Free chapter 路 Read without an account
2
by Aminatu Ibrahim 路 NUUDARR
NUUDARR 馃馃
(A 2025 NOVEL)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
PAGE 2
........ Na mi茩a hannu na kenan da nufin bu蓷e 茩ofa mukayi ido biyu da Aunty Nadee, cikin fa蓷uwar gaba na saki jakar kaya na tare da sakin kuka a hankali murya ta a 茩asa in a pleading tone nace.
"Aunty Nadee pls Allowed me kada kice zaki hanani, Mama tace ba zan auri Emraan ba, ni kuma na gwammace da in shiga duniya wallahi da a hanani auren Emraan Aunty Nadee domin shine duniya ta...."
In a very low tone naji muryar Nurudden a bayana tare da dam茩ar hannu na yace.
"Nuudaar you are mad! What do you think are you doing huhh? Akan Emraan? Emraan 蓷in banza Emraan 蓷in wofi kike nema ki kassara rayuwar ki, to ki tafi kije ina??"
Cikin matsanancin 蓳acin rai na fisge hannu na ina kallon sa nace.
"Nurudden kada ka sake kiran Emraan da banza..."
Hannuna Aunty Nadee ta dam茩a da gudu ta Jani ta shige dani cikin kitchen ganin kamar mama ce zata fito.
Nurudden shima cikin zafin nama ya wawuri jakata ya wulla bayan motar Baba sannan ya bu蓷e 茩ofar gate ya fice daga gidan zuciyar sa na yi masa wani iri akan abinda Nuudaa ke neman aikatawa.
Hawaye na gani kwance a cikin idanuwan Aunty Nadee, cikin karyewar zuciya ta kalle ni tace tace.
"Nuudaa miye yayi zafi haka? Kin san girman abinda kike neman aikatawa kuwa? Idan kika yi hakan kina ganin kin yi mana adalci kenan musamman Mama, yanxu da ace Allah bai sa na zo kitchen 蓷in nan na ganki ba da shike nan sai ki sanya 茩afar ki ki fice daga gidan nan?"
Ina tsiyayar hawaye nace.
"To Aunty Nadee what should I do? Wallahi tallahi ina matu茩ar so da 茩aunar Emraan, I can't live without him Wallahi, Mama Kuma tace ta kai 茩arshen maganar ta cewa ba zan aure shi ba to ya zanyi da raina..."
"Haba Nuudaar! ko mai fa yayi zafi maganin shi Allah, abinda kike neman aikatawa kuskure ne, idan kika fita cikin daren nan ina zaki nufa? Ga gari da mutanen cikin sa babu kyau, sannan shi wanda zaki aikata wannan kato蓳arar domin sa shi ya shirya barin nasa iyayen? ko kuma ya tanadar miki masauki a cikin gidan su da zaki zauna? Nuudaa 茩imar ki da ta iyayen ki ta蓳uwa zatayi har abada a idon duniya, Mama da ta haife ki ta raineki tun kina zanin goyo har kika kawo yanxu baki yi mata adalci ba,Baba da yayi ta miki 蓷awainiya tun haihuwar ki zuwa yanzu shima baki masa adalci ba, kuma duk abinda kika ga Mama ta yi saboda ke take yin sa ba don kanta ba,sannan idan kinyi don ki burgesa wallahi iyayen sa da dangin sa ba zaki burge ki su ba, kinga kin 蓳ata goma kuma biyar bata gyaru ba. Kiyi ha茩uri ki barwa Allah za蓳i shi ne yasan abinda yafi da cewa da rayuwar ki duk ba wannan shirmen ba. Sannan kin san halin Saif sarai kamar yunwar cikin ki even Yah Halifah ban san yadda zai yi ya tsaya miki ba a kan wannan lamarin.... "
Fa蓷awa nayi jikinta tare da rushewa da kuka ba tare da na furta komai ba domin jiki na ba 茩aramin sanyi yayi ba, duk abinda ta fa蓷a babu 茩arya a ciki kawai dai tsabar son zuciya ne irin nawa da kuma tsananin soyayyar da nike yiwa Emraan......
茦ara kwantar da murya tayi taci gaba da fa蓷in.
" Yanxu dan Allah 蓷iyar gidan Al茩ali guda! Al茩alin ma Musayyib wanda ya ke tsayawa a shari'ar iyayen da suka kawo 茩arar saurayi ya gudar musu da '拼a yau shi ne za'a wayi gari ace '拼arsa ta gudu tabar gida ta shiga duniya akan saurayin ta mi kike tunanin zai faru?Nuudaar kiji tsoron Allah ki tuna ha茩茩in iyayenki, kina da ilmi ta ko wane fanni bai kamata ki 蓷auki turbar marasa lissafi da duhun jahilci da rashin wayewa ba, komai cikin hikima da ilmi ya kamata mu ri茩a yin abubuwan mu. Ha蓷a auren mu lokaci 蓷aya babu matsalar da zai baki Nuudaa ki kwantar hankalin ki, Yah Halifah namiji ne ni kuma ba auren farko ba ne, babu abinda zanyi daga zaran an 蓷aura aure shikenan, ko Yah Hadiza ka蓷ai zata saya miki duk abinda kike so ga Mama ga Alhaji, ga Yah Halifah ga yah Saifu, shin duk wa蓷an nan ba su isa su saya miki duk abinda kike so ba? Ni na riga na sayi gadaje na guda biyu tun tuni su Baba suka bani ku蓷i na ha蓷a da nawa na sayi har kujeru abinda ya rage min ka蓷an ne, saboda haka ki daina neman tsaurara abubuwan nan komai zaki yi sa yadda kike so. Auren Hudah 蓷in Yah Hadiza iyaka 10month yanxu shin idan kika ce sai sun zo sun koma kuma su sake dawowa dan Allah baki basu aiki ba? Saboda haka kiyi ha茩uri ku tsara duk abinda kuke so ke da Emraan 蓷in babu wanda zai hana ku"
Ajiyar zuciya na sauke cike da gamsuwa da Kalaman ta na bu蓷e idanuwa da kyau na kalle ta wa蓷anda sukayi luhu luhu tsabar kuka nace.
"Shikenan Aunty Nadee na amince, Allah yasa shi ne mafi alheri, na gode sosai da tunatarwa"
Murmushin nasara Aunty Nadee ta saki sannan tace.
"Yawwa Nuudaa 蓷in Yah Halifah da Mama"
Turo baki nayi gaba ina gunguni nace.
"Ni wallahi ba ta Mama ba ce tunda bata son wanda nike so..."
Juyawa tayi ta janyo fillet guda 蓷aya tana Fa蓷in.
"Naji dai shi kenan to, bari na sanya miki abinci da kaina saboda na san tun break fast 蓷in safe ne a cikin ki kuma kada ki yarda kice ba zaki ci ba..."
"Aunty Nadee Mama fa nike tunani kin san halin ta, kada ta 茩i janye maganar ta"
Juyowa tayi ta kalle ni tana mai bani assurance tace.
"In sha Allah zata amince ba matsala kada ki damu"
Gya蓷a kaina nayi nace.
"Tau shi kenan. Kuma dan Allah Aunty Nadee ina neman alfarma da ki kira Emraan ki bashi ha茩uri akan wannan maganar..."
Cike da Mamaki tace.
"In kira Emraan na basa ha茩uri? Akan wane laifi to?"
Hannunta na dam茩e ina mai magiya nace.
"Dan Allah Aunty Nadee pls! Kada yaga cewa an masa ba daidai ba"
Ita dai Aunty Nadee bi na kawai tayi da ido tsabar yanda gaskiya tayi mata yawa, to kawai tace min don ta huta da ni.
********
ASIYAH
Tunda ta koma gidan Aunty Zainab take banbami tamkar zata tada gidan tsabar masifa. Ita dai Auntyn ta ta sai faman bata ha茩uri take tana fa蓷in.
"Haba Asiyah kiyi ha茩uri mana, it may be akwai uzurin da ya gifta masa tunda bai sa ba yi miki haka ba..."
"Wallahi Aunty Zainab wula茩anci ne kawai irin na Halifah daman ba yau ya saba yi min irin haka ba, Yanxu duk irin uzurin da zai bani ba zai wuce na yace min lalurar 茩annen sa ce ta gifto ta danne tawa lalurar ba shiyasa na tsane su a rayuwa ta musamman wannan shegiyar Nuudaar 蓷in er bura'uba...."
Baki sake Aunty Zainab ta shiga kallon ta tsabar mamakin ta da ya kashe ta. Sai da ta dasa aya sannan Aunty Zainab 蓷in tace.
" Asiyah kin fara shaye shaye ko? Ki samu mutum da en uwansa sannan kice wai kin tsane su tun baki ma kai ga shiga gidan ba..."
Mi茩ewa tayi tsaye jin wani 茩arin 蓳acin ran da Aunty Zainab ta da 蓷a sanya mata tace.
"Aunty Zainab daman na san ba zaki fahimce ni ba shiyasa ban ta蓳a yi miki 茩orafi ba, kuma ke don mijin ki yana shi ka蓷ai ga iyayen sa shiyasa ba zaki gane matsalar 茩annen da yayyun miji ba. Yanzu Aunty Zainab ki duba ki gani kullum idan zance yayi min wani abu sai ya ce min wai ba shine a gaban sa ba ha蓷in lefe yake gini yake miye miye duk sai ya kawo 茩auli da ba'a 蓷i ya rattaba min, amma a gabana wallhy da zaran wani daga cikin su ya kira shi ya tambaye shi wani abu jiki na 蓳ari zai tura, to ni zaunawa zanyi ne kai na yayi murfi? Wallahi ba zai yi yu ba...."
Gya蓷a kanta Aunty Zainab tayi tace.
"Lallai ba shakka! Ke yanxu er jaririyar yarinya da ke haihuwar jiya har kin san matsalar dangin miji tun ma baki shiga ba? Duk da cewa dangin miji suna da tasu matsalar a mafi yawan Lokuta amma mu muke fara sayawa kan mu matsala da ku蓷in mu,idan ba neman rashin zaman lafiya ba miye naki don ya yi musu lalura? Dolen sa ne su ke kuma ba dolen sa ba ce a halin yanxu sai ma idan anyi auren, sannan ko anyi auren baki isa ki hana sa hidimtawa en uwan sa ba matu茩ar kina neman zaman lafiya a gidan auren ki...."
"Aunty Zainab dududu nawa ne samun sa baki 蓷aya da har zai iya 蓷auke lalura ta sannan ya 蓷auki ta su? Iyayen su na da ku蓷i fa tsabar ba茩in ciki ne kawai Aunty Zainab"
"Asiyah! Dan Allah ki rufawa kan ki asiri ki kuma rufa mana muma da 茩urciyarki kada ki 蓷orawa kan ki wahala..."
Jakar ta ta figa daga kan cushion 蓷in Aunty zainab 蓷in ta wuce 蓷akin yaran ta ta kwanta akan gado saboda bata so ma tana sauraren ta, shi kenan shi kullum kwanan duniya bai da wani zance sai na Nuudaa, Nurudden, Saif, Yah Hadiza, Nadee, Fauxa, Hanna... Mtsw! Aikin banza kawai wallahi tallahi dani suke zancen"
Nan tayi zamanta sai da mijin Aunty Zainab 蓷in ya dawo Yayah Sufyan bayan an 蓷auke ruwa sannan ya 蓷auke ta ya kai ta gida wanda har ta bar gidan bata sake yiwa Aunty zainab magana ba.
Tana shiga gida ta fa蓷a jikin Umma ta fara kuka tana fa蓷in.
"Umma nifa na gaji da wula茩ancin da Halifah ke min wallahi"
Cikin rashin jin da蓷i Umma tace.
"Miye kuma yau ya faru?"
"Umma shi ne fa da kansa ya kirani ni ya tambaye ni cewa yaga hadari duk ya game gari ina gidan Aunty Zainab 蓷in ya zo ya kawo ni gida, nace masa eh ina nan sai ya ce to in jira sa, ganin hadari ya taso sosai yasa na fito ina tsumayin ganin sa amma har ruwan nan ya sauko Halifah bai zo ba kuma idan na kira sa baya 蓷aga Kirana har yanxu"
Cikin zafin rai Umma tace.
"Ke nifa idan Halifah yasan zaman 茩unta ta miki zaiyi idan kunyi aure gwara tun yanxu ya rabu da ke zai fi mini kwanciyar hankali, don ba zan sai da a Kuya ta dawo tana gogar mini danga ba, bari Alhaji ya dawo gidan"
"Wai Umma Aunty zainab sai wani ganin laifina ta ke wai na dai na ganin laifin sa miye miye..?"
Mere Baki Umma tayi sannan tace.
"茩yale shegiya er ba茩in ciki tunda ita ta samu nata mijin a 蓳agas ta samu gindin zama ai sai ta miki ba茩in ciki. Ni wallahi abin nan yana bani mamaki wai ciki 蓷aya amma mutum yana yiwa 蓷an uwansa hassada"
Mi茩ewa Asiyah tayi tare da 蓷aukar Jakarta ta wuce 蓷aki tana mai 茩ara kiran wayar Halifah cikin sa'a kuwa sai taji an yi picking.
"Aunty Asiyah kiyi ha茩uri zan kai masa wayar yanxu"
Jin Muryar Nurudden yasa tayi saurin jan mugun tsaki ta kashe wayar kai tsaye tana mai gunduma mai zagi a ranta tana fadin ko me ya kai wayar Halifahn hannun sa Oho!
Bayan kusan 10mnt ta sake kiran sa a lokacin da yake gaban Mama zaune ta fara mai tijara shine fa ya kashe wayar tare da sanya ta a fly mood.
Daman ta kawo iya wuya akan takaici sai kuma gashi ya kashe wayar. Kuka ta fasa tare da wurgar da wayar a gefe tana fa蓷in.
"Na shiga uku ni kam Asiyah, ni tawa jarabawar tun a waje nike ta 茩unsar ba茩in cikin 蓷a namiji da dangin sa, idan ba shi ba miye ruwan Nurudden da kiran da nike yiwa Halifah ko kuma baya son Magana da ni ne?"
Xumbur ta mi茩e zaune tare da janyo wayar ta shiga gidan text message ta rubuta masa.
" Halifah Musayyib Al茩ali ni Asiyah Ma'aji na fasa aurenka ka aiko gobe a kar蓳a maka sadakin ka da kayan auren ka na fasa tun da ba kai ka蓷ai ba ne autan maxa.. "
*******
HALIFAH
Yana baro gaban Mama ya cire wayar a flymood ya kamo numbern Asiyah jiki ba 茩wari ya dailing numbern. Allah ya shine shaidar sa har ya kama hanyar zuwa ya 蓷auko ta kamar yadda yayi al茩awari sai ga kiran Nadee ya shigo tana sanar mai ga abinda yake faruwa shiyasa ba shiri ya juyo kan Mashin 蓷in nasa ya nufo gida, ganin an fara ruwa sosai yasa shi ciro wayar sa ya bu蓷e seat 蓷in Mashin 蓷in 拼a saka wayar a ciki gudun kar ta ji茩e, to shi tun a time 蓷in ma ya manta da wayar a wurin,to amma yanxu duk abinda zai fa蓷a mata yasan ba yarda zatayi ba complain kawai zata cika shi da shi har da kuka. Kira kusan uku yayi amma ana ce masa wayar a kashe take, yana nan yana nazari sai ga text 蓷in da ta tura masa ya shigo.
Yana gama karantawa yayi murmushi tare da girgiza kan sa kawai yana mamakin rayuwa irin ta Asiyah. Kwata kwata ba ta da uxuri ko ka蓷an.
"I'm Sorry Love!, Allah ya huci zuciyar ki"
Abinda ya rubutu mata kenan ya tura mata ya share da zancen ta.
Washe gari bayan ya gama shirin sa na fita kasuwa yazo 蓷akin Mama ya zauna ya kira Nadeeyah akan ta kawo masa break fast 蓷insa.
Ruwan Tea daban ta kawo masa da bread sannan filet 蓷in jollop 蓷in spaghetti daban.
Kallonta yayi yana murmushi yace.
"Nadee Yanxu 11am zaki kawo min Tea? You are not serious! Bani filet 蓷in Sai ki 蓷auke wannan"
Itama dariyar tayi tace.
"Yah Halifah kai ne dai baka shan Tea yanxu, bari kaga Yah Saif Idan yaxo yanxu muddin bai yo breakfast daga gida ba Tea 蓷in zai ce a basa"
"To Saif in dai gidan abinci ne ai kamar mace haka ya ke. Ina Hajiya ne wai?
" Mama fa ta fita tun 10am tacemin idan suka tashi daga school 蓷in zata wuce gidan Baba Usman"
" Ok to ina Mutuniyata na le茩a ta lokacin da na dawo daga masallacin subhi na ganta akan sallayah zaune"
Girgiza kai kawai Nadeeyah tayi tace.
"Hmm! Ai wallahi Yah Halifah arziki mukayi daren jiya"
Spoon 蓷in hannun sa ya ajiye yana fa蓷in.
"Subhanallah! Miye ya faru?"
茦ara yin 茩asa da muryar ta tayi ta bashi labarin duk yadda sukayi da Nuudaar a daren jiya har yanda tayi ta samo kanta.
Cikin tashin hankali yace.
"InnaLillahi wa inna ilaihiraji'un! Har abin nata ya kai haka ashe? In sha Allah ba za'a fasa auren ba, ai gwanda ma ayi a gaggauta kowa ya huta"
"Wallahi Nima dai abinda nace kenan, to 蓷axu na kira Yah Hadiza tunda assusuba na fa蓷a mata abinda ake ciki tace min in bar mata zancen a hannun ta ko kai kada kayiwa Mama da Baba magana"
Gya蓷a kansa yayi yace.
"To shi kenan, Allah yasa ayi wannan auren lafiya a 茩are sa Lafiya ko zamu samu kwanciyar hankali. Wallahi Nadee tunda Emraan ya shigo rayuwar Nuudaa shi kenan ta sauya daga yanda ta ke"
"Ni ma dai shi na gani Yah Halifah, gwanda kawai ayi auren shikenan an kai 茩arshen komai"
Haka dai suka yi ta tattaunawa har ya kambala sannan ya 蓷auki kayansa ya fice zuwa kasuwa.
Gidan su Asiyah ya nufa direct ya ajiye mashin 蓷insa a gefe ya aika yaro akan cewa yana mata sallama.
Bayan Yaron ya dawo yace masa ance tana zuwa sai ya samu wuri ya tsaya a gefen gate 蓷in nasu yana dakon zuwan ta.
"Ina Halifahn yake?"
Zaro ido yayi tare da yin 茩asa ya du茩a yace.
"Umma ina kwana..."
Hannunta ta 蓷aga masa tace.
"Da ban kwana ba zaka ganni ne? Kai ni fa Halifah tsakani da Allah ka fito fili ka fa蓷a min idan baka son '拼a ta ba abin dole ba ne..."
Cikin rashin fahimta yace.
"Umma ita Asiyar tace an yi mata wani abun ne?"
"Oh! Abinda zaka ce kenan ma wato, Yanxu ka bawa 茩anin ka waya ya 蓷auka yana gaggaya mata ba茩a茩en maganganu sannan yanxu ka tsaya a gabana kana tambayata wai anyi mata wani abun ne ko? To don Allah da ka sanya mata hawan jini da kai da dangin naka tun yanxu da 茩urciyarta gwanda kowa ya ha茩ura kawai..... "
Da sauri Asiyah ta fito hankali tashe saboda bata san cewa Ummar ta fito wai da sunan magana da Halifah ba. Ita yau wannan abun kunyar ina zata je da shi ace wai Umma ta fito tana fa蓷a da saurayin Haba! Cikin takaici ta zum蓳uro baki gaba tace.
" Umma ni fa ban ce miki Nurudden ya fa蓷amin ba茩a茩en maganganu ba.......
OUM AMEER