Free chapter · Read without an account
Chapter 15
Babu 'bata lokaci aka wuce asibiti da Rafi 'a ,
Basu wani jima ba Rafi 'a ta haifo qaton yaron ta fari tass me kama da Muazzam kamar an tsaga kara "
Ana tsaka da yimata murna wani sabon ciwon ciki da ciwon baya suka qara kama ta '
Likita yazo ya duba yace yara biyu ne a cikin saboda haka d'ayan yana ciki be fito ba tukun ,,
Seda ta sake wani sabon naquda ta haifo kyakkyawar yarinya me kama da ita ,
Sede ita hasken Muazzam ta d'auko domin fara ce tass .
Idan kaga yadda Faiz yake rawar kai da murna kai kace yaransa ne ,,
Rafi 'a tayi farin ciki sosai sede duk sanda aka tambayeta ko ta ta'ba yin aure se tace ita bata saniba '
Shi kansa cikin kawai ganinsa tayi ,,
Faiz ne yayimusu hud'uba da kansa sukaci suna ,
Aisha da Muhammad....
Ana kiran Aisha da Naznin Muhammad kuwa ana kiransa da Hisham.
Yara kyawawa farare tass tass gwanin sha awa duk wanda ya kallesu sesun burgeshi Tunda aka haifi Hisham da Naznin d'akin Rafi 'a ya koma gurin hirar Faiz Inde yana gidan kullum suna tare domin yana qaunar yaran Jiyake tamkar shine ya haifesu .
Adil kuwa kullum yana maqale da su wai shi a dole yayi qanne ,
Ko abinci aka basa wani lokacin idan Rafi 'a bata kusa se tazo ta samu ya d'ura musu wai yana bawa qannensa abinci dan suyi qarfi '
An saka Adil a makaranta yau itace ranar sa ta farko na zuwa makarantar ,,
Bayan an kammala shirya shi ya shigo d'akin Rafi 'a ya tarar tana shirya Hisham da Naznin '
Aunty shahinas na shirya yanzu zamu tafi ki bani Hisham da Naznin mu tafi makarantar tare .
Aahhh yaya Adil bazasu jeba kaga ai yara ne ko zama basayi bazasuyi karatu ba sede su dameku da kuka Kabari idan suka qara girma suma za a sakasu se kuna tafiya tare .
Yanzu ka je ku tafi kada ku makara naji uncle Faiz yana Kiran ka "
Har Adil ya isa bakin qofa ya dawo da sauri ,
Aunty shahinas kiss me......
Rass gaban Rafi 'a ya fad'i dajin kalmar har seda naznin da ke hannunta ta nemi fad'uwa "
Faiz ne da ya shigo yayi saurin kar'bar ta '
Subhanallah......
Haba shahinas menene haka? Kin rasa hankalinki ki ne? Yarinyar nan fa jaririya ce yanzu idan kika bari ta fad'i tayi wani raunin kuma fah?
Wato de bazaki koyi mayar da hankali akan abu ba koh ,,
Ganin yadda ran Faiz ya 'baci yanata fad'a ne yasa tace '
Dan Allah kayi haquri uncle Faiz bada sani nayiba ban kula bane ,,
Ajiye Naznin kawai yayi a kan gado ya fice ransa a 'bace '
Domin yana mugun qaunar yaran fiye da tunaninsa ,,,
Kiss me...... Kiss me..... Kiss me "
Kalmar da Rafi 'a keta mai maitawa kenan tanaso ta tina wani abu makamancin haka a cikin rayuwar ta amma ta kasa .
Babu irin qoqarin da umai ma batayiba dan ganin ta samu ciki a gidan Muazzam amma abu yaci tura '
Babu ciki babu labarin ciki sannan babu alamar zata samu nan kusa .
Abun ya ishi umai ma saboda haka taje asibiti domin a gwada ta umai ma tayi nadamar wannan gwajin domin likita ya tabbatar mata bazata ta'ba aihuwa ba har abada domin mahaifar ta tayi laushi.
Hankalin umai ma da Momi yakai qololuwa wajen tashi ,,
Babu inda bataje ba dan tasamu koda a guri d'aya ne a fad'a mata sa'banin haka amma duk inda taje maganar d'aya ce Shine bazata ta'ba aihuwa ba domin mahaifarta tayi laushi kuma ta mutu .
Hisham da Naznin se qara wayo suke kyawunsu yana qara bayyana ,
Farinsu yana qara fitowa sosai sunyi 'bul 'bul gwanin sha awa......
Rafi 'a tana zaune tana shirya Naznin Faiz ya shigo ya zauna "
Yakai hannu ya d'ago Hisham yanayimasa wasa Yaro se kyal kyala dariya yake domin suna ganin Faiz suke washe baki sunayimasa dariya '
Yana kula da su sosai domin shi mutum ne me matiqar son yara musamman ma y'an biyu ,,
Sede duk da son yaransa wani lokacin ba sune suke kaishi d'akin ba yanazuwa ne kawai dan yaga Rafi 'a .
Sede shikansa besan dalili ba amma yasan wani lokacin yana tsintar kansa da son kallon ta ,
Seda ya d'an gyara Hisham akan cinyar sa sannan ya kalli Rafi 'a yace "
Shahinas inaso nayi wata magana me muhimmanci da ke saboda haka ina buqatar hankalin ki.
A hankali ta zare Naznin wacce ta fara bacci tun tuni ta ajiyeta a saman gado ,,
Toh uncle Faiz ina sauraronka.......
Inaso ne nasan wani abu a kanki '
Inaso nasan ko kinada aure koda bakida shi yanzu inaso na sani ko a can baya kin ta'ba yin aure ?
Seda ta d'anyi jimm kamar bazatace wani abu ba kafin tace ,
Ban saniba uncle Faiz Wallahi ban saniba ko kad'an na kasa tinawa kuma banason tinawa ,,
Da mamaki Faiz ya kalleta '
Bakyason tinawa fa kikace Amma meyasa bakyaso tinawa?
Ta sunkuyar da kai idanunta na ciccikowa da hawaye cikin rawar murya tace "
Eh "
Banason tinawa domin koda nayi qoqarin tinawan bana iyawa Idan Kuma na matsa da tunani se kaina ya fara yimin ciwo Inajin wasu muryoyi marasa dad'i sunayimin ihu a kunne '
Dazarar na nemi tina wani abun se hankalina ya fara qoqarin gushewa daga jiki na Jinakeyi kamar kaina ze fashe '
Wasu muryoyi nakeji sunayimin amsa kuwa marar dad'in saurara,
Ba a hankali sukeyi ba Sunayine da matiqar qarfin da nakejin kamar kaina ze tarwatse "
Ina matiqar shan wahala shiyasa kuma wasu lokutan kuke kallo na kamar bansan me nakeyi ba kokuma kamar me aljanu Amma wallahi ina sane da komai Kuma ni kad'ai nasan irin abunda nakeji '
Bazan iya kwatantawaba domin babu ta yadda zan iya kwatantawa har a fahimta .
Wata y'ar nannauyar ajiyar zuciya Faiz ya sauqe sannan yace '
Ki kwantar da hankalinki shahinas tabbas watarana zaki tina komai kuma zaki koma gurin danginki .
Muazzam yana tafiya motar sa ta tsaya tana hayaqi saboda injinta ya d'au zafi sosai "
Parking yayi ya d'auko ruwan robarsa se yaga ashe ya qare Saboda haka dole ya tsaya jiran ko wani zezo wucewa '
Cikin sa a be wuce minti uku a tsayeba sega wata yarinya da bazata wuce shekara goma ba d'auke da ruwa a kanta .
Yarinya.....
Dan Allah d'an zomana '
Da sauri yarinyar ta qaraso gabansa tace ,
Ina yini "
Lafiya qalau Ina tafiya ne se mota ta ta d'au zafi gashi ruwa na ya qare dan Allah ko zaki temaka ki tsammin ruwannan?
Toh ba damuwa ,,
Yarinyar ta fad'a sannan ta miqa masa ruwan ,
Da sauri Muazzam ya kar'ba yayimata godiya ya shiga zuba ruwan a motar Sekuma yaji hankalin yarinyar ya burgeshi sosai kawai se ya tsinci kanshi da son sanin sunan ta ,
Menene sunanki yarinya ?
Rafi 'atu..........
Wani mugun bugawa qirjinsa yayi da qarfi har seda bokitin ruwan ya su'buce ya fad'i a hannunsa Da sauri ya juya ya shige mota ya fizgeta a guje ya nufi hanyar gida .
umai ma na zaune a parlor Muazzam ya shigo kamar an jefoshi '
Wacece Rafi 'a ? Ki fad'amin wacece Rafi 'a a cikin rayuwa ta ?
Wani irin miqewa umai ma tayi a tsorace dak'yar ta iya tattaro nitsuwar ta ,,
Rafi 'a kuma? Wacece haka?
Ni ban santa ba babu wata Rafi 'a a cikin rayuwar ka '
Qarya kike fad'amin umai ma......
Babu gaskiya ko kad'an a cikin maganar ki Tabbas inaji a jiki na cewar inada kyakkyawar alaqa da mace me irin wannan sunan .
Yaya Muazzam gaskiya na fad'a maka ka kwantar da hankalinka bakada kowace iriyar alaqa da me irin wannan sunan ,
You are a liar.....
Qarya kike fad'a umai ma qarya ne ke maqaryaci ce "
Kusa da shi umai ma ta matso ta kai hannu zata ta'ba shi ,
Don't touch me......
Muazzam ya fad'a yana ja da baya da sauri ya juya ya shige d'akinsa ya rufo qofar da qarfi .
Da sauri umai ma ta d'auki wayar ta ta shige d'aki ta kira Momi a waya '
Hello Momi na shiga uku........
Me yake faruwa umai ma?
Nashiga uku Momi shikenan yaya Muazzam ya fara dawowa hayyacin sa "
Yazo yana tambaya ta akan alaqarsa da wannar shegiyar yarinyar Rafi 'a ,
Yanata dakamin tsawa har maqaryaciya yacemin '
Wallahi Momi tsoro nakeji idan ya dawo hayyacinsa bansan me zamcemasa ba .
Ki kwantar da hankalinki umai ma baze ta'ba tina ta ba ,,
Domin bazan ta'ba bari hakan ta faru ba har abada Bari na koma gidan boka yadda ban zauna da kishiya ba kema wallahi gidanki nakine ke kad'ai .
Wasa gaske Hisham da Naznin sunyi wayo sosai sunada watanni takwas a duniya ,
Suna rarrafe ko ina suna shiga har tafiya sun fara koya "
Duk inda Faiz ze shiga yana tare da su sun shaqu da shi sosai Ko da yaushe suna tare .
Ranar jumma a da yamma Muazzam yazo garin kaduna saboda wata shari a da sukeyi"
Bayan ya kammala abunda yazoyi yana shirin komawa se ya tina umai ma tace idan ze dawo ya sayomata chocolate da sweet ,
Da sauri ya juya kan motar sa ya nufi super market "
Tunda ya kama hanyar super market d'in gabansa yake fad'uwa yanajin zuciyarsa sa na tsinkewa.......
Bayan ya kammala sayayya yazo biyan kud'i '
Wani mugun duka qirjinsa yayi lokacin da ya hango wani saurayi riqe da wani kyakkyawan yaro me masifar kama da shi ,,
Sosai ya razana da kamar domin hatta kallonsu iri d'aya ne da yaron '
Fasa fita yayi da sauri ya juya cikin super market d'in yana bin bayan saurayin cikin sand'a.
Haka yayita binsa har seda ya kammala sayayya ya fito "
Da sauri Muazzam ma ya fito ya shiga motar sa yana bin bayan matashin ,
Har Faiz ya iso yayi parking a bakin gate ya fito riqe da yaron a hannunsa ya shiga gida Muazzam be dena binsa ba.
Yasha matiqar mamaki tunda yake be ta'ba ganin kama irin tasa da ta yaron ba "
Seda ya d'an jima a qofar gidan sannan ya juya kan motar sa ya nufi garin Gombe ,
Sede ya kasa manta yaron sosai yakejin dad'i idan ya tina shi '
Ji yakeyi kamar yanada wata makusanciyar alaqa da yaron ,,
Take yaji qaunar yaron ya mamayeshi kamar ya d'aukeshi ya gudu yayi nisa da shi ta yadda babu wanda ze iya rabasa da shi '
Seyakejin kamar duk wata nitsuwar sa tana tare da yaron Harya isa Gombe yana tina yadda ya kalli yaron duk sanda ya tinashi se yaji gabansa ya fad'i .
Adil na zaune a parlor tare da Hisham da da Naznin yanayimusu wasa '
Se washe baki sukeyi suna kyal kyala dariya domin suna son Adil sosai ,,
Kiss me Naznin kiss me Hisham ,
Adil ya fad'a dede lokacin da Rafi 'a ta sako qafarta a cikin parlorn ,,
Wani irin yankewa gabanta yayi ya fad'i qirjinta ya bada wani sauti me qarfi "
Dummm...... Dummm......
Tunani ta shigayi akan kalmar Sosai ta tafi tunani tanason tino wani abu akan rayuwar ta Da ta nisa a cikin tunanin se kanta ya kama yimata ciwo Ta fara jin wani hayaniya a cikin kanta tanajin wasu muryoyi masu amsa kuwa sunayimata dariya tare da kuka a cikin kanta "
Ga kukan jarirai had'e da dariya ga wata murya me kaushi da qarfi tanayimata wani irin magana da ta kasa gane wani yare yakeyi .
Hannu ta d'aura a kayi ta saki wani uban ihu ta zube a qasa tana toshe kunne '
Sosai take ihu tana surutai ,,
A'a kubari banaso dan Allah ku kyaleni ku rabu da ni me nayimuku ne?
Dan Allah azo a temakeni sunayimin tsawa zasu haukata ni wayyo Allah ina zansa kaina .
Faiz ne ya shigo da sauri ya nufo inda take tsugunne ta saka hannu ta toshe kunnen ta se faman ihu da qara take"
Sunkuyawa yayi ya riqota amma seyaga gaba d'aya bata cikin hayyacinta ,
Addu o' i ya shiga yi yana tofa mata Seda suka d'an jima a haka sannan ta d'ago kai ta kalleshi "
Na shiga uku uncle Faiz zasu haukata ni sunayimin ihu a cikin kaina kacemusu su dena su kyaleni dan Allah wallahi bana so Ta qarasa maganar tana fad'awa jikinsa tare da fashewa da kuka me qarfi .
Sosai ya riqeta a jikinsa yana sauqe numfashi ,,
Zuwa yanzu shikansa yasan ya kamu da matiqar soyayya da qaunar ta Amma yana shiga damuwa idan yayi tunanin ze iya kasancewa tanada aure tunda dama da ciki ya ganta gashi har ta aihu .
Sorry shahinas..,....
Kiyi haquri kinji babu abunda suka isa suyimiki da yardar Allah kinfi qarfin koma waye "
Shiru tayi tana sauraran yadda zuciyarsa take bugawa ,
Tashi muje in kaiki d'akin ki koh....
Toh "
Da kansa ya tayar da ita tsaye yaja hannunta suka nufi d'akin ta Domin duk da tana samun sauqi wasu lokutan idan tana wani abun sekace yarinya y'ar shekara biyu Idan tayi wani shirmen kamar wacce batada wadataccen hankali ,,
Seda ya kaita d'akinta ya shumfud'e ta sannan ya dawo parlor ya d'auki Hisham da Naznin ya fita ,
Harga Allah yana qaunar ta amma ya kasa fad'awa kowa domin besan da wace fuska za a fahimci maganar ba .
Tunda Muazzam yaga Hisham ya tsiri yawan zuwa kaduna koda babu abunda zeyi a can'
Haka yake zuwa qofar gidan su Faiz ya zauna yana jira Faiz ya fito da yaron dan yasamu ya ganshi Domin kallon yaron koda daga nesa ne yana matiqar ciremasa damuwa '
Idan yazo haka yake ini a qofar gidan yana jiran fitowar su "
Duk da Faiz yana yawan fita da Hisham amma duk da haka wani lokacin har Muazzam ya gama tsayuwar sa ya tafi baya ganin su .
Kamar kullum yauma Muazzam yana tsaye a qofar gidan su Faiz yana jira koda zega fitowar su ,,
Cikin sa a se gashi ya fito amma wannan karon yaran duka biyu suna riqe a hannunsa .
Wani mugun bugawa qirjin Muazzam yayi lokacin da ya kalli fuskar Naznin '
Su waye su?
Tabbas akwai alaqa ta kusa sosai a tsakanina da su Amma su waye su sunada muhimmanci a gareni dole naje na sameshi yayimin bayani a kansu '
Da gudu ya fito daga motar dede lokacin Faiz ya tada motarsa ya fara tafiya .
Kira Muazzam ya shiga kwalamasa yanabin motar da gudu amma ina ko kad'an Faiz be jishi ba,,
Haka yayitabin motar Faiz da gudu yana kwala masa kira '
Har Faiz ya 'bacewa ganinsa ,
A gurin Muazzam ya durqushe ya riqe kansa ya fashe da wani irin kuka "
Wai shin wanene ni ?
Suwaye su? Mecece alaqata da su?
tabbas nasan munada alaqa amma wace irin alaqa ce?
Wanene ni a garesu kuma su su wayene a gareni ? .