Free chapter · Read without an account

#27

by Aunty Mamee · FANSA KO ƘIYAYYA

FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*



_Page 27_

     Kallonta kawai yake baice komaiba, sai can ya numfasa da faɗin  "bayan wannan kuma fa?"   

Kanta ta girgiza alamun ba komai ba tareda ta ɗago kan nata ba dake duƙe .

Wani numfashi ya sauke da faɗin "Ni abinci na tambayeki ba abin rayuwa ba, amma dukda haka bazan bari maganarki tabi iska ba ki bari nanda wata talatin da huɗu (34 months) ki sake zuwarmin da buƙatar hakan ni kuma zan kwatanta miki adalci koya yane" yayi maganar idanunsa a kanta 

  ɗago kanta tayi tana kallonsa cikin mamaki "ban fa fahimci abinda kake nufi ba" ta faɗa cikin rashin fahimtar zancen nasa.

Gashin girarsa ya sosa da ɗanyatsansa manuniya  "saboda so nake har sai kin yi yaye sai mu sake maganan" ya faɗa still idanunsa cikin nata da take neman ƙarin bayani kan kalamansa.

 ɗan yamutsa fuskarta tayi alamun ƙosawa  da maganganunsa tareda kauda kanta gefe tana jinjina girman rainin wayonsa a zuciyarta, tayaya zai tambayeta ta faɗi duk abinda takeso da wanda bataso, ta faɗi masa kuma ya ƙaryata ta da faɗin shi abin ci yake nufi amma zai mata wai wata banzar alfarma nan da 34 months ta ƙara tuntiɓarsa da zancen irin rayuwar nan tata a hannunsa take.

Juyowa tayi cikin ɗan fusata sakamakon riƙo mata hannu da taji yayi.

"sai magana ta biyu, Please ki bani iya tarihinki kawai bana waniba, ni just labarin shekaru biyar da suka gabata a rayuwarki zaki faɗamin"

Shiru tayi kamar mai Nazari can ta numfasa da faɗin  "i promise you Nan da 34months zan faɗa maka bayan na sake zuwa da tawa buƙatar bazan gusa daga wajanba zan faɗamaka, just ka adana tambayarka har zuwa lokacin ka sake zuwar min da buƙatar hakan" ta faɗa itama idanunta cikin nasa.

Wani killer smile yayi haɗida shafa sumar kansa yana ƙara nutsa idanunsa cikin nata this evil wife of him sai ya girgiza kansa kawai tareda ɗaukan hannunta dake cikin nasa yakai bakinsa ya sumbata, tana shirin yin magana Naja ta shigo da sallama, ƙoƙarin ƙwace hannunta take amma ta kasa saima ƙara kaiwa bakinsa da yayi ya ƙara sumbatar hannun wanda sautin sumbatar ne yasa Naja ta ankare da sauri ta ajiye abinda ke hannunta kan gado da faɗin "ga wayarki Aunty, Mummy ta Kira" fitt tabar ɗakin kamar mara gaskiya.

  "Yanzu dan Allah mene ma'anar hakan idan an faɗa maka magana kace anyima rashin kunya saboda cin zali da ƙarancin imani" ta faɗa a zafafe.

Idanunsa ya lumshe ya buɗe su lokaci guda a kanta sannan ya matso dab da ita sosai batayi auneba taji bakinta cikin nasa, duk yadda taso ƙwatar kanta ya gagara hakan yasa ta ƙyalesa ya gama abinda zaiyi, jin yana ƙoƙarin latsa mata jikine yasa tayi saurin riƙe ɗayan hannunsa da hannunta ɗaya daya rage dan ɗayan ya riƙeshi gam cikin nasa hannun.

tana riƙe hannun ya fisge tareda riƙe nata dukkan hannuwanta suka dawo cikin nasa hannun, saida ya tsose bakin tas sannan ya zare bakinsa daga nata ya cikata tareda komawa gefe ya jingina da jikin gado yana sakin numfashi.

"Allah yayi maka fiyeda yadda kayimin" ta faɗa tareda share hawayen idanunta.

Yana daga jinginen ya waigo da kansa gareta tareda sauke dukkan birkitattun idanunsa a kanta

 "Zare idanunka bazai tsoratani naƙi faɗan abinda ke raina ba, kaje kasa likita ya rubutamin sallama dan Kanada wata muguwar manufa taka ta daban a kaina toka sani ba tsoronka nakeji ba kanacin darajar masu daraja ne amma wallahi duk sanda kawaicina da biyayyata ta ƙure zakasha mamakina ba kaɗan ba dan wallahi sai kayi daka sanin sanin mai kamada irin sunana ballantana ni kaina" ta faɗa cikin masifa da tsiwa

Kallonta kawai yakeyi yadda ta runtse idanu tanata faɗa shi bama wannan ne a ransa ba, shi idanun nasane a kanta amma rabin hankalinsa na wani waje na daban, tunaninsa yanaga yadda zai samu annual leave insa ne, hankalinsa ya kasu kaso biyu, ko ya ɗauka yanzu suyi rainon cikin tare kafinnan cikin yayi ƙwari ko kuma ya bari saita haihu yayi mata zaman daɓaro, tun ɗazu a asibiti yake wannan tunanin ya kuma gaza samun mafita, amma zuciyarsa tafi karkata daya bari saita haihun.

Ƙarar wayarta ce da Naja ta ajiye mata kan gado ta fargar dasu, daga abinda kowanensu keyi.

Ƙoƙarin miƙewa takeyi yayi saurin dakatar da ita tareda niƙewa ya ɗakko wayar ya amsa kiran haɗida ƙara mata a kunne, ɗauke idanunta tayi daga mugun hararar da take watsa masa tareda riƙe wayar amma dan neman magana saiya ƙi sakin wayar , sharewa tayi danjinn muryar Mummy nayi mata sallama.

Dukkan wata shagwaɓa da Allah yayi mata ta tattaro ta haɗe su waje guda da faɗin "Mummyyyy tun asuba ina asibiti amma ko kizo dubani"

 "Kiyi haƙiri daughter na kira wayarki bakya nan amma yanzu insha Allah gamunan zuwa da Auntynki Farida zata kawoni, ki faɗa min abinda kikeso naci na tawo miki dashi"

A shagwaɓe tace "Ni wallahi Mummy garin kwaki nakeson ci sai irin kayan ƙauye da ake rabawa a gidan biki idan na rakaki  kuma a tawomin da motana Mummy" 

Idanunsa ya ware sosai a kanta ganin yadda take zuba shagwaɓa kamar wata yarinya, duk haukan Naja sai yaga wannan ta fita koda yake shi dama yariga ya daɗe da sallama lamarinta.

 "Insha Allah komai kikace hakan za'ayi Aminiya zan siyomoki komai sannan zanyi driving car naki ma dawo a Napep" 

"Na gode Mummy na gode sosai Allah ya tarwatsa aniyar duk wanda yayi sanadin rabuwarki da Dady"

  "Ba wanda yayi sanadi daughter ƙaddara ce ta faɗawa Dady saidai muyi masa addu'a amma nikam bana zargin kowa kuma kema ina yawan nausar dake kan hakan" 

Ɓata fuska tayi da faɗin    "sai kun ƙaraso"  sannan ta kashe wayan.

Bin wayar Mummy tayi da kallo tareda sauke Ajiyar zuciya tana girgiza kanta.   "Gaki harda result mai kyau amma har yanzu kin kasa goge komai? Shirmen banza kenan" Mummy ta faɗa a fili tareda nufar farida data bari a palo zaune ita kaɗai.

Shikam murmushi yayi kawai haɗida janye wayar daga kunnenta yana ƙara saita idanunsa cikin nata da faɗin  "kinsan idan an kawo miki abubuwanda kika lissafa wa Mummy tsaf zan iya badasu ga mabuƙata na maye gurbinsu da nawa ko?" Ya tambaya idanunsa kafe cikin nata 

Ƙanƙance idanunta tayi akan nasa tana masa wani irin kallo can kuma sai ta waro idanun tunawa da tayi shiɗin baban babanta ne wajan rashin mutumci hakan yasa ta saki fuskarta tareda ɗauke ƙwayar idanunta daga kansa, yawu ta haɗiye sannan ta ɗakko gorubar ta data koma gefe takai bakinta.

sumar kansa ya shafa tareda miƙewa ya fara tafiya cikin izza da isa.

da harara gefen ido ta rakashi harya fice daga ɗakin, gyara zamanta tayi ta cigaba da cin gorubar ta kaman ba gobe.

kai tsaye waje ya fita nan ƙasan layinsu inda ake Saida fruits da drinks ya siyo.

Koda ya shigo gidan Naja ya nema da faɗa mata tayi sauri ta ɗora abinci sunada baƙi daga haka ya bar gidan gaba ɗaya.

Sai bayan la'asar su Mummy sukazo, Najace taji ƙarar buga gida hakan yasa ta tafi da sauri dan buɗewa dan tanada tabbacin baƙin da za'ayine.

Bazata taɓa mancewa da fuskar Mummy ba, dan ranarda sukaje ɗaukar amarya kallon ƙurilla tayiwa kowa na gidan ga kuma Aunty farida da suka haɗu washegarin biki, hakan yasa cikin fara'a da girmamawa ta tsugunna har ƙasa ta gaidasu tareda basu hanyar wucewa.

Cikin sakin fuska suka amsa Mummy ce ta kalleta da faɗin "taimaka idan zaki iya tura gate innan ki turamin zan shigo da mota"  

Da sauri ta miƙe ta fara kiciniya ganin haka Aunty farida ta taimaka mata suka zuge gate in.

Bayan sun shigo cikine Naja ta shiga ɗakin Binazir, a zaune ta sameta kan sallaya idar da sallarta kenan ta shigo

Cikin ɗoki tace " Mummy sunzo suna palo"

da sauri ta miƙe gudu tasoyi amma saitaji jikinta yayi mata nauyi hakan yasa ta fasa tareda tafiya cikin sauri.

Dariya Naja tasa sannan ta fito daga ɗakin ta nufi kitchen.

Tana zuwa palon ta faɗa jikin Mummy ta rungumeta tareda sakin kuka     "kwana talatin da biyu ban gankiba Mummy" yaƙe kawai Mummy takeyi Dan itama ji tayi zuciyarta ta raunana.

  Naja ce ta ƙaraso da sallama hannunta ɗauke da babban tray ta ajiye gaban su Mummy.

Sannu da ƙoƙari sukayi mata itadai murmushi tayi da barin palon.

Zare jikinta tayi daga Mummy tana share hawayenta tareda kai dubanta ga Aunty farida.    

"Ina wuni Aunty sannunku da zuwa" ta faɗa lokaci guda  

Harara Aunty farida ta wurga mata da faɗin  "ina mugu yake? Sai ga muku da aki gaskiya bai kyauta ba" cikin jimami

"Hmmmm bari kedai Aunty" ta faɗa tsakaninta da Allah, dan bata fahimci kan maganar ba abu dai ɗaya ta sani kalmar mugu kuma ta gane wa take nufi amma sauran zancen ta watsar da sune.

 "Kedai farida akwai zubda girma yanzu meya kawo wannan zancen?" Mummy ta tambaya cikin takaici, shiru tayi bata ansaba hakan yasa Binazir fara bawa Mummy labarin ciwon nata tun daga zuwansu gidan Umma har zuwansu asibiti da irin kulawarda su Umman suka bata.

Godiya sosai Mummy da farida sukayi tareda nuna jin daɗinsu kamar Umman na wajan

 Basu jima sosaiba Mummy ta miƙawa Binazir key da faɗin "saƙonki na ciki, mu zamu wuce" ta faɗa tareda miƙewa tsaye haka itama Aunty farida.

Rau rau tayi da idanunta "kinsan Allah idan kikayi mana kuka ba zamu sake zuwaba" Aunty farida ta faɗa cikin jin haushi

 "Farida mene haka ne wai" Mummy ta faɗa a ƙage dan dagaske batason irin yadda takewa Binazir in.

Taɓe baki Aunty farida tayi tareda fita daga palon

Kamo hannun Binazir Mummy tayi da faɗin "rabu da zancenta zamu dawo insha Allah, kuma gobe zan kaiwa Dady ziyara zan faɗa masa wannan daddaɗan labarin, nidai abinda nakeso dake shine ki kiyaye lafiyarki, banda yawan fita dukda nasan idan ba wajan Dady ba bakida wajan zuwa, kuma naji daɗin yadda kikewa Naja hakan yayimin Allah ya barku tare ya kuma ƙara haɗe kawunanku da zuciyoyinku"

  "Uhummm" kawai tace, dan idan tace Ameen hakan na nufin da kanta tayiwa kanta mugun baki dan muddin zata amsa da Ameen kenan zamanta da Naja daidai yake da zamanta a gidan ɗanuwanta, itakam bata wannan fatan, ita yanzu burinta bai wuce Allah ya kawo sanadin ƙarewar zamanta a gidan ba. dan bata fatan ko kaɗan takai wata goma saɓanin shida yake ambaton wata talatin da huɗu. batun kiyaye lafiya kuma ita duk zatonta saboda wannan zazzaɓin da tayine ake jaddada mata yanda zata kula da lafiyarta.

Janye hannunta da Mummy tayi daga cikin natane yasa ta dawo tunaninta tareda karkatar da wuya.

Hanyar Waje Mummy tayi hakan yasa ta bita ji take kaman tayi kuka amma ta danne zuciyarta.

Jingine jikin mota suka tadda Aunty farida tana waya.

suna dabda isa bakin gate ne sukaga an buɗe gate in.

Shine ya shigo hakan yasa ta tamke fuskarta, yana ƙarasa shigowa ya zube gaban Mummy Yana gaisheta kansa a ƙasa

  "Munafiki" ta faɗa cikin zuciyarta tareda mamakin yadda ya wani maida kansa na Allah gaban Mummy Dan ita tunda take dashi bata taɓa ganin yayiwa wani irin wannan girmamawan da yayiwa Mummy ba.

Taɓe bakinta tayi tareda kauda kanta gefe 

Cikin surukantaka Mummy ta gaidashi da ƙara jaddada saƙon godiyar ta zuwa ga Umma

Ɗago kansa yayi kaɗan ya kalli inda take tsaye sannan ya maida kansa ƙasa.

bai tashiba har saida su Mummy suka fice daga gidan sannan ya miƙe tareda  nufota.

ganin hakan yasa tayi saurin nufar motar ta, ta buɗe dan ɗakko saƙonta har jikin motar ya bita sannan ya tokare jikin marfin da ta buɗe 

 "Da kika kawo wannan abin kika ajiyemin a gida ce miki akayi ni banda itane?"  Ya tambaya idanunsa a kanta .

Fitowa tayi daga cikin motar hannunta ɗaukeda manyan ledoji, kallo ɗaya tayi masa ta watsar tareda fara tafiya cikin isa da taƙama.   "Idan ka gama kallon motar ka rufemin" ta faɗa a raine

Kallonta yayi tareda jinjina kansa yana jinjina wulaƙancinta, rufe motar yayi a hankula tareda biyo bayanta, jin kamar alamun motsinsa ne a bayanta yasa ta waiga bayanta, ganin shine yasa ta zabura tareda kwasa da gudu haɗida watsar da kayan hannunta ta nufi ɗakinta kai tsaye tareda faɗawa kan gado tana haki 

Tsayawa yayi yana kallon zallar hauka da rashin hankali, huci ya fitar tareda shigowa palon ya nufi ɗakinta.

Naja dake zaune a palon bayan gyara shi da tagama yi ta zauna sai kawai ganin Auntyn ta tayi ta shigo da gudu. Zaro idanu tayi tana kallon ƙofar ɗakin nata dan tuni ta shige ciki ita kuma batada masaniyar dawowar yayan nata.

Shigowarsa ne yasa ta fahimci ma'anar gudun, murmushi tayi tareda girgiza kanta saikace wata babba dan zuwa yanzu ta fahimci Auntyn tata akwai rashin kunya. Miƙewa tayi ta fito waje dan shan iskar yamma anan taga kayanda Binazir ta watsar, tsugunnawa tayi ta tsince mata na tsinta , dan wasu sun fashe irinsu agwaluma da casheuw.

Har cikin ɗakin ya bita, a kwance ya sameta hakan yasa shi takowa har bakin gadon tareda kiran sunanta a kausashe idanunsa a kanta.

  "BINAZIR"

Gabanta ne taji ya buga dan batasan da shigowarsaba sai saukar muryarsa a cikin kunnenta.

Tashi tayi zaune tareda ƙoƙarin ɓoye tsoronda ya ziyarci zuciyarta

   "Bazan lamunci wannan gangancinba wallahi, ai haukane ki dinga gudu kamar wadda batasan ciwon kantaba to Allah kikayimin asara bazan ƙyalekiba" ya faɗa a harzuƙe.

Galala take kallonsa ganin ya taƙarƙare yanata zuba masifarda batada ma'ana a wajanta.

Baki ta taɓe tareda ɗauke kanta gefe 

Hakan ba ƙaramin ƙular dashi yayiba cikin tsantsan ɓacin rai yace  "Allah duk sanda haukanki yasa kikayimin gangancin da kika zubarmin da ƙwaina dake cikinki zakisan ni mahaukacine na gaske" ya faɗa tareda barin ɗakin cikin fushi.







*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.