Free chapter 路 Read without an account

37

by Kansa'u Bello 路 AMATURRAHAMAN

馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒

*AMATURRAHAMAN*

_*By*_

*_OUM FATIMA_*

_*(Hakimar D. A. W. A)*_

馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒

_*DASHEN馃尣ALLAH*_

_*WRITER'S馃摎ASSOCIATION*_

_*TEAM*_

_*JAJIRTATTUN馃挭馃徎DASHEN馃尣ALLAH*_

*BOOK 1*

*PAGE 37*

_*亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇 丨賲賳 丕賱乇 丨賷賲*_

Fuska a cunkushe ta 茩arasa 蓷akin Momynta ta sameta itama fuska ba walwala, zama tayi tana 蓷ora kanta saman kafa蓷ar Momyn tace. "Wallahi Momy in na bari Aunty Zaheera ta samu Yaya Zayyad ban haifu a cikin ki ba, ai wallahi in dai ban same shi ba to ba shegiyar data isa ta same shi a cikin gidan nan bare har tazo tana hura mana hanci. Momy wai Kinga rashin mutuncin data min yanzu kuwa!".

"Kin ga ki rabu da ita zamuyi lokacinta, yanzu Dadynku ne ya kira yace ki shirya kije ki gaishe da wa蓷an can mutanen suna sashen Hajiya Iya." Momyn ta fa蓷a tamkar ta fashe da kuka tsabar haushi.

"Momy ni dai ba zanje ba, ai naga sanda suka shigo nayi wucewa ta." Cewar Anisa tana gyara kwanciyarta.

"Kinga maza tashi ki shirya muje tare ai shi ya茩i 蓷an zamba ne, kuma sannan kin san halin Dadynku sarai dai ba sai an tuna maki ba." Momy ta fa蓷a tana janye jikinta ta mi茩e. Tashi Anisa tayi ba don taso ba tana 茩un-茩uni ta shiga 蓷akinta ta sako hijabi akan doguwar rigar English wears 蓷in dake jikinta suka wuce ita da Momy data ha蓷a abin motsa baki a 茩aton tire aka rufe da farin 茩yalle ta bawa Anisa ta ri茩e tana tura baki suka wuce.

Sun same su sunci sun sha suna ta hira da Hajiya Iya Sarkin zance, zama suka yi suka shiga gaisawa fuskar Momy cike da fara'a kai ba zaka ta蓳a cewa bata son ha蓷in ba. Suna haka Dady ya shigo da sallama ya zauna shima aka shiga gaisawa, ya mai jiki Alhaji Abba gana ya masa ya amsa masa da "Alhamdulillah."

Hira suka ci gaba dayi irin ta aminai, tayin zuwa sashin su Momy ta yiwa Hajiya Shuwa. Ba musu kuwa suka bita ita da 拼anmatanta guda biyu, Anisa ma binsu tayi don ta tsani irin kallon da Abdulmajid yake binta da shi. Suna fita maimakon sashin su sai ta waske ta nufi sashin Ammah, lura da hakan da Momy tayi ne yasa tace ma Anisan "Ga 拼an'uwanki nan ku tafi tare mana." Ta 茩are maganar tana murmushi n ya茩e gudun kar Hajiya Shuwan ta zargi wani abu.

Safah data lura da yanda Anisa take wani shan 茩anshi tace "A'a Momy taje kawai." Dama ba wani son zuwan nasu take ba sai kawai ta ka蓷a kai tayi gaba abinta. Murmushin ya茩en itama Hajiya Shuwan tayi suka wuce.

A can 蓳angaren Baba Alhaji kuwa Alhaji Abba gana ne ya sako maganar 蓷aurin auren, yace ko za'a 蓷aga ne har Baba Alhajin ya 茩ara war-warewa.

"Ai jiki yayi sau茩i Alhamdulillah, nan da sati 蓷aya kawai sai a 蓷aura a wuce wurin kawai." Cewar Baba Alhaji. Wani irin da蓷i ne ya mamaye zuciyar Abdulmajid yaji tamkar ya taka rawa don murna.

Basu bar gidan ba sai da aka tabbatar da maganar 蓷aurin auren ranar Asabar.

*Muzaffar.....*

A 蓳angaren Muzaffar kuwa tunda suka dawo daga duba Baba Alhaji ayyuka suka masa yawa, wani case ne mai sar茩a茩iya yake gudanarwa a Kotu wanda yake da matu茩ar saka masa zafin kai. Hakan ne yasa ya tattara gaba 蓷aya hankalinsa don ganin ya kamo bakin zaren sar茩a茩iyar dake damfare a cikin case 蓷in. Wannan ne dalilin ne ya hana shi komawa Matazu domin duba jikin Amaturrahaman.

馃崈馃崈馃崈馃崈馃崈馃崈馃崈馃崈

A can Matazu kuwa Amaturrahaman ta zama Boss a gidansu dama umguwarsu gaba 蓷aya, domin kuwa yanzu kowa mugun tsoronta yake ji ba wanda ke shiga gonarta koda wasa. Wanda yayi kuskuren hakan kuwa koda a cikin rashin sani ne ya san abinda zai biyo baya domin bata yafiya ana mata zata yi hukunci.

Wannan jajircewar da tayi ta tsaya wa kanta yasa masu shirin hai茩ewa rayuwarta don ganin yanzu ita ka蓷i ce babu masifaffiyar Yayarta suka maida mugun yawunsu a kanta, domin kuwa kowa ya samu labarin irin ta'asar da karen Labor ke yiwa mutane dasu Labor 蓷in kansu.

Ta kai ta kawo yanzu Amaturrahaman ta saba da karen sosai saboda kyautata masa da take yi, tana bashi umurni yake bi babu gardama don haka rayuwarta take gudanarwa hankalinta kwance ba tare da fargabar suwa zasu kawo mata hari ba.

Taso ta ha蓷u da Gaddafi domin huce haushinta a kansa, sai dai su Labor sun bincika duk wani wuri da ake ganin Gaddafi amma ba'a same shi ba. A 茩arshe dai sun zo mata da labarin cewa Mahaifinsa ya fitar da shi 茩asar waje Karatu. Wani miskilin murmushi ne ta su蓳uce mata lokacin data samu labarin.

Ta tabbatar da manufa Alhaji Tanimu ya tura Gaddafi wata 茩asar amma ba komai duk ma inda ya shiga zai dawo komin da蓷ewa, itama kuma bata manta bashin gaba bare 蓷aukar fansa. Da wannan tunanin ta ture babin Gaddafi kamar yanda ta manta da Doctor Farhan taci gaba da rubuta jarabawarta da ita kawai take so ta kammala domin fara karatunta wanda ta canza 茩uduri daga abinda tayi niyar karantawa a farko saboda wani dalili nata na kanta.

馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅

Kamar yanda Hajiya Ru茩ayya ta tsarawa Salim ya fara bin tsarin kamar yanda take so domin kuwa ya rage yawon da yake yi yanzu yana kwana a gida, sannan kullum da safe yana shiga 蓳angaren Baba Alhaji ya gaishe su shida Hajiya Iya wacce mamaki yasa ta kasa shiru sai da ta magantu. "Ikon Allah! Salim yau kaine a natse haka kazo gaishemu da safiyar Allah?." Ta 茩are maganar da tsananin mamaki don rabonta da taga Salim a cikin natsuwarsa haka har ya kwana a gida da safe yazo gaishe su har ta manta ranar.

"Nine mana Hajiya Iya Allah ne ya kawo min shiriya na gane gaskiya." Salim ya fa蓷a yana wani sunkuyar da kai kamar mutumin kirkin da gaske.

"Masha Allah, ai haka muke son ganinka dama Salim sai kaci gaba kamar yanda ka fara domin rayuwarka tayi kyau." Baba Alhaji dake kishingi蓷e saman shimfi蓷arsa ya fa蓷a.

"In sha Allah Baba zan ci gaba da kasancewa haka ko don in samu soyayyarka nima." Salim ya fa蓷a yana jin zuciyarsa na masa zafi akan yanda Baba Alhajin ya fifita wan can guy 蓷in fiye da kowa a cikin family 蓷in gaba 蓷aya. Murmushi Baba Alhaji yayi saboda ya jima da sanin cewa da yawa daga cikin yaran jikokin nasa suna ganin cewa yafi son Zayyad da fifita shi a cikin su.

Eh 茩warai hakane soyayyar da suke yiwa Zayyad ta da bance a cikin yaran gidan saboda kasancewarsa jika na farko da suka samu, sannan kuma yaron yana da shiga rai tun yana jariri. 茒aya girma kuma nagartattun halayensa su suke 茩ara saka soyayyarsa a zukatan mutane. Amma duk da haka suna 茩o茩arin ganin sun ha蓷a kan ahalinsu da nuna musu su 蓷in abu 蓷aya ne a wurinsu.

Sai dai Hajiya Ru茩ayya a kullum tana rusa wannan ginin da suke yi ta hanyar horar da zuciyar yaranta a kan 茩iyayyar 拼an'uwansu musanman shi Zayyad daya tsonewa mutane da dama ido, a kullum nuna musu take su 蓷in abokan gabarsu ne wa蓷anda suka tare musu samun ci gabansu musamman Zayyad da Allah ya 蓷aukaka a cikinsu ta hanyar bashi arzi茩in daya zo ya zarta na Mahaifinsu da suke tutiya dashi.

Abu na biyu Allah ya yi shi kamilin mutum nutsatstse mai matu茩ar kamewa sannan mai tausayin na 茩asa da shi mai kyauta da karamci, sai dai baya 蓷aukar raini. Wa蓷annan halaye nasa na kyautatawa shike 茩ara janyo masa farin jinin al'umma a duk inda yaje ya mu'amalancesu. Sannan kuma Allah ya masa albarkar hannu ta yanda duk abinda ya kasa da sunan sayarwa sai dai ku蓷insa, yanzu bai da蓷e da bu蓷e Companynsa na sarrafa abinci ba amma a 茩an茩anen lokaci Companyn ya sanu ya kuma kar蓳u ga al'umma saboda ingancin kayan da yake fitarwa da kuma sau茩insa.

Yanzu babu inda ba'a kaiwa kaya daga Companyn a fa蓷in jahohin Nigeria, sannan ba 茩ananan ku蓷a蓷e Companyn ke kawo wa ba, banda ma sauran shares da yake dasu a wasu kamfanonin musamman na Mahaifinsa da ya kusa mamaye wa saboda duk kamfani zaka samu yana da 50 ko 70% na hannu jari. Ga kuma gidan gonarsa dake fitar da manyan ku蓷a蓷e da albarkatun gona da kuma dabbobi. Duka wannan 蓷aukakar da Allah ya masa itace ta tsonewa mutane ido ta haifar masa da tarin ma茩iya duk da irin kyautatawar da yake yiwa kowa dai-dai gwargwado duk da ma shi aikinsa yafi bawa mahimmanci baya zama ya sadaukar da lokacinsa da lafiyarsa da basirarsa wurin bawa 茩asarsa kariya, dukiyar tasa ma wasu ya 蓷ora suke kula masa da ita.

Wasu daga ciki suna hannu 蓷an'uwansa wasu kuma Mahaifinsa ne ke kulawa dasu, yayinda wasun kuma aka 蓷ora amintattu mutane suke gudanarwa.

Ajiyar zuciya Baba Alhaji ya sauke lokacin daya gama tunaninsa yayi murmushi ya dubi Salim yace "Ni dama ban ta蓳a 茩inka ba Salim kai 蓷in jikana ne ina jin ka a zuciyata tamkar yanda nake jin kowa daga cikin Jikokina. Abinda nake so ka fahimta shine ba'a ta蓳a 茩in mutum sai dai a 茩yamaci halinsa, nima halayenka mara kyau su nake 茩yamata kuma ina maka addu'a kullum akan Allah ya shirye ka ka gane gaskiya, Alhamdulillah kuma ka gane yanzu komai ya wuce." Ya 茩are maganar cike da tausasawa a gare shi, sai dai hakan ko ka蓷an bai yi tasiri ba a zuciyar Salim domin 蓷aukar hakan yake a matsayin da蓷in baki Baba Alhajin ke masa saboda ya riga yayi nisa a wannan tunanin da kuma turbar da Mahaifiyarsa ta 蓷ora shi a kai. A zahiri kuwa murmushi yayi ya masa godiya ya mi茩e ya fice yayinda Hajiya Iya ke binsa da kallon mamaki don ita dai ganin abin take yi kamar a mafarki.

"Anya yaron nan shine kuwa?." Ta fa蓷a still dai tana mamakin abin, domin abin ayi mamakin ne.

"Shine mana, fatana dai shine Allah yasa da gaske yake ya gane gaskiyar, sannan ina fatan Allah ya ha蓷a kawunansu ya ka蓷e fitina. Zanyi farin ciki idan naga kan iyalina a ha蓷e sun zama tsintsiya ma蓷aurinki 蓷aya, zan kasance a cikin farin ciki koda ace bana raye a wannan duniyar wannan shine fatana da burina a duniya!". Ya 茩are maganar rauni na cika zuciyarsa saboda ganin duk yanda yaso hakan bai samu ba, duk da dai ya samu nasara ta farko ta hanyar ha蓷e kaf zuri'arsa suke rayuwa a cikin gida 蓷aya ba tare da sun rarrabu ba.

"In sha Allah burinka zai cika Alhaji." Hajiya Iya ta fa蓷a cikin son kwantar masa da hankali saboda jikin nasa har yanzu ba wai yayi 茩alau bane, Alhamdulillah dai yana samun sau茩i.

Salim kuwa yana fita tsaki ya saka ya nufi 蓳angaren mahaifinsa dake cikin gininsu, shima gaisuwar yaje ya masa tamkar yanda yayi wa su Baba Alhaji. A 蓳angarensa ma yaji da蓷in ganin Salim 蓷in a natse don haka yayi masa nasiha sosai kafin ya sallame shi. Wurin Mahaifiyarsa ya koma wacce ke jiransa don sanin yanda abubuwa suka gudana, da wannan damar ta zaman gida da Salim keyi tayi amfani ta ri茩a bashi ruwan rubutun da Malam na kan buzu ya bada a bashi domin ya daina abinda yake ita kuma ta mallake shi ya zamana cewar duk abinda ta saka shi shi zai yi.

Ana samun ci gaba tunda yanzu baya fita yawon banzan, sai dai abinda bata sani ba shine in ya shige 蓷akinsa ya kulle ba abinda baya sha na kayan mayensa. Sai dai ya rage sosai kuma cikin tsari yake shan domin sai da dare idan zai kwanta. Masu aikin 蓳angarenta kuwa da take tura masa domin yi masa hidima yanzu dasu yake mua'amalarsa ba tare da saninta ba.

___________&

Ba 茩aramin rikici aka kwasa tsakanin Hajiya Sha'awanatu da Dady ba lokacin daya sanar da ita taci gaba da shiri nan da sati 蓷aya za'a 蓷aura auren Anisa. Sosai ta saka masa daru akan bata amince ba saboda Anisa bata so, wanketa tas yayi ya kuma mata rantsuwar zai iya sakinta idan ta kawo masa wargi a kan maganar auren nan.

Dole taja bakinta tayi shiru saboda bai ta蓳a furta mata haka ba tunda suka yi aure tsawon shekara ashirin da wani abu, sannan kuma gaskiya na 茩aramin son Mijinta take yi ba, bata bu茩atar abinda zai taba igiyar aurenta don haka tabi shawarar aminiyarta da tace ta lalla蓳a Anisa ayi auren daga baya zasu san yanda suka yi suka kashe auren ba tare da an zarge su ba.

Duk da bata so hakan ba amma haka ta ha茩ura ta lalla蓳a Anisar wacce tayi ta botsarewa akan bata so sai da tace zata barta da Dadyn nasu san nan ta ha茩ura zuciyarta tamkar zata fashe.......

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol