Free chapter · Read without an account

Chapter 19

by Fatima Usman Abdullahi · UQUBA

‎BY
‎
‎FATIMA USMAN 
‎SHA LELEN TERAWA.......
‎
‎
‎
‎Da wani mugun gudu Muazzam ya shigo cikin gidan umai ma na zaune a parlor ,
‎Magana takeyimasa amma ko bi ta kanta beyiba D'akin Rafi 'a ya shige a guje yana kiran sunanta ,
‎
‎Rafi 'a...... Rafi 'a...... Rafi 'a ta '
‎Ina kika shiga ne dan Allah ? Ki fito banason irin wannan wasan da ze danganta rabuwata da ke "
‎
‎Wani irin sauti qirjin umai ma ya bada da sauri ta miqe tabi bayansa ,
‎
‎Ina Rafi 'a ta?
‎umai ma ina kika kaimin Rafi 'a ? Please umai ma dan Allah idan wani gurin kika kaimin ita ki temaka ki nunamin ita  Wallahi banajin zan iya jurewa rasa ta .
‎
‎Muazzam yayi maganar cikin wata siga me ban tausayi '
‎Ko ba a fad'a ba daga yanayin yadda yake magana zaka fahimci zuciyar sa tayi mugun karyewa Musamman yadda yake magana yana kuka kamar wani qaramin yaro .
‎
‎Seda umai ma tayi qoqarin dedeta nitsuwar ta sannan tace "
‎
‎Wace Rafi 'a ?
‎Rafi 'ar da ta gujeka ta tafi ta rabu da kai kuma tayimaka walaqanci ba tare da ta duba halin da zaka shiga ba tayi tafiyar ta yau itace kake cewa bazaka jure rashinta ba ?
‎Yarinyar da ta watsar da kai tayi tafiyar ta bayan ta cimma burinta a kan ka '
‎
‎Dama ta aureka ne saboda wata manufar ta yanzu Kuma tasamu cikar burin ta saboda haka bakada wani amfani a gare ta .
‎
‎Noooooo.....
‎Baze ta'ba yiwuwa ba Rafi 'a bazata ta'ba gudu na ba Babu inda zataje tana d'auke da jariri na a cikin ta Ni nasan Rafi 'a fiye da yadda nasan tafin hannu na kuma nasan bazata ta'ba gujemin ba koda ina halin jinya .
‎
‎Muazzam ya qarasa maganar yana durqusawa a qasa tare da sakin wani irin kuka me sauti ,,
‎Yanajin zuciyarsa tana yimasa wani irin zafi kamar zata fashe A yanzu duk duniya babu abunda yake buqata sama da ya saka Rafi 'a a idanunsa .
‎
‎Kusa da shi umai ma ta matso ta durqusa ta riqe hannayensa '
‎Ka yarda da ni yaya na kasan bazanyimaka qarya ba Idan har Rafi 'a bata gujeka ba to yanzu ka nunamin ita tana ina?
‎
‎Kawai tayi amfani da kaine kuma yanzu amfaninka ya qare shiyasa ta za'bi tafiya ta rabu da kai .
‎
‎tana ina?
‎Muje mu nemota na bata haquri umai ma wallahi na tabbata Rafi 'a bazata ta'ba guduna haka kawai ba dole akwai dalili ,
‎
‎Dan Allah ki tayani mu nemota mu tambayeta idan wani lefin nayimata zan bata haquri "
‎Har qafar ta ma zan iya dafawa inde zatayi haquri ta dawo mu zauna Bazan iya jure rasata ba umai ma wallahi bazan iya ba  Zuciya ta zata fashe itace rayuwa ta Please umai ma dan girman Allah ki nemomin Rafi 'a zan bata haquri ta dawo muci gaba da rayuwar mu kamar da ,
‎Ki fad'a mata bazan iya jure rashinta ba ......
‎
‎Muazzam ya kai qarshen maganar yana rungume umai ma tanajin yadda kukan yake fita tun daga can qasan qirjinsa "
‎Fuskarsa tayi jazur abunka da farin mutum Gaba d'aya jijiyoyin kansa sun mimmiqe kansa ya d'au zafi kamar wuta' Jikinsa se wani irin kerma yake da alamar zazza'bi ne ya rufeshi ,,
‎
‎wani abu me d'aci umai ma ta had'iye dak'yar tayi qoqarin danne 'bacin ranta ta dedeta nitsuwar ta sannan tace '
‎
‎To zamuje mu nemota amma kabari ka samu sauqi tukunna kaga bakajin dad'i zazza'bi ya kama ka.
‎
‎A'a "
‎Ni lafiya ta qalau babu abunda ya sameni Kitashi mu tafi yanzu muje mu nemota .
‎
‎Gaba d'aya Muazzam a gigice yake baya cikin hayyacinsa ,,
‎Miqewa yayi da niyyar fara tafiya neman Rafi 'a se kuma ya yanke jiki ya fad'i ya suma '
‎
‎Rafi 'a kuwa d'akin ta aka kaita,
‎Alhj Hafiz da kansa ya qira likitan su ya dubata amma yace ba abunda yake damun ta "
‎Kusan qarfe hud'u na yamma ta farka,
‎
‎Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un.
‎Barrister........
‎Ina Barrister ? Ku fad'amin ina mijina yake nan a ina nake?
‎
‎Kwantar da hankalinki shahinas kidena wannan ihun ki nitsu kinji ,
‎Shahinas kuma Wacece shahinas ?
‎
‎Da mamaki suke kallonta gaba d'ayan su Humaira tace........
‎Idan ba shahinas ba menene sunanki toh ?
‎
‎Rafi 'a ,,
‎Ni sunana Rafi 'atu Dan Allah inane nan d'in ? Ina cikina ? Ina mijina yake ?
‎
‎Hajiya Maryam ta rungumeta tana fad'in  Ki kwantar da hankalinki yanzu ke ba me ciki bace uwace ke domin kin riga kin aihu .
‎
‎Na aihu ni Ina yaron ? Dan Allah ku banishi nagansa.....
‎
‎Humaira ce ta fita ba a jima ba ta dawo tare da Hisham da Naznin "
‎Rafi 'a ta rungumesu tana hawayen farin ciki ,
‎Sannan ta qurawa Hisham ido tanajin wani irin kewar Muazzam na damun ta .
‎
‎Muazzam kuwa dak'yar ya dawo hayyacinsa ,
‎Seda Dady yazo yace ze nemo masa Rafi 'a da kansa sannan ya nitsu '
‎
‎Bayan sati biyu........
‎Rafi 'a na zaune a bakin gado hajiya Maryam ta shigo ta same ta ,,
‎
‎Sannu da shigowa hajiya .
‎Yauwa sannu Rafi 'atu '
‎Angon nawa da kishiyar tawa bacci suke ne ?
‎Ta fad'a tana kallon inda Hisham da Naznin suke kwance sunata shaqar bacci ,
‎
‎Rafi 'a tayi mur mushi tace "
‎Eh wallahi sunyi bacci sun gaji ne shiyasa kika jisu shiru .
‎
‎Dariya hajiya Maryam tayi tace '
‎Gaskiya sena yimasa saki uku tundade ragon maza ne  shi Daga d'an yin wasa kad'an se bacci .
‎
‎Ai hajiya aurenku auren zobe ne babu rabuwa ke da shi mutu ka raba ,
‎A 'a ni rabani da wannan lusarin mijin bazan iyamasa ba .
‎
‎Dukkansu sukayi dariya sannan hajiya Maryam tace "
‎Rafi 'a tunda kinga yanzu kin samu lafiya Alhamdulillah jikinki yayi kyau Inaso ki bani labarin rayuwar ki da abunda ya baro da ke gidan ku kodan musan asalin ki kamar iyayenki mijinki da sauransu .
‎
‎Wasu hawaye masu d'umi ne suka cicciko a idanun Rafi 'a sannan tace cikin rawar murya '
‎
‎Ni shegiya ce banida iyaye tsinta ta akayi .
‎Subahanallahi.......
‎Wannan wani irin magana kikeyi haka ?Meyasa kike jifar kanki da irin wannan mummunan sunan ?
‎Haba Rafi 'a gaskiya banji dad'in kalaman ki ba .
‎
‎Wallahi hajiya da gaske nake ni y'ar tsintuwa ce ,
‎Bansan iyaye na ba ko kad'an domin ko sau d'aya ban ta'ba ganin su ba "
‎
‎Haka Rafi 'a ta kwashe labarin tun daga rayuwar ta a gidan Amo zuwa auramata Gaddafi da akayi har zuwa rayuwar ta a gidan Muazzam ,
‎Da yadda ta baro gidan Muazzam da tsohon ciki Ta qara da cewa "
‎
‎Baffa ya ta'ba fad'a min akwai abunda ze bani wanda ya tsinceni da shi wataqila hakan ze iya temakamin na gano iyaye na Amma be bani ba har nabar gidan .
‎
‎Hajiya Maryam tayi kuka sosai da jin labarin Rafi 'a kuma ta tausaya mata '
‎Sannan bugu da qari ta sake tabbatarwa zarginta a kan Rafi 'a ze iya zama gaskiya Domin ta jima tana saqa wani abu a ranta akan Rafi 'a Musammn idan taga yadda take kama sosai da Alhj Hafiz '
‎
‎Miqewa tayi ta fice daga d'akin tana share hawaye ,
‎
‎D'akin ta ta shige ta fad'a a kan gado ta fashe da kuka tana jin abunda ya faru da ita shekaru sha takwas da suka wuce yana dawomata sabo fil .
‎
‎SHEKARU ASHIRIN BAYA DA SUKA WUCE....
‎
‎Lokacin Alhj Hafiz yana matashi '
‎Ya kasance d'a ne a gurin wani babban me kud'i Alhj Atiku marafa......
‎
‎Sede duk da kasancewa d'an me kud'i hakan be kashemasa zuciyar sa ba '
‎Ya kasance matashi me k'wazo da son neman na kansa Ko da wasa baya sha awar yin kasuwanci da kud'in mahaifinsa ,
‎
‎Hakan ne yasa ya bud'e nasa kasuwancin a gefe guda '
‎Kafin kace me shima Allah ya d'aga shi kasancewar shi mutum ne da yasan yadda ze zauna da kowa kuma ya iya kasuwanci .
‎
‎Yana yawan tafiye tafiye"
‎Wataran yaje garin kaduna a can ya had'u da wata kyakkyawar budurwa me suna Maryam ,
‎
‎Abun kamar wasa har soyayya me qarfi ta qullu tsakaninsa da Maryam '
‎Kwatsam mahaifiyar sa hajiya Aisha ta bijiromasa da maganar auren y'ar qawarta hajiya Hauwa wato Habiba .
‎
‎Hafiz yayi iyakar qoqarinsa dan ganin ya fahimtar da hajiya Aisha mahaifiyar sa cewa yayiwa Maryam alqawari Amma taqi saurarar sa.......
‎
‎Tace Habiba itace matarsa kuma bata amince ya auri Maryam ba .
‎Daga d'ayan 'bangaren kuma hajiya Hauwa da y'ar ta Habiba sunanan suna shirya yadda zatazo ta haifi yara a gidan Hafiz idan ya mutu suci gado "
‎
‎Babu yadda Hafiz ya iya haka ya amince ya auri Habiba badan yana sonta ba,
‎Domin shi mutum ne me bin umarnin iyayensa '
‎
‎Ba a jima da yin auren ba Allah ya kar'bi rayuwar hajiya Aisha mahaifiyar Hafiz .
‎Shekarar Habiba guda a gidan Hafiz ya auro Maryam ,,
‎
‎Babu irin makirci da kirsa da Habiba batayiba dan ganin ta raba tsakanin Hafiz da Maryam amma abun ya faskara '
‎Maryam tana zuwa batafi watanni biyu ba a gidan ta samu ciki sa'banin Habiba da ko 'batan wata bata ta'ba yi ba .
‎
‎Wannan cikin yayi matiqar tsolewa Habiba da hajiya Hauwa mahaifiyarta ido ,
‎Damuwar su kawai taya zasu kawar da wannan cikin "
‎
‎Magunguna iri iri babu wanda Habiba bata sakawa Maryam ba domin cikin ya zube amma yaqi ,
‎
‎Hafiz kuwa ya mayar da hankalinsa akan kula da Maryam domin tun yana d'an qarami Allah ya jarabceshi da son aihuwa ,,
‎
‎Yayi mugun k'wallafa rai akan cikin hatta bacci me kyau baya iyawa ,
‎Da zarar Maryam ta motsa ze tashi yana tambayar me takeso ko kuma me ya faru ?
‎
‎Duk inda ya fita yaga kayan yara seya sayo ya kawo yace a ajiye dan a sakawa babynsu idan yazo duniya .
‎
‎Tun Maryam tanayimasa fad'a har ta gaji ta dena domin ta fahimci ba denawa zeyi ba ,,
‎Musamman ya sayo wani bargo me kyau da tsada had'e da wasu kayan sanyi masu kyau sosai da tsada yace su za a fara sakawa yarinyar idan an haifeta Domin likitoti sun riga sun tabbatar masa da cewar mace zasu haifa  .
‎
‎Musamman yasa aka qeramasa wasu qananan y'an kunne da zobe na gold da diamond sabota jaririyar "
‎A taqaice de ya d'auki duk wata soyayyar sa ya d'aurawa yarinyar tun kafin tazo duniya wanda hakan ba qaramin quntata wa Habiba da mahaifiyar ta yake ba.
‎
‎Ranar laraba da yamma Maryam ta haifo kyakkyawar yarinya me matiqar kama da Hafiz kamar an tsaga kara '
‎Murna da farin ciki kam a gurin Hafiz ba a cewa komai Domin seda ya biyawa mutum hamsin aikin hajji ,
‎
‎Gidaje kuwa ya sayawa mutum sama da d'ari "
‎Kaf  y'an aikin gidan sa se da ya bisu da kyautar dubu d'ari biyar biyar A cewarsa ta hakan yakeso ya bayyanawa Allah godiyar sa ,,
‎
‎Hatta a asibitin da Maryam ta aihu a ranar se da ya biyawa kowa kud'in aihuwa inde a ranar ta aihu a cikin asibitin .
‎
‎Se d'oki yake yana rawar kai wai a dole shima ya zama uba "
‎Sede abunda be sani ba tun suna asibitin Habiba ta had'a baki da habu me gadin gidan akan cewar zasu sace yarinyar cikin dare su kashe ta .
‎
‎Haka kuwa akayi....,..
‎Da dare kusan qarfe biyu da rabi Habiba ta shigo ta d'auke yarinyar tare da bargo da kayan sanyi da kuma y'an kunne da zoben "
‎Ta kaiwa habu me gadi ita sannan ta miqamasa ledar kayan tace yasan yadda zeyi da kayan ,
‎
‎Sannan ta d'au kud'i nera million biyar a jaka ta miqa masa shine kud'in sallamar aikinsa "
‎
‎Da asubah Maryam ta tashi dan ta shayar da jaririyar ta amma lalubawan da zatayi se taji babu ita ,
‎Abu kamar wasa wankin hula yana nema ya kaita dare domin kamar almara take kallon abun Taya zasu kwanta tare da jaririya da dare amma ace an wayi gari babu ita ,,
‎
‎Tsabar tashin hankalin 'batan jaririyar da Hafiz yanki jiki ya suma seda yayi wata guda besan inda yake ba ,
‎Koda ya dawo hayyacinsa haka ze saka kayan jaririyar a gaba yayita kuka kamar qaramin yaro '
‎
‎Duk da Maryam uwa ce Kuma tanajin ciwon 'batan jaririyar ta amma harga Allah tasan duk yadda take son yarinyar batakai Hafiz ba. ,
‎Domin ya mayar da yarinyar komai a rayuwar sa tun kafin tazo duniya"
‎
‎Hakan ne yasa Maryam take matiqar tausayawa Hafiz .
‎Sede tunda yarinyar ta 'bata ko da wasa Habiba batayimusu koda sannu ba duk dayake dama ba kula Maryam take ba '
‎
‎Wata biyar da 'batan yarinyar Hafiz yayi hatsari kuma likitoti suka tabbatar masa da cewa Kwayoyin aihuwarsa sun lalace saboda haka baze sake samun aihuwa ba har abada .
‎

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol