Free chapter · Read without an account

Chapter 18

by Fatima Usman Abdullahi · UQUBA

‎BY
‎
‎FATIMA USMAN 
‎SHA LELEN TERAWA........
‎
‎
‎
‎Da sauri mutumin ya kai hannu ya kar'bi Hisham dake qoqarin zamewa daga hannunta '
‎tayi saurin duqawa tana dafe qirji had'i da mai maita kalmar ,,
‎Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un........
‎
‎D'ayan hannun sa ya kai ya d'ago ta "
‎Wani irin yarrr taji a jikin ta kamar an jona mata lantarki Zuciyar ta ta qara tsananta bugawa da sauri ' Ita kanta bazata iya tan tance halin da take ciki a yanzu ba .
‎
‎Kina lafiya kuwa ?
‎Mutumin yayi tambayar da kamilalliyar muryarsa dake d'auke da isa da dottaku "
‎
‎Kai Rafi 'a ta d'aga masa tanajin muryarsa na amo a dodon kunnen ta .
‎Hannunta ya ja a hankali ya nufi cikin gidan da ita hajiya Maryam ta rufa musu baya ,
‎
‎Wani qaton mu had'u a parlor ya nufa da ita wanda yaji kaya na alfarma ,,
‎Tsayawa tsara yadda parlorn ya had'u ma kamar qauyanci ne Domin yawuce duk yadda za a iya fad'a abun sede wanda ya gani .
‎
‎Babu motsin kowa a cikin gidan da alama kowa yayi bacci ne kasancewar dare tayi sosai"
‎A kan wata lallausar kujera ya zaunar da ita sannan ya kai hannu ya dafa goshin ta ,
‎
‎Duk da idanuwanta a bud'e suke seda ta qara bud'e su sannan ta lumshe saboda duk sanda mutumin ya ta'ba ta se ta kasa gane a wani yanayi take .
‎
‎Seda ya kalli hajiya Maryam sannan yace cikin nitsuwa '
‎Da alama batajin dad'i ne Ki kaita d'aki tayi wanka ta kwanta ta huta Mu kuma zamu kwana da yaran tunda naga kamar bata cikin yanayin da zata iya kula da su .
‎
‎Babu musu hajiya Maryam ta kama hannunta ta shiga wani qaton d'aki me d'auke da komai na more rayuwa '
‎Seda ta tabbatar tayi wanka ta kwanta sannan ta kashemata wuta itama ta nufi nata d'akin ......
‎
‎Wani irin yanayi Rafi 'a takeji tanajin kamar bata ta'ba kasancewa a guri me aminci irin wannan ba ,
‎Jitake inama ace zata iya qarasa rayuwar ta a nan Domin tunda take bata ta'ba kasancewa cikin nitsuwa da cikakken gamsuwa irin na yau ba ,
‎
‎Tanata tunane tunane a cikin ranta har bacci ya d'auketa ta .
‎Asuba nayi hajiya Maryam tazo domin tada Rafi 'a tayi sallah amma se ta tarar har ta kammala alwala ta tada sallah "
‎
‎Hakan ya matiqar bawa hajiya Maryam sha awa da tabbacin Rafi 'a yarinya ce me son addini ,
‎
‎Qarfe goma na safe wata kyakkyawar matashiya ta shigo d'akin Rafi 'a ,,
‎Da alama y'ar aikin gidan ce Ta sanar mata ance ta fito su karya domin al adar gidan ce tare sukecin abincin dare da na safe .
‎
‎Hijabi Rafi 'a ta saka tabi bayan y'ar aikin suka fito ,,
‎Alhj Hafiz Atiku marafa ta tarar a gurin cin abincin tare da matarsa hajiya Maryam Se wata mata wacce zata girmewa hajiya Maryam da alama itace uwar gida ko daga ganin yadda take cika tana batsewa '
‎
‎A d'an rud'e matar tayi saurin miqewa tsaye tana kallon Rafi 'a ,,
‎Lokaci guda yanayinta ya canza jikinta ya d'au kerma kamar an sakata a ruwan qan qara '
‎
‎Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un.......
‎Ta furta cikin yanayi na gigicewa da firgici ,,
‎
‎Cike da mamaki Alhj Hafiz ya kalleta ,
‎Lafiya kuwa Habiba ?
‎Eh lafiya qalau babu komai Wacece wannar kuma ?
‎
‎Tayi tambayar a rikice a cikin ranta tana fatan Allah yasa ba abunda take zato bane ,
‎Domin kuwa idan hakane tasan ta gama yawo .
‎
‎Alama yayiwa Rafi 'a da hannu ta zauna sannan yace "
‎Mu kammala karyawar tukun na zakiji komai zanyimuku bayani yadda zaku fahimta .
‎
‎Zama tayi tana share gumi duk da sanyin A . C da ya gauraye parlorn tako ina ,,
‎Ta d'au ruwa ta kora dan ya wuce da wani kakkauran yawu busasshen da ya tsaya a maqogoron ta .
‎
‎Har suka kammala cin abincin hajiya Habiba batayi ko loma uku me kyau ba "
‎Se wasa kawai take da abincin tana cakalar sa ita kad'ai tasan abunda take tunani a cikin ranta ,
‎
‎Bayan sun kammala karyawa Alhj Hafiz yace gaba d'aya su sameshi a 'bangaren sa .
‎Bayan sun gama hallara Alhj Hafiz yayi bayanin yadda akayi suka samu Rafi 'a sannan ya qara da cewa Zataci gaba da zama a tare da su .
‎Sannan ya sallamesu kowacce ta koma part d'in ta ,,
‎
‎Hajiya Habiba tana komawa part d'in ta ta d'au wayar ta ta kara a kunnen ta '
‎Hello hajiya lubuna maza kizo inason ganinki yanzu baya ta aihu Jiya Alhj da wannar makirar matar tasa Maryam sukaje gaisuwa garin kaduna se gashi sun dawo da wata yarinya ita da Alhj kamar an tsaga kara Kumama ba ita kad'ai ba wai harda yara biyu.....
‎
‎Kambala i "
‎Dama yanzu zan fita ne amma kibani 15 minutes yanzu zan qaraso gidan naki ,
‎
‎Muazzam be iso garin Gombe ba se qarfe uku na asubah......
‎Gaba d'aya wani irin yanayi yakeji kwata kwata bayajin dad'i  Haka ya iso gida yanajin kamar kada ya shiga Domin a yanzu haka kawai yakejin bayason ganin umai ma.
‎
‎Sede yanajin kewar da batada iyaka kuma shi kansa besan na meye bane '
‎Haka ya shiga' gidan ya shige 'bangaren sa yayi wanka ya kwanta ,,
‎
‎Se kusan sha d'aya na rana umai ma ta shigo d'akin ta tarar da shi a kwance yana bacci '
‎A kusa da kansa ta zauna qamshin turaren da boka ya bata ya daki hancin sa ,,
‎
‎A hankali ya bud'e Idanunsa yana kallonta '
‎Me yake faruwa ne kikazo kika tasheni ina bacci ?
‎
‎Umhm...,...
‎Babu komai kawai nazone muyi hira kode lefi ne idan mata tazo domin tayi hira da mijin ta ?
‎
‎A'a......
‎babu wani lefi a ciki ,
‎Mur mushin jin dad'i ta d'an yi ta juya idanun ta sannan ta qara matsawa kusa da shi sosai .
‎
‎Har ga Allah Muazzam bajin dad'in kasancewar ta a kusa da shi yake ba "
‎Sede baze iya korar ta ba domin jiyake tayimasa kwarjini kamar ma tsoro take bashi ,
‎
‎Tashi yayi ya zauna umai ma ta matso daf da shi sosai yana shaqar qamshin jikin ta ,,
‎Ta d'auki hannunsa ta d'aura a saman qirjin ta.......
‎
‎Shikam Muazzam kallo kawai yake binta da shi kamar wani soko '
‎A hankali ta qara matsawa kusa da shi ta d'aura lips d'inta a kan nasa tana wasa da shi .
‎A hankali Muazzam ya lumshe idanunsa yanajin wani irin yanayi yana ratsa shi ,
‎
‎A hankali ya lumshe idanunsa ya shiga mayar mata da wani zazzafab kiss .
‎Gaba d'aya ya soma ficewa a hayyacinsa ya rungume umai ma da qarfi '
‎
‎I love you so much Rafi 'a ta.......
‎Abunda Muazzam ya tsinci kansa da fad'a kenan .
‎Wani irin sauti qirjin umai ma ya bada take cikin ta ya karta "
‎
‎Wani abu me d'aci ya tsaya mata a maqoshin ta ,
‎Amma seta basar bata nuna masa ba domin bataso ta matsa masa da maganar Dan ta kula idan ta cigaba da jan maganar ze iya tina komai .
‎
‎daga hajiya Maryam har Alhj Hafiz suna son Rafi 'a sosai "
‎Kasancewar ta yarinya me nitsuwa da son addini ga hankali da biyayya ,
‎
‎Ta saba sosai da Humaira y'ar aikin gidan Domin humaira ma yarinya ce bazata girmi Rafi 'a ba ,,
‎
‎Hatta ayyukan gidan kusan tare sukeyi da Rafi 'a domin jininsu ya had'u ,
‎Dayake itama Humaira akwai hankali da nitsuwa .
‎
‎Hisham da Naznin kuwa kullum suna tare da ita '
‎Dayake yaran sunada shiga rai wani lokacin haka kawai Alhj Hafiz yake sakawa a d'auko su a kaimasa su 'bangaren sa .
‎
‎Hajiya Habiba kam daga Rafi 'a har yaran ta kai hatta hajiya Maryam d'in bata isheta kallo a cikin gidan ba "
‎Humaira ta zama qawar Rafi 'a sosai Wani lokacin ko aikanta akayi se Rafi 'a ta bita su tafi tare ,
‎
‎Ganin duk sanda ta fita se wani ya biyota da sunan soyayya ne yasa hajiya Maryam ta hanata fita gaba d'aya .
‎Wasa gaske kusan watan Rafi 'a biyu Kenan a gidan Alhj Hafiz Hisham da Naznin sun qara kyau da girma domin suna gudu ko ina Ga wayon tsiya musamman Naznin da takeda surutu sosai......
‎
‎Wani d'an saurayi a wani qauyen fulani da yake jahar Gombe wato jamarin "
‎Yazo d'iban ruwa a rafi ya duqa ya saka tulun sa  Yana d'ebowa yaga wani abu a nannad'e da baqin k'yalle......
‎
‎Ya saka hannu ya ciro abun ya war ware k'yallen "
‎Se kuma yaga wani jan k'yalle a ta ciki ya war ware Wani abu ya gani a ciki nannad'e da farin k'yalle Anyi rubutun Arabic ta ko ina a jikin k'yallen ,,
‎
‎Gashi ta ko ina an rubuta sunan Rafi 'a da Muazzam......
‎Yana war ware farin k'yallen sega wasu zabga zabgan kayukan qadangaru guda bakwai a ciki tare da wata baqar laya "
‎Ko wani d'aya daga cikin kan qadan garun an sossoka allura ta ko ina Sannan an d'inke bakin kowanne daga ciki .
‎
‎Se zuciyar wata dabba wacce aka d'id'd'inketa kota ina ,,,
‎Wata y'ar qaramar askira ya ciro ya ware gaba d'ayan d'inkin sannan ya war ware layar Ya ciro wata farar takarda daga ciki wacce aka nannad'e ta sosai Ya war wareta.......
‎
‎An rubuta ayar fal fariqati qafa uku da wasu ayoyi daga cikin alqur ani ,
‎A tsakan kanun ko wace aya an rubuta sunan Muazzam da na Rafi 'a .
‎Anyi rubutun ne da jinin al ada da kuma Spam na mace da namiji , wa iyazubillah .
‎
‎Sannan anyi wasu rubutun larabci a hargitse ta ko ina a jikin takardar "
‎Gaba d'aya ya had'a ya tattara ya kunnamusu wuta Wani baqin hayaqi ne me wari yake tashi sama ,,
‎
‎Muazzam na zaune a office d'in sa yaji kamar an tsikara masa kifiya ,
‎Wani azababben ciwo kansa yakemasa  kamar ze fashe "
‎
‎Jiyakeyi kamar wani tururi na fita daga cikin kansa .......
‎Gaba d'aya nema yake ya fita a hayyacinsa kafin kace me idanunsa sun kad'a sunyi ja kamar garwashi ,
‎Da sauri ya d'auki makullin motar sa ya nufi hanyar fita a gigice "
‎
‎Rafi 'a na kitchen tana taya Humaira girki taji jikinta ya d'au rawa ,
‎Kanta nayimata wani irin sarawa ta fara ganin wani baqin duhu na gifta wa Ga wani jiri na d'ibar ta ta dena ganin komai ,,
‎
‎D'aga qafar ta tayi da niyyar fara tafi amma ina abun yaqi "
‎Hannu ta d'aura a kayi ta saki wani uban ihu ta fad'i qasa bata ko motsi .
‎

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol