Free chapter · Read without an account

Chapter 22

by Fatima Usman Abdullahi · UQUBA

‎BY
‎
‎FATIMA USMAN 
‎SHA LELEN TERAWA ........
‎
‎
‎
‎Jikinsa kawai Rafi 'a ta qara shigewa tana kuka tana fad'in' 
‎Barrister nayi kewarka sosai bazan iya jure yin nisa da kai ba Dan Allah kada ka sakeyin nisa da ni .
‎
‎Rafi 'a ina cikin jikin ki ?
‎Kizo mu tafi gidan mu da babu ke gidan yayi duhu sannan kuma yayi qunci da waya Saboda rashinki shiru ya maye gurbin komai a tare da ni ,,
‎
‎Suna tsaka da magana Hisham da Naznin suka shigo da gudu sunata gwaranci irin na yara '
‎
‎Barrister wad'annan sune yaran mu yaran da na haifamaka wad'an da baku ta'ba gainin juna kai da su ba.
‎
‎Sarai Muazzam ya gane yaran yana ganinsu ya cika da farin ciki "
‎Alhamdulillah Rafi 'a ta kece kika bani wannan kyautar......
‎
‎Yayi maganar yana rungume ta had'i da fashewa da kunkan farin ciki .
‎
‎Rafi 'a tacewa su Hisham suzo ga Abbansu' 
‎Da gudu yaran sukazo suka rungume shi sunata murna '
‎
‎A nan Rafi 'a ta bawa Muazzam labarin komai game da kasancewarta yar Alhj Hafiz ,,
‎Yayi farin cikin gano asalinta sosai yaso su koma gida amma Alhj Hafiz da hajiya Maryam sukaqi yarda sukace ya bari se nan da sati d'aya '
‎
‎Haka ya tafi ba dan ransa yaso ba domin gani yake kamar yana tafiya zata sake 'bata.
‎Tunda ya koma gida umai ma ta kula yana cikin farin ciki ko kad'an bataga damuwar da ya sabayi akan fuskar sa ba ,
‎
‎Ko da yaushe yana tare da Rafi 'a a waya........
‎Ga yawan zuwa a rana guda se yaje sama da sau goma Gashi bayajin kunyar bata kulawa a gaban kowa ,
‎
‎A rana ta uku da dare Muazzam yazo suna zaune a parlor tare da Rafi 'a da su Hisham '
‎Alhj Hafiz ya shigo yace......
‎
‎Muazzam d'auki matarka ku tafi bazan iya wannar masifar ba,,
‎Muazzam yana d'an sosa kai yace '
‎
‎Abba naji kunce ai se nan da sati d'aya zata koma shine nace ai babu komai sati d'ayan ma kamar yau ne. .
‎Karka damu d'auke ta kuje kawai ai matar kace ya kamata ta kasance tare da kai koda yaushe "
‎
‎Rafi 'a kam kunya ce ta hanata cewa komai dan ita kanta tasan zuwan Muazzam yayi yawa dole zasu gaji ,
‎
‎Haka suka tattara kayansu a daren suka koma....
‎umai ma ta d'anji hayaniya sama sama amma bata fito ba se da safe "
‎
‎Tana fitowa taga abunda ya kusan tarwatsa kwa kwal wa da zuciyar ta ,
‎Rafi 'a kuma wai harda yara biyu wad'an da ko baka tambaya ba kallo d'aya zakayimusu kasan jinin Muazzam ne su. 
‎
‎Yaya Muazzam..,...
‎Sunansa kawai umai ma take Nanatawa cikin firgici da tashin hankali '
‎
‎Muazzam kam yana cikin farin ciki sosai shiyasa kobi ta kanta beyiba ,,
‎Dak'yar umai ma ta ja jiki ta koma d'aki tanajin kanta na Sara mata Ga wani mugun zazza'bi ya rufeta lokaci guda .
‎
‎Dak'yar ta d'auko wayar ta ta kira layin Momi "
‎Hello Momi.......
‎umai ma lafiya kuwa naji muryar ki a haka ?
‎
‎Inafa lafiya Momi ?
‎Wallahi ba lafiya wannar tsinanniyar mayyar yarinyar ce ta dawo ashe tana raye kuma ta haifi cikin har yara biyu .
‎
‎Wani irin miqewa Momi tayi tana mul mulo ashar ,,
‎Wallahi bazata sa'buba wankan kuturu da sabulu......
‎
‎Mu munanan bonono wai an rufe qofa da 'barawo muna jira mu kasheshi mu d'ebi dukiya ashe wannar tsinanniyar tananan tana rusamana shiri ta qar qashin qasa  ,,
‎To wallahi baze yiwuba kawai kizo mu koma gurin boka asan yadda za ayi '
‎
‎Ya kashemana su gabaki da'ya har da shi Muazzam d'in .
‎Wallahi Momi banajin dad'i bazan iya zuwa ba amma ke kije ki tabbata anyi aikin da babu wanda ze tsira a cikin su har shi yaya Muazzam d'in kawai a kashe shi Amma de nafiso a fara da wad'annan tsinannun twins d'in da uwar su ,
‎
‎Duk da nasa an 'batar mata da hankali an koreta daga gidan kuma na saka yaya Muazzam ya manta da ita seda tasan yadda tayi ta dawo ya tina da ita '
‎
‎Kede kada ki damu umai ma semun kawo qarshen komai a yau bari na koma gurin bokan .
‎
‎To shikenan Momi a dawo da labari me dad'i ,,
‎Ta fad'a sannan ta kashe wayarta ta miqe.....
‎
‎Jin motsin ta ne yasa Muazzam da tunda ta fara wayar ya taho da niyyar fad'a mata yadda akayi ya samo Rafi 'a da kuma asalin Rafi 'a yaji tana wayar ya dakata '
‎
‎Yayi saurin sakin handle d'in qofar ya juya ya nufi d'akin sa da sauri .
‎Jikin window ya kama wasu zafafan hawaye suna sulalowa daga idanun sa '
‎
‎Dama ashe duk wahalar da Rafi 'a ta sha a cikin gidan nan sanadiyyar umai ma ne ....
‎
‎Why umai ma me yasa kika aikata haka ?
‎Dama nasan kinada kishi sosai amma ban ta'ba tunanin rashin imaninki haryakai ki barranta da Allah saboda kishi ba .
‎
‎Tunanin irin hukuncin da ya kamata yayimata yakeyi amma kwa kwal warsa ta kasa tunano masa komai ,,.
‎
‎Hakan ne yasa ya shige toilet ya sakarma kansa ruwa '
‎Yakai kusan 30 minutes kafin ya fito daga toilet d'in ,,
‎
‎Rafi 'a ya tarar duk ta wargaza d'akin ta 'balle kan gado tana shirin d'age katifa "
‎Menene kikeyi kaha Rafi 'a ?
‎
‎Yayi tambayar yana janyota jikinsa....
‎Barrister d'akin ne gaba d'aya yayi qura da alama ka Jima baka canza fasalinsa ba shiyasa zan gyara maka ,
‎
‎Sosai ya qara maqaleta a jikin sa yana mur mushi "
‎I miss you so much Rafi 'a ta nayi kewarki sosai wallahi.......
‎
‎Mur mushi kawai tayi tace ,
‎Zan iya tafiya naqarasa aikin da na fara ?Seda ya d'an qura mata ido sannan yace yana mur mushi ,,
‎
‎Kiss me.......
‎Barrister zaka fara koh ni rabu da ni na qarasa aiki na yara na suna jira na .
‎Ta fad'a tana tureshi tare da kai hannu da niyyar d'age katifa se ta hango wata y'ar tukunya nannad'e da baqin kyalle "
‎
‎Da sauri ta kai hannu ta d'auko jikinta na rawa ,.
‎Menene wannan Barrister ?
‎
‎Tukunyar yake kallo cikin mamaki sannan yace kawo mu gani  '.
‎Ya kai hannu ze kar'ba tukunyar ta su'buce ta fad'i a hannun Rafi 'a tayi kaca kaca ,,
‎
‎Wani baqin hayaqi ne ya turnuqe d'akin a hankali ya 'bace suna kallo ,
‎Muazzam ya kalli inda tukunyar take sannan ya duqa ya d'auko takardar da ya gani a nannad'e ya bud'e ta "
‎
‎Sunansa da sunan umai ma ya gani ga wasu kalan rubutu da ya kasa gane kansu ,
‎Ga zuciyar zakara nannad'e a cikin takardar wanda aka d'ad'd'aure da wani baqin zare .
‎
‎Gashi an soke tsakiyar zuciyar da wata y'ar qaramar kifiya "
‎Duk da kana gani kasan ta jima a haka amma har a lokacin zubar da jini take ,
‎
‎Wannan aikin umai ma ne.......
‎Ya fad'a yana sake bin kayayyakin da kallon mamaki ,,
‎
‎Haba Barrister meyasa kake zarginta da wannan abun kanada hujjar fad'anr cewa ta aiketa ?
‎Ya wuce hujja tunda da bakinta naji tana fad'a .
‎
‎Rafi 'a tayi matiqar mamaki da Muazzam ya bata labarin wayar da yaji umai ma da Momi sunayi '
‎
‎umai ma kuwa tana kwance a d'aki tana jiran abunda boka ze basu Momi ta kira wayar ta ,
‎
‎Da sauri ta d'aga ta kara wayar a kunnen ta......
‎Hello Momi ya akayi me bokan yace ?
‎
‎Gaskiya ba a daceba umai ma domin yanzu haka ina gidan bokan amma nasamu jiya da dare ya mutu "
‎
‎Ya mutu fa kikace Momi........
‎Shikenan na shiga uku tawa ta qare na gama yawo .
‎
‎Se kuma ta kece da dariya tana sosa kanta ,,
‎Ya mutu ya mutu shikenan boka obina ya mutu Rafi 'a ma zata mutu '
‎
‎Yaya Muazzam ma seya mutu nida Momi da Daddy ne kawai zamu zauna mu cinye kud'in yaya Muazzam duka yeeee,
‎
‎Haka tayita surutu tana yagar jikinta tana dariya tana had'awa da kuka "
‎
‎Muazzam da Rafi 'a suna d'aki suna hirar yadda Shari ar Ajimal zata kasance ,
‎Tana fad'a masa da zazar an kammala maganar zasu kaishi gidan warkar da y'an shaye shaye .
‎
‎Kamar daga sama suka jiyo dariyar umai ma da surutun ta ,
‎A tare suka fito domin su duba me yake faruwa '
‎
‎umai ma suka tarar zaune a tsakiyar parlor gaba d'aya tayi kaca kaca da komai na cikin parlorn Se dariya take tana kuka tanata surutai......
‎
‎Gashi se yagar jikinta take gaba d'aya tajijjiwa kanta ciwo .
‎
‎Gabanta Muazzam yazo ya tsugunna yana kallonta ,,
‎Zokaji na fad'a maka yaya Muazzam wallahi yau zaku mutu dukkanku '
‎
‎Hehehe.......
‎Kuma kaima harda kai tunda de yaya yazid ya mutu lokacin da yaje kasheka kaima semun kasheka "
‎
‎Ha ha ha.....
‎Ka tina lokacin da ni da Momi mukaje gurin boka yabani magani na saka a lemo Rafi 'a Tasha ,
‎Ai dama da jini nace a had'amin ita kuma wallahi yanzuma senace amata haka.
‎
‎Yanzu umai ma qiyayyar da kikeyimin hartakai haka ?
‎Haba dan Allah me na tare miki haka da zakimin wannan d'anyen aikin ?
‎Banyi tunanin ko mahaifanki na kashe zaki hukuntani ta wannar hanyar ba .
‎
‎Eh na tsaneki kuma bana sonki dama ai seda nacemiki gidana ni kad'ai ce amma kika kama kika shigo saboda maita da naci '
‎
‎Yanzu gashi ai na haukataki a banza kuma boka yace bazaki warke ba ,
‎Wai harda wani samun ciki bayan ni ance bazan aihu ba wato ke zaki aihu ki mallaki dukiyar yaya Muazzam koh ,,
‎
‎To wallahi baki isaba shiyasa nace a haukataki kuma gashi yaya Muazzam ya manta da ke se naga ta ina zakici gadon '
‎
‎Kuma wallahi Momi ma ta tafi kufto wajen boka obina tace duka zatasa a kasheku ni da ita da Daddy ne kawai zamu kwashe kud'in su zama namu....
‎
‎Yessss........
‎Sedamu wallahi ai munsan kan tsiya Momi tana dawowa zata kawomin magani nasakamuku kuci ku mutu dukkanku ,
‎
‎Ahayye se damu wallahi mun riga munci dubu se ceto .
‎
‎Cikin fushi Muazzam ya damqo hannun umai ma ya jata ya wurgata a cikin d'akinta ta yasa makullin ya rufeta ta baya "
‎
‎Yanaji tanata ife ife tana buge buge ko saurarar ta beyi ba ,
‎A yau ta fito fili ta bayyana qarara a cikin maqiyansa yake rayuwa be sani ba '
‎
‎Da gaske a matsayin iyaye yake d'aukar Momi da Daddy amma a yau yaji matiqar kunyar rayuwa tare da su da ya gane ainihin gaskiyar dake 'boye a qar qashin zukatansu .
‎
‎Momi kuwa a hanyar ta ta dawowa taci karo da wasu bororin daji irin marassa imanin nan ,
‎Suka tareta ba lefin zaune ba na tsaye haka sukayita sarar ta a cikin daji Tun tana iya ihu har ta dena iya motsi' 
‎
‎Seda sukayi gutsi gutsi da naman ta sukeyimasa yankan naman miya sannan suka watsama karnukansu naman ta .
‎
‎Bayan kwana uku da mutuwar Momi abun umai ma se qara gaba yake ,
‎Da kanta take tsigar gashin kanta jini na zuba '
‎
‎Babu ci babu sha se surutai da dariya gashi duk kayan da aka sakamata seta yaga ta zauna tsirara aihuwar uwar ta ,,
‎
‎Ta gama yiwa jikinta rauni kota ina ga wani tsinkakken jini baqi qirin me wari da yauqi da yake fita daga gaban ta ,
‎
‎Muazzam na zaune Rafi 'a ta shigo ta sameshi jikinta babu kwari "
‎Yanzu Barrister haka zamu zuba mata ido muyita kallonta ?
‎
‎To ya kikeso nayimata Rafi 'a ?
‎Munje asibiti sun koremu sunce jinyar bata asibiti bace domin sunga babu abunda yake damunta ,
‎
‎To tunda haka ta za'barma kanta se tayita rayuwa a haka ai bani na aiketa taje ta gina ramin qeta ba Saboda haka koma me ya biyo baya ni ba ruwa na  ,
‎
‎Idan ubanta ya gaji da ganinta a haka se yazo ya d'auke ta yaje ya nema mata magani Tunda tare suke abun ai yafimu sanin inda ze samu makarinsa .
‎
‎Amma dan Allah koda masu maganin........
‎Kiyimin shiru Rafi 'a kada ki sake cemin komai inde akan umai ma ne dan wallahi nera biyar d'ita bazata sakeyin ciwon kai akan cutar da ba asan maganinta ba ,
‎
‎Tunda ita ta d'auko kayanta seta qarata da shi dama ai duk tsun tsun da ya kira ruwa a qarshe shi ruwan yake duka .
‎Yana gama fad'ar haka ya miqe ya fice daga d'akin "
‎
‎Daddy yana tuqi duk abun duniya ya ishe shi ya rasa me yake masa dad'i a rayuwar sa ,
‎Tuqi yake amma ko kad'an hankalinsa baya kan tuqin '
‎
‎Beyi aune ba wata qatuwar mota tabi kansa ko bur bud'in sa babu wanda ya gani saboda yadda ya markad'e a cikin motar .
‎
‎Bayan watanni shida Ajimal ya dawo daga gidan warkar da y'an shaye shaye ,
‎Gaba d'aya ya canza kamalarsa ta da ta dawo......
‎
‎Ya zama kamilin mutum nitsattse haskensa ya qara fitowa sosai kyansa ya qara bayyana "
‎Rafi 'a tayi murnar sake ganin yayan nata a haka '
‎
‎Duk da lokacin cikinta ya tsufa hakan be hana ta kunna kid'a ta taka rawa sosai ba ,,
‎Har seda Hisham da Naznin suka taya ta......
‎
‎Rafi 'a ta kula tunda ya shigo gidan babu abunda yakeyi se bin Humaira da kallo '
‎Kyautar company guda Abba ya basa saboda farin cikin shiryuwar sa .
‎
‎Rafi 'a kuwa ta mallakamasa gida wanda kud'in sa yakai nera million d'ari biyar da hamsin ,,
‎
‎Hajiya Maryam kuwa ta basa kyautar nera million d'ari bakwai sannan tace ya za'bi qasar da yakeso yaje yayi karatu .
‎
‎Shi kansa Muazzam seda ya bashi kyautar motar million biyar "
‎
‎Banda kuka babu abunda Ajimal yakeyi.....
‎Domin koda a mafarki be ta'ba tunanin rayuwarsa zata inganta kamar haka kuma ta dalilin Rafi 'a ba .
‎
‎Bayan kwanaki Rafi 'a da kanta ta samu Humaira ta tambayeta ra ayin ta akan Ajimal kuma ta tabbatar mata da tana sonshi "
‎
‎Babu 'bata lokaci aka saka ranar biki nan da wata d'aya .
‎Rafi 'a da Muazzam babu irin gayyatar da basuyiba Saboda farin cikin yayanta d'aya tilo zeyi aure,
‎
‎Ranade bata qarya an d'aura auren Ajimal da Humaira '
‎Anyi biki na gani na fad'a na bawa mara d'a kunya ...
‎
‎Baqi kuwa ta ko ina sun halarci gurin bikin sosai ,,
‎Har Faiz yazo da matarsa da jariran twins d'insu wad'an da ya mayar musu sunan Hisham da Naznin .
‎
‎Aikuwa Hisham da Naznin sunyi farin cikin ganin jariran se tsalle suke suna murna musamman ma da akace sunansu iri d'aya ne "
‎
‎Har Muazzam da Faiz suna tsokanar su suna cemusu suma nan da wata d'aya umminsu zata qara juyo musu wasu twins d'in su samu qanne ,
‎
‎Bayan auren da sati biyu Alhj Hafiz da kansa ya biyamusu kud'in jirgi suka tafi Honey Moon qasar Dubai .
‎
‎Alhj Hafiz yaje prison dan dubo hajiya Habiba sede ya sameta a wani mawuyacin yanayi ,,
‎Idanunta ko gani basayi ga jinya yaci qarfin ta Ga azabar da y'an prison d'in suke gana mata da duka da hantara Wani lokacin ko abinci aka bata se su kwace su cinye su hana ta ,,
‎
‎Idan ta gayawa ma aikatan prison d'in haka zasuyimata duka da dare saboda haka take tsoron fad'ar duk abunda sukeyimata .
‎
‎A ranar da su Ajimal suka dawo daga Dubai Rafi 'a ta aifo kyakkyawan d'anta namiji  "
‎Zo kaga tsalle da murna a gurin Hisham da Naznin.......
‎
‎Ranar suna yaro yaci Sunan Alhj Hafiz amma suna kiransa da Abee ,,
‎
‎Sun gama shiryawa da yamma za a tafi walimar sunan Abee Humaira ta shige toilet da gudu tana amai  '
‎Seda ta gama ta fito ta zauna a bakin gado Rafi 'a ta bita da wani irin kallo ,,
‎
‎Seda Humaira ta d'an tsargu da kallon tace.....
‎Na d'an sha faten wake ne d'azu kuma kinsan ciki na baya so shiyasa '
‎
‎Seda Rafi 'a ta dafata sannan tace "
‎Ke yarinya Fad'amin gaskiya kode yaya na ya kusa zama baba ne ?
‎
‎A'a ,,
‎Babu abu me kama da wannan na fad'a miki kawai ciki nane ya d'an 'baci '
‎
‎Maji ma gani tunda nasan ai bazaki iya 'boye kabewa a qar qashin rigar ki ba zanga qarshen 'boye 'boyen naki ne  .
‎Rafi 'a ta fad'a tare da ficewa tana dariya ,,
‎
‎Watan Abee takwas da kwana goma Humaira ta haifo kyakkyawar yarinya me kama da Ajimal ,
‎Idan kaga yadda Rafi 'a take murna kai kacema itace ta aihu .
‎
‎Ranar suna anyi shagali sosai yarinya taci sunan Rafi 'a Wacce suke kira da ukti....
‎
‎Lokacin Rafi 'a ma da d'an qaramin cikin ta sede ita kad'ai ta sani domin befi wata d'aya ba ,,
‎
‎Bayan kwana arba in Humaira tazo wa Rafi 'a yawon arba in '
‎A kwance ta tarar da Rafi 'a batajin dad'i ko Abee  su Naznin ne suketa renonsa ,
‎
‎Ko abinci bata iya ci ga amai da kasala tayi wani haske ta qara ciccikowa tayi Kyau sosai "
‎Tun Humaira tana shiru harta kasa yin shiru tace ,
‎
‎Nikam anya Rafi 'a ke kad'ai ce kuwa yadda naga gaba d'aya jikinki ya canza kinyi kyau kamar ba ke ba ?
‎
‎D'an yatsina fuska Rafi 'a tayi tace '
‎Ba komai kawai na d'an samu nitsuwa sosai ne kwana biyu shiyasa kinga su Hisham sun fara zuwa makaranta acan suke wuni ,
‎
‎Dariya Humaira tayi tad'an bugi kafad'ar Rafi 'a tace.......
‎Ke yarinya Fad'amin gaskiya kode ukti ce tayi sabon qani da wuri haka ?
‎
‎Fillow Rafi 'a ta d'auka ta jefamata tana dariya tace ,
‎Wannan kam ai munriga mun girma munbarmuku daga Abee na rufe qofa  '
‎
‎Maji ma gani watarana gaskiyar zata fito ,,
‎Humaira ta fad'a tana dariya,
‎
‎Okay "
‎Wato kin rama koh to shikenan zamu ganin ai .
‎
‎Babu abunda za a gani bayan d'an qaramin kabewan da yake 'boye a qar qashin tumbin ki '
‎muazzm ne da ya jima da shigowa d'akin ya fad'a yana dariya .
‎
‎
TAMMAT BI HAMDULILLAH

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol