Free chapter · Read without an account
Chapter 21
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA.......
Duk da irin tsufa da ramar da yayi hakan be haka hajiya Maryam da Alhj Hafiz ganeshiba ba '
Habu me gadi........
Suka kira sunan a tare sede duk sunyi mamakinta ganinsa babu qafa d'aya ,,
Kuka kawai habu me gadi ya farayi yana fad'in '
Tabbas na cutar da ku naci amanar ku nayimuku abunda ban can canci ku yafemin ba Amma dan Allah ku yafemin ba dan hali na ba kodan lahira ta tayi kyau "
Rayuwa ta kam ta gama lalacewa tun ranar da na za'bi son zuciya ta sama da tsoron Allah na ,
Ina roqon dan Allah ku temaka ku yafemin sannan kuma ku Yanke min duk wani hukunci da kukaga ya dace da ni .
Se da suka fara basa guri ya zauna sannan Alhj Hafiz yace "
Akan me kake neman yafiyar mu ?Sannan kuma wani lefi mukayimaka da muka nemeka lokaci guda muka rasa ka ?
Gir giza kai habu yayi yana share hawaye kafin yace ,
Jaririyar ku da aka d'auke a wancan ranar ba kowa bane ya d'auke ta nine .
What...... ?
Alhj Hafiz ya fad'a tare da miqewa tsaye cike da mamaki '
Qarya yakeyi Alhj......
Baida hankali kada ka yarda da maganar sa ko ranan na gansa a gidan mahaukata ba mamaki ma wataqila gudowa yayi yazo zeyimana hauka a nan .
Cewar hajiya Habiba da keta faman yarfe gumi "
Kallon ta habu me gadi yayi ya kad'a kai yace ,
Dole zaki fad'i haka tunda kinga asirin da kikayita qoqarin 'boyewa a cikin shekaru sha takwas yana neman tonuwa '
Nayi mamaki da har yanzu baki gane kus kuren ki kikaji tsoron Allah kika canza halinki ba .
Au haukar taka kuma yau kaina ta dawo?
Ni zakayiwa sharri yau habu ?
Ba maganar sharri bace gaskiyar da kiketa qoqarin dannewa ne tafi qarfin ki takeso ta fito ta nuna kanta Domin sanin kanki ne komai daren dad'ewa qarya bata danne gaskiya komai jimawa se gaskiya tayi halin ta ,,
Qarya kakeyi habu.......
Wai taya ma haka ta faru ne ?
Dole ki tambaya taya akayi hakan ta faru domin bakiyi zaton matacce ze taso yazo bada hujja akan abunda kika aikata bayan shekaru ba '
Nasan kina mamakin taya akayi na kasance har yanzu a raye bayan kin shirya maqar qashiyar da za a halakani dan gudun kada nazo na tona miki asiri watarana "
Se gashi kuma Allah ya bani tsawon rayuwa domin nazo na gyara kus kuren da zuciya ta ta jani na biyemiki muka aikata .
A'a habu.......
Kada ka sake ka fad'a domin idan ka fad'a ba ni kad'ai bace kaima seka fiskanci hukunci ,,
Kallon ta habu yayi yana mur mushi Sannan yace '
Tunda har na iya tako qafata nazo domin na fad'i gaskiya akan abunda muka aikata ya kamata kisan banajin tsoron ko wani irin hukunci ne ze biyo baya ,
Zefimin ace na kar'bi hukunci na tun daga nan domin inajin tsoron zuwa gaban Allah da wannan hakkin '
A yanzu babu wani abu da yake bani tsoro sama da had'uwa ta da Allah .
Qarya yakeyi ba gaskiya bane "
Alhj kada ka yarda da maganar sa wallahi mahaukaci ne baida hankali Dan Allah ka koreshi kada yayimana hauka a wajen nan .
Kiyimana shiru Habiba....
Alhj Hafiz ya fad'a a kufule yanajin kamar ya rufe Habiba da duka Domin dama ya jima yana zarginta amma ya rabu da ita dan babu yadda zeyi saboda baida hujja '
Babu wani hauka malama kawai abar bawan Allah ya fad'i abunda ke ransa .
Hajiya Maryam ta fad'a tana 'ballawa hajiya Habiba harara '
Wallahi qarya.......
Kiyimana shiru kada na sakejin bakinki a nan .
Alhj Hafiz ya fad'a cikin tsawa "
Haka hajiya Habiba tayi shiru tanajin kamar zata saki fitsari a jikinta saboda tsoro ,
Malam habu ina sauraronka ka fad'amin duk wani abu da kasan kun aikata kai da Habiba a baya.
Cikin kuka habu ya fara bawa hajiya Maryam da Alhj Hafiz labarin yadda komai ya faru ,,
A ranar da aka kai Maryam asibiti domin ta aihu hankalin Habiba yakai qololuwa wajen tashi '
Ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda haka tazo har bakin gate ta samu habu me gadi tace yazo tanaso tayi magana da shi ,
A nan ta sanar masa tanaso idan Maryam ta aihu suna dawo gida zata san yadda zatayi ta sato yarinyar cikin dare se ta kawomasa ita ya tafi waje me nisa ya kasheta ya jefa gawarta a cikin ruwa .
Da fari yaso yaqi amincewa amma Habiba tayimasa barazanar idan beyi abunda take so ba '.
Zatayimasa sharrin da se an koresa daga aiki kuma se tasa an rufeshi Idan kuma ya aikata tayimasa alqawarin nera million biyar.......
Abunka da zuciya batada qashi "
Se habu yaji gara ya kar'bi kud'in ko babu komai ze gyara rayuwarsa da su Saboda haka yace mata ya amince........
Haka kuwa akayi ,,
Qarfe biyu na dare ta fito da yarinyar ta basa ta had'a masa da kud'in sannan ta qara jaddada masa cewar ya tabbatar ya kasheta ya jefa gawar ta a ruwa .
Habu na fita Habiba tayi tunanin habu ze iya zama mata matsala idan ta barshi ,,
Saboda haka ta d'au wayar ta ta shiga contac ta lalubo wata number wacce aka rubuta d'an mutuwa a jiki ta kira ,
Bugu biyu aka d'aga wayar.....
Hello hajjaju kwana biyu kin watsar da mu tunda kika nemeni nasan akwai magana me kikeso ayi yanzu ?
Kanaji d'an mutuwa......
Aiki ne da na jima ban sakuba zan baku a yau "
Kice yau lahira zatayi baqo wani me tsau tsayin ne ya shigo layin ki ?
Habu ne me gadin gidan mu nabasa wani aiki Naga kamar hankalin sa be kwanta da aikin ba banaso daga baya a samu matsala shine nakeso a gama min da shi .
Ok to ba damuwa hajiya gamawa ne yanzu zamu cika aiki kawai ki aikomin da hoton sa yanzu '
Habu kuwa yayi nisa da anguwar sosai ya je anguwar abganistan da jaririyar ,,
Sede zuciyar sa taqi amincewa da kashe yarinyar saboda haka ya tsaya yana tunani ,
Seda ya kusa mintuna biyar a tsaye sannan a fili ya furta '
Banida rashin tausayin da zan iya kashe jaririyar da batajiba bata ganiba batasan komai ba .
Da sauri ya nufi qar qashin gada ya ajiye jaririyar da ledan kayan ta "
Astagfirullah Allah.......
Ya fad'a yana hawaye sannan ya kama hanya yana tafe yana waigowa yana kallon jaririyar cike da tausayi ,
Yana tafe yana sharar kwalla kamar daga sama yaga wasu mutane uku sanye da baqaqen kaya fuskokinsu d'aure da baqin kyalle "
Kamar binsa sukeyi a baya saboda haka ya qara sauri ,
Sede ya kula suma qara sauri suke aiko bewi wata wata ba ya kece da gudu Suka rufamasa baya da gudu.......
Sosai yake gudu yana shiga cikin daji suna binsa iyakar qarfinsu ,,
Ganin yana nema ya basu wahala ne suka harbi qafarsa na dama ya fad'i .
Dama da yake ya riga ya gama galabaita hakan yasa yana fad'uwa ya suma baya numfashi '
Ganin hakan ne yasa sukayi tunanin ya mutu ne suka juya suka barshi a gurin cikin jini ,,
Washe gari da safe wasu Makiyaya sunzo wucewa suka tarar da shi '
Suka qaraso cikin gari dashi Kai tsaye suka wuce da shi specialist general hospital Gombe ,,
Duk wani temako da ya kamata likitotin sunyi qoqarin basa amma sede qafarsa ta riga ta lalace saboda haka aka yanke ta '
Bayan ya fara samun sauqi makiyayan sukace sukam zasu tafi dama wucewane ya kawosu suka tarar da shi suka temakesa "
Amma tunda ya samu sauqi zasu wuce ya nemi danginsa su qarasa jinyar sa .
Haka suka tafi suka barsa daga baya da likitoti suka gaji da zamansa suka koreshi daga asibitin '
Domin baida kowa a qasar nan dama asalinsa d'an Cameron ne ,,
Neman kud'i ne ya kawoshi Nigeria Baida inda zeje saboda haka ya fara bara '
Idan dare tayi se ya samu bakin titi ya kwanta .
A haka yake rayuwar sa komai tsananin ruwa da iska kuma komai sanyi baida gurin da ze shiga ya kwana "
Shiru parlorn ya d'auka na d'an lokaci babu wanda yace komai kafin Alhj Hafiz yace ,
Babu shakka biri yayi kama da mutum Dama na jima ina zargin Habiba ban ta'ba fad'a ba domin banida hujja Amma tabbas a yau zaki girbi abunda kika shuka .
A'a Alhj......
Sam kada ka yarda da maganar sa wallahi qarya yakeyimin kawai dan ya shiga tsakani na da kai '
Kuma nasan wannan duk sharrin Maryam ne dama batasona da kai amma wallahi Alhj "
Kimana shiru......
Muguwa munafuka azzaluma makira qanwar mutuwa me raba uwa da d'an ta ,
Wallahi Allah ya isa tsakanina da ke bazan ta'ba yafemiki ba azzaluma kawai .
Yarinya da gatan ta amma kin maida ita abun tausayi Babu abunda mahaifinta ya rasa a duniya amma kinsa ta tashi rayuwar almajirai tana bata sha awa '
Baqar macijiya kawai Allah ya isa tsakanina da ke baqar ashana qona gari ,
Allah ya toni asirinki wallahi sekin girbi abunda kika shuka kuma in Allah ya yarda bazaki gama da duniya lafiya ba .
Hajiya Maryam ta fad'a cikin kuka "
Da gudu hajiya Habiba ta tashi zata fita daga parlorn Ajimal ya samata qafa ta fad'i ,
A sukwane hajiya Maryam tayi kanta ta rufeta da duka Alhj Hafiz yana kallo beyi yunqurin hanata ba domin yadda yakeji a yanzu kome yaga za ayiwa Habiba baze ta'ba nemar mata sassauci ba ,,
Madadin yayi qoqarin kar'bar Habiba sema qoqarin kiran y'an sanda yayi sukazo suka tafi da ita .
Bayan sun wuce da ita Rafi 'a ta kalli habu me gadi tace "
Baba ka sanni ?
Sosai ya qare mata kallo yaga kamar ya ta'ba ganin fuskar amma ya kasa tina a inane hakan ne yasa kawai yace da ita ,
A'a......
Zaka iya tina wata yarinya wacce tazo tana bara da tsohon ciki har ka temaketa ka bata breadi ?
Shiru ya d'anyi yana tunani Rafi 'a taci gaba da magana '
Wacce har ka fara bata wani labari akan wani hamshaqin me kud'i amma baka samu qarasa mata ba.
Ohh Allah sarki na ganeki yanzu me kikeyi a nan ?
Wannar jaririyar da ka d'auka domin ka kashe amma ka kasa saboda tausayi tabbas nice "
Alhamdulillah Allah na gode maka da kasa yarinyar bata mutu ba ,
Dan Allah ki temaka ki yafemin yarinya tabbas na aikata kus kure na biyewa son zuciya ta na lalata miki rayu '
Babu komai baba kuma ni ko kad'an baka lalatamin rayuwa ba Hasali ma a yau ina raye ne saboda kai '
Domin inda baka d'auko ni a wancan daren ba da tabbas zata iya neman wasu marasa imanin su aiwatar mata da qudurin ta a kaina .
Ajiyar zuciya Alhj Hafiz yayi sannan yace ,
Gaskiya ne saboda abunda kayi na tausayawa jaririya mun yafe maka abunda ka aikata Sannan Kuma ka duba duk gidan da yayimaka a ko ina a duniya zamu saya maka Kuma zan had'a maka da jari dan kaima ka dogara da kanka .
A nan Habu me gadi ya fashe da kuka yana tayiwa Alhj Hafiz godiya ,,
Muazzam kuwa jiki yayi sauqi babu lefi harya fara fita aiki '
Sede ko da yaushe a cikin neman Rafi 'a yake kullum yana cikin qunci da damuwa domin yanzu ko dariya baya yi ,,
Suna zaune a parlor suna hira Rafi 'a ta kalli Ajimal tace '
Yaya Ajimal.......
Naji baffa yace nan da sati biyu za a kaika kotu saboda ka yankewa wani yaro hannu Me yasa kayi haka ?
Nema yayi ya gwada kwanji da ni shiyasa na nuna masa sama tayiwa yaro nisa ,,
Gara da ka nuna masa ai yanzu wa gari ya waya ?
Idan kayi wasa seka kusa qare rayuwar ka a gidan yari to ina amfanin wannan dan Allah ?
Yanzu da ka aikata haka kanada abunda zaka fad'a idan an shiga kotu ne ?
Baza a shiga kotun ba zanyi magana da lawyer na wanda case d'in Habiba yake hannunsa Zamu d'auki nauyin karatun yaron a duk qasar da yakeso kuma zamuci gaba da d'aukar d'awainiyar mahaifiyar sa ,
Saboda haka anjima idan lawyer na yazo zamu tattauna batun inyaso se a samu matar domin a samu mafita "
Cewar Alhj Hafiz da shigowar sa kenan yaji suna maganar .
Yauwa Abba dan Allah ka temaka a kashe case d'in nan kada yaje kotu '
Wallahi banaso a rufe yaya Ajimal zamu kaishi gidan warkar da y'an shaye shaye kuma nasan ze dawo cikin nitsuwar sa .
kusan qarfe hud'u na yamma Alhj Hafiz ya gama magana da lawyer d'in sa yayimasa sallama ze tafi ,
Yana shirin fita Rafi 'a kuwa tana shirin shigowa cikin parlorn a tare sukaja wani dogon burki suka tsaya '
Zuciyoyinsu suka shiga bada wani irin sauti a tare......
Gaba d'aya jikinsu ya d'au rawa idanuwan su suka shiga kawo ruwa ,,
Barrister........
Rafi 'a ta fad'a cikin rawar murya tare da fad'awa jikinsa ta fashe da kuka ,
Muazzam ya qan qame ta yana fad'in.....
Rafi 'a ta ina kika tafi kika barni ?
Me yasa kika rabu da ni inata shan wahala why Rafi 'a ? .