Free chapter 路 Read without an account

.

by Khadeejarth Sabi'u Yahyah 路 SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

___*馃拫 SARAUNIYAR KYAU 馃拫*




A can 蓳angaren kuwa


Zama Dr_Salahah tayi kana suma suka zazzauna a kujerun dake Kallon wanda ta zauna shiru office 蓷in ya 蓷auka gaba 蓷aya sun zuba ma ta ido suna jira suji abin da zata fa蓷a, a kalla sunkai mintuna biyar a haka.


Sannan Dr_Salahah ta 蓷ago daga rubuce rubucen da take yi tana kallon su, ta cire farin glass dake sa茩ale a fuskar ta fararen idanunta suka bayyana kana ta fara magana cikin harshen hausa yadda gaba 蓷aya zasu fahimci abinda takeson fa蓷a musu da kyau.


"Wato Abin da Rahoton binkciken da muka gabatar akan Dr Haleesat Rashid Rayyan shi ne, akalla an 蓷auki tsawon kwanaki biyar ana gana ma ta a zaba sannan binkciken mu ya nuna cewa an 蓷auki tsawon kwanaki goma a kullum sai anyi Raping 蓷inta sau biyu, bayan an gama kuma ana saka wani abu mai tsatsa kodai sanda ko 茩arfe ana goge duk wata alama ko hujja wacca zata nuna anyi ma ta fya蓷e.馃槶


Da蓷in da蓷awa kuma binkcike ya nuna ba iya maza ne kawai suka yi amfani da ita ba hadda ma mata sannan ta 茩arfi suke yi wanda hakan ne yasa duk taji ciwuka a jikinta da bakinta sai kuma hannunta da aka Rubuta wasu alphabet guda biyar.


"M_M_R_D_L."


Sune abin da aka Rubuta a hannun daman ta sai kuma tsakiyar hannun hagunta nan ma aka Rubuta "X" da alama 蓷aukar fansa ne yasa aka sace ta ba wai saboda ku蓷i ko wani abun ba."


Tana fa蓷in haka tayi shiru tana kallon su.


Tun lokacin da Dr Salahah ta fara magana gaba 蓷aya shiru suka yi suna kallon ta Alhaji Rafiq ashe suma ya yi ma lokacin da Dr ta ce anyiwa Haleesat 蓷iyar 蓷an uwanshi fya蓷e, shi kuwa Alhaji Riyaz ba abin da yake iya furtawa sai kalmar inna lil lahi har 茩arshe.


Abubakar ne kawai ya yi 茩arfin halin yin magana cikin murya wacca al茩alamin 'Nainarh Kd' bazai iya bayyana yanayin da yake ba.


"Yanzu Dr Salahah kina ganin Haleesat zata iya ci gaba da Rayuwa kuwa?...'


Shiru Dr Salahah tayi sannan ta bashi amsa da


"Gaskiya bani da amsar wannan tambayar naka Mister Mai Kyau sai dai kawai abin da na sani shi ne bamu da kayan aikin da zasu taimaka wajen kulawa da Lafiyar ta yadda ya kamata, sai dai akwai wani Babban Likita da muke bu茩atar taimakon sa amma a halin yanzu baya 茩asan nan."


"Za'a iya fita da ita Abroad kuwa wannan ta茩in da ake ciki?.''


Abubakar ya tambaya a dabke, Dr Salahah ta ce 


"Mister Mai Kyau ke nan wannan ai ba'a ridaga anzo maganar fita da ita Abroad ba tukunna, saboda Yanzu abu 蓷aya muke tsoron faruwar sa."


"Menene shi wannan abun?.''


Abubakar ya kuma tambaya, Dr Salahah ta ci gaba da cewa 


"Wannan abu 蓷ayan shi ne, muna tsoron kar ta sama Abrogating, ko kuma mental illness, da sauran su saboda abin da ya same ta."


Abubakar har ya bu蓷e baki zayyi magana ke nan aka banko 茩ofar aka shigo, Sailuba ce hankalin ta a Mugun tashe da alama taji abin da suke tattaunawa ne, 茩arisowa wurin su tayi cikin kuka take fa蓷in 


"Auntie Haleesat ce take bu茩atar ganin ku dukan ku hadda Yaya mai kyau...''


Wata 蓳oyayyiyar ajiyar zuciya Dr da Abubakar suka sauke fahimtar da suka yi bataji komai daga abin da suke tattaunawa ba.


Da sauri Abubakar ya mi茩e tsaye ya fice daga office 蓷in a 360 ita ma Sailuba tabi bayan shi, hannun Alhaji Rafiq, Uncle Riyaz ya kamo ganin ya茩i tashi amma sai ji ya yi hannun ya biyo shi. Da sauri ya juyo yana kallon shi a mugun tsora ce.


Kallon Dr Salahah ya yi a tsorace yake tambayarta. 


" Dr duba min ya mutu ko?.."


Ya yi ma ta Tambayar Like a Little kid sannan kuma hawaye yake yi.


Da sauri Dr Salahah ta 茩arisa wurin ta shiga duba Alhaji Rafiq bayan tayi abin da zata iya ta 蓷ago tana kallon Alhaji Riyaz da ya zuba mata ido sannan cikin hawaye da murmushi ta ce 


"Bai mutu ba ya dai fa蓷a doguwar suma ne."


Wani wawan burki yaja daga 茩ofar 蓷akin yana hango yadda Haleesat Rashid Rayyan ta koma wata abun tausayi.

A hankali kamar kazar da kwai ya fashe ma a ciki ya fara taku a hankali yana 茩arisawa wurin gadon da take kwance.


Dur茩usawa ya yi da duka 茩afafunsa yana kallon ta yayin da yake tariyo abubuwan da suka ta蓳a faruwa tsananin sa da ita, tun farkon ganin ta da ya yi a gidan su, da son ta da ya ke ma ta daga kallon farko, da ma yadda ya bayyana ma ta soyayyar sa a gare ta, amma saboda wani dalili nata tayi rejection nasa, da kuma yadda tasa ya 蓷auka ma ta al茩awarin dashi kansa yasan bazai yuwu ba.

Na ya taimaka ya cire ta daga zuciyar sa domin kuwa ita 蓷in ba wani tsawon rayuwa ne zatayi ba a doron duniya.


Komai dawo masa yake sabo fil a zuciyar sa, bai san kuka yake yi ba, har sai da yaga tana girgiza masa kai, alamar a'a sannan yasa hannunsa wanda yake faman rawa saboda tsananin tausayinta da 茩aunarta dake zagaye dukanin ilahirin jikinsa da ruhin sa.


Ya share hawayen fuskarsa amma wasu 茩ara zubowa suke hannun damansa yakai ya kamo nata hannun yana kallon ta cike da tausayawa game da tsananin 茩aunarta.


Zayyi magana, tayi saurin girgiza masa kai tana murmushin 茩arfin hali.


Sannan ta kalla su Hajiya Zinaru da Sailuba dake tsaye gefe sunyi curko curko sai share hawaye suke yi, murmushi tayi kana ta mayar da kallonta kan Rafi'at dake dur茩ushe can jikin gadon tana hawayen tausayin 瞥ar uwan nata, da hannu Haleesat Rashid Rayyan tayima Rafi'at alama da ta 茩ariso wurin, ko damuwa da cikin jikinta Rafi'at batayi ba ta 茩arisa wurin da sauri.


Har yanzu murmushin dake saman fuskar ta bai gushe ba, ga fuskar nan tata tayi wani haske na musamman sai faman shaining take yi, ga wani kyau na musamman da ta 茩ara, amma kana ma ta kallon gurilla komai Rashin imanin ka saika tausaya ma ta wata 茩ilama saika zubar da hawaye saboda Abin bakyan gani, tana jin jiki sosai sosai. 馃槶


Kamo hannun Rafi'at tayi sannan ta kamo hannun Abubakar tana murmushi ta ha蓷a wuri 蓷aya kana cikin murya irin wanda daga ji kasan mai ita ba 茩aramin jin jiki yake ba ta fara magana.


"Kamar ko yaushe anaso mutum 蓷an adam ya kasance mai kyautatawa 蓷an uwansa zato ko ya ya ne, amma wannan zamani mutane masu kyautata zato sunyi 茩aranci a wannan Rayuwa...

Mister Mai Kyau ga 瞥ar uwata kuma Auntie ta Rafi'at Rafiq Rayyan please ka taimaka ka ri茩e ta da amana, ka sota ka 茩aunace ta kamar yadda na tabbatar da cewa ita ma tana 茩aunar ka fiye da Rayuwarta please Mai kyau ka taimaka ka ri茩e mana ita amana. ir vosotros o铆r m铆 u cu谩l ?.. { did you hear me or what ? }...."


Tayi maganar tana dariya duk da cewa cikin ciwo take, murmushin ya茩e kawai Abubakar yake yi yama kasa magana sai faman girgiza ma ta kai yake yi alamar yaji kuma ya yadda zai ri茩e al茩awari, kallon Rafi'at tayi kana cikin murmushi ta ce 


"Auntie Rafi'at please ga your lawful naki ki ri茩e shi amana kin san fa yana 茩aunar ki ko?, dan Allah zaki ri茩e shi da amana tunda kin san yana 茩aunar ki."


Cikin hawaye da murmushi Rafi'at ta shiga girgiza kai kana ta ce 


"Nasani Haleesat nasani sister..."


Kallon su Hajiya Zinaru da Sailuba tayi kana tayi musu alama dasu 茩ariso da saurin su suka 茩ariso wurin gadon har rige rigen riqe hannunta sukeyi.


Murmushi Sailuba tayi kana cikin hawaye da dariya ta ce 


"Auntie Haleesat kin warke zaki tashi mu ci-gaba da girka abinci tare muna wasanni kuma, Daddynmu yace za'a kama mutanen da suka miki wannan ba za'a gyalesu ba har sai sun fa蓷a Wanda ya saka su kinji ko?."


Tayi maganar tana kuma kamo hannun Haleesat dake cikin nata, dariyar 茩arfin hali Haleesat Rashid Rayyan tayi kana cikin muryar marasa lafiya ta fara magana.


"Sailuba kinji ki rabu da mutanen da suka min haka kinji?."


"Saboda mene Auntie Haleesat?."


Sailuba ta tambaya cikin sauri hawaye na zuba, Haleesat ta bata amsa da "Saboda Allah ya fisu, kuma Allah yana tare da masu Ha茩uri."


Mai da kallonta kan Hajiya Zinaru tayi kana ta fara magana bayan ta kamo hannunta.


"Hajiya! please! Yau 蓷aya dai zan iya kiranki da wannan Babban suna wato Mahaifiya?, domin kuwa kin cancanta da na kiraki da wannan suna, a dalilin kin ri茩e ni da amana da gaskiya kinyi min ri茩on da ko iyayena sai haka, amma ni kuma ina ganin baki kai na kiraki da wannan suna ba, dan Allah Hajiya zaki iya yafewa wannan 茒iyar taki sannan ki bata damar kiranki da wannan sunan Mahaifiya?..."


Hawaye Hajiya Zinaru take amma hakan bai hanata murmushin farin ciki ba, jin yau 茒iyar da ta Raina da hannunta wacca tsawon shekarun da suka yi tare bata ta蓳a kiranta ko tayi ma ta kallon uwa Mahaifiya ba sai yau gashi tana ro茩on ta.


Da kyar ta iya bu蓷e bakinta dake tsananin rawa ta ce 


"Eh na yadda Haleesat 蓷ita kullum kiyita kirana da sunan mahaifiya domin hakan ba 茩aramin farantamin raina zaiyi ba kinji?."


Cikin kuka da dariya Haleesat Rashid Rayyan ta bu蓷e bakinta a hankali kana cikin dabara ta furta a saman la蓳蓳anta


"UMMA NA, MAMA NA, MAMY NA..

 Hakan ya yi daga yau zan dinga kiran ki da UMMATA...''


Da sauri Hajiya Zinaru ta amsa ma ta da sosai ma hakan Ya yi tana maganar ne kamar bata cikin hayyacinta tsoro take karta rasa Haleesat kamar yadda suka rasa iyayenta Sanadin hatsari mota.


"Ummata ina Abbana Yake da Uncle Riyaz bangansu ba wai suna ina ne?."


Haleesat Rashid Rayyan tayima Hajiya Zinaru tambayar tana 瞥an waige waige, murmushi Hajiya Zinaru tayi kana cike da zaulaya take fa蓷in 


"Yau wannan nema neman haka sekace kina mana bankwana kodai kinaso Dr Salahah tayi sauri tayi Discharged namu tunda kin warke ne?..."


Murmushi Haleesat Rashid Rayyan tayi Yayin da fuskar ta take 茩ara wani haske da shaining gunin burgewa kana ta ce 


"Ummata ba bazaki fahimci abin da nake ji bane, ina kallonsu cikin fararen kaya sunayi min murmushi Yayin da wasu suke mi茩o min hannu, kin san miye kuwa?."


Bata jira Hajiya Zinaru ta amsa ma ta ba ta ci-gaba da cewa.


"Ummata dan Allah keda Abban mu dasu Rafi'at da Sailuba da kowa duk Wanda nayi wa wani laifi a Rashin sani kuya femmm..."


Tarin da ya taho ma ta ne yasa ta kasa 茩arishe maganar da zatayi nan ta shiga tayi 蓳a蓳蓳aka tarin tambar kayan cikin ta zasu yo waje.馃槥


Tana mai furta kalmar shahada su duka suna tayata sun 蓷auki lokaci a haka kana can suka ji tayi tsit hannunta dake sar茩e cikin nasu ya sage ga fuskar ta 蓷auke da qayataccen murmushi.馃槗


Ganin tayi shiru yasa Rafi'at 茩ara kamo hannunta tana mai kiran sunanta amma ina rai ya yi halin sa Wanda yafi su 茩aunar ta ya amshi abin sa.


Ganin da gaske dai batayi magana ba yasa Abubakar dake gefe 茩arisowa wurin cikin sauri ya shiga duba ta, duk da cewa shin 蓷in ba Likita bane amma kuma yasan cewa Haleesat Rashid Rayyan bawai tayi bacci ba ko kuma zata farka zuwa anjima ba, a'a bata duniyar gaba 蓷aya shikenan TAFARU TA茦ARE Haleesat Rashid Rayyan ta tafi inda muma muna nan 茩arisawa idan lokaci ya yi domin kuwa kowa lokacin sa yake jira, lokaci nayi ba jira za'a tafi tafiyar da babu dawowa har abada har duniya ta na蓷e shikenan kuma.馃槶馃槶馃槶


Ja! da baya ya farayi cike da matsanancin tashin hankali babu abin da yake iya furtawa sai kalmar inna lil lahi har 茩arshe yana mai rumshe idanunsa Yayin da wasu siraran hawaye suke zubowa akan kyakyawar fuskar sa.


Fahimtar abin da yake faruwa wai Haleesat ta tafi, tafiya na har abada yasa Rafi'at ta yanke jiki ta fa蓷i a wurin sumammiya.


Ita kuwa Sailuba kusan zaucewa za'a iya cewa tayi saboda tsananin tashin hankali, Yayin da Hajiya Zinaru ta koma Tamkar mutum mutumi.


/Yau abin dai Al茩alamin Nainarh kd bazai iya rubutawa Yanda yake ba saboda is very vThither Ban tausayi over 馃槶馃槶馃槶....Kuyimin Afuwa....馃槗馃槗馃槗/


Gaza jurewa Abubakar ya yi domin kuwa zai iya cewa tunda yake a tsayin Rayuwar sa bai ta蓳a shiga tashin hankali irin wannan ba.


Fita ya yi daga 蓷akin kai tsaye office na Dr Salahah Gashwa ya wuce ashe camma wani tashin hankalin zai kuma tarar wa domin kuwa Alhaji Rafiq Rayyan ne ciwon zuciyar sa ya tashi Ashe ma har gado aka bashi anan Asibitin.


Tashin sense.!馃槴


Tashin Hankalin Wanda ba'a saka masa Rana zuwa Yammacin Ranar gaba 蓷aya dangin Alhaji Rafiq Rayyan suka hallara a wannan Asibitin zuwa lokacin kuma Sailuba ta fara dawowa hayyacinta amma ba gaba 蓷aya ba.


Yayin da ita kuma Rafi'at abin yazo da sauki ta farfa蓷o shima dai Alhaji Rafiq Rayyan abin sai godiyar Allah sai dai shi Asibitin sun ri茩e sa saboda tsaron lafiyar sa.


Saboda haka bai sama damar Raka maragayya Haleesat Rashid Rayyan izuwa makwancinta ba.


Da yake a wancan lokacin waya tayi 茩aranci yasa ba kowa ya sama damar zuwa ba cikin Ahali wa'inda suke da nisa, sai washe gari suma mutanen Jigawa State suka 茩ariso.


Rafi'at gaba 蓷aya ta 蓷auki damuwar duniya ta sakawa kanta domin kuwa koda abinci bata iya ci sosai ta saba kafin suyi aure da Abubakar Mai Kyau a kullum tare suke da Haleesat Rashid Rayyan koda wani wuri zasuje to tare suke zuwa, bama ita ka蓷ai ba gaba 蓷aya 蓳angarorin abin sai a hankali.


Satin Haleesat Rashid Rayyan biyu da Rasuwa Rafi'at ta koma gidan mijinta Abubakar zuwa lokacin kuma an sallami Alhaji Rafiq Rayyan daga Asibitin.


/RAYUWA KE NAN馃槶/


_*BAYAN_WANNI_BIYU*_


Rayuwa ta ci gaba da tafiya sumuluquii ta wasu 蓳angarorin amma banda 蓳angaren Rafi'at da mijinta Abubakar domin kuwa zama suke zaman doya da manja tun rasuwar Haleesat Rashid Rayyan komai ya ta蓳ar蓳are tsakanin su ko 蓷an kulawar da Abubakar yake bata a Sanadin cikin jikinta Yanzu babu, domin kuwa wani miskilanci Yake ji dashi haka suke zaman abin sai addu'a.


Ranar wata litina Rafi'at ta tashi da na茩uda ba'a ja lokaci ba da yake da wata tsohuwa Babah Ladii 茩anwar Kakansu a gidan saita taimaka ma ta zuwa Yamma lokacin Abubakar ya dawo ya tarar da halin da ake ciki, bai 蓳ata lokaci ba, ya kira Hajiya Zinaru ta waya ya sanar da ita abin da ke faruwa.


Ko kafin Hajiya Zinaru ta 茩ariso Rafi'at ta haifo kyakyawan Jaririn ta 茩ato mai kama da ubansa kamar an tsaga kara komai iri 蓷aya sak, Like father Like son 馃


Koda suka 茩ariso ita da wata 茩anwar ta sai kuma Sailuba nan suka ha蓷u da Babah Ladii suka shiga kula da mai jego da kuma Jaririnta.


Zuwa kwana uku da haihuwa gaba 蓷aya Ahalin Alhaji Sameer Lami蓷o dana Alhaji Rafiq Rayyan ba Wanda baizo duba lafiyar mai jego da kuma Jaririn da ta haifa ba, kowa yazo sai ya yaba da kyau irin na wannan jariri.


Ranar suna Yaro Yaci suna


ABDUL'MALEEK.!


/THE KING/


Mutane na kiran sa da Maleek Yayin da iyayen sa suke kiran shi da


BUDDY


Wato Aboki

Duniya sabuwa fil a wurin Rafi'at da Jaririn ta Abdulmaleek domin kuwa tun a Ranar da ta haihu wani kulawa na musamman Abubakar Yake bata ita da Jaririn su sunyi 茩iba sunyi 蓳ul蓳ul abinsu.


ABDUL'MALEEK Ya taso Yaro ne shi mai 茩iriniya sosai da sosai domin ko Asibiti Rafi'at ta tafi dashi tofa Ya dingi dukan Yaran mutane ke nan gashi ita kuma Likitar Yara ce, gashi daga ita har uban sa suna 茩aunar shi sosai 茩aunar da ta sa basa ganin laifin sa koya yake.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.