Free chapter · Read without an account
Chapter 13
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA........
Yana shiga cikin asibitin yayi parking ,
Da gudu' ya fito ya d'auko Rafi 'a Kai tsaye ya nufi office d'in babban likitan da gudu '
Da qarfi ya banko qofar ya shiga ya jefawa likitan Rafi 'a akan cinyar sa ,
Dr . Dan Allah ka temaka kaceci rayuwar Rafi 'a ta kada ta mutu Dan Allah ka temakeni Dr. Please.
Muazzam ya qarasa maganar yana durqusawa a cikin office d'in tare da sakin wani irin kuka "
Nurse's ya kira suka wuce da Rafi 'a emergency aka fara qoqarin ceto rayuwar ta .
An d'aura mata jini yakai leda biyar sakawa kawai akeyi yana fita '
Seda ta kusa kwana uku kafin ta fara dawowa hayyacinta Muazzam baya iya zuwa ko ina ya barta koda yaushe yana asibiti yana kuka ,
Satinta biyu a asibiti Alhamdulillah jiki yayi kyau sosai domin har abinci tana iya ci yanzu.
Muazzam na zaune yana bata ayaba a baki ta zubamasa ido tana kallonsa '
Menene kike kallo na haka?
Barrister ina qaunarka sosai wallahi kewarka nakeji koda ina tare da kai .
Inajin fiye da haka a kanki Rafi 'a kullum jinake ina qara samun kusanci da ke '
Rafi 'a duk ranar da akace babu ke tabbas zan manta yadda ake rayuwa domin kece rayuwa ta '
A hankali ta d'an rungume damtsen hannunsa tana sauqe ajiyar zuciya ,,
Rafi 'a......
Meyasa kika 'boyemin larurar ki har kika bari tayi qarfi tana neman rabani da ke ?Nayi qoqari fad'a maka amma baka bani dama ba Naje d'akin ka dan na sanar da kai ban sameka ba A ranar na jiraka sosai har nayi bacci baka dawo ba ,Washe gari danaje na sameka a d'aki seka koreni '
Nayita qoqarin sanar da kai sau da yawa amma ko sau d'aya baka bani dama ba "
Kullum idan naje da niyyar sanar da kai se ka kore ni kokuma ka fita ka barni ,
Barrister Allah ya sani larurar nan tana damuna sosai Amma wallahi nafi hukuntuwa da fushinka sama da larurar ,,
A duk lokacin da naje gurinka ka koreni ....
Mantawa nakeyi da duk wata larura ta domin rashinka yafita komai zafi a gareni ,
Barrister.....
Dan Allah koda nayimaka lefi kadena hukuntani ta hanyar nesantani da kai "
A shirye nake da kar'bar duk wani hukunci daga gareka amma zuciya ta bazata iya kar'bar rashinka ba .
Ta qarasa maganar tana sake qan qame shi sosai wasu hawaye suna malalowa akan kuncin ta.
Rungumeta Muazzam yayi sosai yana fad'in '
Sorry Rafi 'a Nayimiki alqawarin bazan sake nisanta kaina da ke ba Domin na fiki cutuwa akan hakan Rafi 'a duk lokacin da kikazo guri na na koreki bake kad'ai kike kuka ba nima kuka nake sosai Kewarki tana damuna sosai wani lokacin ko bacci bana iyawa Rafi 'a , Bansan ta yaya zan iya nunamiki soyayya ta ba '
Jinakeyi duk yadda zan bayyana baza a fahimta ba domin inajin sama da yadda zan fad'a kokuma na nuna shi a aikace ,,
Babu irin binciken da likitoti basuyi ba akan Rafi 'a amma an kasa gane damuwar ta Domin koda yaushe aka gwada ta se aga komai lafiya batada wani damuwa amma jinin yaqi tsayawa ,
Saboda haka ne wata likita a asibitin Dr . Latifa tace zata gwada kar'ba mata maganin gargajiya a gurin kakan ta idan sun amince zasuyi "
Muazzam yace inde Rafi 'a zata samu lafiya a kar'ba mata magani koma a ina ne .
Dr. Latifa ta fad'a masa maganin bazeyiwu a asibitin ba saboda haka Muazzam ya nemi sallama suka koma gida ,,
Dr. Latifa ta kar'bo mata magani sha da wanka da hayaqi Kuma ta sanar da shi Rafi 'a bazata iyayin maganin da kanta ba saboda wahalar shi ko shi ma seyayi juriya ze iya yimata ,,
Maganin na sati biyu ne kullum da dare za anayi za a nayimata wanka da hayaqi '
Na shan kuma yazama kamar ruwan shan ta na koda yaushe kuma koma wani irin wahala Rafi 'a zata sha kada a dakatar da yin maganin ,
Kullum Muazzam da kuka yake yimata maganin saboda wahalar da yaga tana sha "
Ba ita kad'ai ba shi kansa yana shan wahala wajen yimata wanka da hayaqin ,.
Duka, cizo yaguni.....
Babu wanda batayimasa saboda azaba "
Ihukam harda majina kullum idan anyimata maganin setayi fitsari wataran ma har suma take Domin idan yanayimata wankan jitakeyi kamar yana zubamata ruwan wuta a jikin ta ,,
Idan akazo hayaqin kamar borkono yake turara mata takeji gashi yana hawa har tsakiyar kanta .
Kullum idan yayimata maganin haka suke kwana babu bacci daga shi har ita '
Muazzam yasha jin kamar ya dena yimata maganin Amma yana buqatar ta samu lafiya saboda haka yake danne zuciyarsa yayimata yana kuka.
Hartakai Rafi 'a na tsoron Muazzam idan taganshi har neman shid'ewa takeyi saboda tsoro "
Sede babu lefi ta samu sauqi sosai domin jinin ya rage yawan wataran tana ini bata ganiba ,
Barrister dan Allah kadena yimin maganin nan '
Wallahi idan kaci gaba da yimin mutuwa zanyi Wasu irin hawaye suka cikamasa idanu shikansa yana mamakin wani irin qaddara ce haka Wahalar tana yawa gaba d'aya Rafi 'a nawa take '
Har yanzu ko shekara ashirin batayiba a duniya amma babu irin azabar da bata gani ba a rayuwarta .
Kiyi haquri Rafi 'a Ai lafiyar ki ake nema kinga harkin fara samun sauqi da akeyimiki magani Ki qara haquri saura kwana uku ne kawai zamu kammala Nima kaina banajin dad'in ganinki a haka Rafi 'a Amma babu yadda na iya inaso naga kin warke Banaso na dinga ganinki a cikin ciwo hakan bayamin dad'i ko kad'an .
Shiru kawai tayi tana hawaye amma ita kad'ai tasan irin azabar da takeci akan wannan maganin '
Idan anayimata jitakeyi kamar zata haukace Ta gwammaci dukan Amo da Gaddafi sau dubu akan wahalar wannan maganin.
Gashi kullum kamar qara azaba da wahalar akeyi idan anayimata "
A ranar da akayi na qarshe se da tayi suma bakwai kafin a gama Har seda Muazzam yaji kamar ya haqura da yimata Sede an fad'a masa Idan aka sake ba ayiba koda na rana d'aya ne maganin bazeyi aiki ba .
Alhamdulillah yanzu Rafi 'a ta warke sumul kamar batayi wani ciwo ba ,
Muazzam kuwa kullum qara kulawarsa yakeyi a gareta,,
umai ma kuwa kullum qara tsanar Rafi 'a take tana qarawa sharrita qaimi.
Yazid da Momi suna zaune a parlor Yazid kalli Momi yace.....
Wai Momi me muke jira da Muazzam ne?Zuwa yanzu ya kamata ace an shafe labarinsa Yaci ace mun shiga jerin masu kud'i ba masu gadin dukiyar Muazzam ba '
Kallon sa Momi tayi tace "
Saurin me kakeyi ne haka yazid? Mun aurawa Muazzam Umai ma ne domin muna buqatar ta aihu dashi A ranar da umai ma ta aihu a gidan sa a ranar zamu kawar da shi da abunda ya haifa "
Kaga kenan idan babu shi babu magajinsa dukiyar ta zama tamu kenan.
Amma Momi har zuwa yaushe ne zamu ci gaba da jira? Shekara biyu da wani abu fa kenan da auren amma har yanzu shiru '
Kullum lokaci qara qurewa yake bazan iya ci gaba da jiraba .
Ka kyale shi yazid .....
Akwai lokacin da muka yanke idan lokacin ya cika to ko umai ma ta aihu da shi ko kar ta aihu da shi tabbas zamu kawar da shi mu mallaki dukiya ta zama tamu ,,
Yade kamata kusan abunyi kokuma ni nasan abunyi da kaina.
Rafi 'a na zaune a gaban dressing mirror tana kwalliya Muazzam ya shigo......
Seda ya d'an tsaya a bakin qofa ya qaremata kallo yana mur mushi Sannan ya qaraso "
Rafi 'a ta......
Kullum qara kyau kikeyi nayi sa ar samunki a matsayin mata kuma ina alfahari da hakan.
Mur mushi Rafi 'a tayi sannan ta d'an riqe hannun sa ,
Nice nayi sa ar samunka a matsayin miji "
Badan kai ba da yanzu haka bansan wani irin hali nake ciki ba Na gode da irin soyayyar da kake nunamin idan kana kusa da ni ji nake kamar nafi ko wace mace sa a a duniya.
Juyo da ita yayi suka fiskanci juna '
Kiss me "
Baki ta d'an turo cikin shagwa'ba kamar zatayi kuka ,
Idan bakiyiba yau bazan yimiki uzuri ba sena cinye wannan d'an qaramin bakin '
Yayi maganar yana jan kumatun ta .
Rafi 'a tana kai bakinta kusa da shi cikinta ya murd'a "
Da gudu ta shiga toilet ta dinga kwara amai seda qarfinta ya qare ,
Muazzam se sannu yakeyimata '
Da kansa ya wanke mata baki ya d'auko ta ya kwantar da ita a kan gado.
Zazza'bi ne me zafi ya rufe ta ,,
Dama kusan sati uku kenan bata ganewa jikinta sosai ,
Washe gari Muazzam ya kaita asibiti aka tabbatar masa tana d'auke da ciki wata biyu da kwana ashirin da hud'u .
Wayyo Allah.....
Zo kaga farin ciki a gurin Muazzam ,,
A take ya damqawa Rafi 'a takardun fili da makullin mota Kuma yace idan cikin yakai watanni takwas zasu tafi Qatar ta aihu acan Daga nan su wuce aikin hajji .
Amma Rafi 'a ta roqeshi kada ya fad'a wa umai ma maganar cikin yanzu '
Koshima dama beyi niyyar fad'a mata ba domin yasan bazataji dad'i ba .
Dayake yawanci Rafi 'a a d'aki take wuni itama umai ma ta wuni a nata d'akin "
juriyya batasan komai game da cikin ba seda ya kai wata shida da sati biyu .
umai ma ta fito zata tafi wuni gida Rafi 'a kuwa ta fito zata shiga kitchen "
Wani mugun burki umai ma ta ja ta tsaya tana kallon cikin Rafi 'a da ya tsufa ,
Kokuwa ta farayi da numfashinta da yake neman rabuwa da gangar jikinta.
Wani abu me d'aci ta had'iye tanajin qafafunta suna qoqarin kasa d'aukar ta "
Batasan sanda wasu hawaye suka sulalo mata ba Dak'yar ta iya jan jiki ta fita daga gidan ta shiga motar ta ta ja ta nufi gidan Momi '
Tafi minti talatin a zaune tana rusa kuka Momi na tambayar ta abunda ya faru ,,
Seda tayi me isar ta sannan tace wa Momi .
Shekarata kusan uku kenan a gidan yaya Muazzam ban ta'ba yin koda 'batan wata ba Amma wai yanzu wannan shegiyar karuwar yarinyar tanada tsohon ciki harta kusa aihuwa.
Wani uban ashar Momi ta mul mulo ta maka '
Kutumar uban can kayyasa umai ma ke daqiqiyar ince kina zaune har yarinya tazo tayi ciki ya tsufa baki sanar da ni mukayi maganinta daga ita har cikin ba?
Wallahi Momi nima kaina bansan da cikin ba ko yaya Muazzam be fad'amin ba '
Kuma kinsan ba shiga harkar ta nakeyi ba ba ganinta nakeba seyau naga ashe cikin harya tsufa Yanzu Momi dan Allah yaza ayi ? Wallahi idan yarinyar nan ta aihu a gidan yaya Muazzam shikenan na kad'e har ganyena .
Ke dalla gafara can sha sha shar banza kawai "
Ke ta mijinki kikeyi nikuma tunanina shine yarinyar nan tana aihuwa duk wani shirin mu ze lalace ,Tana aihuwa shikenan dukiyar Muazzam ze koma nata ita da d'an ta kuma wallahi abunda baze ta'ba yiwuwa ba kenan .
Yau naga shegiyar yarinya tazo ta samu guri ta baje tana nema tasa wankin hula ya kaimu dare Bari na d'auko mayafi na mu tafi gurin boka "Wallahi dole ne asan yadda za ayi da cikin nan ,
Kusan qarfe biyar da wani abu suka isa gidan boka '
umai ma ta fad'a masa tanaso a lalata cikin ne a zubar da shi yabi makwarari .
Seda boka yayi wata dariya me ban tsoro sannan yace ,
Kull Kada ki sake kiyi yunwurin ta'ba wannan ciki domin yafi qarfin ki "
Duk abunda zakiyi ki tsaya akan uwar da uban amma wannan cikin duk randa kima sake kikayi yunqurin ta'ba shi zaki mutu ko ki haukace d'an da yake cikin ta yafi qarfin ki saboda haka ki gaggauta shiga cikin hayyacin ki babu ruwanki da shi Idan kuma kika qi ji kikayi yunqurin ta'ba shi sekinyi walaqantacciyar mutuwa marar dad'i .
Na shiga uku boka to yanzu meye abun yi?
Zamu iyayin aiki akan ta amma yaron cikin ta yafi qarfin mu .
Boka inaso idan ze yiwu a kad'ar mata da hankali A kad'a ta can wani guri a mantar da ita komai A 'batar da hankalin ta inaso tabar gidan na har abada ,
Kuma inaso a saka Muazzam ya manta da ita ya manta labarin ta ya manta ya tabayin wata mata me suna Rafi 'a banaso ya sake tinata har abada .