Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Fatima Usman Abdullahi · UQUBA

‎BY
‎
‎FATIMA USMAN 
‎SHA LELEN TERAWA.......
‎
‎
‎Umai ma kuwa tun satinta na farko a gidan suke lissafin kwanakin samun ciki amma shiru,
‎Tun suna irga kwanaki suka dawo satuttuka har suka fara irga watanni "
‎Se gashi shekara guda ta shud'e babu ciki babu labarin ciki .
‎
‎A cikin shekara d'aya adadin gurin maganin da sukaje dan samun ciki baze irgu ba ,
‎Kuka kam umai ma tayishi kamar ba gobe 
‎Wani lokacin Muazzam ne yake kwantar mata da hankali da cewa du du du auren nasu ma yaushe akayishi '
‎Shekara d'aya ai be wuce samun tazara dan hutu ba .
‎
‎Yana nuna mata akwai wad'anda suka shekara goma da aure amma babu labarin aihuwa "
‎Idan tayi haquri idan da rabonsu suma zasu aihu. 
‎
‎Wata biyar da rasuwar Bom boy Muazzam yazowa Rafi 'a da maganar aure ,
‎Da fari tayi qoqarin qin amincewa saboda Umai ma da Momi '
‎Dak'yar Muazzam ya shawo kanta ta amince da auren .
‎
‎Saura sati biyu a d'aura auren Muazzam da kansa yazo ya fad'awa Momi "
‎Da tayi qoqarin hanashi se cemata yayi yanzu shi ba yaro bane ,
‎Saboda haka yanada damar za'bawa kansa matar da ze aura kuma yana da damar auren mata ko nawa ne inde yanada halin riqesu kuma yanajin zeyi adalchi a tsakaninsu .
‎
‎Da dare umai ma na kwance Muazzam yazo ya sameta ,
‎umai ma Ki tashi inason yin magana da ke '
‎
‎Dan Allah mu bari se gobe wallahi na gaji sosai bacci nakeji ,.
‎Ki tashi nace .....
‎Maganar tanada muhimmanci sosai bazan 'bata lokaci ba .
‎Tashi tayi ta zauna tana turo baki wai ita a dole ranta ya 'baci ,
‎
‎Muje parlor akwai abunda nakeso na nunamiki "
‎Miqewa tayi tabi bayan sa tana qun quni qasa qasa ,
‎
‎Turus ta ja ta tsaya ganin akwatuna kamar an kawo lefe gidan  '
‎Yaya Muazzam.......
‎Wad'annan kuma na wanene? Me sukeyi a nan?
‎
‎Zauna zakiji komai yanzu ,
‎Gefensa ta samu ta zauna kafin ya fara yimata magana cikin nitsuwa .
‎Wad'annan kayan na sayosu ne domin ki zaki iya dubawa idan akwai abunda kikeso a canza ko a qara miki a kai ,,
‎
‎Sannan kuma zan canzamiki kayan d'aki da kayan kitchen '
‎And zan sakamiki million biyu da rabi a account d'in ki kije a gyaramiki jiki ,
‎
‎Da mamaki take kallon sa "
‎Duka wad'anna abubuwan na menene yaya Muazzam?
‎
‎Yanzu zaki ji ai........
‎Ya fad'a sannan ya miqe ya d'an fara takawa a hankali ,,
‎
‎umai ma aure nakeso zan qara nan da sati biyu za a kawomin amarya ta cikin gidan nan .
‎
‎Dumm ..... Dummm.....
‎Qirjinta ya amsa da qarfi ,Wani irin mul mulowa tayi ta fad'o daga kan kujerar '
‎D'an kwalin kanta ya zame ya fad'i kitson kanta guda hud'u suka bayyana ,,
‎
‎Sunyi mugun tsufa ko layinsu ba a gani da kyau domin sunkai wata biyu a kanta ko arziqin wanki basu samuba balle tsifa bare aje maganar sabunta su.
‎Domin dama tun a gida umai ma ba gwanar gyaran jiki bace ,
‎Wani lokacin se Momi ta takurata takeyin wasu abubuwan "
‎
‎Yaya Muazzam ammade da wasa kakeyimin koh?
‎Ka dena yimin irin wannan wasan banaso kasan babu abunda na tsana a duniya sama da sunan kishiya ,
‎
‎Juyowa yayi ya kalleta babu alamar wasa a fuskar sa "
‎Abokin wasa kine ni da zanyimiki wasa?Idan zanyimiki wasa da komai ai kinsan bazanmiki wasa da maganar aure ba '
‎Tunda shi kanshi auren ba abun wasa bane .
‎
‎umai ma ta miqe ta nufoshi da gudu da nufin cakwamar sa tana fad'in ,
‎Munafuki mayaudari macuci maci amana Ni yaya Muazzam ? ni zakayiwa kishiya yau?
‎Duk halaccin da ni da iyaye na mukayimaka karasa da me zaka sakamin se kishiya Wallahi baka isa ba......
‎
‎Yaya Muazzam kai nawane ni kad'ai na Kuma babu wacce ta isa nayi shearing naka da ita ,
‎Wallahi duk yarinyar da ta sake ta shigo gidan nan a matsayin matarka sena kashe ta.
‎
‎Ta qarasa maganar dede lokacin da take kai hannu da niyyar cakwamar kwalar sa '
‎Saurin riqe hannun ta Muazzam yayi sannan cikin muryar da babu alamar wasa yace,,
‎
‎"You can say whatever you like about me, but don't you ever make the mistake of laying a hand on me. If you dare touch me, I'll teach you a lesson you'll never forget."
‎
‎Yana gama fad'ar haka ya ture hannunta baya da qarfi ya shige d'akinsa yabar umai ma tsaye a gurin tana ta faman surutai da zage zage '
‎Tana ball da akwatunan da ya kawo mata .
‎Kuka kawai takeyi gaba d'aya zuciyar ta ta cunkushe tama rasa abun yi "
‎
‎Da sauri ta koma d'aki ta d'auki wayar ta ta lalubo number Momi ta danna ,
‎Bugu biyu Momi ta d'auka '
‎
‎Hello "
‎umai ma lafiya kuwa kike kirana cikin daren nan ?
‎Inafa lafiya? Nashiga uku Momi shikenan zuciya ta zata fashe ,
‎Yaya Muazzam aure ze qara wallahi kashe kaina zanyi bazan iya zama da kishiya ba ,,Gara na mutu da ace nayi shearing d'in miji na da wata '
‎
‎Momi ki fad'amin ya zanyi dan Allah wallahi Momi duk ranar da yaya Muazzam ya auro wata sena kashe kaina .
‎
‎To ki kashe kannaki mana sha sha sha wacce batasan ciwon kanta ba kawai ,
‎Dan kawai mijinki ya qara aure seki kashe kanki?
‎Haba umai ma ya kike abu kamar ba mace bane?
‎
‎Bazaki mutu saboda kishiya ba Kuma kamar yadda ban zauna da kishiya ba y'a ta ma tafi qarfin kishiya wallahi '
‎Ki kwantar da hankalinki gobe da safe kizo zamuje gurin boka obina ,
‎Wannan auren wallahi se an fasa Shi.
‎
‎Toh ,, Momi ni ko yanzu za a tafi wallahi a shirye nake inde za a fasa maganar auren nan  ,,
‎A'a ba yanzuba ki bari se da safe zamu tafi da wuri dole ma Muazzam seya fasa wannan auren .
‎
‎Yadda umai ma taga rana haka taga dare domin ta kasa rintsawa "
‎Banda kuka da tsinewa Muazzam babu abunda takeyi .
‎
‎Asubar fari umai ma ta fice daga gidan ko izinin Muazzam bata tsaya tambaya ba ,
‎Isowar ta gidan Momi yayi dede da kwala kiran sallar asubah "
‎
‎Tana shiga taci karo da Dady a parlor '
‎Da gudu ta rungumeshi tana kuka .
‎Daddy na shiga' uku yaya Muazzam aure ze qara wai nan da sati biyu ze qaramin kishiya "
‎
‎Ki nitsu umai ma ki kwantar da hankalinki mahaifiyar ki ta sanar da ni komai kuma zataji da komai kinji .
‎Toh Daddy......
‎
‎Ta fad'a tana qoqarin shigewa d'akin Momi ,
‎Momi kizo mu tafi dan Allah muje gurin boka ya hana auren nan ,,
‎Mutafi yanzu so kawai nake naji yaya Muazzam yace ya fasa auren nan wallahi Momi banason kishiya .
‎
‎Ki nitsu mana umai ma yanzu fa ko sallar asubah ba a idar ba ki bari gari ya waye mana ,
‎Ko break fast umai ma batayiba saboda tashin hankali "
‎Babu yadda Momi batayiba akan taci abinci amma taqi saboda kishi ya rufe mata ido ,
‎
‎Tun shida da wani abu suka d'auki hanyar garin kufto Wajen boka obina.
‎Jeji ne sosai babu gida a gaba babu gida a baya ,,
‎Ga duwatsu da hawa da sauqa '
‎Tun daga bakin hanya suka ajiye motar su suka shigo cikin jejin da qafa domin mota bazata iya shiga ba .
‎
‎Seda sukayi tafiya ta yada d'an shege kafin su iske bukkarsa ita kad'ai a tsakiyar jejin ,
‎Takalmansu suka cire suka riqe a hannu sannan suka fara shiga bukkar ta baya baya "
‎
‎Suna zama umai ma ta bud'e baki zata fara magana boka obina ya dakatar da ita da hannu ,
‎Nasan me ke tafe da ku .....
‎Kuma inaso ki sani wannan auren babu fashi se an d'aurashi ,,
‎Saboda haka ki rabu da shi ayi auren nan salum alum '
‎
‎Idan kuma kika matsa se an dakatar to tabbas zaki mutu.
‎Kuma ba ke kad'ai ba duk wani wanda yayi qoqarin dakatar da auren sede ya mutu amma aure babu fashi za a d'aura shi "
‎
‎Na shiga uku.....,...
‎Toh boka ni a kashe amaryar kawai koma wacece a kasheta wallahi da ta auri miji na gara ta mutu ,
‎Kada ki fara wannan gan gancin domin tabbas abunki ze dawo kanki "
‎Ki bari a d'aura auren mu munsan yadda zamuyi Amma wannan yarinyar a yanzu kam bazata ta'bu ba .
‎
‎Duk yadda umai ma taso a cutar da Rafi 'a boka ya fad'a mata ba abune me sauqi ba ,,
‎Domin yarinyar tanada riqon addini sosai ba komai ne ze iya ta'ba ta ba .
‎Haka umai ma da Momi suka dawo gida cike da takaicin rashin samun nasara ,
‎
‎umai ma tacewa Momi su canza gurin boka tunda obina ya kasa yimusu aiki suje su nemi wani "
‎Momi tace ,
‎Kada ma ki fara tunda kikaga wannan aikin ya gagari obina to babu bokan da ze iya ,
‎Duk wanda kikaje gurin sa wallahi sede yaci kud'in ki a banza kuma babu biyan buqata  ,,
‎
‎kede kawai ki bari a d'aura auren wallahi seta bar gidan da qafafunta .
‎
‎Aure yanata matsowa saura kwana uku ,
‎Muazzam yanata rawar kai kamar wannan shine auren sa na fari "
‎Da kansa ya d'au amarya Rafi 'a ya kaita gurin gyaran jiki akayimata komai da komai ,
‎
‎Tayi wani bala in kyau idan kaganta ba dan tanada duhun fata ba bazakace y'ar qasar Nigeria bace .
‎Muazzam kuwa tsabar zumud'i jiyake kamar ya d'auke ta ya kaita gidansa tun ya zu ,
‎
‎Tana tsaye a gaban mirror tana shafa turarurrukan ta da mayukan da take shafawa kafin ta kwanta Muazzam ya shigo '
‎Amarya ta kinsha qamshi wallahi ji nakeyi kamar kwana ukun na bazata qare ba "
‎Gani nakeyi ta yimin nisa da yawa jinakeyi kamar tun yanzu na d'auke ki na kaiki gida na .
‎
‎Mur mushi Rafi 'a tayi tace ,,
‎Dama ai gidan ka kam a ciki nake sede kawai kace ka matsu a shafa fatiha ,
‎
‎No Rafi 'a.....
‎Wannan ba gidana bane dominki na saya saboda haka mallakin ki ne "
‎na damu ne naga na d'auke ki daga nan na kaiki asalin gida na ba wai nan ba ,
‎
‎Asalin gidanka Kuma?
‎Wai dama ba a nan zamu zauna ba?
‎Eh Rafi 'a bazamu ci gaba da zama a nan ba dole zamu koma asalin gida na idan mukayi aure .
‎
‎A'a "
‎Barrister dan Allah muyi zaman mu a nan kawai ba semun koma can ba wallahi inajin tsoron masifar matar ka '
‎
‎No ,,
‎Gaskiya ya zama dole mu koma can baze yiwu muci gaba da zama a gidan nan alhali inada wani gidan ba ,
‎To Barrister idan nan d'in ne baka so zaka iya nema mana wani gidan koda haya ne '
‎Amma dan Allah kada ka had'ani da matar ka wallahi bazan iya da ita ba.
‎
‎Look Rafi 'a.....
‎Idan gida d'arin wannan nakeso inada kud'in da zan saya mu zauna a ciki But bana buqatar raba kan iyali na Inada iko a kan gida na kuma na isa na auri duk wacce nakeso na sakata a ciki  '
‎
‎Babu wacce ta isa ta takurawa y'ar uwar ta domin babu wacce take zaman wata a cikin ku ,
‎Idan misali na aureki na 'boyeki a nan muka tara yara "
‎Idan ta Allah ta kasance akace babu ni a raye waye yara na zasu nuna a matsayin dangin mahaifin su?
‎Wanene shaidar cewa ke matata ce kuma tare muka haifi yara?
‎Kinada tabbacin dangina zasu kar'bi yaranki a matsayin nawa ne idan babu raina?
‎
‎A'a ,
‎To saboda haka dole ki koma ki zauna tare da mata ta '
‎Ko babu komai duniya zata shaida cewar ke mata ta ce kuma yaran da zaki haifa nawa ne ,,
‎Dan haka kada ki sake cewa kinajin tsoron mata ta domin ita ba Allah bace .
‎
‎Toh '
‎Yauwa amarya ta mar atus saliha ta ,,
‎Sosai Rafi 'a tayi d'ari....
‎Muazzam ya turo mata bakin sa yana fad'in ,
‎
‎Kiss me "
‎Mur mushi Rafi 'a ta d'anyi sannan ta d'an kaiwa bakin duka a hankali '
‎Ka jira akwai sauran kwana uku tukun na.
‎
‎Dariya kawai Muazzam yayi yayimata sallama ya tafi ,,
‎Ranar aure Daddy ne da kansa ya kar'bawa Muazzam auren Rafi 'a  a hannun limamin anguwar su .
‎
‎Ba ayi taron komai ba domin Rafi 'a batasan kowa ba '
‎Se wasu tsofi ne Muazzam ya roqi su kawo masa Rafi 'a gida a matsayin amarya,,
‎
‎Haka kuwa akayi anayin sallar insha suka kawo Rafi 'a gidan ,
‎Ganin umai ma bata fito bane yasa suka d'auki Rafi 'a suka nufi 'bangaren ta da ita da niyyar damqa mata amanar ta "
‎Kwance suka tarar da ita tana rusar kuka kamar ranta ze fita ,..
‎
‎Ko kallon banza basu isheta ba balle har ta amsa gaisuwar su ko gurin zama bata basu ba seda suka gaji da tsayuwa sannan suka samarwa kansu masauqi'
‎Watace daga cikin su tayi qarfin hali tace ,
‎
‎Yarinya ga amaryar ki nan mun kawo,,
‎Dan Allah ki riqe ta amana ki d'auke ta a matsayin qanwar ki kuma abokiyar zama Dan Allah banda fiti na ku zauna lafiya .
‎
‎Bata kai aya ba umai ma ta fara bala i tana fad'in ,
‎Amanar uwar wa kuka kawo min?
‎To wallahi ban kar'ba ba tsakanina da ita sede fad'a da gaba "
‎kuma wallahi tunda ta shigo gida na ita da zama lafiya har abada ,
‎
‎Da kike faman kiranta da qanwa ta a gidan uwar wa ta zama qanwa ta?
‎Ta aurar min miji kuma ki kirata da qanwa ta "
‎To wallahi baze yiwuba kuma wallahi se ta bar gidan nan dan uban ta ,
‎Tunda ba gidan ubanta bane kuma babu kwandalar ubanta a cikin gina gidan  '
‎Gida na nawane ni kad'ai kuma wallahi kamar yadda ta sako qafa ta shigo da kanta haka zata fita da kanta .
‎
‎Haka umai ma ta had'a Rafi 'a da tsofin nan tayimusu tatas qarshe tamusu koran kare daga 'bangaren ta  ,,
‎Rafi 'a kam banda kuka babu abunda takeyi ,
‎Haka tayita roqonsu kada su tafi su barta daga ita se umai ma a gidan '
‎Seda suka jira Muazzam yazo sannan suka tafi .
‎
‎Muazzam 'bangaren umai ma ya nufa ya miqa mata leda d'aya daga cikin ledodin da ya shigo da su  '
‎Ganin bazata amsa bane yasa ya ajiye mata yayimata se da safe ya juya ,,
‎
‎A can qarshen gado ya hango Rafi 'a ta takure tana kuka  ,
‎Menene haka Rafi 'a ta?
‎hawaye fa nagani a kan fuskar ki madadin mur mushi "
‎Wannar ranar fa ranace ta farin ciki amma naga akasin haka a tare da ke ,
‎Rafi 'a kode bakya so na ne kika aure ni saboda kinajin nauyin cemin a'a?
‎
‎A'a wallahi Barrister.....
‎Ko kad'an ba haka bane na aureka ne kawai saboda ina son ka '
‎Amma wallahi bala in matarka yafi qarfi na bazan iya ba  ,,
‎Inajin tsoron zama tare da ita dan Allah ka canzamin gida kada wataran ta illata ni.
‎
‎Rafi 'a tayi maganar tana share hawaye da bayan hannun ta "
‎Ki kwantar da hankalinki Rafi a ta '
‎Kidena jin tsoron komai inde ina tare da ke babu wani abun cutarwa daze kusance ki .
‎
‎Dak'yar Muazzam ya samu ya shawo kan Rafi 'a ta d'an fara sakewa '
‎umai ma kuwa ball tayi da ledan kazar da Muazzam ya ajiye mata ,,
‎Ta shiga kai komo a tsakiyar d'akin "
‎
‎Shikenan na shiga uku yanzu yaya Muazzam ze kwana da ita kuma har ya ta'ba ta wai '
‎A'a.....  No "
‎
‎Wallahi baze yiwuba..... 
‎bayan ni yaya Muazzam be isa ya kwana da wata y'a mace ba  ,
‎Wallahi yau ko ni ko ita a cikin gidan nan amma baze kwana a d'akin ta ba .
‎Ta fad'a tana ficewa daga d'akin ta nufi kitchen a haukace ko gabanta bata gani da kyau '
‎
‎Wuqa ta d'auko ta nufo d'akin Rafi 'a ,
‎Da qarfi ta banko qofar ta shiga da sauri "
‎Wani irin zabura Rafi 'a da Muazzam sukayi a tare suka miqe tsaye suna kallon ta.
‎

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol