa nan ya juya ya fice da sauri '
‎Yaya Muazzam dan Allah kayi haquri ka dawo ,,
‎Kada ka fasa aure na ina sonka kuma wallahi zan fad'a maka gaskiya ,
‎Ko sauraronta Muazzam beyiba balle tasa ran ze dakata yaji me take cewa yaja motar sa ya fice daga gidan da sauri .
‎
‎Babu inda Muazzam be shiga ba yana neman Rafi 'a amma shiru ,
‎Be ta'ba sanin ya Shaqu da yarinyar har haka ba ya kasa nitsuwa babu inda be shigaba dan nemanta amma shiru kuka kam yayi harya shiga uku.
‎
‎Qarfe goma da hamsin da bakwai na dare"
‎Rafi 'a na zaune a bakin wani layi dake anguwar tumfure ,
‎Gurin yayi shiru babu kowa daga ita se wani tsoho me qafa d'aya da yake bara a wajen . 
‎Ganin har dare Rafi 'a tana zaune a gurin ne yasa ya taso ya qaraso inda take '
‎
‎Barka da dare yarinya..
‎Yauwa sannu baba , Akwai wani temako da kike so ne kokuma de akwai abunda kike nema ne? naganki a nan har yanzu kode bakida lafiya ne?
‎
‎Eh baba "
‎Yunwa nakejin rabona da abinci tun jiya da dare , Dan girman Allah idan kanada abinci komin qan qantarsa ka temaka ka bani naci.
‎
‎Bredi ya ciro ya miqa mata da da ruwa '
‎Seda ta gama ci sannan yace ,,
‎Yarinya me ya faru kika baro gida da wannan tsohon cikin haka?
‎Nagade bakiyi kama da me bara ba sannan kuma daga ganinki kinada qananan shekarun da yakamata ace yanzu kina tare da iyayenki "
‎
‎Amma me yasa kika za'bi kasancewa a haka kina roqon abinci a gurin walaqantacce me bara kamar ni?
‎Wasu hawaye suka gangaro daga idanun Rafi 'a '
‎
‎Ina ma ace na kasance mabaraciya kamar kai tun da fari ,
‎Ina ma ace rayuwa ta tayi kamanceceniya da taka ,,
‎Da wallahi nafi kowa jin dad'i a duniya zan zauna a kan titi nayi bara '
‎Idan bayin Allah suka temakeni naci abinci na kwanta a gefen titi babu tsoro ko fargabar kowa a rai na "
‎Babu wanda ze yimin qage kokuma ya kirani da shegiya ,
‎
‎Fad'a zanyi da rayuwata babu me d'uramin talle bare ya hukuntani idan ban sayar ba '
‎Inda kamar kai nake nasan babu me yimin aure koda raina bayaso.
‎
‎A'a yarinya "
‎Kada kiyi sha awar rayuwa ta ko kad'an domin bakisan wanene ni ba , Inda ace kin kasance kamar ni da tabbas a yau kin tsani kanki  ,
‎Domin a rayuwata na aikata kus kuren da nakejin da na bar duniya kafin nakai ga aikatashi da seyafimin '
‎Wallahi yarinya na aikata' lefin da nakejin bazan ta'ba samun gafarar Allah a kansa ba.
‎
‎Na aikata' abunda yake damu na wanda tun daga ranar da na aikatashi zuwa yau shekara goma sha bakwai kenan "
‎Dede da na daqiqa d'aya zuciya ta bata ta'ba samun nitsuwa ba ,
‎Tabbas a zahiri ina raye amma a cikin zuciyata kullum mutuwa nake ,
‎
‎Sannan kuma ba ni na za'bi bara ba itace ta za'beni domin ta hukuntani bisa zunubai na "
‎Tabbas nayi asara kuma rayuwa ta ba abun tausayi ko abun sha awa bane.
‎
‎Subhanallah.......
‎Haba baba ,,Wani irin zunubi ka aikata haka wanda har kake fad'ar irin wad'annan maganganun akan kanka?
‎
‎Seda ya share hawaye sannan yace '
‎Shekaru goma sha bakwai da suka wuce ni me gadi ne a gidan wani babban hamshaqin me kud'i ,,
‎
‎Alhj Hafiz Atiku Marafa .....
‎Mutum ne shi me dukiya sosai da adalchi ga sanin darajar d'an adam ' Duk da mu y'an aikin gidan sa ne amma yana mu amalantar mu kamar abokai kokuma y'an uwan sa ,
‎
‎Yanada kamfanunnuka sama da guda hamsin '
‎Shaguna a kasuwa sama da guda d'ari biyar ,
‎Gidaje da motiti kam ba a ma magana a kansu domin bazasu lissafu ba ,,
‎Yanada wasu kamfanunnuwa a qasashen waje sannan yanada hannun jari a kamfanunnuwa da dama '
‎
‎Idan yace ze cire hannun jarinsa a kowani company wasun zasu tafka babbar asara wasun kuwa sanadiyayyn durqushewar su kenan.
‎Ya gina asibitoti masallatai makarantu gidajen marayu da sauransu '
‎
‎Shahararren mutum ne me kamala wanda idan za a irgo jerin masu kud'in duniya tabbas idan bezo a na farko ba zezo a na biyu ,,
‎Shi na kowane manya da yara kowa nasa ne '
‎
‎Kud'i ilimi iko babu abunda be had'a ba '
‎Sede duk wannan ni imar da Allah yayimasa duk duniya y'a d'aya Allah ya ta'ba basa a rayuwarsa.
‎
‎dede lokacin Muazzam ya qaraso gurin a guje yana haki ,
‎Gaba d'aya ya fita a hayyacinsa idanunsa sunyi ja saboda kukan da yaci kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankali domin harya rame"
‎
‎Da wani mugun qarfi qirjinsa yake bugawa ,
‎Wani irin mari Muazzam ya d'auke ta da shi sannan ya rungumeta cikin kuka ya sauqe wata nannauyar ajiyar zuciya ,
‎
‎Ina kika shiga Rafi 'a?
‎Me yasa zaki tafi baki sanar da ni ba? Kin kuwa san irin halin da kika sakani a ciki?Rafi 'a tun safe nake ta faman nemanki babu inda ban je ba ,
‎
‎Babu wani titi ko layi da lungun da ban jeniba ina nemanki kamar mahaukaci "
‎Kin kama hanya kinyi tafiyar ki ba tare da tunanin irin halin da zaki sakani a ciki ba ,
‎Rafi 'a tun dafe ko ruwa ban iya sakawa a ciki na ba saboda ke d'in nan.
‎
‎Idan wani lefin nayimiki kikeson hukunta ni to ki hukunta ni ta wata hanya mana amma meyasa zaki hukuntani da rashin ki?
‎Ban ta'ba sanin yadda akejiba idan zuciya ta karye ba se yau d'in nan ,,
‎
‎Rafi 'a tunda nake a rayuwata ban ta'ba sanin me ake kira da wahala ba seda kikayi nisa da ni '
‎Ina qaunarki dan Allah kada ki sake barina please....
‎
‎Ya qarasa maganar da wata raunatacciyar murya yana qara rungumeta had'e da fashewa da kuka.
‎
‎Rafi 'a kam ta rasa kukan farin ciki takeyi ko na damuwa ,
‎Ashe a duniya akwai wanda ze damu da rayuwar ta har haka?
‎Ashe akwai wada zeyi kuka saboda rashinta kuma har ya kasa cin abinci duk saboda ita?
‎
‎Kayi haquri Barrister ba da gangan nayi ba kuma bazan sake tafiya na barka ba.
‎Kizo mu tafi Rafi 'a kiyi haquri mu koma gida ,
‎
‎A'a Barrier kayi haquri amma bazan iya komawa wannan gidan ba.
‎Saboda me? Anyimiki wani abun ne?
‎Kode su Momi ne sukayimiki wani abun?
‎
‎Shiru tayi wasu sabin k'walla suna taruwa a idanun ta "
‎Su Momi ne koh ?
‎Kada ki damu da su Rafi 'a bazasu sake ganinki ba ,
‎Bazasu sake sanin inda kike ba balle har su 'batamiki rai ki tafi ki barni '
‎Na sayamiki sabon gida kuma can zaki koma da zama,.
‎Anguwar da babu wanda ya sanni balle yakai suka ta wajen Momi .
‎
‎Da kansa ya sakata a motar yaja suka tafi sabon gidan da ya saya a G . R . A ,
‎Be qara tabbatarwa yana mahaukacin son yarinyar ba se yau Ji yakeyi kamar ze had'iye ta "
‎
‎A bakin gado ya zaunar da ita ya qura mata ido ,
‎Se a lokacin ne ya kula da yadda ko ina a jikin ta ya tashi '
‎Menene wannan Rafi 'a? Dan Allah kada ki cemin su Momi dukanki sukayi ,,
‎Me kikayimusu ne Rafi 'a?
‎
‎A hankali ta zare hannunta daga cikin nasa cikin son kawar da maganar tace ,
‎Umhm"
‎Barrister gaskiya mamarka tana da kyau sosai amma kamar ka fita '
‎Meyasa qanwar ka tafi kama da ita sama da kai bayan kuma kaine babba?
‎
‎Saboda ita mahaifiyar ta ce ni kuma riqo na kawai takeyi.
‎Ban fahimta ba.....
‎Kenan kana nufin itad'in ba mahaifiyar ka bace?
‎To wacece mahaifiyar taka? Kuma meyasa ita ta reneka ba mahaifiyar ka ba?
‎
‎Ni maraya ne Rafi 'a ,
‎Banida uwa banida uba"
‎Allah ya kar'bi rayuwar su tun ina d'an shekara takwas ,
‎Sun barmin dukiya sosai da kadarori da company '
‎
‎Mijin Momi qanin mahaifi na ne da ya d'auko matarsa daga qauye suka zauna tare da ni kuma suka reneni kamar su suka haifeni ,,
‎Sun riqeni da dukiya ta da niyyar idan na mallaki hankalin kaina zasu damqamin komai '
‎Amma ni banida sha awar kar'bar komai daga garesu saboda riqon da sukayimin ,,
‎
‎Shiyasa na tafi qasar Jordan nayi karatu na a can har na zama cikakken Barrister domin inaso na riqe kaina da gumi na ,
‎Saboda idan suka maidamin da komai hakan yana nufin basuda komai nikuma banason hakan.
‎
‎umai ma na kwance a jikin Momi tanata aikin kuka "
‎Momi idan yaya Muazzam ya fasa aurena na shiga uku wallahi Bazan iya rayuwa babu shi ba Wallahi ina sonsa Momi,
‎
‎Ki kwantar da hankalinki umai ma inde ina raye wallahi sekin auri Muazzam '
‎Bari Daddyn ku ya dawo zan kar'bi kud'i a gurinsa naje wajen boka obina ,,
‎Dole za a d'aura wannan auren wani sati yarinya kuma baze ta'ba samun ta ba .
‎
‎Yauwa Momi na dan Allah ki temaka kada a fasa auren '
‎Ki kwantar da hankalinki umai ma Muazzam bashida wata mata se ke.
‎
‎Da dare Momi da Daddy suna hira a d'akin su ,
‎Momi tace....
‎Nikam Alhj, me yasa kace mu bari juriyya
‎ta auri Muazzam?
‎Kamata yayi mu gama da shi tun kafin ya buqaci wani abu daga garemu '
‎Baka tunanin idan yayi aure ze nemi mu bashi gadon sa?
‎Tunda ai kaga yakai ya kula da dukiyarsa yanzu.
‎
‎Daddy ya d'an numfasa sannan yace '
‎Ki bari ya aure ta koda ya buqaci dukiyar se mu bashi kayansa ,,
‎Mu bashi kayansa fah kace Alhj....
‎
‎Kenan duk riqon da mukayimasa ya tashi a banza mu bamuga tsun tsu bamuga tarko '
‎Na kula so kakeyi ka rusa mana shirin mu gaba d'aya saboda umai ma.
‎
‎A'a,
‎Kema kin sani bazan ta'ba bari tsarin mu ya wargaje a banza ba '
‎Ina sane na bari ya auri umai ma domin se ya aure ta ne zamu samu damar mallakar dukiyar gaba d'aya "
‎Idan ya aure ta ta haifa masa d'a kinga yaron shi ze gaji dukiyar gaba d'aya ,
‎Daga nan se mu aikashi lahira shima yaron musan yadda zamuyi da shi ,,
‎
‎umai ma takaba kawai zatayi da kuka da damuwa na wani d'an lokaci,
‎Amma dukiya zata zama tamu har abada .
‎
‎Jim Momi ta d'anyi tana jinjina maganar Dady '
‎Kuma fa tunani na be ta'ba bani haka ba ,, Gaskiya Alhj kanada lissafi sosai' Gaba d'aya kwa kwal wata bata ta'ba haskamin wannan ba.
‎
‎Kuma dama inaso ka bani kud'i da safe zanje gurin boka obina '
‎Dan yaron nan ya fara barazanar fasa auren nan '
‎To so nakeyi naje a rufe masa baki ta yadda dole ze amince da auren ko baya so.
‎
‎A ranar jumma ar qarshen sati aka d'aura aure Muazzam da umai ma Momi da umai ma sewani rawar kai ake a tunanin su akin da boka yayimusu ne ya kama Muazzam,,
‎
‎Daga Muazzam har Rafi 'a babu wanda auren yayiwa dad'i domin Rafi 'a kam ko bacci kasayi tayi a ranar '
‎Kuka kuwa babu irin wanda batayiba domin itama har ga Allah tana son Muazzam matiqa .
‎
‎Shi kansa seda yayi kuka ,..
‎Ko da ya shiga d'akin umai ma be shiga harkar ta ba "
‎Se ita ce tayita shisshige masa .
‎
‎Haka zamansu ya ci gaba da tafiya a daddafe ,
‎Muazzam baya wani shiga harkar ta sosai hasali ma idan yana tare da ita ji yake kamar an dabai bayeshi da qaya "
‎Yana jin sauqi ne kawai idan yana tare da Rafi 'a.
‎
‎Watan Muazzam biyar da yin aure ,
‎Rafi 'a ta haifi kyakkyawan jariri me kama da ita kamar an tsaga kara .
‎
‎Muazzam shine yayimasa duk wani abu da ya kamata mahaifi yayiwa d'an sa '
‎Shine ya rad'awa yaro sunan baffa suna kiranshi da bom boy.
‎
‎Muazzam yana son yaron sosai kullum cikin yimasa sayayya yake ,,
‎Wata ranar jumma a da misalin qarfe 2 na dare jikin bom boy ya rikice '
‎Rafi 'a ta rasa yadda zatayi se kuka take domin ta tsorata da jikin bom boy sosai"
‎
‎Ta yiwa Muazzam kira yakai hamsin beji ba saboda ya saka wayar a silent kuma wayar tana parlor .
‎Kafin safiya bom boy yace ga garin ku nan rai yayi halin sa '
‎
‎Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un......
‎Rafi 'a tayi kuka kamar ranta ze fita "
‎Shi kansa Muazzam seda yayi kuka sosai a 'boye domin bom boy yaro ne me matiqar shiga rai sosai.
‎

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol